Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
samu hutu ba.
Nasan ya fadi hakane ya kawar da zargin wani abu a ranta nan take fada mashi cewa
taji baban su yace zai kira baban su Sani yaji yadda za,ayi kan zancen auren shi.
Ban ji amsan daya bayar ba amma naji tace ai ina ga ba wani dadewa za,ayiba ayi
bukin.
Bai dade ba yafito yabar gidan kada ya sake layi uwarshi ta gane shi tunda ga
manyar yarinyar nan ma ta gane balle maji.
Da dare muna zaune Baba ya aiko kiran maji tafita zuwa amsa kiran shi andan jima
kadan sai ganin ta mukayi tashigo rai a bace.
Idanuwan ta sunyi luhu, luhu sun kada sunyi jawur dasu duk muka bita da idanuwan
mu muna kallon ta.
Amirace tace Maji may akayi kuma yaya sadauki ya dawo magana ya tashi ko.
Ta dago fuskanta ba yabo ba fallasa tace bashi bane Amirah na sauke ajiyan zuciya
daga inda nake.
Tambayan ta suka matsayi nace anty kubar mama harta huce tukun koma may ye kuji
daga baya.
Dalilin dayasa mukai shiru ke nan gaba daya a falon ba wani mai kwakwaran motsi
sai tv dake ta aiki shi kadai.
Sai wayan mama yai kara ta dauka da alaman lalashin ta ake ga,wayan kuma kamar
muryan Baba ne.
Mama na aje wayan sai kawai tasaka,wani irin kuka mai ban tausayi tana cewa ita
dai gidan zata bari gaba daya ma kowa ya huta.
Da sauri na mike na isa gareta na ce mama don Allah don Annabi koma maynene kiyi
hakkuri kibarwa Allah.
Ban kai ga fadin wani abu ba,sai ga yaya sadauki ya fado dakin ganin yanayi uwar
yasa shi saurin karasawa gare ta yana tambaya cikin tashin hankali.
Su Amira sai faman kuka sukeyi suma hankali duk a tashe nima kukan ne yazo min
lokaci guda.
Kara tambayan ta yayi tare da bata hakkuri kafin ta dan sarara kukan nata sai
kuma dakin yai tsit.
Tace babana ban taba zaton Alhaji sani da kan shi zai iya muna wanan cin mutuncin
ba a matsayin shi na mahaifi gare ka.
Amma sai gashi tau ya,wanke ido yana fadawa Alhaji maganan banza a kanka.
Yace bazai ba mashayi yar shi ba kaje ka samo maahayiya yar uwar ka ka,aura shi
yar bata auren mashayi.
Cikin wani murya naji yaya yai magana yace maji shine abin tashin hankali ni haka
ma,yafi min nono fari wallahi.
Dama don naga kina sone yasa kawai na yarda amma ni ban ga abin bata rai ba kowa
ya rike nashi.
Ba aba ban ta ba ganin Alhaji na kuka da hawayen shi ba sai yau din nan akan
yadda Sani ya rufe ido ya fada mai magana akanka.
Kuma yace daga nan gidan aka kai maganan gidan shi don haka ba zai yarda ka
lalata mashi ya ba.
Furza iska yayi ya mike tsaye yace don Allah maji ki kwantar da hankaliki Allah
yabani wata,wace tafita ba,shike nan ba.
Amira tace wallahi ko shike nan maji kinga ma,shi bai damu ba.
Maji tace Amira baku ganewa ne shima ke nan jini kuya hana yar shi wa zai bashi
yar shi a garin nan.
Maryam tace gari da yawa ai maye baicin kan sa maji in sun hana yarsu sai may
Allah zai bashi wace tafita da yarda Allah kuwa.
Ga mata gari da yawa birjit in wani yakika da kwana wani da yini zai nemaka.
Shiru mukayi kowa da abinda yake tunane a ranshi har yagaji da zama yafita nasan
shima abin yaci mashi rai sosai.
