Advertisements
Chapter 60 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   60 / 92

177K to 180K   out of 275.8K words

wani abu zai shigo daki ya fada min.
Sai dai a nawa bangaren ina hankalina a tashe yake don ina ganin bazan iya cika
alkawarin mama ba akan shi don a halin yanzu ban san wani rayuwa ma yake ciki ba
agidan sunan muna gida daya ne kawai dashi.
Satin mu uku da aure na gama komai gashi hutun mu ya kusa karewa zamu koma school
wani sati.
Sai ganin shi nayi dakin lokacin ina kwace na kifa cikina a saman gado ina
sauraren kira,a a wayana kaina babu dan kwali na daure gashi na da ribon ta baya ,
Ganin ya shi ya shigo yasani saurin lalabo dan kwalina na daura akaina kallona
kawai yayi ya basar kamar bai san may nakeyi ba.
Yace ke nazo na fada makine yau da dare zan koma gurin aikina don haka sai ki
fada min abinda kike bukata a sayo maki idan na fita.
Nace ni ban bukatar komai sai dai Monday mai zuwa zamu fara school insha Allahu.
Yace gashi ke baki iya mota ba balle na bar maki motana kiyi amfani dashi sai
kuma idan wani driver zan samo ya dinga kaiki.
Nace ai ko da kake daukata yar kauye ba wai doluwa nake ba yadda kake tunane don
ni mota kuma yanzu sai dai na koyawa wani tuki.
Fatan kawai yanzu Allah ya hore min yadda ya horewa kowa na samu nawa na kaina
insha Allahu.
Kallon mamaki take min kaman zaiyi magana sai kuma yai shiru kawai yafita daga
dakin.
Duk da nace komai akwai shi a gidan amma sai ga kaya niki niki maigadi ya shigo
dashi wanda kusan yan kayan lashe lashe ne a cikin kwalayen.
Sai da yai wanka yafito ina kitchen ina girka abincin dare ya zo bakin kitchen
din ya tsaya yake ce min zancen motan da mukayi dazun na binciki maryam ta fada min
ki gwane don kece ke jan ku zuwa school don haka ga motana nan zan bar maki ki fara
amfani da ita kafin na duba wanda ya dace a sayo maki.
Ni zan shiga gurin maji nai masu sallama kagin dare yayi min sai ji nayi nace ni
dawa zan zauna cikin wanan katon gidan haka.
Yace kedawa kikazo gidan nan dama baki san gidan yadda yake bane kika shigo kai
tsaye.
Shiru nayi nace to don Allah ko na roka kanina musa yazo ya zauna dani kafin ka
dawo.
Yace no kada ki fara min aanan tarkace inama laifin ki ce nace Amirah tazo ta
zauna dake har na dawo.
Nace amma kana gani ita anty zata yarda tazo gidan nan saboda ni kuwa ?
Gidan ki ne ko gida na Amira fa yar uwatace kada ki man ta da hakan don haka ki
barni da tsarina kawai.
Ya juya yafita na ce o Allah takawo ni gidan gwauna kaida sai dai obey the rules
kawai ba jin views din mutum.
Ya samu mama zaune falo tana zaman kadaici na rashin mu tare da ita bayan mun
gaisa take tambayan shi lafiya na yace ina lafiya kalau.
Tace da fatan dai ba wani matsalan komai a tsakanin ku ko?
Ya kai haba maji matsalan may kuma dai ni nama zo ne nai maku sallama yau zan
tafi Spain ne muna da wasan da zamu buga har agentina zan tafi ina ganin kuma zan
kwana biyu a can idan na tafi.
Da sauri mama tace ita matarka da,wa zata zauna tsawon wanan lokacin haka dake
fadi?
Yace da cewa nayi ko Amirah zata koma can har na,dawo, amma ita kuma naji tana
fadin wai ko za,a dauko mata kanin tane agida ?
Sai dai na kashe wanan magana don ban yarda da yan kauyen na su zo su zauna min
gida ba suyi min barna.
Kana da hankali kuwa yan kauye kan tunda ka dauko diyan su ai kashiga ganin su ke
nan a gidan ka.
Ina yaron kanin tane uwarsu daya kuma ba wani babba bane can fa shi yaron.
Kuma ma ita wanan malaciyar inba kwanciya ba may zata yi a gidan amma shi yaron
ko wani aike ne ko aiki ai zata iya saka shi yayi mata ko ?
Kada fa kace zaka hanata zumunci da yan uwanta, tun yanzu dan sune gatan ta.
Ya ce maji ba wai zan hanata zumunci dasu bane kawai gani nayi dauko yaron kaman
wani long process ne kuma yanzu.
