Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
ya ciro magani daga aljihun shi ya bare tare da hadewa tukun ya fara dan
kurban tea din a hankali don zafin shi.
Baja jin dadi ne naga kasha magani mana mama take tambayan shi da hakan ?
Da kyat yasha cokali kamar shidda ya aje cibin tare da mayar da jikin shi saman
kujera ya kwanta da bayan shi a hankali.
Muryan maji yaji don a lokacin na koma cikin dakin mu, maji tace mashi.
Ka sa damuwa a zuciyar ka ko dubi yadda duk ka lalace lokaci guda, kana ganin zan
cutawa rayuwan ka ne ko may sadauki?
Ya dago kai tare da bude idanuwan shi yace namay kuma maji ?
Tace akan auren da kake gani ina son tirsasa makayi ba da son ran ka ba mana.
Yace maji ni fa banda zabin daya wuce naki a rayuwana akan may zan tayar da
hankalina ga abinda kike shirin yi min gata.
Mama taji dadin kalamin shi sosai a ran ta har fuskanta ya dan baiyyana murmushi
kadan.
Nan ta shiga mashi nasihohi akan hakkin aure tare da saka mashi albarka kwando
kwando na mata biyayyan da yayi tana mashi fatan alheri.
Sosai ya dan ji sasauci a zuciyan shi dan kasancewan da sukayi da mahaifiyar ta
shi na dan lokaci, abinda ya dade baiga hakan ba a tare dashi tsakanin su.
Ni dai tun wanan lokacin ban kara bi takan komai ba don ko kallon inda yake
banayi balle nasha harara.
Hakan yana matukar bata mashi ran shi sosai yakance a ran wai wanan abar ce zata
zauna da mutum har ta farauta mashi ran shi yaji dadi a haka?
Mace komai bata iya ba ban da dunkulewa a cikin hijjabi kulun kaman munafuka ko
muguwa.
Wama yasani ko maganan Amira gaskiy ne asrice maji sukayi don suci arzikin su.
Don shi baiga abinda maji tagani gacwanan yarinyar ba har take kokarin yi mashi
baki a kanta inba hasken fata ba kawai.
Gashi baida yadda ya iya dole yasawa zuciyar shi hakkuri da wanan auren kaddaran
don ya dadawa mahaifan shi rai kawai tunda suna so amma shi kan yasan an tsere
mashi gurin matar gwadawa tsara kan.
Ta ko wani bangare na gidan kowa sai shirin buki yakeyi banda mummy da babu nata ko
daya a cikin bukin don ita yaran ta kanana ne kwarai agidan.
Sai dai kusan tare suke harkan bukin bangare mama da ita don ta saka kanta
tsunbul a ciki inda su umma ke fadin wai kwadai ne kawai ya kaita ciki don taga
gurin ci.
In bashi ba ai su ma yaran su ai diyan mijinta ne may sa zatafi bada karfi a
dayan shiyan kawai.
Ta bangare na ni kan ba wani abinda na shiryawa aure sai harkan bukin Anty maryam
kawai nake yi kamar nima ba amarya bace,
In dan anyi min magana nakance ni ba wani bukin da zanyi sai dai dan dama dama
walima indan zan samuyi.
Su mummy sun tafi sun gyara gidajen mu yadda ya dace duk da ba wasu abu za akaiba
mai yawa saboda ko wani ango yasaka kayan komai a nashi gidan.
Baba yai fadan haka yace don may zasuyi mashi haka da su bari shima yai wa diyan
shi nashi bajinta da ko wani abu kewa yar shi idan zatayi aure.
Kayan aiki ne aka kai muna irin na amfanin mata ko shi ba wasu masu yawa ba don
sauran abubuwa irin su gas, su tv, fridge, toaster da yan kayan kitchen electronics
akwaisu a kitchen din.
Yan zuwa jai kaya suka dawo suna fadawa mama abinda ya faru a gidajen mi mama
tace a daikai nata da ta saya muna hakk8n mune ta sauke muna ai.
Saura kwana hudu buki ya shigo cikin gidan duk gidan a lokacin cike yake da baki
yan zuwa buki yan uwan hauhuwan maji da ga garin su sunzo.
Dakin ta ya samay ta da wata yarta ta dagin su mama take ce mai bayan sun gaisa
dama ina son na gan ka don gobe ko jibi nake son akai Fatima gurin iyayyen ta don
su ma suyi nasu bukin a can tunda ita yar fari ga mahaufin ta.
Shiru yayi bai dago kai ba tace don haka sai naji naka shawaran akan tafiyan nata
don ban san ko kana da wani shiri ba ?
Yadago idon shi da suka canza launi yace maji ni wani shiri nake dashi duk abinda
kuka tsara ai daidai ne.
