Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
min
da haske ga sabon da naga sunyi da mama sosai yanzu.
Itako yar bakin rai na kusa awa daya a dakin bata fito ba tana can tana ji da
kanta a daki don suna da wata yar dattijuwan da ke masu komai a shiyan su basu ko
kauda kara sai matar ce mai aiki.
Can tafito tana wani cika tana batsewa nace a, a anty Amira ai na zata kin fitane
ban san kina ciki ba wallahi.
Ta zauna tana cewa ina ciki na kwanta ne ina jin shigowan ku bandai fito bane
kawai.
Nace Allah sarki mun samay ku lafiya tace Alhamdullahi a takaice inda Amir yake
zaune yana wasa ta kalla tace my boy kaine wai kazama wani bulele haka dakai?
Nace anty aiko yama ramay sosai don tun shekaran jiya da muka dawo bai faye
lafiya ba baya son cin abinci sosai sai anyi da kyat yake dan shan tea.
Ai dolr kuyi kiba kuna cin gashin kanku kun manta da kowa kina kokarin raba muna
dan uwa damu.
Nace kai haba anty ni na ma isa na rabaki da yayan ki kin dai fada ne kawai
ra,ayinki.
Amma ai tsakanin ki da yaya sai Allah tace lalaikan gani nan bari nan takalmin
kaza.
Murmushi yayi daga inda yake zaune kusa da mama yace wai ke yaya zance da mukayi
ne na ma,aikacin bakin da kikace min kin samu.
Ta wani lumshe ido tare da bin lafiyan kujeran da take zaune akai tace yana nan
yaya.
Naga baka da lokaci ne ai sai na matan ka yanzu shi yasa ban fito ma da zancen ba
ranan da kazo.
Yace kin san Fatima yanzun queen ce lalaba abata nakeyi a hankali don banson
ganin bacin ranta akan komai.
Haka kuma duk wanda yai niyar bata mata rai wallahi sai inda karfina ya kare akan
mai shi don bazan dauki rozarci akan iyalina ba ko kadan.
Tasan da ita yake wa warning don haka taja bakin ta tai shiru tana sauraren shi
har ya kare zancen shi.
Yace mata ki fadawa mutumin yazo mu gana gobe da dare karfe takwas don kafin aiki
ya taso min idan son samu ne ma har aurwn nake son ayi akafin lokacin.
Sai ya mike tsaye yana fadin shi zai fita nace don Allah yaya rogo nake so da
zogala na dade ina son cin sa tun muna turai nake kwadan shi wallahi.
Na juya gurin mama ina cewa mama akwai man shanu ai ko ?
Tace akwai shi fatima yace yau kuma abinda kuke son ci ke nan kuma kayan yan
kauye.
Abinda aka samu a turai ina shi ina kwadayin abincin yan kauye kuma maimakon yai
kwadayin kayan sanyi.
Mama tai murmushi don sai yanzu ta fahinci wanan mugun kyau din da nayi bana
banza bane ashe dama tai hasashen hakan amma sai taga ai Amir ko shekara daya bai
kaiba watan shi ma na takwas ke nan da haihuwa.
Ko iya sai lokacin tagane ciki gare ni tace kai masha Allahu uwar dakina Allah ya
raba ku lafiya yasa wanan karon ba dan zama asibiti bane kuma aka samu kamar
maigidana cewa Amir.
Au ita yanzu cikine kuma da ita ina ruwan naga banza wai kina nufin kiyi saurin
cika gida da diyan ki kafin wata ta shigo ko may?
Banza kuma Amira wai ke wata irin shashan yarinya ce mara wayo haka dake ?
Abin arziki ya samu maimakon kiyi farin ciki da karuwan da aka samu amma mugun
halinki yakaiki ga hasashen banza kuma.
Kai maji nidai ba dama nai magana akan Bintu sai an zageni don tabi ta hada
mutane da ku baku ganin kowa sai ita haba maji.
Nace nima anty wallahi ban so cikin nan yanzi ba Allah dai ne ya kawo shi don ban
manta da wuyan da nasha ba gana wanan din.
Amma to yaya zanyi Allah ya riga da ya kawo shi basai na yi hakkuri ba da ikon
Allah.
Amira kada fa naji kinzo kina karamin murya naba yara suzo maki weekend na hanaki
kice zakiyi fushi ya fada mata hakana.
Komai Amira tai mai yana kokarin shanyewa ne don ya fahinci ita haka Allah yayita
da bakar magana.
Shi kadai ne kawai nasu ke zuwa masu daya koshi don baya biye mata ne kwai suke
zaunawa lafiya amma ita haka take da kowa ba dadi nata kalar rayuwan ke nan kuma
ita.
