Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
fito falo yana zaune yana kallon
ball .
Guri na samu na zauna tare da gaishi shi ga kayan fruit da naman da yaci saman
table a gaban shi.
Yace yaya jikin kuma nace yai min sauki sosai dana sha magani .
Zauna ki ci nama ga milk nan kuma kisha baida sanyi sosai nace na koshi yace kin
koshi da kikaci may kuma ?
Banci komai ba na dai sha lemon da ka kawo min sai naji na koshi sosai.
Oya ki kara da,naman kisha milk din ko zakiji jikin ya kara sake maki ban yi musu
ba na fara cin naman a hankali sai dai duk bakina ba dadi cikin shi ko kadan.
Yace kisha milk din mana ina kaiwa a baki naji kaman zanyi amai nan na cire cup
din da sauri a bakina .
Na mayar da kaina baya saman kujera ina mayar da numfashi guda guda cikin wahala.
Ban san tasowan shi ba sai jin shi nayi a gaba na yace oya kwanta ki mike shi da
kan shi ya gyara min kwanciya nan ya shiga dan tausa min ciki na a hankali.
Naji dadin hankan har na fara lumshe idanuwa na ban sani ba sai barci bai bari ba
sai da yaga barci ya dauke ni sosai.
Sannan ya daina yadan kura min ido yaga yadda nake barcina a tsanake nan ya koma
saman kujeran da ya taso kada ya tayar dani.
Mukai wani lokaci a falon yana kallon shi bai son ya tayar dani na falka daga
barcin da na keyi.
Sai da dare yayi sosai ya tayar dani muka koma daki sai dai makale ni yayi haka
muka kwana dashi.
Washe gari na gyara jikina nai wanka nashirya tsab nashiga kitchen hada muna
breakfast, ina tsaka dayi ya dawo daga gurin motsa jikin shi.
Kitchen din ya shigo ya samay ni yana cewa har kin ji sauki ke nan ko idan bazaki
iya ba ki barshi kawai sai a sayo muna muci nace zan iya ai har na kusa gamawa ko.
Yace yau fa kina da bakuwa don Nafisa zata shigo gidan nan don Allah idan tazo
ba runki da ita don kin san yanzu ta burge sosai.
Sai misalin sha daya da rabi suka shigo gidan su uku ne da kawayen ta da ganin su
tantiran yan duniya ne sauran don sun fita,wayewa sosai.
Da fara,a na fito daga dakina ina masu sannu da zuwa duk suka zubo min idanuwan
su nan dai bayan mun gaisa na kawo masu abin sha suna godiya.
Nace gashi ko yaya ya fita ya jiraki baki zo ba yace zai fita amma ba nisa zai
tafi ba.
Kada ki damu ai zan jira shi ta bani amsa nace anty may zan dafa maku ne yanzu.
No ki barshi inji wace tafi haske daga cikin su nace ,a,a Allah bari na girka
maku abinci mana kafin ku wuce.
Na juya nan na barsu a zaune suna bin gidan da kallo na shiga kitchen na fara
hada abinci.
Basu dade sosai da zuwa ba yaya ya dawo gidan shi da Bashar ne wanan karon.
Suka gaisa dasu fuskan yaya a daure nagan sbi nafito muka gaisa da bashar nakoma
ciki.
Yaya ce wa yan nan fa tace tie friends dina ke nan yaya wanan Raiha akace mata
amma anakiran ta da Rayye ne ita kuma wanan Nura ance mata Nuriyya.
Yace ok sai dayan tace amma sai naga kamar na sanka da dadewa ko sai dai in ba
kai bane amma nasan wanan fuskan gaskiya.
Nafisa tace ke banza shine fa U F da kike jin ana fadi dan kwallon wasan duniya.
Yadda tai maganan kamar a buge yasa kowa yin dariya a lokacin banda yaya daya
daure fuskan shi.
Nakwao masu yaya ruwan sha da drinks na aje masu nakoma gurin girki na.
Yaya yace amma ba yanzu zaki wuce ba ko don kin san nace ina son ganin ki ko.
Tace ai shine nazo mana ko don nazo da kawaye nane baka samun ganin nawa.
Yace ashe kin gane nufi na nafito masu dauke da kulan abinci da plate na aje masu
tare da masu bisimillah.
Can dayan tace na tuba inda na sanka yanzu muna haduwa da can baya gurin Brosha
mai kayan harka ko?
Daure fuska yayi kamar badashi take magana ba Nuriya ta jawo kula ta bude abincin
dana aje masu tace wowwo kamshi ke nan aiko mu gode wallahi dama yunwa nake ji
sosai.
