Advertisements
Chapter 27 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   27 / 92

78K to 81K   out of 275.8K words

wa uwar
shi kudin ta,saura ya samu guri ya boye.
Kamshi turare taji a jikin shi tace kai kai kai ina,kasamu wanan turaren haka mai
kamshi.
Nan ya shafto karya yana fadi wani yaro ya ysunci kwallaban turare shine muka dan
sawa jikin mu.
Tace yaci abinci yace sai ya dawo ba yanzu don haka tace yai niya yafita koshi da
kyat tasamu ya fita don ya kwata jikin shi yana mai ciwo ga kuna kayan sanyin da ya
cika cikin shi dashi fam.
Amma ita da yake son kudi ya rufe mata idon ta sam bata hango illa ga rashin cin
abincin da yaron baiyi a kwanakin nan ba.
Yaro idan ya,fara talla ko yarinya komai zama kamilin yaro kwana kadan da,fara
tallan yaro idon shi zai bushe.
Idan sau daya kakewa yaro tsawa ya bar abu yanzu sai kayi uku masu karfi kfin ya
bat abinda ka hanne shi.
Yaro idan ya fara talla baijin naiyi ko kunya fada wa babba magana yadda yaso
sai dai kai babba kaji kunya.
Yanzu duk irin haka ke faruwa,da,Aliyu amma uwar bata da fahinta ita bukatar ta
kawai ya kawo mata kudi a rayuwan ta.
Mahaifin yaron ya ga matukar canji akan dan shi sai dai ya danganta halin yaron
sai ya dangata shi da girma yasa shi canzawa a baki daya.
Tun wanan ranan kullun sai Aliyu ya,tafi gurin sisko saboda dan kudin da yake
samu gare shi.
Gashi uwar ba ido take sakawa akan yaron ba ita gurinta kawai shine, taga ya kawo
mata kudin da yawa.

****** ********* ******
Tun wanan ranan da suka hadu suka zama abokai tsakanin su da Nafisa.
Ance abokin barawo barawo ne don Nafisa bata san ya akayi tafara shan abubuwan
dasu Raiha ke shaba saidai kawai ta tsunci kanta a cikin shaye shaye dumu dumu da
ita.
Ga uwar ta,Umma a kullun zancen ta sai zagin sadauki da yiwa uwarshi dariya bata
san na dakin ta yafi illa,ba ma.
Sai dai tana kokarin ganin kowa a gidan su kada ya,san zancen har a,kyamce ta ita
da uwarta kamar yadda akewa Maji da diyan ta gaba daya da abin bai shafa bama.
Yanzun takai har fitan da,su Raiha keyi zuwa wani gari tare da Nafisa suke yin
shi, don sai ta,shirya karya cewa za su wani gurin yan uwan su ko gidan kawarta sai
kawai su fita garin suyi kwanakin da zasuyi ba ta gidan.
Gashi ir8n na fitsara ba komai bane a gurin ta don wayewan ta tana ganin yakai
haka ita.

Al,amarin ciwon maji yasa Alhaji baro aikin shi ya dawo gida don ganin yadda
jikin naya yake saboda hankslin shi yaki kwantawa da jin da yayi an bata gado.
Yana isowa ya wuce asibiti direct Don ganin jikin nata, ya samu Tana zaune ina
tsaye agaban ta ina we, mata lemun tana Dan sha a hankali.
Baba yashigo dakin da,sallaman shi Nan muka shiga gaishe shi dadawo daga tafiyan
da yayi.
Idanuwan shi kyar akan ruwan da ke kafe daga gefen mama ya Kara juyo kallon shi a
gareta Yana mata sannu da jiki.
Ganin shi yasa mu kokarin Fara barin dakin don mu kauce masu daga dakin.
Yake cewa ku tsaya abinku Fatima ance kece Kika kawo ta asibitin har aka baku
gado to Yaya likitan yace yanzu .
Nace cikin dukar dakai likitan yaiwa Yaya sadauki bayani dazun da safe Kuna ya
Kara rubuto wasu maganin da za,a saye.