Ta kara cewa ina son ka basu mota da sauran kayan da zasu bukata a can akai masu
don zirga zirga da amfanin su.
Baiyi magana ba nan ma shiru yayi yana tunane wa maji ke son na tura wanan bakin
kauyen ya kwana can gari ba wuta ba wani abin more rayuwa can.
Ranan da za ai kamu gidan mu ya cika makil da mutane yan uwa da abokan arziki ta
ko ina na bangaren dakunan gidan.
Mata mu hudu ne maza ukku, sai dai a lokacin na bata tsarin abin don duk yadda
akayi dani na fito zuwa gurin kamun naki futowa nashige bandaki na kulle kaina
ciki.
Mama tace a kyaleni tunda bani son fitowa agan ni ai hakan ba ibada bane ga
mutane yan gulma da basu sanni ba sun cika gurin don son ganin kwam.
Sai da naji ba kowa a shiyan duk sun watse sun tafi gurin kamu nafito na zauna a
bakin gadon mu nai tagumi ni kadai a dakin.
Sai ganin mama nayi tashigo dakin abinda ya dan sani firgita ke nan zan tashi
tace koma ki zauna abinki na fahinci baki son ai maki kamu a garin nan sai a gaban
iyayyen ki ko?
Don haka kada ki damu gobe insha Allahu za,a tafi dake can zamu washe gari muyi
maki naki a gidan mahaifan ki.
Kuma kinyi gaskiya don wanan halin naki yasa nake kara kaunanki Fatima a raina
don baki dauki karyan duniya ba ke a ran ki.
Muna nan zaune tare da mama a daki har mutane suka fara shigowa tana kara yi min
nasiha akan duk rayuwan da zamuyi na daure nayi hakkuri watarana sai labari insha
Allahu.
Ganin mutane sun fara shigowa yasa ta barni ta koma dakin ta sai lokacin ne na
dan sake jikina nan na fara shirin tafiya don tace da safe zamu tafi garin mu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN KARANTA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA ALLAH NE SHEDA HAKA MUNA BINKU
BASHI,,,,
Tun da safe na na shirya komai nawa ina jiran ace nafito ne kawai, a lokacin don ko
karyawa ban yi ranan.
Ina nan zaune a takure maryam ta shigo dakin tana cewa a,a matar yaya ba dai har
kin shirya ba kamar mai gudun mu kuma ?
Hararan ta nayi idanuwa na sun dan ciko da hawaye a lokacin cikin murya mai kama
da ta shagwaba nace haba dai anty maryam.
Nice kuma matan yaya don Allah dai ki bari mana please wallahi kina kara tayar
min da hankali Allah.
Dariya ta kwashe dashi tace au to yanzu kuma may ya rage maryam ai kin zama matan
yaya ko shafawa kawai ya rage insha Allahu.
Abinci mama ta aiko min ni da maryam din wai mu karya da taimakon ta na samu har
na dan kurba ruwan shayi a cikina.
Ina nan ina zaman jira ina saye cikin wasu lace brown color sai duwatsun da akai
mai ado dashi don nafi son dinkin riga da zani a rayuwana.
Tun lokacin da naji wa,azin mace ta rasu an rasa zani a cikin kayan ta da za,a
yafa mata zuwa makabarta nake jin tsoron dinka skirt sosai, ina dinkawa amma ba ko
yaushe ba.
Mama ta shigo dakin guri na muna zaune saman gado da maryam take ce min Fatima
har kin shirya ne?
Maryam tace ai tuni da anbi ta nata ma ai da yanzu mai kaita ya dawo ko tundazu.
Murmushi mama tayi tace ai yau insha Allahu kuna zuwa ba fashi sai dai ban son ki
kwashi kaya da yawa tunda kwana biyu kawai zakiyi a can.
Nace cikin yar muryana kala hudu kawai na dauka mama tace yayi kyau haka sai ki
hada duk wani abinda kike so anjima su hajiya lami zasu kai sauran kayan ki can
gidan ina son naga kafin buki ya kankama na gama da komai naku ko.
Mama koran mu ma ake kenan inji maryam tace ai muna tare balle ku da zaku zauna
kusan uguwa daya da junan ku ai ba a rabu ba.
Da sauri na kalli maryam tace nima haka naji ana fadi wai nesan gidan baikai gida
goma ba a tsakani.
Tace mama amma dai Bintu idan an dawo sai andawo da ita ta nan kafi a wuce ko?
Tace sosai ma kuwa tare da masu zuwa daurin aure fa zasu dawo kuma kinga su nasu
can da safe ne goma na safe za,a daura naku kuma sai da rana karfe biyu na rana.