Mama tace aa ka aje da zai kaita makaranta kuma don dazun maryam ke fada min wani
sati zasu fara school insha Allahu.
Yace mun gama wanan magana ko zanbar mata motana tayi amfani dashi don ashw
maryam ma ta koya mata mota ko.
Tace madallah ubangiji Allah yai maka albarka Allah ya baka zuria masu albarka da
zasu tausaya maka kaima.
Yace amin maji nan ya ciro kudi masu yawa ya bata yace ta rike a hannun ta idan
da bukatan wani abu a bayan shi sai ayi.
Yadda ya saba tafiya a gida ba tare da daukan kaya ba yauma haka yayi sai yar
bakar jakar tafiyan shi kawai ya rataya.
Ina zaune falo don na kasa zama daki kamar mai tsoro yafito ganina zaune a falo
tasa shi zama a falon shi ma yana waya ina ganin bashar ne don naji yana fadi ya
biya ta gida yazo da Amira kafin ya wuce.
Sai da ya gama waya ya miko min kudi yana fadin karbi na nan nakali kudin tare da
karba sai baice min komai ba.
Cikin karfin hali nace namay nene kuma yace ki rike a hannunki don amfani idan
kuma ma da wani matsala bashar yana gari sai ki nemashi.
Ni gaskiya kudin nan sunyi min yawa ban da abinda zanyi dasu haka dubu biyu ma
sun isheni saboda naga komai akwai a gidan ai.
Kallon mamaki yai min yace wanan kudin ne sukai maki yawa dubu darine fa kawai
idan kuna son sayen wani abin fa bana gari.
Nace ni dai sunyi min yawa don ban saba kashe kudi ba komai mamane take saya muna
na fadin cikin sanyin murya.
Ok sai ki aje a gurin ki idan na dawo sai na karba don ban saba alheri ba na
karba ni.
Bashar suka shigo da Amirah sai wani shan kamshi take kamar an sata zuwan dole ne
nake gani.
Amma tana ganin shi ta dan sake tana fadin yayana dazu shine kaje gida ina barci
baka sa atayar dani ba sai dana tashi maji ke fada min kazo wai yau zaka koma.
Yace Amira ai ina ce baki gidan ne ma a lokacin da dake zanyi magana yanzun dai
ga wanan nan zaki zauna min da ita har na dawo ba zan dade ba nake gani sosai sai
dai kuma yadda tafiyan ya kaya min dai idan naje.
Kudi yabata itama madu yawa yace ina tsan mani akwai komai da zakuyi amfani dashi
abinda babu dai ga Bashar sai ku tuntube shi kawai.
Bashar ya shigo ina gaishe shi yake fadin kaunata ashe yau wanan mayen ball din
zai koma ya bar min ke ai yayi arziki hutun ku ya kare da kafanshi kafan ki
wallahi.
Tsaki sadauki ya mashi yace dan Allah mu tafi ni ban iya shirmay ka da ka saba
kaji.
Sai naga na mike nima da suka mike kallo na yayi cikin yanayin da bazan fahinci
na maynene ba, sai suka fara tafiya daga ni har Amirah muna bayan su tafe.
Sheri bashar ke mashi wai ashe shine bakauye yana kira min kauyan ci murum zaiyi
tafiya mai nisa shine zaiwa matar shi wanan sallaman haka.
Yace kai dai kasani jarababen banza ni yanzu ma har ina tausayawa maryam da wanan
shegen jaraban naka da ka samo.
Yace ni matata ba irinka bane don chakwai muke abin mu ban kuntata mata bata
kuntata min kaine aka bari da jan ajin banza kawai.
Suna shiga mota muna masu Allah yakai lafiya ya bada sa,an tafiya.
Sai da suka bace muka shigo ciki mai gafi ya rufe get inda suma naga ya tsaya ya
basu wani abu.
Muna shiga ciki batai min magana ba naga tafara jan dan troler din ta ta nufi
dayan dakin dashi nace ,a a anty ba anan zamu zauna tarw bane.
Ta wani juyo a wulakance ta dube ni tace ina ko kin mata ni bani zama da kowa
daki dayane don ban son yawan takura.
Sai kawai taci gaba da tafiyan ta can kuma taja ta tsaya ta juyo duk ina tsaye
ina kallonta tace Bintu kada fa ki manta gidan dan uwana ne nan ina da right din
shiga duk inda naga dama batare da wani shamaki ba.
Kiyi hakkuri anty ni bada wani manufa nai magana ba gani nayi gidan nada girma mu
zauna daki daya kawai shi yafi.
Tace to ba zan zauna ba sai inda naga dama zan zauna kuma kada ki kara cewa zaki
min katsalandan ga al,amarina kinji na fada maki ko.