Shi dai ya fita da yaji fadan mama ya tsanan ta akan Amira din yana cewa haba
mama kiyi hakkuri da yar sister na ta dai kusa wucewa tabar maki dakin ki itama ta
huta hakana kamar kowa.
Bai dade da fita ba sai ga yaro da rogo cike da zogala nan na zauna da kaina na
shiga gyarawa hankali kwance kowa sai da yaci banda Amira da take ta faman fushi
ita kadai.
Mukan sai faman hira muke da mama da su iyya da yar aikin mama din don mama bata
dauke ta wata yar aiki ba can.
Ina basu labarin abubuwan mamaki da na gano a tafiyan mu da irin daulan da na
gani a gidan Abu sifiyanu mai kudin duniya.
Duk sun natsu ina ta basu labarin irin daukakan da yaya sadauki ya samu a duniya
ta wasan kwallo.
Tsukin Amira mukaji ta mike fuuu ta shige ciki cikin bacin rai dama kuma don ta
kule ne nake kara bada labarin tunda na gane ita yar hassada ce a rayuwan ta.
Don maganan da tayi kan cikin dake jikina ya bata min rai dakewa kawai nayi kada
mama ta fahince ni ta kara mata fada.
Baba ya aiko yana kirana nan na mike na saka gyale na nufi dakin shi nan na samay
su zaune da mummy kusa dashi.
Na shiga da sallama na tare da gaishe shi yake cewa yanzu kubura take fada min
cewa kun shigo ina barci nace takiraki mu gaisa.
Nace eh baba ance ka samu barci shine nace a barka tunda anan zamu wuni mun samay
ku lafiya ko ?
Yaya karfin jikin naka kuma yace Alhamdullahi Fatima ai iyayyen ki gasu nan suna
bani kulawa sosai wallahi.
Kinga ita wanan ma yanzu ta aje aikin ta don lalura na itace take min komai ita
da hauwau.
Jiki kan naji sauki sai dai tafiyan da ban iya yi ne kawai har yanzu matsala
koshi likita yace insha Allahu da sannu zan dan iya fara takawa.
Nace Allah ya nufa baba ya amsa da Ameen Fatima yaya maigidan naki kuna dai
lafiya ko?
Nace lafiya muke baba ai tare ma muka shigo dashi ya tafi ys dawo ne yabar mu
anan.
Fatima Allah yai maku albarka a rayuwan ku ina mai alfahari da kasancewar ki mata
a gurin sadauki.
Don nasan wani abin tare da taimakon ki ne yake yin shi a rayuwan shi yasa
Allahda Annabinsa sukace ku auri mataye na gari don ku sama ma diyan ku uwaye na
gari a rayuwan su.
Ke alheri ce sosai Fatima a rayuaan dana wanda ina matukar alfahari da hakan ko
yaushe kasancewan shi tare dashi yasa sadauki gaba daya ya sauya daga sadaukin da
muka sani a baya.
Duk wani mumunan halaiyar shi yanzun yazama tarihi a gurin mu da bakece ya aura
ba da sai dai muce Allah ya kyauta kawai.
Gashi natashi kudi suna shigo mai ta ko wani hanya may zai sashi tunanen gyara
wani mugun halaiyar shi can na baya da basu da kyau da ai saidai kawai yaci gaba da
gurbatacen rayuwan shi babu mai kwabon shi a kai.
Amma duk irin kokarin da kikeyi a kan shi ina da labarin komai a kunne na Fatima.
Allah dai yai maku albarka yasa ku gama da duniya nan lafiya yabaku zuria dayyaba
masu maku biyayya kamar yadd kuke muna.
Na amsa cikin kunya da Amin baba na gods nima da kuka mai da rayuwana haka don
kune silar komai da nake ciki a yanzu.
Yace kai haba dai Fatima ai mune dai da godiya a kanki yadda kikai muna biyayya
haka yau gashi ya zama muna alheri ga baki dayan mu ko.
Haka dai nabar gurin baba yana ta saka muna albarka da fatan gamawa da duniya
lafiya a rayuwan mu kamar yadda ko wani da ke bukatan addua ga mahaifan shi kullun.
Sai dare ya dawo ya kwashe mu muka bar gidan zuwa gidan mu cikin farin ciki a ran
mu yadda iyayyen mijina suke zuka ma rayuwan mu albarka haka.
Muna hanya nake cewa ashe mummy tabar aikinta ne akan rashin lafiyan bab ?
Yace wallahi fa haka sagir ya fara fada min da kuma naje gun baba din shima yake
fada min haka din.
Nace ai ko ta kyauta wallahi don haka shine zama tare yace ai zan duba akan al,
amarin don asan abin da za, ai mata akan haka din.
Nace yaya bafa mummy ba kawai dukkan su sun bukatan taimako wallahi don alama ya
nun sun a cikin wani hali wallahi ba dadi da ganin su.
