Advertisements
Chapter 79 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   79 / 92

234K to 237K   out of 275.8K words

ina zai tafi tare
muke zuwa yana nuna masu ni a matsayin matar shi.
Mutane da yawa suna cewa basu taba tsanmanin yai aure ba ma a rayuwan shi don
basu ji ba ana fadin zancen auren shi akasa ba.
Akwai wata hjy wai shi take so ranan da ta ganmu mun fito gurin wani shakatawa
sai da ta girgiza da ganin mu.
Nagane hakan a fuskanta tun da muka hadu gasu su uku hamshakai sai wani
shakiyancin duniya sukeyi wai su karuwai.
Bayan mun rabu dasu ne naso na tambaye shi ko su waye su amma sai kawai na basar
da zancen su.
Shi da kan shi naji taja tsaki yace rabu da mahaukaciya wai a haka sona takeyi
bata san ni ba irin shashan matasan nan bane masu kwadayin tsofin mata ba.
Ni yanzu ko budurwa bata gabana balle wata tsuhuwar kwama can na banza.
Har Lindan shi sai da muka hadu da ita a Dubai wai tazo tare da mahaufin ta wani
business nace tir da kafurci ta sa ni dan skirt dan mitsitsi iya cinyar ta kawai
duk komai nata a fili.
Ita kanta Linda ranan da ta ganni sai da ta girgiza sosai don yadda taga nai mata
kyau ga dress din jikina ya karbe ni nan tasan dole ne U F ya manta da wata Linda
can.
Tasan lalai yanzu Fatima ta sace zuciyar U F din ta don babu ta inda za a kwata
mu da ita gashi kuma addinin mu daya dashi gamu yan uwa kishi ya rufe ta taji kawai
tasakawa ranta hakkuri ga tunanen zai dawo gare ta wata rana.
Daga ita har mahaifinta da muka hadu wanda yasab soyayyan su da yaya sai da suka
bimu da wani irin kallo .
Mahaifin Linda yake tambayan wanan ce matar shi daya aura din linda tace ita ce
dadd.
Yace so young pretty how are you tare da mika min hannun shi na girgiza kaina
nace mashi dai yana lafiya tare da tambayan family din shi.
Yaji dadi yai murmushi yace sorry na manta addinin ku ya hana hakan nan ya
shiga muna murnan aure ya dafa yaya yana cewa kinga shi nan ki rike mijin ki da
kyau don mijin ki big man ne sosai yana cikin lokacin shi.
Dariya mukayi a tare har dan dimple dina ya dan lutsa kadan .
Linda taja tsuki tace ai dole ne UF ya rikice dadd a kan wanan karamar yarinyar
ji yadda ya mayar da ita kamar wata queen can .
Ta juya tabar gurin ya ce don't mind her she is jealous of you taga kin fita
komai baby ki rike mijin ki kinji yarinya.
Nai mashi godiya ya bani kyautan wasu irin mahaukatan kudi kamar bau san zafin su
ba.
A mota hanyan mu na dawowa ne na ciro kudin ina bawa yaya yace na may ye fa
nakine fa kece akabawa don haka kibar abinki gurin ki.
Tsaraba kan nasha shi gurin yaya don bai bari na kashe koda kwandala ba daga
cikin kyautan da nake samu.
Mun baro kasan mun dawo gida Nigeria don hutuna da ya kare ba don yaya yaso
yakare din ba don bai gama morewa ba can.
Sai da mukai kwana uku a Abuja san nan muka ahugo jirgi zuwa sokoto birnin shehu
cikin jin dadi da walwala muka iso gidan mu.
Nai mamaki kwarai yadda muka samu yan uwa sun cika muna gida gurin taron mu.
Anty maryam na ganina lokacin cikin ta ya tsufa sosai ya kara girma tazama wata
mama da ita.
Muka rugumay juna muna murna daganawan mu again ta sake ni tace wai ko Fatima don
Alkah kece haka kodai yaya yakaiki cikin injin ne please.
Na dan shafo cikin ta nace masha Allah ubangiji ya raba lafiya ya bamu mai
albarka.
Nan muka samu yan uwa sun cika falon sai faman sanu suke muna kowa kallon mamaki
yake min don ganin yadda gaba daya na sauya na koma,wata yar larabawa dani abu ga
dana,asalin buzaye.
Mun samu a girka abinci kala kala wanda nasan aikin maryam ce haka na.
Ban lura da Anty Amira a falon ba sai da naji yace mata haba sweet sister ba ko
gaisuwa ne ?
Sai lokacin na dago na dubi inda yake kallo tana zaune ta yi irin zaman dacta
saba yi ta dunkule saman kujera sai chatting takeyi abinta.