Ni dai nabita da kallon mamaki don ban san laifin da nai mata ba har muka koma
haka da ita kaman wasu makiya can.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKK8N WASU PLEASE,,,,


IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYABA,,,,


Shine ya shigo gidan kai tsaye yana saye a cikin kananan kaya farare cikin mutunci
musa da ya gane shi yake mashi sannun da zuwa .
Murna da yar tsalle Amira tayi sai a gaban sho tana fadin yayana ashe kana hanya
shine ban sani ba tun da,safe.
Yace common yanzu ba gashi kin sani ba what else ?
Har lokacin yana tsaye daga kofa yana rataye da yar jakar shi ta maza mai dogon
igiya da suke ratayawa,a,kafadar su.
A hankali na karaso garesu cikin tako daidai har na iso gare su jakar kafadan shi
na sa hannu ina cirowa daga kafadan shi tare da mashi sannu da dawowa cikin wata
murya sai ido ya bini dashi cikin shagala da kallo na.
Da kyat ya iya amsa min da hanya lafiya saboda hannu na da ya dan taba jikinshi
ya sakar mai da wani irin kasala lokaci guda.
Daga inda Amira take tsaye tare dashi sai kallon mamaki take binshi dashi a cikin
mamaki, can ta saki wani irin ajiyan zuciya jin haka yasa shi saurin juyowa gareta
daga shagalan da yayi ga kallona.
Tace yaya na ko shiga baka karasa yi ba mun barka tsaye a kofa tau matar gidan ce
wata barkatatta da ita can.
Ya saki ajiyan zuciya a hankali tare da lumshe idanuwan shi cikin wani yanayi
yana shafo fuskan shi da hannayen shi .
Cikin falon suka karaso tare dashi inda suka zauna akan kujerun dake falon gaba
dayan su har musa kani na dake tsaye daga gefe daya.
Drinks ne mai sanyi na jera a wani dan tiren silver mai ruwan golden da cups din
shi ture din tafiya nake zakace wai sallon jan aji nakeyi wanda ban san dalilin
kara shagalan da yakeyi ba haka.
A gaban su na girke tire din ina masu bisimillah tare samun dan guri daga gefe
daya na zauna na dan zamo daga kujera inda saboda dan dukawan da,nayi gaban rigana
ya baiyyana suran jikina a fili, da sauri ya lumshe idanuwan shi da sauke ajiyan
zuciya a hankali,
Cup din da na tsiyayawa abin sha na dauko na mika mashi ina fadin ga ruwa mai
sanyi yaya.
Yakarba ba tare da ya juyo gare ni ba nace abinci fa ko sai kai wanka ne zakaci
cikin wata irin yar siririyar murya da ban san ina da ita ba a lokacin.
Ya dan girgiza kan shi tare da kara lumshe idanuwan shi sai dai fuskan shi a
dauresuke mai yadda,na,saba ganin shi a koda yaushe.
Kamar da kyat ya iya furta cewa bari nai wanka idan na dawo daga sallah zanci
abincin kafin na kwanta.
Yana dan kurban drinks a hankali yana wani lumshe idanuwan shi abinda ya daurewa
Amira kai ke nan ta kasa fahintar yayan nata gaba daya.
Shi da kan shi yai masu bisimillah tare da cewa musa bissimila dauki mana may ma
sunan kane please
Musa ya bashi amsa cikin dan murmushi da fadin musa yace malam musa ke nan naga
kaman kai ustaza ne ko?
Musa dai murmushi yayi saboda ba sabawa sukayi ba bai sake jiki dashi tukun.
Dawowa nayi falon tare da dafa kan kujeran da yake zaune nace yaya ga ruwan wanka
can an hada maka magariba yana kusan towa.
Duk da yana mamakin ganin sauyi a tare dani amma sai yake daukan hakan a matsayin
wani sabon yaudara ne na ke kula mashi don naga Amira a gidan.
Amira bari na je nai wanka yace mata tare da kokarin mikewa tsaye daga falon zai
shige ciki.
Yana shiga daki mamaki ya kara kamashi ganin yadda dakin yasha gyara ga kamahi
ko ina yana tashi daga dakin.
Jiki a sabule mashi yadan bi ko ina na dakin da kallin mamaki gaba daya tarasa
may nene dalilin wanan sauyin da ya gani a gare ni lokaci guda haka amma zai natsu
ya fahinci may abin ke nufi ne wai.
Daga Amira ko maryam ko kuma dai akwai wani plain a kasa nake boyewa.
Haka ya shiga wanka zuciyar shi fam da tunane a cikin ta na tambayan kan shi may
ke faruwa ne haka akwai yaudaran da nake shiryawa a boye.