Yace nima nai tunanen hakan amma banji kince komai ba shi yasa nai shiru nima.
Nace kai haba yaya nice kuma zanyi magana akan taimakon iyayyen mu yace bakece P
A ba ke ce ya kamata ki tsara abinda ya dace a kan su ai.
Nan na shiga zaiyano mai abinda ya dace ai masu din don a taimakawa rayuwan su
har muka kai gida kowa ya shiga part din shi don watsa ruwa ajikin mu ko zamuji
dadin hakan.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,
IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA IDAN KINYI HAKA MUN BARKI GA ALLAH.
Alheri sosai ya tanadarwa su Mama da Umma da mummy har motar shiga sai da ya canza
masu tare da gyara masu dakunan su tsab.
Wanan ya zamo karo na farko da sukaji dadi a ransu abinda taya sadauki yake masu
na alheri wanda hassada baya bari suga irin alherin da yake masu abaya.
Yanzun ko abu yakai babu gare su duk yadda mutum yai masu alheri komai kankantan
shi suna godiya sosai.
Don yanzu wanda suke samu gurin shi watau baba shima ta kanshi yake yi baida
komai duk diyan su sun wawashe mai shago baida wani abin hannun shi kuma inba gonan
da sadauki ya saya mai ba farkon fitan shi wasan kwallo da yafara zuwa.
A takure suke komai da suka fi karfi a baya yana basu sha, awa yanzu shi yasa
suke ganin wanan kyautan na baya yazo masu kamar kyauta na farko da ya taba masu.
Har daki mama Asiya ta samu mama tana mata godiya wanda mama ma a lokacin bata
san da wanan alherin ba inba yanzu da mama Asiya tashigo mata da zancen ba.
Mama tace ikon Allah wallahi yaya banda labarin wanan zancen yanzun ma nake jin
shi a gurin ki.
Godiya dai ta karayiwa maji tare da fatan alheri tana ta saka albarka wanda maji
ke gani yau kamar a mafalki.
Mama Asiya ce sakawa dan ta albarka haka akan alherin da yai mata don jin dadin
zuciyar ta.
Mama Asiya tana fita har tsakar gida tana godiya Nafisa ta gamu da ita dakin su
tashiga gurin mahaifiyarta tana cewa kina nan zaune halan may ya faru naga mama
tana ta godiya a waje tafito dakin maji.
Umma tace nasan taje godiya ne godiya akan may kuma Umma ?
Tace yanzu Sagir ya samay mu da kyautan alherin da yayan ku dan kwallo ya aiko
muna dashi mu uku motace ya sake muna da kujerun daki da gadaje sai kudi wai mu
saka mai a mota da kayan abinci.
Nafisa tace tirkasa amma ko Allah ya saka mai da alheri wallahi to umma shine
kike zaune ke baki zuwa kiy godiya?
Koda yake yadda naji kina magana kamar har yanzu kin saura hassadan abinda yafi
karfin ki fada.
Dadai kin sakawa ranki ruwan sayi kibi kici arziki dayafi maki wanan hassadan da
kukeyi shekara da shekaru yaki kare.
Ga yar uwar munafuncinki ta sulala taje tayi godiya tabarki nan kina hassada ga
banza.
Kallon takaici taiwa yar tata da suke dauka a matsayin mara hankali ga maganan ta
da dabiun ta amma kuma gaskiya ai Nafisa ta fada mata don tasan mama Asiya yanzu
tana zare jikin ta tana hurda da al, amarin maji da yayanta.
Nafisa kan dakin ta tashige takwanta abinta yanzun ta daina sha sai dai bata bar
harkan bazan ta ba da ta saba.
Sagir ya shigo ya samu umma zaune tayi tagumi ganin shi ya dan sata sake jikin
ta tana mashi tayin abinci.
Yace Umma na fada maki yanzu a gidan yaya sadauki muke karyawa ni da Abdul komai
dare sai Fatima ta kira mu muzo muci abincin mu yana aje haka ma dasafe.
Umma taji wani iri a ranta ba dadi tasan cewa ko ba komai anyi hadin zumunta a
gurin kafin takai karshen tunanen ta taji muryan shi yana cewa.
Wai ko Umma kin san wani abu fatima fa tai muna kanfen gurin yaya ga sabon gurin
aikin da za, a bude a abuja nasu.
Shi da kanshi yaya sadauki din ke fada muna cewa wai yar uwar mu ta nuna son kai
ta matsa ita sai dai muma a nema muna babban gurbi a can mu kama aiki dasu ko kuma
wanda ke nan sokoto.
Umma wallahi yadda suke gwada muna halarci irin haka ni abin ma har kunya yake
bani yadda a baya mukai ta gwada masu kiyayya a filin Allah .