Yace zasu kwantar da it's na sati biyu anan don ta samu Hutu sosai a jikin ta
tare da treatment din ta.
Ok hakan na dakyau ai said dai ku dinga barinta tana samun barci sosai zaifi Kara
mata lafiya .
Bai dade dashigowa ba sai ga sadauki ya shigo dakin ya sayo maganin da likitan ya
rubuta mai yana fadin da kyait muka samu maganin babu shi nan cikin asibiti.
Yaiwa mahaifin shi sannu da dawowa tare da tambayan shi Yaya aiki a can inda ya
fito.
Muna waje zaune saiga Yaya Imiran yazo don sunyi waya da baba yace sure hadu a
Nan asibiti dashi.
Zan iya cewa tunda mukazo asibiti bai shigo gurin Maji ba don ya Dubai lafiyan ta
Amma salmanu Dan wurin mama Asiya zuwan shi biyu Kuma harda fruit yakawo Muna.
Ya na isowa ya gan mu, zaune mu uku nan Suka fara gai da shi cikin ladabi, Banda
ni dake zaune ina mashi wani kallon raini kawai.
Tambaya yayi ko baba Yana ciki suka bashi da amsa da eh Yana Nan cikin dakin.
Yana kokarin shigewa naja wani tsuki da karfi Yana ji sai dai bai juyo ba ya
shige ciki kawai abinshi.
Muryan anty maryam ce naji tana cewa ke may ya hana kiki gaida yayan mu Bintu?
Nace bai isa na gaida shi bane kila don da nagaida shi inda mutumin kirki ne.
Fitowan shi yasa su yin shiru suna mashi sai anjima, bintu tace haka dai za,a
kare .
Wai ke Bintu harda yaya Imiran da ba,ruwan shi da kowa, amma sai k8n tsula mashi
halinki na tsiya?
Maryam tace a,a anty Amira tunda kikaga haka akwai dai koni ranan mun dawo school
bakiji, abinda yake fadawa Bintu bane,
Nace aini Anty Amira idan mutum bai shiga gonata ba ni bani shiga nashi don haka
kibarni kawai dashi dan iska kawai.
Haba Bintu haka,kawai ki dinga zagan muna dan uwa a gaban mu haka gaskiya zamu
saka wando kafa guda dake a gidan nan.
Nace maida yukanki kube anty Amira ai ni ba haka nake ba da ace da yai min ban
dauki mataki ba,ai da ko yanzu bata kare muna,ba,wallahi.
Ke dai yanzu kin zama disturb wallah kamar ba Bintu Maji ba wallahi nace lokaci
ne idan baka baki sai a shaka a,banza.
Wai don Allah may ya,hadaki da yaya Imirana kodai laifin maganan ranan ne har
yanzu kike kule dashi.
Nace a,a ai anan cikin asibitin muka yi case din mu dashi ban ma,san yaya sadauki
na gurin ba,sai da naji ya daka mai tsawa yace mai ya sake min hannu na.
Tace ashe kin kuru, ne harda yaya,sadauki a gurin lalaima Bintu kinyi nisa sosai
wallahi.
Nace marin shi fa kawai nayi saudaya shine wani abu wallahi har yanzu a kule nake
dashi a raina .
Da sauri sukace mari da,gaske mari Bintu nace don ma banda karfi aida abinda zan
mai sai yafi mari wallahi.
Yadda yake dan iska haka yake ganin kowa dan iskane shine harda daukan kazamin
hannun shi wai zai shafa min jiki niko nakai mai mari sosai Allah yaban sa,a na
samay shi da kyau.
Da sauri Amira tace don Allah da gaske marin shi kikayi nace wallahi Allah kuwa
nan na,basu labarin abinda ya faru a tsakanin mu dashi har takai na mare shi.
Maryam tace dan iskan mutum kawai mara mutunci yau da wani ne da uwar shi ta samu
abin kasawa a,ture tana baradawa a gari.