Da safe sai gani mukayi su umma su biyu wai zasu uguwa mudai san can gidan zasu
sukara bata zancen.
Haka ko akayi don gaba daya sun kara jagula al,amarin baki daya kare baici.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,,
Tun bayan fitan yaya Sadauki a falon dakin shi ya nufa kai tsaye ya fada a kan
katifan shi ya kwanta yai lamo tankar wanda yake barci, sai dai ba barcin yake ba.
Damuwa ce tayi masa yawa a ran shi a hankali wasu yan siraran hawaye suka rika
silalowa daga idanuwan shi.
Ya dade a haka ya mirgina gefe daya yana fadi a fili, wayyo rayuwata may yasa
nake yawan tsintar kaina a cikin mawuyacin halin komai na tashin hankali akaina
yake faruwa ni kadai a gidan nan.
Allah ya jarabci rayuwana da masifa saka uwata a tashin hankali ko da yaushe .
A yadda ya lura maji ta dauki son duniya ta kwallafa mashi shi kuma gashi ya
kasa bata farin cikin rayuwa.
Ya kai zaune daga kwancen da yake yana cewa ya Allah kada kasa na zamo sanadin
jefa uwata a masifan rayunwata.
Gashi tunda ya tafi waje bai mai da hankali ga sha ba amma yana dawowa gida sai
ji yake zuciyar shi tana azzalzalar shi sai da yaje yasha ya samu natsuwa a zuciyar
shi.
Ba don wanan yar kauyen yarinyar mai saka ido ba da ta taimake shi da bai san
yadda zai yi ba idan maji tafito ranan ta fahinci a buge yake.
Can kuma ya tuna zancen baffan shi wai ba zai ba mashayi yar shi ba shi dama
Rahama bata gaban shi abudai ne in Allah ya nufe ka dashi ba yadda zakayi.
Tuna siffan Rahama yayi bai san lokacin da ya sake wani tsuki ba akan wanan abin
har za,ai masu wulakanci shi da uwar shi a cikin gidan su.
Yana da,budurwa da ta lake mai yar adamawace amma saboda zancen Rahama da maji ta
nace shiyasa ya,fita zancen ta kuma yarinyar irin masu son abin duniya din nan ne
ko yaushe cikin bani bani take shiyasa bai son al,amarinta.
Sai dai abinda ya daure mashi kai shine kishiyoyin mahaifiyan shi da bai san may
tare masu ba haka a rayuwa.
A,sanin shi dai komai yana masu wanda ya dace in ma ba yanzun da yaga tsana tayi
yawa a tsakanin su dashi ba yake nisanta kan shi da al,amarin su.
Kiran wayan shi akayi bai tsaya duban ko waye mai kiran nashi ba ya daga wayan
tare da karata a kunnen sa yace hello.
Muryan Fatiman adamawa ce tace sweety na baka kirana sai dai ni na kiraka ko?
Dan guntun murmushi ya sake iya bakin shi, yace Fatima ya akayi ne, ?
Tace my life nayi missing dinka sosai, tunda ka tafi gida baka kirani ba banji
daga gare ka,ba.
May yasa kake min hakane, baka damu dani ba sai nice ke yawan nuna damuwata a kan
ka,
Yai yar guntun murmushi yace Fatima bakiyi min komai ba wallahi nima rashin ki
yana damuna abubuwane sukai min yawa a nan gida shiya sa baki jini ba.
Tace karike min kanka kada kaci amanata don min ni taka ce, ka sani.
Yayi murmushi tare da,cewa ban maki alkawarin ni naki bane don haka ban dauka ba.
Dariya tayi daga bangaren ta tace kanace ina wasa ne ko gaskiya nake fada maka.
Yace ni ban yi alkawari ba don ki sani aure ma zanyi very soon don har an kammala
komai ko.
Cikin wata irin murya mai karfi tace what are you joking?