Don haka tana nan gida za, a daura naku ai insha Allahu, ko akwai wani magana
kuma ?
Maryam tace a,a shike nan ai dama ina ce ko shike nan daga yau dai mun rabu ke
nan.
Kun rabu mana tunda kowa zata kama dakin ta ku barni da wanan mara hankali muyi
ta fama da ita.
Mama tace bari na fita kinji Fatima na aika akira min sadauki naji yaya zancen
tafiyan naku kada ai rana ba,a tafi ba kuma.
Yana daki kwance yaji wayan mama ya shigo mashi ya dauka a kasale yana fadin
salamu Alaikum.
Ta amsa mashi yadda ya dace tace baka shigo ka karya ba mana tin dazun ga wanan
yarinyar Fatima kuma zancen tafiyan ta fa may ka shirya akai?
Yace maji bazan iya shigowa gidan nan ba yanzu don mata sunyi yawa wallahi,
dariya yaba mama tace to ai duk uwayen kane a dakin zallan mu kawai.
Yace No maji gaskiya ba zan iya shigowa ba saboda yawa ba zan sake ba anan.
Tace ko abada akawo maka dakin ka ne yace shike nan maji hakan yayi.
Sai da aka shirya komai na karyawan mama tace nazo na kaiwa sadauki breakfast din
shi yana dakin shi.
Wani irin faduwan gabane ya kamani amma dai haka na dake na fita da kayan a
hannuna.
Ina fita na samu Abdul dan wurin mama Asiya zai fita na bashi nace don Allah ya
kaiwa yaya sadauki.
Yace kai amma dai ke Bintun nan ke da mijin ki kuma kice baki iya kai mashi abin
karyawa da kanki.
Na dan marairaice nace yi hakkuri yaya Abdul bashi kadai bane a dakin shiyasa
nake jin kunya.
Yana min sheri ya karbi kayan ya shige mai dashi ina ganin ya shiga na juya cikin
gida da sauri na.
Abdul na shiga ya samay shi a kwace ya fara gauda shi tare da aje mai kayan
abincin yace kai amma dai Bintu shine tace min wai tana jin kunya bakai kadai bane
a dakin bazata iya shigowa ba don Allah na taimaka na kawo ma ashe wayo tai min ke
nan.
Murmushi yayan nashi yayi yace kyale yar kauye bata son shigowa ne tai maka
haka .
Yace ai zamu hadu da ita ne sai na rama nima har yakai kofa zai fita yajuya yana
cewa yauwa yaya UF dama ina son ka bamu kudi zanyi party da kuma ball na mu yan
unguwa akan auren ka.
Yace kai Abdul party may kuma kawai da ka share da zancen wani party can ni kaga
ba wani shirin da naiwa wanan auren.
Kai yaya auren da muke son aji labarin shi a gari zakace haka auren ka ne fa na
farko yaya muka gaskiya zamu cashe sosai ne wallahi.
Sadauki ya mike zaune tare da jawo kulan abinci a gaban shi yace ka bari karfe
biyar sai na ganka ba shi ke nan ba.
Yana cin abinci yana tunanen rainin wayyo irin nawa common abinci da zan kawo mai
wai bazan iya ba sai na bayar akawo mai.
Kuma yasan da wani manufa maji tace ni na kawo mai abincin da kaina.
Yai tsuki tare da fadi a fili yar kauyen banza kawai wai a haka zan zauna da ita
kuma.
Kiran wayan maji yayi tace maji yaron da kika ba abinci ya kawo min bai kawo min
ruwun sha ba fa.
Tace yaro kuma ba Fatima nace ta kawo maka ba yace ni Abdul ne ya kawo min abinci
yanzu.
Murmushi mama tayi tace kai Fatima wanan kunyane wai ko tsoro har yanzu ?
Kaga abinda nake fada maka gashi ka saka tsoron ka a ranta tun yanzu yaushe zata
sake dakai kana mata mugun ta haka.
Tana gama waya ta nufi dakin mu ina kwance na kifa cikina a saman filo naji tana
fadin Fatima yayan ku yace baki kai mai ruwan sha ba fa.
Kara faduwan gaba naji na dai ansa a fili da to mama ina mikewa zaune kamar da
gaske.
Har tajuya tace ki tabbatar kece kika kai mai ruwan da kanki don in akwai maganan
da zakuyi kafin ki tafi kan bukin ki sani.
Kunya ya kamani na sanin da mama tayi bani ce nakai mai abinci ba kamar yadda ta
umurce ni.
Dogon hijjab dina na saka tare da daukan ruwa a jug na nufi dakin sai faduwa
gabana ke yi a lokacin don nasan cewa zan samo wani sabon bacin rai ke nan kuma
again.