"Dan kowa ,dan banza ne, nata ne diyan kwarai a duniya, nace wallahi ni ko gobe
yai min maganan iskanci sai na,dauki mataki ko a gaban waye.
Maryam tace ya ganki haka ya zaci irin yan matan shi da ya saba yaudara ne.
Nace shi dai jarabar shi ce ta motsa kawai har idon shi ya rufe, irin yan iskan
ga ai su kowa bi suke basu da zabi mace da mai aure da mara aure in sun, samu, duk
so sukeyi.
Nace Allah ya kyauta Allah dai ya,shirye mu, don wanan shima ba karamin masifa
bane wallahi.
Don ai zina ya mafi komai muni a rayuwan mutum da ban kyama, ga al,umma.
Nifa ban yarda da maza don a mayaudara nake daukan su baki daya inji Amira nace
ai ba duka maza bane basu da hali don ko matan ma,akwai marasa hali a cikin su
sosai don sai kiga diya,mace yanzun tana abinda wani da namijin ma ba,zaiyi ba.
Har Baba yafito shi da su sadauki suka rakashi nan muka mike a inda muke zaune
muna mashi a huta lafiya.
Sadauki dake tsaye ya bude motan ya dago kai ya kalli gurin da mu ke tsaye, yai
muna inkiya da dakin da,maji ke ciki .
Nan take, na juya da sauri na nufi dakin suko sauran basu gane may yake nufi ba
don haka suka tsaya jiran baba dake waya ya gama.
Ina shiga daki nasamu, maji ta farka daga barcin da ya dauke ta, na karasa gurin,
da take ina mata ya jikin
Tace min ina yayan ku Fatima ya tafine ko yana cikin asibitin nace to na dai
barsu waje da Baba zai tafi gida .
Kamar kira sai gashi ya turo kofan ganina tsaye a,bayan mama ina gyara mata filo
yasa shi karasowa gurin da sauri yana cewa Maji kin falka,ashe ya jikin yanzu da
sauki dai yanzu ko?
Likita ya shigo ganin ta a,zaune yake tambayan ta mama ya jikin naki da sauki ko
Ya dan dubata ya dago yana cewa abata abinci taci zuwa shidda na yamma za,azo ai
mata allura.
Sadauki yace wani iri abinci ya kamata a,bata yanzu wanda zaifi mata, amfani.
Likita ya dago kai yana fadin tea mai kauri da fruit sai kuma anta da koda mai
kyau ta dinga ci.
Sai kuma likitan yai shiru tare da kurama sadauki ido yace you look like U,F
footballer yace cikin dakewa yes iam d one,
Nan suka fara shocking din hannun su suna gaisawa mutun yana faman dada wasan
yaya,sadauki.
Likita baifi yan mintina da fita ba sai ga,wasu group din likitoci sun shigo
lokacin yana gyarawa mahaifiyar shi kwanciya suke fadin lalai kuwa shine shine.
Nan suka cika dakin da surutu wa yannan group su shigo su fita wasu su shigo har
abin ya fara isa ta don sun hana mama samun hutu.
Saida dare Baba ya,dawo tare da su Umma da mama Asiya ya,taso su gaba bayan ya
gama masu fitina rashin zuwa duba yar uwar su dake kwance asibiti.
Inda yace na,tabbatar wallahi da dayan kune a,asibiti da maijidda sai inda karfin
ta ya kare.
Nan dai yai masu tas yasa fito su zo tare su duba lafiyan ta .
Sun kai wani lokaci sai, suka mike zuwa gida, dama duk a matse suke kamar dole
suka zo gaida ita.
Suna fita Mama tana kwance na mike na gyara ko ina tas a dakin tare da,kawar
da,wasu kaya dake waje.
Sai ga,Sadauki ya,shigo dakin ya,aje ledan da ya,shigo dasu gurin flask ya nufa
ya tsiyaya ruwan zafi tare da hada tea mai kauri sosai.
Yazo gabana ina zaune yake cewa gashi na,dube shi nace tasha tea ai kafin ta
kwanta.
