Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
ita zata wuce duk yadda
maji tayi ta tsaya bata yarda ta tsaya idan yana nan part din.
Gwago tana son zuwa kauye don uzuri na tafiya ya taso mata zuwa gida shine taga
bazata iya barin Bintu gida ita kadai ba.
Don haka tazo da kanta gurin maji tana neman arzikin Bintu ta zauna a gurin su
har ta dawa daga gida.
Don babu damar ta tafu da ita a na cikin makaranta a lokacin ana karatu ne ba
hutu akeyi ba.
Da yar ledae kayan ta tazo gidan aka sauketa daki daya dasu Amira da maryam.
Tunda gwago ta, tafi a takure Bintu take gidan su Amira din koda kowa yana falo
Bintu tana daki ita bata fita zuwa ko ina ko kallo bata fitowa tayi a falon kamar
yadda kowa keyi.
Yau da ya dawo daga wasan ball ya samu maji a kwance bata jin dadi don haka
tana ganin shi tasan cewa abinci ne ya kawo shi don haka daga inda take kwance ta
kwalawa Bintu kira tazo.
Mamakin jin tana kiran wani bakon suna daga ciki Umar keyi sai dai halin shi bai
barin ya tambaya ko bakuwa,ce uwar tayi mai suna hakan.
Bintu tafuto tana saye da dan farin hijjab din ta a jiki don dabiar tane bata
zama jiki ba hijjab ko kadan.
Mama gani inji Bintu duk da jin muryan ta da jin muryan ta da yayi ta shigo da
sallama bai sa ya dago kan shi ba daga abinda yake a,wayan shi ba.
Bintu don Allah kawo wa yayan ku abincin shi kin ji,
Tau mama tace tare da juyawa zuwa dauko mai abincin dan lokaci kadan sai gata da
ture ta ta dauko kayan abincin har ruwa duk a cikin ture din.
Kujeran da yake zaune akai hankalin shi a,waya ta nufa, ya dora kafan shi daya
saman daya.
Ya mayar da bayan shi a makarin kujeran da yake sama zaune yana ta faman la
tsan wayan shi.
Bintu ta karaso gaban shi ta dire mai turen abincin a gaban shi ta juya da,sauri
zata bar falon,
Muryan shi taji kamar mai jin barci bayan ta juya yana cewa,
"Ke, yace da dan karfi abinda yasa Bintu ta,tsaya guri guda cak ke nan bata daga
kafa ba kuma bata juyo ba.
Kizo ki zuba,mana zaki ajewa mutum abinci hakana kamar wata yar kauye can
dalllah,
Da hanzari Bintu ta juya don bin Umurnin shi ta duka tare da jawo plate tafara
zubawa a plate din dake cikin ture din.
Sai da Bintu ta shake plate din fam sannan take cewa nazuba tana shirin mikewa.
Ke Uban wa zai ci wanan abinci haka kamar jaki ko an fada maki cewa kowa irin ki
dan kauye ne.
Kai Babana inji Maji wanan wani irin hali ne maka yarinya ta,dafa,ta kawo maka
kuma cine kawai naka har kake kokarin kiran ta,da,sunan dabba.
Ke wuce ki shige abinki kinji Bintu kar ki tsaya,sauraren shi da zancen banzan
shi.
Da hanzari Bintu ta juya zuwa cikin uwae dakin mama inda dakin su yake da,su
Amira gaban ta yana faduwa irin yadda yai magana ya bata tsoro sosai.
Tun ranan bata son taji koda muryan shi don tsoro yake ba bintu din idan ta gan
shi.
Da wani dare yashigo gidan sai wani lumshe idanuwan shi yake anyisa,a Bintu ma
tana falon do Amira ta takura mata tafito suyi kallon wani hausa film sabon
fitowa.
Bayan ya,samu guri ya zau a suka,shiga gaishe shi daya bayan day suna mashi
sannu da,zuwa,
Ya zauna tare da mayar da hankali shi ga mahaifiyar su da ke zauns daga gefe
saman salaya tana jan casbi ta a hannkali suka gaisa dashi daga gurin da take zaune
,
Sai dan wa lokaci ya dan nisa yanacewa Maji abinda yasa ta,dawo da hankalinya ke
nan gurin dan nata don tasan magana yake son yi da ita.
Yace dama nazo maki da wani magana ne akan al,amarn da ya,shafe ni.
May kuma ya faru ne babana Maji dama ina son fada maki ne na,samu wani contarac
akan zancdn ball din da nake yi wasu club suna son dauka na zuwa yi masu wasa.
Cikin sauri Maji tace ban amince ba kaji na,fada maka kada ka,fara ka,tayar
da,zancen nan har wani yaji ko mahaufin ku a gidan sai nai matukar bata maka rai
wallahi kaji na fada maka gaskiya.