Yace bana wanan da ke ai gaskiya na fada maki tun farko ina da mata a gida da zan
aura.
Kalaman Sadauki sin tayarwa Fatima adamawa da hankali don haka sun gama waya
bayan ta kashe ta kasa zaune ta kasa tsaye shawara daya ta yanke wa ranta shi kuma
zatayi.
Washe gari haka na muka tashi ba dadi a gidan kowa zuciyar shi a cushe take mai.
Daga cikin matan gidan su mama ba wace ta damu da damuwan mu sai sha,anin su
sukeyi da raha da yaran su.
Hjy kubura ce kawai ta shigo dakin namu zuwa rana don Saturday ne bata fita ko
ina.
Ta samu na hada wa mama abin kari ina duke ina zuba mata sugar tai sallama falon.
Muka karba mata take cewa, daidai lokacin maji nace nabar mata sugar hakana.
A,a hjy maijidda ke ma bakin son sugar ashe da yawa ni gashi na rasa yadda zanyi
na daina shan wanan sugar don ba lafiya yake ba mutane a jiki ba yanzu.
Murmushi Maji tayi mata tace ni sugar dama bai damay ni ba wanan yar tawa ce ma
take yawan son samin sugar ko yaushe.
Ta zauna saman kujera a kusa da maji nan muka shiga gaishe ta mummy ina kwana
tace lafiya yau ana gida ba,a fita ba ne.
Maji tace sun samu hutu ne shiyasa kika gan su a gida tace ayya har hutu yazo
ashe?
Nan ta juya gurin Maji tace ashe kuma haka Alhaji sani yai muna akan zancen yaran
nan ?
Maji tai dan murmushi tace kila shine yafi zama alheri a rayuwan su damu ma gaba
daya.
Amma gaskiya Alhaji sani bai kyauta ba yaci kafa bai yada ganye ba yadda Alhaji
ya rike shi har yakai haka kuma yanzu kan yar matsalan rayuwa zai kawo wanan dalili
haka.
Ai yana da gaskiyan shi don ba mai son ya dauki dan shi ya bayar inda babu
tarbiya.
Haba sadauki ne baida tarbiya hjy maijidda sai dai ace kawai wanan lalurar dake
kan shi.
Kuma wanan aiba wai wani abin da za,a ki mutum bane kan shi shidai kawai yana da
wata manufa ga hakan ne kawai ya sha zugi daga cikin gidan nan.
Tau koma dai maye sai ya,rike dan shi shima Allah ya bashi wata wace tafita ba
shi ke nan ba.
Hjy kubura tai matukar mamaki a ranta yadda maji tai saurin basar da zancen a
lokaci guda.
Don ita a zaton ta abin zai jawo mata matukar tashin hankali amma sai gashi tashi
daya sunga ta basar da zancen ita ma.
Shiru sukayi a lokaci guda falon babu wanda,yai magana a cikin su sai hjy Kubura
ta mike, tana cewa dama cewa nayi bari nazo na jajanta maki kan al,amarin.
Maji tace nagode Allah ya saka da alheri, ai zaki kai ga sarakuwa ba da dadewa ba
insha Allahu.
Lokacin Bintu ta shigo dauke da ruwan da maganin maji a hannun ta .
Sai ta ce yar gidan maijidda ni dai da ma da Bintu kika hadasu da zaifi don kin
san halinta tasan nashi.
Gaba daya muka kalli hjy kubura wace ni ban ma fahinci maganan ta ba,sai da naji
mama tace ai da hakan zai faru sai nafi kowa farin ciki .
Da sauri hjy kubura tace mai zai hana hjy maijidda abu tuwona maina.
Fatima tana da mijin ta da zata aura ai bada dadewa ba ma zasu kawo kayan auren
ta.
Allah sarki ashe har wani ya riga mu niko tun jiya nake anyana hakan a raina,
wallahi ni dai da haka zai yiyo da yafi komai sauki wallahi.