Fuskan shi a daure yake cewa ke zaki sha ba Maji ba, ya kara miko min yace karbi
mana kisha idan kin gama ga nama a leda kici tunda wa yan nan sun tafi gida don
lalaci.
Zanyi magana yace min shishsh bana son magana shaye shi kawai
Ban san ya akayi na fara kurban shayin ba saida naji na dan kai cup a bakina karo
na farko.
Yace yaushe, likitan yace za,a kara mata allura ne wanda ya saura ai mata.
Nace ni ban ma tsaya tambayan shi ba,don ya ishi mutane da labarin kwallo kawai
ya fita.
Ke kuma shine baki so zancen kwallo ko don kina jin haushi da hassada ko?
A kwallo ne mutum zaiyi bakin ciki ko kan may aiki wahala.
Kallona yake galala,har na, mike tsaye tare da dauko baredin na zauna a makure
nasha ya dan kai kurbi hudu batare da bread ba.
Na aje tare da son na,rufe sauran sai yake cewa to ki jawo kazan kici don cikin
ki ya kara,walwalewa da kyau.
Nace wanan ma,Alhamdullahi don nakoshi tace shiyasa bakya kiba har yanzu kamar a
kallaki saboda baki son cin abinci.
Ya mike yaje bakin gadon mama ya dan tsaya can yake cewa ina ga shidda na safe
zasuyi mata allura don gaka idan basu zo ba sai ki bisu.
Nace mashi tau ya kai kofa yake cewa idan ta farka kice mata na tafi sai da safe
in Allah ya kaimu.
Yana fita naja kofan na rufe nan na, dako ledan naman na fara ci tare da karasa
shan cup din tea dina.
Sai da nai nak na ture dama duk iya,shegena,a gaban mutane ne ban ita cin abinci
saboda kawaicin da nakeyi kawai.
Zuwa dare maji ta,farka nan na mike ina mata sannu tare da tambayanta ko tana son
cin wani abu.
Tace a,a tana tambayana su Amira nace yau a gida zasu kwana don likita yace mu
dan rage yawa don ki samu hutu.
Tace hmmm kai Fatima boye su kuma,zakiyi bayan nasan halin abina sun dai tafi
gida don su samu barci yau ko?
Banyi magana ba sai hira take min mai kama da nasiha tana ta bani labaran tun
kafin nazo gidan su irin yadda su ke kwasa da kishiyoyin ta.
Nace mama Allah ya kyauta amma mutane kamar ba,a mutuwa sai a manta da ranan
haduwa da Allah.
Sai kusan asuba,muka,samu barci sosai Allah ya taimaka na,farka da akazo yiwa
mama Alluran karshe.
Ban koma barci ba na dauro alwala nahau sallaya na fara sallah har akai sallah
asuba ina gurin a zaune abina.
Zaune nake inajan tasbi amma kuma zuciyata tana tunane akan hiran mu da maji
daren jiya da irin wahalan da tasha a gidan miji amma tazauna tai hakkuri don
yaranta.
Gashi kuma yau an wayi gari saboda dan tilon danta guda ciwo nason shigan ta.
Har na,soma gyangyadi a gurin sai jin muryan mutum nayi a akaina yana fadin ki
kwanta mana ki dan huta hakana.
Yaya sadauki ne yana saye da kayan exercise na maza dogon wando da rigan shi mai
dogon hannu dark blue.
Yanufi gadon mama yana duban ta sai ya juyo inda nake ina kallon su yake cewa,
tasha maganin an kuma yi mata alluran kuwa?
Nace eh sunzo sunyi mata sun bata magani shiyasa mata ke barci haka don maganin
barci yake sa mutum sosai.
Ya ce ba tare da ya juya ba ina ga daga wanan allura ya kare sai dai magani
kawai.
Jin nai shiru yasa shi juyawa gyangyadi nake nai barci a gurin hakan ya nuna mai
ina son hutu nima.
Kujera yaja zuwa gaban gadon mama yana mai kura mata ido cikin jin tausayin ta ta
ramay tai baki duk ta canza kaman ta.