Ashe tun shigowan mu ta daga kai ta kalle mu taji wani abu ya tsaya mata arai
irin yadda gaba daya taga na koma wata matar manya ko diyar manya can dani sai
kamshi da annuri ke tashi gare ni.
Gani cikin wani irin dogon riga kore yaji duwatsu tun daga sama har kasan shi
hannayen rigan shara shara na yafa mayafin rigan a kaina ina rataye da jakka ja da
takalma mai duwatsu kamar na rigan.
Ga yan uwan su sai haba haba sukeyi dani mu kamar sunga wata basarkiya can daban.
Haushi ya kumay ta tace wai wanan Bintun kauyen ne yau ta murje ta zama haka da
ita kai kai maji why please maji taja wani dogon tsuki tamike tana fadin ita zata
tafi gida ke nan.
Nace a,a haba Anty Amira yanzun nan da shigowan mu hatta hausana ya sake ba
sakwatancin nan sosai a cikin shi .
Tace a,wulakance wani abun kuma zan tsaya nai maki bayan naga kun sauka lafiya ko
so kike na tsaye ina,fadanci a kanki kuma ?



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYABA MUN BARKI GA ALLAH YABI MUNA HAKKIN MU
AKAN KI,,,


Maganan yaya yai matukar tsaya min araina nace a raina wanan kuma matsalar Allah
yasan dalilin shi amma har yaushe ma mukai aure da za,a dinga damuna kan haihuwa
hakane wai ?
Ban fito ba ina dakina don abin yadan damay ni a raina sai nake jin ba dadi a
tare dani kawai.
Kira,an sheck Ahmad suluiman kano na saka a wayana shine yake tashi ina zaune ina
bi a hankali nai makari da gadona ta baya kadan.
Dakin yashigo yana saye da doguwar rigar jallabiya a jikin shi yake ce min lafiya
kike kuwa ?
Dan murmushi ne na kakaro a fuskana nace lafiyata kalau kawai dai sai naji nagaji
ne.
Yace ok ni zanje gida naga baba nakuma yiwa maji barka daga can don yar gaban
goshin ta ta haihu nasan tana can tana murna yau.
Nace ba dole ba duk wanda nashi yai ciki kuma ya sauka lafiya ai abin farin ciki
ne haka sosai.
Nace adawo lafiya yace baza,a sayo komai ba ko idan nafita ?
Nace yaya ai akwai komai nake gani adai dawo lafiya muna gaida su kafin na shigo
nima.
Koda yafita yaje gida bai samu komai ba sai bacin rai kawai don yasamu mama da
Baba suna jidali akan Ahmad.
Wai yana zuwa duk abinda aka sayawa mama yana koshewa yakai gidan shi shi da
matar shi mara kunya suci.
Yaya ya samu dakyat yaba Baba hakkuri sai cewa baba keyi idan saye yana da dadi
shi ya dinga saya suna amfani dashi mana can.
Aishi yace yaji yagani ita yake so ga Imirana nan da lalacewan shi da komai yana
fita yana samun nakan shi ai.
Amma shi sai darga da rikicin kayan mutane da yasawa ran shi yakeyi duk ya zubar
min da mutunci ga mutanen arzikina.
Shine yau zuwa gurin wanan gobe yana gurin wancan yana bakin roko da yaudaran
daya saka kan shi ciki.
Umma dake daki tace ai babu dan kwarai a gidan nan yanzu sai dan son ka don shine
mai abin hannun shi.
Dama Atika aike butulu ce baki da godiyan Allah yanzu in ma don abin hannun shi
ne ai tare dai dake muke cin komai ko ?
Yaya ya samu baba ya shiga dakin shi da kyata ya kwanta da murya yana bashi
hakkuri sai faman fada yakeyi.
Yana cewa nai nadama da zama da matan a rayuwana ni nasan iya tsawon rayuwan da
nayi suna,wahal dani suna cutar dani da sauran iyalina a gidan nan.
Bai dade ba gurin baba yafita zuwa gurin maji dake zaune falon ta duk abinda
akeyi sunaji ita d Amira.
Ya gaisa da ita tare da mata barkan haihuwan maryam tace ni wanan gidan fitinan
shi yana bani tsoro wallahi.
Kullun ba,a san an girma ba sai anyi jidali a tsakani kuma na rashin gaskiya.
Karo na farko maji taji yakira ta da mama yace mama hakkuri zakuyi kawai don kowa
da irin halin da ke gare shi dashi kuma ake zama da mutum.
Nan dai suka dan taba hira kan zancen yadda gidan ya koma yanzu yace shi zai tafi
don dare yayi a lokaci.
Ko da ya dawo ya samu nayi barci a lokacin ina kwance a dakin shi bai ta daniba
shima ya kwanta sai da dare dana falka nagan shi kwance yana barci.
Da Asuba yafita zuwa masallaci nikuma na koma part dina nai sallah na kara nadewa
a gado na nakoma barci don weekend ne yau.