Sam basu da kunya atare dasu ko kadan sai wani girgiza suke yi adole sunga maza
mata sa yaya yace muje na sauke ka gida Nafisa ki jirani fa kinji na fada maki.
Nan muka zauna dasu suna cin abinci muna hira jefi jefi dasu dayan take tambayan
Nafisa ita kadai ce matar shi halan Nafisa taba amsa da eh.
raiha tace wai amma kan zakiyi fama da arnan yaki ga mijin ki matashi kuma mai
lokaci ai akwai aiki.
Sai da sukaci abinci suka koshi yaidda nai masu sunji dadi haka sosai basu boye
min ba don cewa sukayi da suka gama kai amma gaskiya munji dadin yadda kika tare mu
ba kamar gidan wancan yayan naku ba da mukaje suna ce muna wai yan kwaya sun shigo
gidan su.
Nace subbahanallahi ai ba wanda ya wuce jerabawan ubangiji don kuma ba haka
kukaso ba a ran ku.
Shiru sukayi sai Nurace ke dai ganan min hanya yar uwa ina mamakin mutane wallahi
mutum na da abin fadi amma sai ya takw nashi yaje fadin nawani.
Nace Allah Allah dai ya yayewa kowa wahala kuma Allah ya kawo maku mazajen aure
ku huta duniya yanzu ba tausayi wallahi.
Raihane ta jefo min tambaya halan ke yar wace garice sister kafin na bata amsa
Nafisa ta ce yar uwar muce fa agidan mu ta tashi ai.
Ai ko ban taba sanin taba gaskiya nai dariya nace niko nasan ku ai yakai sau uku
muna hafuwa daku ai.
Allah sarki ban ko gane kiba wallahi, tace min suka mike suna cewa zamu tafi
mungode kwarai da taron da kikai muna nace kai haba ba komai aiku yan uwa na ne.
Suna fita nan Nafisa takife saman kujera sai barci koda yaya ya shigo ya samay ta
tana barci sai baita da ita ba dakina yashiga ya samay ni zaune yace ita wanan
barci tai muna anan.
Nace ina ruwan Anty Nafisa taci ta koshi sai barci abinci yace na bashi nabi
bayan shi muka fita tare sai da ya zauna yake cewa ina ganin yau zanyi tafiya fa.
Amma sai dai yadda nagani amma iyakata Abuja zan tsaya kawai.
****** ********* ******
Bayan Nafisa ta tashi yana falon zaune ganin shi yasata mikewa zaune yace har
kin gama barcin ke nan tace tana mikewa zaune wallahi fa yaya.
Yace haba Nafisa ya kamata ace yanzu kin wa kanki fada fa gaskiya baki kyauta wa
iyayen mu musan man ma Umma da take mace tana zama dake a gida ko yaushe.
Shiru tayi tare da dukar da kan ta kasa yace lokaci yayi nafisa da zaki bar wanan
harkan haka duk da nasan abune mai wuyan bari amma don Allah kiyi kokari ki dan
rage wasu daga cikin halaiyar ki don Allah dai ba don niba Nafisa.
Abin mamaki sai gata kawai tana hawaye tace wallahi yaya nima kaina ban san may
ke kaini sha ba ko naso na bari sai naji kwata kwata bazan iya ba.
Lokacin nafito falon ganin suna magana yasa na juya zan koma ciki sai yace No dawo
ki zauna aikema maganan ya shafe ki tunda ya shafe ta.
Tace wallahi yaya ni ina ganin Alhakin kune da maji ne ya sauka aikaina dakin mu
don irin mugun abinda Umma da mama suke shuka maku kullun tun ina karama nakejin
irin tugun da suke kullawa akan maji da ku.
Dariya yayi yace kai haba Nafisa ai shi zama kishi ina ganin haka yake sai ta
share hawayen tace yaya bazaka gane bane wallahi.
Amma nasan ko nayi rantsuwa ban kaffara don su Umma ne suka sa kayin shaye shaye
a baya.
Na fadawa umma su bari kada Allah yajerabesu watara tundai ina suna zagin ka da
mashayi dan maye mukan mata magana ni da yaya sagir amma umma bataji.
Munafukan ga mama bata bari umma tabar aikin ta yaya yaya kake ganin zan iya
dainawa idan su basu daina sheri ba.
Tace umma tana sakaci da yawa tana yarda da mama asiya batan cewa muguwa bace ta
karshe har yanzu bawai sun dai jifan ku bane fa.
Allah daine ke kare ku kawai amma kai kan ka da,wuya in ka daina sha yanzun haka?
Da sauri na dago kai ina kallon shi sai naga yai murmushi kawai yace Nafisa koma
maynene ki sa a ranki cewa zaki daina sai kikaga kin daina din.