Dan sallama na tsaya daga kofan dakin inayi cikin yar muryana yagane nice sarai
sai yaki karbawa.
Na kara dan daga murya da sallaman naji yace please kada ki cika min kunne da
wanan muryan naki kamar na munafukai don Allah.
Jin haka na sa kai cikin dakin yana kwace rigigin gine daga shi sai dan wando
three quarter a jikin shi da yar singileti.
Na kai ruwan inda naga kayan abincin farko suke na aje tare da juyawa zan fita
daga daki.
Naji yace manya kawai watau sai da kika nace sai kin aure ni ko don bakin jaraban
ki da nacin tsiya.
To ki saurara sai ki shirya zama da U F don baki san koni wane ba da baki yarda
da wanan bakin hadin auren ba.
Murmushi nayi nace niko nasan ko waye mijina fiye da kowa don ni san akwai aiki
ja a gabana na sharan amai da fitsri irin ta mashaya.
What ya yunkuro kafin na karasa fita ya cafko hijjab dina ta baya sai naji gaban
ya shake ni sosai, na sa kara da dan karfi ya karasa riko min kai tare da rufe min
baki yana fadin .
Ashe ke yar karamar yar iska ce tukun may zaisa ki gudu tunda kin isa nine mai
amai da fitsari ko?
Nace baka taba min bane karya nai maka idan ka manta aini ban manta da hakan ba,
kaga nafi kowa sanin halinka ke nan.
Yanzu abinda yarage min na goge na kwashe idan kuma nayi arziki baka hada min da
kashi ba ai na gode Allah.
Wani irin shaka da karfin shi yakai min sai da idanuwana suka fifito waje kwala
kwala kaman zan somay.
Yana fadin zaki ci uban ki kuwa inkince ke yar iska ce don zaki dan dani wahalan
ki a gidan.
Yace good haka ma nake so gara ki shiga shegiya na gasa maki kwakwa ga hannun ki,
kagin na wullakantaki na mayar dake karamar bazawara gidan nan.
Nace shine dama sauki na in har kai min haka da sauri ka ceci rayuwana don, zaman
kaddara dama kawai zanyi da kai.
Yakai wa kaina bugu da karfi sai da na gwauro da bango idona ya kawo hawaye nace
dama duk matar mashayi wanan ne sakamakon ta ai duka da zagi da cin zarafi banyi
mamakin haka ba don na shiryi taron irin wanan ddaga gare ka tun tuni.
Akan mama zan iya hakkuri da duk wani cin zarafin da zakai min matsawon hakan zai
mata dadi a ran ta.
Don nasan darajan mama nasan kimar mata a rayuwana kuma ban manta da irin
halarcin da tai min ba a baya.
Don haka kaga tunda wanan ne kadai hayan da take ganin zan iya saka mata da
alherin da tai, min ashirye nake da na rugumi duk wani kaddaran da zan tunkara a
gidan ka.
Fita min daga daki yar kauyen banza kawai mara tarbiya wace bata san komai ba sai
rashin kunya.
Nace nagode na gyara hijjab dina na fito daga dakin, idona taff da hawaye, sai
da na saita kaina na shiga cikin gida.
Dakin mu na koma na kwatan ina tunanen makomar wanan auren da ake shirin kullawa
a tsakanin mu a haka.
Ni dake fanin da safe zamu tafi sai gamu sai sha biyu da rabi na rana muka bar
sokoto zuwa kauyen mu.
Tare da rakiyan yan uwan mama da suka zo daga Niger state gurin buki sai kawaye
na muyi yan layin mune kuma school din mu daya dasu tun secondary school muke tare
dasu.
Mun samu gidan mu ya cika makil da yan uwa da abokan arziki, da suka zo gurin
buki nai matukar mamaki yadda na samu an gyara gidan mu a lokaci guda haka.
Dakin da zamu zauna an saka katifa maya guda biyu a cikin shi, nan muka sauka
bakin da muka zo dasu basu dade ba suka koma don akwai event din da za,ayi na matar
Ahmad gidan su suna son zuwa.
Sai bayan mun hutane nake jin wai mamana tana gari ta zo amma tana gidan su.
Da yamma aka sakani lalai kamar yadda al,ada yake a garin mu nan aka shiga
shagalin buki, sai abinci ake ta faman tukawa na farar shinkafa.
Muma munzo da kayan cima da abokaina zasuyi amfani dashi a garin don haka ba sha
wani wahala ba sosai.
Sai da safe naje gaida mahaifina yake ce min Fatima Bintu kinzo kin samu alherin
da mutanen arzikin nan sukai muna a gida nan ko?
Alhaji ya aiko daga can birni an gyara muna guri don