Amma sai gashi yanzu da ya samu mune na farko samun alherin shi harda mota fa
yace zai saya muna wallahi.
Bamu kadai ba har dasu yaya Imiran naji ana magana a kansu suma za, a basu
appointment a gurin.
Tace kai amma ko da ya kyauta muna wallahi don zaman banzan nan na Imiran ya fara
ista wallahi.
Umma yanzun dai jekiyi naki godiyan kafin wani lokaci kuma kin san irin wanan
alherin na bazata shi ake kira da kyautan dan aljanna.
Kyantan da zaizowa bawa a lokacin da bawa yake a bukace da wani abu a rayuwan shi
dubi fa wa yan nan kujerun yadda suka koma kamar tsunma ni har kunyan nake jin azo
agansu a dakin nan haka wallahi.
Bai bar dakin ba sai da yaga Umma ta mike yaga ta nufi dakin maji hankalin shi
ya kwanta.
Don bai zai yuyuba ana masu alheri irin haka amma ace su har yanzu basu daina
hassadan su ba da sukeyi.
****** ********* ******
Allah mai iko a yanzu ankai duk inda sadauki ya sa kafan shi yana tare da manyan
body guard masu tsaron lafiyan shi dana iyalan shi wanda goverment da kansu suka
bashi su don tsaron lafiyan shi.
Saboda gashi karamin matashi amma yana daya daga cikin manya masu shigo da manyan
ababen amfani daga kasashen duniya.
Haka yasa ya zamo abin kula sosai a gurin manya na kasa da suke fada aji.
Saboda ya zamo daya daga cikin yan kasa masu kishin kasan su don sun cigaban
matasa.
Gashi akan kamfanin da suke son kafawa har guda biyu na mai dana manyan jiragen
ruwa da zasu dinga shigo da kaya daga waje.
Ga manyan injima na haska wutan lantarki da za, a shigo dasu kasa don amfanin
kamfanonin da za, a gina nan n
Nageria.
Ban fita sosai zuwa yanzu don cikina da yai matukar girma don ko a wanan ma
likitoci sun kara bani bedrest sai dai ba kaman wancan na baya ba danayi na Amir
din.
Ina kwance saman dogon kujera a falo na dan mike kafafuna na da sukai min nauyi.
Yashigo gidan a gajiye dashi su Sagir suna take mai baya shi da Abdul dauke da
dan briefcase din takardun shi da laptop dinshi a cikin case din.
Ya zauna yana cewa kai nagaji da yawa wallahi nazaci a nan idan na dawo ko zan
huta amma gashi duk ba wani hutu da mutum ya samu tare dashi.
Na dan lumshe idona tare da kokarin mikewa zaune don na karbi case din zuwa dakin
shi.
Yace da sauri No No kwanta abinki ki huta barshi idan zan shiga zan shiga dashi
ai.
Bayan ya karasa kaiwa zaune ne yake cewa duk rashin samun hutu ya saka har
kirjina yana min ciwo wallahi.
Da sauri na dago ina kallon shi nace amma gaskiya tunda ka fara jin haka ya
kamata ka samu hutu ka zauna a gida koda na kwana biyu da zaifi ma.
Yace na kwana daya dai Fatima kwana biyu yai min yawa ga mu da tulin aiki mai
yawa a gaban mu.
Idan ba naga angama gina muna komai ba hankalina bazai taba kwanciya bane ai
kinga dukiyar mutane ne nauyin shi ya hau kaina dole na kula masu da abinsu ko?
Nafisa ce tashigo gidan da alamun damuwa a fuskanta nan muka zauna da ita ana
hira suko abinci suka wuce ci a dining.
Yana gamawa ya shiga ciki ya dan jima bai sauko ba yana sama koda zai fito ya
sauya kaya jikin shi a lokacin.
Tun bai kai zaune ba ya soma magana yana cewa gaskya kauna ya kamata ace kifito
da miji hakana kiyi aure na hada ku da Amira dama yan sa, a daya kuke kinga kowa
sai ya huta abar Rukaiya har su karasa nasu karatun.
Cikin wani langabe kai tace ni yaya wama zai aure ni kawai ni na fitar ma da rai
ga wani aure can
Da sauri nace haba anty ce astangafurullahi mana yaya zaki magana kamar ba musulma
ba dake.
Tace to madam wakike gabin zai aureni a haka yadda nake duk masu zuwa gurina ba
da sunan aure suke zuwa min ba sai dai da tasu bukata kawai.
Gaba dayan mu tausayi tabamu ga maganan ta don mun san cewa gaskiya ta fada
maganan ta.
Amma kuma ai abin Allah ba a yanke kauna a gare shi nace anty gaskiya yaya ne ki
natsu ki rage wasu halaiyar ki ko Allah zai tausaya maki.
Don kinga ai