Kallon mamaki yakewa mahaifiyar nashi don tabashi mamaki don shi a,zaton shi yai
tsanmanin zatai farin ciki dajin wannan labarin tunda kullun gori take mashi akan
wasan ball din da zaman banza bai zuwa shago kamar sauran yan uwan shi na, nagidan
da,suke taya mahaifin su sana,a.
Shiru yayi tare da,dukar da kan shi guri guda bai daga ba har tsawon wani
lokaci .
Tsam Bintu ta mike zuwa ciki don tsoro takeji naganin fushin wanan jarumin kada
ya hada fushin shi dasu.
Maji amma,wanan abin fa alheri ne sosai idan har anyi nasara akai don Allah ki
bari naje.
Bazaka banace na fada maka,gaskiyan magana ta ke nan har cikin raina .
Nan ma da kake a gaban mu yaya muka kare dakai balle can inda babu kowa naka.
Shiru yayi sai ya mike zuwa fita Maji tace abinci fa yace makoshi kawai yasa kai
yafita daga dakin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,
Ya na fita daga waje ya,ci karo da,bucket din roban da mama ta,aje a tsakar gida
shuri daya yayiwa bucket din din yai sama ya maku da,bango.
Ji kake pappp karan fashewan bucket din da ya maku da bangon dakin mama Asiya ji
kake tayau,
Da sauri mama Asiya tafito daga dakin ta,tana ganin irin ta,asan da Umar yai
mata tafara salati tana tafa hannayen ta cikin salalami da mamaki.
Maijjidda fito fito kiga,ta,asan da,danki yai min, dan iskan yaro kawai mara
mutunci, kawai bucket yana aje may ya tare maka don kawai kana haushina zakai min
wanan aika aikan haka,
Bari ubanka ya,dawo yau gidan nan akwai ta don sai an biyani kudin bucket dina a
gidan nan.
Haka mama Asiya taita faman masifa inda take shiga ba nan take fita ba sai yan
kore da suka fito kara zugata tana hawa.
Maji dai tana daki bakin ciki da takaici ya hana ta fita waje a lokacin.
Sai dai duk abinda suke fadi a kunnuwan ta yake irin yadda suke kara aibanta mata
yaro duk da ran ta ya baci amma bata da bakin magana dan kuka maija wa uwar shi
jifa.
Sadauki ya jawo mata wani sabon masifa don tasan yadda mama Asiya ta fadi sai an
biya ta haka zancen yake sai an biyata din.
Don haka ta mike tsam zuwa kuryan dakin kwanan ta ta dauko kudi, a take ta dauko
kudi taba Amira wai ta sayo mata bucket.
Haba maji don kawai tace sai anbiya ta basai taje gurin shi shida ya fasa mata
taje gurin shi mana in ta isa, ya biyata abinta.
Maji tace,ban son rashin kunya Amira ki tashi ki tafi inda na aike ki kawai.
Bintu tace mama kawo naje yanzu zan dawo sai maji tace a,a Bintu yi zaman ki bari
dai Amira din ta tafi.
Mama barshi kawai ni na tafi anty Amira ta huta kawai ta duka ta karbi kudin daga
hannun Maji ta saka silifas din ta dake ta kofa tafita daga dakin.
Inda Amira ke zaune Maji ta dan kalla tace kin ga ikon Allah karamar yarinya
haka da kaifin hankali,
Don tafahinci baki bukatan zuwa yasa ta karbi kudin ita ta tafi, da sauri Amira
ta daga kai ta kalli maji tace bance banzuwa ba maji ,
Allah dai ya kyauta Amira ina tsoron kada ke ma kizo ki zama min irin dan uwan ki
nan gaba wallahi.
Haba maji don Allah kibar fadin haka mana idan ranki ya baci kiyi hakkuri don
Allah ta fadi a,dan marairaice,
Allah ya kyauta ta furta a fili a cikin zuciyar ta kuma fadi take ya Allah ka
shirya min yaran nan shiri irin na addinin musulunci.
Wannan adduan ya zama kamar waka a bakin Maji don duk abinda take adduan ta akan
zurian ta dana sauran yan uwa musulmai yake.
Exactly kalar roban da ya fasawa mama Asiya Bintu ta sayo don ma saida tai yawo
kusan shago uku ta samu roban.
Gap da zata shiga gidan ne a daidai side din samarin gidan dake daga wajen
haraban gidan ta hango shi zaune yai zaman kamar tsuguni saman dan dakalin dake
gurin.
Kamar ance ya dago kai ya hango bakuwar yarinyar da yake yawan gani dakin
mahaifiyar shi yanzu tafe da buket din roba kalar dayai shuri dashi a cikin gida
kuma tun kan ya karasa fita daga gidan yaji bambamin mama Asiya akan wai ya fasa
mata buket wanda ba ma fashewa yayi ba.