Yana nan zaune har wata nurse tashigo dakin take tayar da,maji zasu bata maganin
safe. Shine dalilin farkawan mu ni da mama din
Sai da nurse din tagama ta tafine maji take tambayan dan nata sai yanzu yazo ne.
Yai murmushi yace maji na,tsaye nazo maki da,budurwana ta gaida ke sai na samu
bata shirya ba .
Murmushi naji uwar tayi tana cewa kai kama isa kaida akaiwa mata tun kana karami
kasan dai Alhaji ba zai canza maganan shi ba.
Sai yace wai wa kike nufi Maji Rahaman Baba Sani ko wa wai?
Tace itace mana ba itace matar taka ba da iyayyenku suka yima ko kw canza watace.
Yace maji ni may zanyi da Rahama yanzu ga mata yan gayu ko ina suna kawo min hari
sai wace na zaba.
Dariya uwar tayi tace adaiyi sanni kada ruwan ido yai ma mutum yawa amma dai
kasan zancen Rahama ba,tashi yayi ba har yanzu.
Wai maji da gaske kuke zancen Rahama har yanzu a da dawasa ne bayan ko wani
shekara sai na hada toshin sallah ankai mata.
Kwanaki ma naji Alhaji na zancen yakamata wai kuyi aure ku uku tundai kai da kudi
yake shigowa yanzu ko yaushe.
Yace ni gaskiya da za a bani zabi gaskiya Rahama batai min ba tayi min local da
yawa gaskiya.
Murmushi uwar tayi tace kai har kana da zabi bayan ka bata tsallen ka ko?
Kuma Rahama yar uwarka ce ta jini zata zauna dakai tayi hakkuri ba,ajiku ba akan
baren da kake son daukowa kan ka.
Nace ko kuma waye Rahama cikin yan uwasu oho koma wacece idan lokaci yayi ai mu
ganta.
Banji ya kara magana ba sai ma motsin da yaji nayi yasa shi tuna cewa ina dakin
lokacin nan ya dakai kallon shi gareni, nikan na kawar da kaina gefe ina cewa
kaidai ka,sani.
Na kara hada kaina na da bango ina mai lumshe idanuwana ni adole ga mai jin
barci.
A ranshi yace muna fuka kawai kamar bata jin may ake fadi wai tana gyangyadi.
Idona a rufe amma tunanen wacece Rahama ya hanani sukuni wanda ban san dalilin
yin hakan ba gareni.
Tun ina barcin karya har na gaskiyan yazo ya kamani ban farka ba sai kusan karfe
daya da wani abuna rana.
Duk ko da hayaniyar masu shigo gaida mama a lokacin nikan sai faman barcina
nakeyi hankali kwance.
Dana farka sai naga Baba ne zaune a dakin yana ba mama abinci da hannun shi.
Naso na sulale na fita amma sai hakan baiyi ba don suna jin motsina baba ya juyo
yana cewa a,a Fatima kin tashi sannu kinji.
Jeki wanke fuska kizo ki karya kinji sannu da kokari jiya mamanki tace ta hanaki
barci ko?
Nai murmushi nace Baba ina kwana ya gajiyan tafiya yace Fatima aikece dagajiya ke
mai jinya.
Bandakin dake dakin na shiga na,wanke fuskana tare da dauro alwala don lokacin
sallah ya kusa.
Ina fitowa Baba yace oya maza zoki debi abinci ki zauna kici don mamaki tace baki
son cin abinci.
Inbanda abinki Fatima ana jinya ba acin abinci ai sai ciwo ya kamaki ke ma.
Na dai daure na dan dibi kadan a plate Baba yace wanan abin fa kamar za,aba yaro
dan goye kin dai ga ko ita mai jinyan taci abinci yau sosai.
Alaman sauki ya samu ke nan don haka kara kici kema kada ciwo yakama,min yar
amana na.
Sallama akayi dakin gwagona ce tashigo tare da sadauki daya dauko ta daga gida
don bata san guri ba.
Nan suka fara gaisuwa da Alhaji tana tambayan shi ya

27 / 92