Ki samu miji kiyi aure koma may nene kike so ni nai maki alkawari zan sai maki
duk lokacin da kika tashi aure.
Kai ta kifa tafara wani irin kuka take nima bansan lokacin da na fashe da kuka ba
shima dai ina ganin kukan yakeyi a lokacin yadda na ga ya dukar da kan shi kasa.
Can ya mike ya shige dakin shi ya bar munan muna kuka tai matukar bani tausayi
namike zuwa inda take na dafata.
Duk da nima kukan nakeyi amma sai na dafata ina bata hakkuri kawai sosai nake
mata nasiha har nagama batace min kalla ba nace tazo tashiga tai wanka ko zataji
dadin jikin ta.
Ta kalle ni da mamaki tace Bintu ke baki kyamanane yadda sauran yan gidan mu ke
yi min yanzu nace kyama kuma anty akan may zan kyamace ki kina da cutane ko may.
Tace har fa ciwon aids mama Asiya da yaya Ahmad ke fadin ina dashi yanzun haka
kallon mai cutar aids wasu mutane ke min.
Nikuma wallahi komai mayena ban bari mutum ya shige ni baida roba a jikin shi.
Ban san lokacin da na runtse idona ba danaji abinda tace min ba kunya take fada
min tana amfani da maza haka.
Dakina nakaita tai wanka na bata wani dogon riga na mai kyau tasaka muka dawo
falo nan muka samu yaya yace tazo ya sauke ta gida don can zai tafi yanzu.
Tare sukafita da ita tana min godiya nace haba anty aiyiwa kaine tausayin ta yai
matukar kamani sosai.
A hanya ma sosai yaya yaita mata nasiha ya na kwantar mata da hankali na ta natsu
ta daina wanan harka baida amfani don babban illa da cikas yake kawowa mutum a
rayuwan shi.
Sai yamma ya dawo yake ce min tafiyan shi yana nan yace ko bazan iya zama ni
kadai bane yaiwa Inna magana maman su Bashar a turo min daya daga cikin yan matan
ta nace a,a zan iya zama mana yaya.
Ai yanzun na saba da gidan ban jin tsoron komai kuma kamar baya yai min sallama
bayan ya shirya ya wuce Abuja .
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,
A LOKACIN MUKE,,,
Suna zaune tayi murtuk da fuskan ta yarasa mai zaiyi wanda zai iya jawo hankalin ta
ta sake mai fuskan ta ko zai dan ji sanyi a ranshi.
Shi dai tun auren su shi dai ba zai ita cewa ga wani dadin wanan amaryan tashi ba
da yaji a zaman su.
Kullun a cikin bashi commad take yau tace wanan take so gobe tace wancan take so.
Gashi iyanzun duk dan zarahin shi ya tafi baida wani kudi da zai juya a tare
dashi.
Gashi kuma a bangaren ta idan ba kudi ne ya kashe mata babu zaman lafiya a
tsakanin su ko kadan.
Shi da gidan shi amma har kofa sai Jamila ta rufe mashi don cin mutunci sai ya
samo mata kudin nan da ta furta mashi tana so a gurin shi.
Jin sunan shi da ta ambata yasa shi saurin juyowa da sauri a dan firgice da tace
Ahmed fa dakai nake magana ka zauna kana min wani tunanen can dakai.
Kaji na fada maka dubu dari shidda nake so ina son na kai babana asibiti saura
kuma zanyi amfani dashi ne akwai bukin kawata da za,ayi ina son nasai mata abu mai
munhinmanci don tasan inayin ta sosai.
Nisawa yayi tare da gyara zaman shi yace Jamila wallahi ban san inda zan samu
kudin nan ba yanzu don wallahi dan abinda ke hannu na kwata kwata baifi dari uku ba
ma in har sunkai shine kuma nake dan juya muna.
Rufe min bakin ka kai baka ji kunyan fada min haka ba kai dan gidan Alhaji
Abubakar deller shine har zaka fada min haka ?
So kake na yarda da karyan ka kana nufin haka zan zauna dakai ba wani karuwa
sunan ina auren dan mai kudi ko may wai ?
Kaji na fada maka in har kana son zaman lafiyan kakan ka nemo min wanan kudin
dana fada maka.
Ehe, don shine kawai kwanciyar hankalin ka don a zauna lafiya kawai kaji abinda
na fada maka daga haka ta mike tashige dakin ta tare da rufo kofan dakin garam da
karfi yamike yana fadin Jamila Jamila tsaya mana ki saurare ni.
Amma ina har da key taiwa kofan dakin nan ya dafe kan shi yace oh my god wanan
balin na jamila da may yai kama ne wai.