Ya dawo daga masallacine ya samu wayan shi tana ringing a daki da sauri ya daga
wayan mamace a layin take kiran shi.
A ranshi yace lafiya kuwa maji take kirana da safe haka ?
Ya dauki kiran da,sauri yana sallama yana fadin maji lafiya dai ko ?
Tace lafiya lau babana na idar da sallah ne nace bari na kiraka naji yaya jiya ka
koma kafita da bacin rai a gidan.
Yace a ran shi Allah sarki maji ashe takwana tana tunanen shi ke nan tunda ta
kurashi da safe haka.
Yace lafiya na isa mama tace nima ina zaune ne ina addua akanku Allah ya kara
tsare min ku yabaku saukin rayuwa da haske ga,al,amarin ku.
Don na fahinci har yanzu su yaya basu san Allah ne mayin yadda yaso ba ga bayin
shi.
Ya saki ajiyan zuciya yace mama ki kwantar da hankalin ki ai tunda basu iya komai
damu muna kanana ba ko yanzun ma Allah bai basu sa,a .
Tace kaga kwanaki haka Alhaji sani yazo gidan nan yai min kaca kaca wai ni na
hanaka hurda da kowa a cikin yan uwa sai yan uwana dana matanka kawai yanzun ka
sani.
Don wai yaji labarin irin abin arzikin da kake tura masu a can kauyen su nan
kabarsu hakana.
Kai maji ni har yaushe ma nakewa iyayyen Fatima ma,wani abu mutanen da ma nake
matukar jin kunyan su sosai ban fako je ba tunda mukai aure.
Dasu da baba tsoho wallahi suna a raina ina son mu samu lokaci na ziyar ce su.
Baba tsohon da yake nufi mahaifin mama dake zaune a Niger state shi da sauran
iyalin shi noma ya mayar dasu can sun zama yan kasa yanzu ko.
Yace amma zan ga baba sani din sai asamu abinda akai mai bashi ke nan ba.
Mama tace kaifa baka da zuciya babana duk wanan abinda sukai maka shi da su yaya
maganan su fa daya ne
Yadan kwantar da murya yace maji kiyi hakkuri don Allah don kin ga akanki suke
sauke haushin su ko yaushe don haka zan masu yadda yake so a zauna lafiya.
A hankali mamatace Allah yai maka albarka ya baka ikon kyautata masu ko yaushe.
Yace amin maji tace ina fatima yace ta koma barci yau weekend bata fita tace yana
dakyau ta dan huta don nasan anjima kadan yau gidan maryam zasu dire.
Yace kaman ko kin sani mama aini dai yanzun nasan ni da samun kanta,sai sun gama
bukin nan kan.
Tace kaima ka sani tsakanin maryam da Fatima ai sai Allah yace da yake muna fukai
ne ba sun hade wa sister na kai su biyu.
Ba wani hadin kai halinta dai ne sai ita Amira tafita daban a cikin ku sai kace
diyar umma.
Dariya tabashi cewan da tayi sai kace diyar umma take yace itama dai zatai auren
ai ta huta da fadan kowa hakana.
Dadai yafi mata alheri taje kowa ma ya huta da bakin halin ta hakanan.
Suna gama wayan da mama sukai sallama kowa yana cikin farin ciki duk kan su.

****** ********* ******
Sai da nai barci na mai ista na tashi batare da ya tayar dani ba nata shi wanka
na fada nafito ne ina zaune ina shafa mai ya shigo dakin.
Shima yai wanka don a shirye yake a lokacin idanuwan shi a kaina yace ashe barcin
ba mai nisa bane inace ko sai biyu zaki tashi.
Nace cikin murmushi da yau anty maryam ta yankani ai tun fa safe take kirana a
waya.
Sai da na shirya duk yana zaune a bakin gadona yana dakilar wayan shi tsab na
gama nace mashi nashirya yaya.
Yadago kai yana kallona yace au yaune zakuyi bukin ke nan da sauri na,ware
idanuwana nace yau kuma yaya ?
Yace to wanan uban kwalliyan haka dana ga kinyi aina dauka zumudi zai sa kuyi
shagalin bukin ne yau ?
Yamike yana cewa ni dai yanzun nasan ba a da time dina sai dai yadda Allah yayi
dani kawai.
Nace haba dai yaya yanzun ne ma fa zan bar gida to eleven fa yanzu ake nema
kamata yayi ace ina gidan tun bakwai ai.
Eh tunda gaki ungwazoma ba sai kije bakwai kiwa jariri da uwar shi wanka ko.
Dariya nayi kawai nace tau ni fa ai yanzun komai zanji amma bazanyi fushi ba
tunda ina son abar ni na tafi.