Gaskiya ba zai yuyo ba a haka ma ya suka kare kullun yana samin yarinyar gaba da
hattara sai na jajirce mashi akanta.
Wanan ai ba matsala bace don bari zasuyi dasunyi aure amma wanan cin fuskan da
Alhaji sani yaiwa mutane ban son a wuce lokacin auren nan Sadauki bai samu wata ya
aura ba.
Komai na Allah ne inji maji tace an auri mahaukaci ma balle dan shaye shaye,
Hjy kubura tace ai shine lokaci ne dai bai yi ba amma sadauki yanzun ai abin so
ne ga ko wace mace.
Zasu dawo suna da sun sani ai a baya don sun wa yarsu ai ba wani sukaiwa ba amma
may ye abin kushe ga sadauki inba wanan harkan ba.
Tana fita dakin su maryam suka ce munafuncin banza kawai kamar da gaske.
Maji ta katse su tace ko na munafuncine tayi min don shine dama zaman kishin.
Tafi sauran dake ta nuna farin cikin su akan al,amarin amma ita dai ko tana da
manufa ta dai nuna halarci ai.
Sai maryam ta,kwashe da,dariya tace kaji mummy da,wani zance wai Yaya Sadauki ya
auri Bintu.
Kirmitsi ke nan inji Amirah, tace cikin kwashewa da,dariya, sai kuma tace wallahi
fa da sun dace, don itace kawai ta karanci rayuwan shi.
Nace don Allah Anty bari zancen nan kina son ya kashe ni ke nan mama tazo ta
kwashi gawata.
Maji tace da shima na kashe shi ranan yadda ya kashe min "ya.
Aka kwashe da dariya a falon nan sukai ta hira suna dariya wanda hiran tasu nake
jin yana kona min zuciya daurewa kawai nayi ina dariyan yake.
Kada nai magana mama tace nima na kyamaci dan ta duk halarcin da zatai min amma
saura kiris nace wa zai auri wanan kazami.
Don ni yanzu balain haushin da takaicin shi nake ji don wallahi duk yafita raina
kwata kwata.
Sannu sannu aka fara rage zancen don sunga wa yanda su keyi a kan su basuma damu
da zancen ba don ko a jikin su ma.
Min fita zuwa kasuwa don sayo yan abubuwan da ake bukata a gurin mu na girkin mu
ni da Anty Amirah muka fita,mun bar maryam tana girki a gida.
Komai mun sayo harda ma abinda muka manta bamu saka a list ba duk mun sayo da
sauran canjin hannun mu.
A gajiye muka dawo gida da kayan mu niki niki, nan muka zube a falo bamu dade da
zama ba sai ga yaya yashigo wanda shigowan shi gidan ke nan tun safe da ya fita.
Tv yana kunne ya zauna suna kallo da maji suna gaisawa tambayan inda ya shiga
take tunda safe haka.
Ya dan yamutsa fuskan shi yace wallahi ina cikin gari ina dan zagawa ne kawai.
Maganan da ake a tv shi ya daukewa kowa hankali a falon don photos wani yaro aka
nuno bai wuce shekara sha, goma ba zuwa sha daya.
Wai wani yai mashi fyde ana neman gudun mawan gurin mutane don a,tallafawa
iyayyen shi ai mashi aiki.
Salati falon ya dauka lokaci guda ga mahaifin yaron annuna yana kuka yana bayani
acikin tv.
Hankalin kowan mu ya tashi nan maji tace oh wanan duniyar ina zaki damu haka
yanzu wani daukan alhakine wanan karamin yaro haka ace wai kato yai mashi aika aika
haka ba dadin gani.
Maji bari na,dawo abinda ya fadi ke nan ya,mike yabar falon da sauri.
Ashe yana fita asibiti ya nufa gurin da aka sanar akai taimakon kan yaron nan
sadauki ya ba da kudin aikin dubu dari biyu dana sayen magani amma yace kada a
fadawa mutane shine.