A lokacin na juya zuwa cikin dakina na bar falon da suke zaune sai da na
kwatanci ya shige bayi na budo turare a jikina, sun kai kala uku nafito falon
sautin takalman dake kafana, yasa Amira saurin dago kai tabi ni da idanuwan ta.
Sai ga kamshi yana taron hancinta a lokaci guda sai taji wa ni irin wani abu ya
tokare mata makoshin ta a lokaci daya.
Dakin yaya sadauki na nufa nai sa,a na samu ya shiga bathroom a lokacin cikin
sauri na bude wardrobe din kayan shi, na fito mai da doguwan jallabiya fara kal mai
laushi da,santsi jikin shi na bishi da turaren shi masu kamshi na fashe rigan, na
aje mai wani wando gaje daga cikin kayan shi dake wanke na tafito nabar dakin kafin
ya fito.
Yana fitowa kamshi ya daki hancin shi sai lokaci yaga komai da zai bukata na aje
mai a saman gadon shi ko.
Musa kaje kayi alwala na fadi tare da shigewa dakina na muka barta a falon zaune
ita kadai kamar manya.
Tana batun mikewa don ta gane nice silar a,watse a,barta a gurin zaune ita kadai
sai taji motsin kulle kofan dakin dan uwan nata.
Da fara,a a fuskan shi yake cewa Amira kina nan zaune ne bari na dawo mosque
nazo mu zauna ko ?
Tare da musa suka wuce zuwa sallah mukuma kowan mu ya,shige dakin shi a lokacin.
Wanka nayi na fito nai sallah tare da canza sutura a jikina irin da ya dace mace
taiwa na miji shiga dashi da dare tankar wace zata halartan wani bukin dinner can.
Dogon rigane mai hannu kamar ta shimi za,a iya ganin hammatan mace a fili daga
ciki sai zuwa kasan riga an matse shi an fitar da sharp din mace sosai wanda ko
wanene yaga wanan shiga sai ya yaba da shiga na daure gashina da ya sha gyara a
cikin dan kyallen riga mai kama da ribbon din daure kai.
Ba yaya saudauki ba har anty Amira da muke zama koyaushe a gida guda,
Ina fitowa falon wanda shigowan shi ke nan daga sallah nafito ina kamshi ina
fadin sannun ku da dawowa tun da nake da Anty Amura babu wanda yasan cewa na iya
wani yare sai yau din nan dana canza harshe da musa ina mashi yaren uban su wanda
nima da karfin hali na iyaren mutanen Niger din.
Kallo biyu suke min na mamaki kwalliya na da kuma jin canza harshen da nayi wanda
basu san ina da,wani yare a,harshe na ba sai yau din nan.
Inda yake zaune na nufa sai da,na kai zaune gefen hannun kujeran na fara
gaidashi tare da kara mashi sannu da zuwa .
Amirah ta cika fam tun zamana a gurin ta wani hade rai hankalina ya dauke ga
kallon tv gaba dayan mu duk wani film din action ake a lokacin.
Sai da aka gama gurin da ya dauke muna hankali na dan juyo gare shi cikin kwantar
da murya nake cewa abinci fa yaya.
Yace kin shirya daning din din ne nace mai eh tare da mikewa yace malam musa muje
muci abin ko.
Ko ba komai ni dai sai naji dadin yadda ya kula min da dan uwana batare da nuna
mai yadda nazata ba daga gare shi.
Sai da suka mike da musa yake cewa Amira taso mana sister ta wani bata rai tace
naga kaman ka fara mantawa danine ai yaya.
Kai haba Amira wani irin magana ke nan kuma yace mata kin taba ganin mutum ya
mata da dan uwan shi ne ?
Sai bayan sun zaunane nazo na fara zuba mai abincin sai wani faman lumshe
idanuwan shi yakeyi don kamshi da desire dake damun zuciyar shi.
Kujeran da yace itace nawa na zauna akai tare da dan zuba abinci kadan a plate
wanda zanci .
Bai wani ci abinci ba amma yasha fruits salad din dana zuba mai sosai da ruwan
kayan yajin da nai mashi drinks din hausa dashi.
Yana ci aka bugo mai waya nan hankalin shi ya dauke da hannu ya yafuto ni da
alamar nazo sai na zo inda yake ya daina waya yana ce min ki dauko liptop dina ki
dan dafa min kafin na kwanta zan sha.
Dakin shi na nufa naga liptop din gasu nan da yawa kala kala na dauko wani mai
steberry na nufi kitchen dashi.
Musa yana gamawa ya mike tare da komawa gurin tv yaci gaba da kallon shi.
A flask na zuba mai tare da daukan cup na nufi dakin shi da ruwan shayin zalla ba
madara a

60 / 92