Shi yajamu zuwa gidan ya sauke mu a kofan gidan ni da iya don maryam tana dakin
ta bata koma gida ba.
Uwar mijin ta daine tadawo gidan nasu da zama inda yake zaine na dan kalla tare
da gyara tsayin mayafina don gyale na saka yau nace sai mun dawo ke nan yace four
zan dawo na dauke ku fa.
Kaina na langabe nace haba yaya four fa inace ko sai magariba yace idan kika bata
min rai wallahi yanzun zaki shiga ki fito mu wuce nace da sauri iam sorry sir don
nasan karamin aikin shine hakan.
Ko don ya batawa maryam din rai na bude mota zanfita naji yace ban son fitina fa
da kowa kuyi lafiya a watse lafiya nace insha Allahu yaya.
Nafita ina cewa mun gode sai ka dawo yaja mota yanajin dadi komai kankantan abu
sai nayi godiya akan shi.
Ya furta a fili simple life .
Muna shiga gidan tun a kofa muke jin hayaniyan mutane yan uwan yaya bashar sun cika
gida sai surutu sukeyi.
Nai sallama iya tana bayana nagaidasu ina fadin to abani ruwan zafin ajuyo nai
mata wanka duk aka kwashe da dariya.
Inna dake gefe tana gasa jariri tace hai Fatima kwana nawa ance ma maye ga nama.
Daga daki maryam ke fadin ki koma ban so tunda bakiyi farin ciki da zuwan baby
naki ba sai yanzun ne zaki zowa mutane.
Na daga labulen daki tana zaune da cup din kunun kanwa a gaban ta sai zufa takeyi
tako ina nace bura uban nan wani abu ko sai haihuwa wallahi anty kece haka kace
kace cikin zafi.
Na zauna saman gado ina cewa wayyo Allah na wallahi duk na gaji sai kace nice na
haihu wallahi.
Ta kurba kunun tare da lumshe idon ta tace da waye ya haihun bake ba ni sunan nai
cikine kawai ai dan nakine.
Nace kada ki sa na gudu dashi fa yau gidan mu tace aida yayan ki ya tare maku a
gida kinko ga jiya da kyat inna ta samu yatafi ya kwanta ya barmu wai shi anan zai
kwana nace Allah yabaku maryam.
Ke da yaya wallahi kuna sha,anin ku harara ta kara watso min tace kunan daban ne
Bintu ?
Tace wai da sauri na manta ina gadon asibiti ma nace Bintu ance za,a balbalani
balle yanzu ina dakina zaune.
Wanan dan rikici halin shi sai shi wallahi yanzun ma cewa yayi wallahi idan nai
tsiya dani dake yanzun zamu shiga mu fito tace dako na hada shi da maji wallahi.
Nace kina hada shi da ita nabi mijina don ban son fadan nan dakike sa ana mashi
ko yaushe.
La la la Bintu ni kike fadawa haka yau kan yaya eh lalai kan mage yaji gishiri
kuwa.
Waya na jawo na fara dan dana nomba sai ko naji ya dauko yana fadin hello
na,shake muryana nace yaya love kaji anty maryam tana ce min Bintun daka hana ko.
Ya ko hau fada maryam wallahi zan zo na balbalaki tace iyye watau karana kika kai
ma ke nan lalai Bintu wai Fatima wuyan ki yai kauri ashe.
Nace sorry yaya ta gyara yanzu tace Fatima din kayi mata hakkuri tsuki yaja yace
mashiririta kawai kuka sani nace asauka lafiya na kashe wayan.
Tace yar iska ke dai kin kirashi da,wayyo kiji muryan shi kawai ba,wani kai
karana da kikayi.
Indai yayane wallahi naga take taken shi yarinyar har tausayi kike bani don nasan
baki da hutu.
Nace abu cikin duhu sirine ne tace kwarai kuwa nayarda sirine don nagani yanzu a
zahiri.
Sai lokacin Iyyan Rabi ta leko dakin tana gaida maryam din na tuna nace Allah
sarki iyya na manta fa kina waje kiyi hakkuri kinji.
Muna nan dakin sai hira mukeyi shigowan matan yaya Imirana dakin shine yasa muka
kwasa muka yo waje can sai ga wasu yan school din mu da suka kare da ita sun shigo.
Wasa wasa gida ya fara cika iya ta mike zuwa inda ake aiki takama masu aiki.
Shigowan matar yaya Ahmad tanbele ya tashi sai hira take muna ana kwasan dariya
wanda hiran nata duk kusan batsa take yi wai ita hira ke nan.
Sai ga Umma da mama sun shigo barka da wata kawar mama makwabciyar mu nan muka
shiga gaidasu sai dai yadda Jamila matar yaya Ahmed tayi masu banji dadi ba.
Don ta nuna rashin da,a sosai a gare su kamar bata san

79 / 92