Daga hannun buket din ne ya balle hannu daya na bucket din ya balle daga jikin
roban.
Sauri take ta shige gidan sai taji muryan shi kamar daga sama yace.
"Ke,
Cak taja ta tsaya don balain tsoron shi take ji don ko yaushe fuskan shi babu
rahama cikin shi, don har takanyi mamakin ace wai wanan mai siffan bugai yafito
daga mace saliha kamar Maji.
Zo nan yace mata inda ta dan taka a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki, har
ta karasa gurin shi.
Waya aike ki sayan wanan robar ya tambaya cikin daga muryan shi.
Cikin dan in,in,niya take cewa, mamace tace na,sayo mata,
A gatsale ya tambayeta, waye mama ? Don ya tantance ko wa ya aike ta sayen robar.
Bintu tace mama ta dakin ku, kina nufin Maji ke nan, tace eh cikin daga kanta.
Miko min bucket din kice mata na karba ya,fadin cikin dakewan fuska mika mashi
tayi ta juya simi simi ta shige cikin gidan yabi bayan ta da harara yana fadin
munafuka kawai.
Maji tana zaune Bintu tashigo gidan tana dan kiukiu da idanuwar ta alamar damuwa
a fuskan ta.
A,a Bintu ba,a samu roban bane ko kudin shine baikai ba?
Kafi Bintu tai magana Amira tace a,a ya za,ace ba,a samu irin roban ba kodai baki
san inda ake sayarwa bane ?
Harara Maji ta maka wa Amira da sauri taja bakin ta tai shiru tare da kawar da
kan ta don tasan har yanzu Maji a kufule take da ita ke nan.
Bintu tace na,sayo amma ya karbi bucket din a gurina.
Shi wa ya karba ?
Shi wanan yayan namu da ya,fasa roban yace na bashi roban dana sayo din .
Sadauki ke nan ko ?
Eh shi yace na bashi nace ya karba.
Mikewa Maji tayi ta saka hijjab din ta ta nufi hanyan waje fuuu a cikin fushi da
hasala.
Ya na kulle kofan dakin shi zai fita ne Maji ta karaso gurin tana fadin miko min
roban mara mutunci kawai.
Wani kallo ya waigo yaiwa uwar sai kuma ya,dukar da kan shi kasa ya dan fara
kokarin bude kofar dakin shi daya rufe.
Yafito da bucket din yana cewa wallahi matar nan yar rainin wayo ne naso ne ki
barni da ita, tun da tace yau akwai balai akan bucket din roba a gidan nan.
Fisgan roban Maji tayi daga hannun shi ta watsa mai harara tana cewa.
Duk abinda tace waja min ida baka taba kayan ta ba ai bazatai wanan fitinan ba.
Ksi tayi sadauki tunda na fahinci kwanciyar hankalina ne baka bukatan gani a
duniya.
Maji ni fa ba haka nake ba ki barni kawai na wuce gurin kwallo na in huta da
wanan munafukan matan.
Anki a barka anan ma da kake yaya aka kare dakai balle ka sa kafa ka tafi wata
duniyan da babu mai kwabon ka a can.
Indai zaka gyara halinka ka gyara don bakai kadai bane yaro a gidan nan da kullun
a ce sadauki dai sadauki.
Ta juya zuwa cikin gida kamar yadda tafito a hasale daga gidan da farko.
Maji bata shiga daki ba,saida takaiwa mama Asiya bucket din dakin ta takuma bata
hakkuri akan ta yi hakkuri da halin sadauki din .
Ba kunya mama Asiya takarbi bucket din tana zuba bakar magana tana cewa wallahi
da ba,a,sayo min kayana ba da yau akwai magana a gidan nan.
Da maji ta shigo lokacin Bintu da su Amira suna zaune a falon ta, Amira ce
tace bai bayar bane maji ?
Kamar yaya bazai bayar ba aiko ya sha giyar wake ne bai fara shi wallahi.
Sai Amira din take cewa to Maji ina shi tsohon bucke din ai naga bai wani fashe
ba fa .
Amira ki fita idona don ni ba,sa,ar ki bace, don naga kina son raina ni.
Shiru Amira tayi tare da kokarin mikewa tabar falon don gudun fadan Maji a kan ta
don yanzu tana sauke mata haushin dan uwan ta a kan ta in batai hankali ba.
Inda Bintu take Maji ta kalla tana cewa Fatima kinci abinci kuwa, cikin sauke
ajiyan zuciya a hankali.
A cikin natsuwa Bintu tace ina jiran su anty Amira ne muci tare dasu.