Amma duk da haka abin yanzu bai boyuwa don saboda al,amarin media da yai yawa.
Da dare muna zaune falo sai hira ake yana tare da uwarshi suna maganan da ta
shafe su amma mu hankali mu baya a kan su.
Maganan da ake a TV ya mayar da hankalin kowan mu akan tv din labari ne akan
yaron da aka nuna dazu da yamma.
Nan suke sanarwa cewa an samu wani matashi mai kishin kasa da addinin shi yazo
yabiya kudin aikin yaron tare da daukan nauyin duk wani magani da za aiwa yaron har
yaji sauki.
Wanan kuma ba kowa bane sai matashin dake tashe muke alfahari dashi acikin garin
nan watau UF.
Shahararen dan wasan kwallon nan dake bugawa kasa kwallo yanzu ayaune kuma muka
samu labarin yatafi wasu unguwanni na,tallakawa inda yaiwa mata da yara marayu
kyautan kudi da kayan abinci da sutura.
Waya ya dauka ya kira wani nomba zai fara magana yaga wani irin kallo da uwarshi
ke mashi na mamaki.
Yace yanzu danace kada a nuna wanan abin sai da kuka nuna amma sai mai labaran ke
fadin duk da yace mu boye shi kada mu fadi wanan alheri nashi ga al,umma.
Munga ya dace ace mun fadawa duniya don matasa masu hannu da,shuni irin shi suyi
kishi da halin shi suma.
For god sake banji dadin wanan nuna program din nan ba da kasa ayi cikin fushi ya
kashe wayan nashi.
Sadauki muryan maji ce take cewa dashi wanan alheri keyi a gari haka bamu da
labari.
Dukar da kanshi yayi kasa yana cewa maji Annabin rahama yace idan zakai alheri ko
hannun hagun ka kada ya sani,
Amma kinga mutanen nan sai da suka baiyana ni a fili haka.
A dakin Umma kuma tana ganin abinda ake fadi ana yabon sadauki tace cikin wani
tsawa don Allah ku kashe min wanan shegen karyan haka kafin na,bata maku rai.
Dole yaran suka kashe TV suka kunna kaset suna kallo ba don ran su yaso ba don
sun fi son suga labarai akan dan uwan su saboda yanzu akan shi har wani jiji dakai
suke a gari.
Baba kuma yana zaune a falon shi yaga wanan labarin sai cewa yayi Allah nagode
maka da wanan baiwa da kaimin ta tsatsona.
Gidan hjy saude kuma tana kallo taja tsuki tana cewa aikin banza adai karata can,
sai ga yarta tashigo dakin tana cewa yanzu ake min waya wai anga yaya sadauki yana
raba alheri a tv.
Ke rufe min baki ki rabani da zancen wanan mashayi mai kyau dan maciji.
Nafada maki ki fita zancen wanan mara mutuncin, yaron da baida tarbiya ko kadan.
Rahama tace mama amma ni gaskiya na fada maki na ina son shi ko a hakan.
Bazaki so shi ba nace yaron da akace idan yasha har fitsari yake a wanda da amai
kacakaca shine zaki wani ce nabarki ki aure shi bata karasa maganan taba Rahama
tasa kai tabar dakin cikin turo baki gaba.
Washe gari mukayi bakuwa a gidan mu kowa bai santa ba sai dai tashigo gidan tana
tako daidai da ita tana tambayan mahaifiyar U F.
Mama Asiya tai mata nuni da dakin maji cikin binta da kallon ke kuma daga ina.
Tana cewa o mun shiga uku U F kuma a gidan mu kamar gidan wasu arnaku can mukan
wanan yaro yazama muna jaiba agidan nan wallahi.
Daga kofa ta tsaya tana sallamu alaikum daga ciki muka amsa mata.
Tashigo yar gaye ce ta karshe ga kyau ga ilimi yana nunackan shi a fili.