A falon ya kwanta saman dogon kujeran su a takure haka ya kwana shida gidan shi
ya koma kwana falo don masifa.
Washe gari ma da masifan suka tashi a gidan don yana zaune ta hado abin karyawa
duk dashine yasayo amma yana zaune, yana kallo tana shan shayi da kwai a gaban shi
har ta shanye tass
Ga jamila bata wasa da ci duk yawan abin nan zata iya cinye shi tas ita kadai
yace a ran shi shiyasa take mulkan dan bura uban kiba haka tana curewa ita kadai.
Shi ko sai rama yake yana aje dan dogon wuya kamar matikin lema dashi ganin babu
sarki sai Allah yasa shi mikewa don fita ya dan samu abinda zaiciwa ran shi tun
jiya da ya karya bai ci koma ba don fitan jamila a kan shi yai yawa .
Gidan su ya nufa gurin mama Asiya don ya dan samu abin karyawa a can , duk yasan
kullun yaje neman abinci sai mama tai mashi korafi kan shi matar shi da bazata
girka mashi ba shi ke nan kullun zuwa gida cinye masu abincin su.
Yau ma yadda yai tunanen masifan mama hakane a kan shi don fada ta haushi dashi
tana fadin sai da nai maka gudun haka amma ka dage kai sai wanan yar daban matar
taka zaka aura yanzun ga shi ko abinci ba ta iya baka sai ka kama labe labe gidajen
mutane.
Bai damu shi dai yace Rukaiyya ta debo mashi abinci kawai yaci nan ya hago kayan
tsaraban da sadauki ya labto masu a gida.
Yace kai mama har yanzu tsohon nan yana sayo maku abinci haka mai yawa ashe.
Tace wani tsoho kanin ka dai sadauki shine ai yanzun zance mai muna sayen abinci
duk wata.
Kamar Alhajin ya barshi da wanan nauyin ne kasan su da son neman suna da iyayi
waishi gamai hali kowa zai gwadawa hali .
Dama ba musan uwarshi bace matsiyaciya yar taulali kawai su suka sani da shegen
iyayin su wai su ga yan iyawa ke nan.
Nan dai ya kwashi abincin shi sai da yai kat dashi yana ta sake sake a zuciyan
shi.
Sai da ya gama yamike yana cewa zai shiga gari yaga may gari ya waya yau kuma.
****** ********* ******
Ganin ya juya zuwa dakin shi yasani fahintar fushin abinda nai mashi na rashin
nuna mashi nai wanka da yadawo yayi.
Sai da na bata lokaci na sosai gurin gyaran jikina a gaban mirror na mike ina
sake sake a raina na na kashe wutan dakin da A C nafito na nufi dakin nashi.
Na samu ya kwanta ya kashe wutan dakin a lokacin jin motsina bai sa shi koda dan
motsawa ba a lokacin inda na tako zuwa bakin gadon na kwanta a hankali a bayan shi.
Bai motsa ba don jina saman gadon a tare da shi ganin ba zai motsaba nakwanta a
hankali tare da dora hannuna a bayan shi.
A hankali na dan fara shafa mai bayan shi amma bai sashi motawa ba sai dai ya dan
sauke ajiyan zuciya kawai da naji yayi.
Ban daina mai abinda nake yi ba sai ci gaba da nayi da mashi a lokacin ina kai
gayi har na kai ga,tura hannu na acikin blanket din da yake rufe a jikin shi.
Inda na sauke hannu na a kan abin shi na fara dan amfani da hannuna ina dan
shafan shi a hankali tun yana daure ma abinda nake mashi sai gashi ya gyara
kwanciyan shi da kyau ta yadda zaiji dadin abin da nake mashi da kyau.
Ganin haka danayi yasa na ci gaba da mai yadda yake so sai kawai naji ya rugumoni
shima ya shiga mayar min da martanin abinda nake mashi da farko.
Mun dauki lokaci mai tsawo muna farautawa junan mu rai a tsakanin ni dashi har
sai da naga na kawar da fushin da akeyi dani da farko.
A hankali muke sauke numfashin mu don yadda muka aikatu da junan mu.
Hannun shi naji saman kaina a hankali yake kwantar min da gashin kaina da ya
tarwatse a lokacin can ya sauke ajiyan zuciya yana fadin.
Fatima may yasa kika min abinda kikai min kika hanani more abinda Allah ya
halasta min a kan ki.
Shiru nayi sai da ya kara maimata min tambayan nace a hankali yaya kayi hakkuri
please ni da naji ba ka tambaye ni ba shi yasa na kyale ka
kawai don na