Haba Bintu kada ki biyewa wa yan nan don su cin abinci a gurin su kamar shan
zuma ne sai sunga dama suke ci.
Tashi kici abinci kada gwagon ki ta dawo ta samu kin ramay kan wa yan nan mara sa
kai.
Haba mama aiko suna da kai adduan ku a gare mu shine takin mu akoda yaushe cikin
murmushi da kwantar da murya Bintu tai maganan ta.
Allah sarki Allah yai maki baiwa da kaifin basira karama dake Bintu amma kin san
abinda ya kamata ko yaushe.
Tashi jeki ki debi abinci kici mai isar ki kin ji diyata Allah ya bar muna ku.
Bintu ta mike a hankali fon bin umurnin maji amma bafon ranta nason cin abincin
ba ta shiga kitchen din su ta dan debo abinci dan kadan a cikin plate tare da ledan
ruwan pure wata.
Maji tabi abincin da kallo tana cewa haba Fatima wanan dan abincin may zai maki
ashe shiyasa baki kiba don baki son cin abinci sosai.
Ko har yanzun kina kewar gwagon ki ne kin ki sake jikin ki da mu.
Murmushi Bintu tayi kawai tare da cewa a kunyace a,a mama ai ban damu ba.
To dayafi maki don ko gwago ta dawo zance tabarki a nan don halaiyar ki ni dai
yana min wallahi saboda yaran nan su dan kara daukan darasi a gurinki.
Don duk irin halaiyar yaran gidan nan shine diba,ar su a rayuwan su basu san
halin rayuwan duniya ba.
Da,sauri Bintu ta dago kai tana kallon Maji sai kuma ta dukar da kanta tana dan
juya abincin dake cikin plate a hankali ba tare da takai a bakin ta ba.
Yadda maji take jin sha,awan Bintu yasa take so da kaunar yarinyar har cikin ran
ta ganin zata takura mata yasa maji ta dan mike tabar falon zuwa waje.
Bintu tana gamawa ta kwashe kayan zuwa inda suke wankewa ta wanke har ma da
wanda tagani saura a gurin duk ta hada ta wanke su.
Daidai zata shigo da kayan, maji ta ganta take cewa Fatima baki hutawa duk aiki
bai baki wahala ke.
Murmushi kawai tayi ta,shige da kayan ciki ta aje tana fitowa ta shiga wanka don
magariba ya kawo jiki a lokacin.
Tsab Bintu tafito cikin wasu kayan da aka bata na Amira an gyara mata sun mata
matukar kyau kamar don ta aka dinka kayan dama.
Maji dake zaune ta idar da sallah tana jan tasbaha takalle ta lokacin duk suna
falo da yaran ta a zaune.
Duk suka bita da kallo a lokaci guda ta,zo har inda Maji take zaune tana cewa
ina wuni mama.
Kai Maji dake lazumi ta kada mata tare da daga mata hannu Bintu ta mike zuwa
bakin dayan kujeran ta zauna a kasa.
Maryam ta kalleta tana cewa may yasa ke baki son hawa saman kujera ne Bintu bata
ce komai ba sai dan halinta watau murmushi.
Can suka fara jin dan hayaniya daga cikin gida yana tashi inda duk sukai shiru
suna saurare don suji may ke faruwa ne wai.
Maji daga inda take tai murmushi tana cewa Alhaji ya dawo ke nan nasan an fada
mashi.
Kai wanan matar batayi ba wallahi yanzu bayan an biya ta bucket din ta kuma,shine
sai ta fadawa Baba zancen.
Maryam tace ai in bata fadi yayi masifa wa maji ba hankalin ta baya kwantawa.
Mikewa Maji tayi bayan ta shafa tafita daga dakin zuwa gaida Baba da dawowa daga
kasuwa.
Ta samay shi shi da mama da uwargidan su a falon shi zaune tai mashi sannu da
dawowa,da yaya kasuwa.
Ta juya zata wuce sai maigidan nasu ya ce maijidda yaya akayi dan ki ya fasawa
Asiya roban ta da gangan?
Shaye shayen nashi har yakawo a,cikin gida cikin iyalina kuma?
Shiru maji tayi tana maijin kunan zancen baba a ran ta sai dai cikin dakiya yau
karo na,farko tun da ya fara mata cin fuska a gaban kishiyoyin ta kan dan ta tace.
Da na ko dan mu Alhaji ina bani kadai na samu yaron ba tare da kaine kuma a tare
mukai mashi ladabi a cikin gidan nan gaba dayan mi daku.
Don haka sai makiyin Allah zaice ban ba sadauki ingantaccen tarbiya ba a cikin
gidan nan.
Kawai dai Allah ne mai yin ikon shi akan duk wanda yaso ni kuma nasan bawai Allah
yakini bane