Advertisements
Chapter 92 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   92 / 92

273K to 275.8K   out of 275.8K words

Allah miskaraziratin ne ba abinda ya gagari ubangiji sai kinyi
mamakin irin mijin da Allah zai kawo maki idan kin natsu.
Kafin tabani amsa wayan ta yai kara jin sunan wace ta kira da Raye yasa na gane
da Raiha take waya a lokacin.
Tambayan ta tayi tana ina tabata amsa da cewa gani nan gidan su madam ina shan
sanyin A C.
Tabata amsa da gata nan tafe tana gamawa yake ce mata kinga ni maganan ki bawai
ya karbu bane gareni fa kiyi tunane a kai ki gyara halaiyar ki Nafisa .
Mace fa dan guntun lokaci ke gareta tun anayi daku watarana masu neman naku gudu
za, suyi su koma ga
wasu yan matasan
Ta amsa a marairaice da tau naji yaya insha Allahu zanyi kamar yadda kace amma
zaka dinka min hijjabbai na fara sakawa ko?
Murmushi yayi yace gatanan yana nufin ni zata dinka maki ko guda nawa kike so
kaunata.
Nidai kawai ki natsu ki daina wanan halin please.
Shigowan Raiha ne yasa muka daina zancen suka gaisa da shi ya mike zuwa babban
falon shi na waje da yake taron baki a cikin sa yabar mu nan zaune a na cikin gida
da waya a hannun shi yanayi.
Nan muka fara hira dash nake tambayan Nuriya suke ce min wai tabi wani
saurayinta dan Ibo sun tafi lagos tare.
Banji dadi ba na kasa boye bacin raina nake cewa haba dai haba ace kuma mutum
yana hurda da harda wanda ba musulmi ba kuma ai abin yayi muni gaskiya.
Raiha tace madam kawai dai Allah ya gafarta muna zamuce don dai gaskiya nima
yanzu da hankali yafara zo min na gane hakan ba daidai bane.
Ni yanzu fatana kawai Allah ya kawo min miji wanda zai soni tsakani da Allah
wallahi ko yaya yake zan zauna dashi na natsu bakiga yadda al, amarina har yasakawa
iyayyena cutan hawan jini ba.
Tace to mazan ne yanzun sai a hankali wallahi na rasa wanda zaizo ma da tsigar so
na gaskiya bada bukata ba.
Nafisa tace maganan da muka gama ke nan da yayana kafin ki shigo abinda na fada
mai ke nan kema yanzu sai gashi kinzo dashi.
Tace wallahi muna son auren bawai bamu so bane to amma wazaka aura shine
matsalan.
Istigifar bai bar komai ba ku koma ga Allah kwana biyu kuga ikon Allah wallahi
bana jin dadin irin wanan rayuwan da kukeyi yanzu ya kamata ace kunyi wa kan ku
fadan hakan.
Shi yasa nake son ki madam wallahi kece kawai zan iya cewa a yanzu kina tsayawa
ki nusar da mutum hanyan alheri bayan kowa ido yakawo ya saka muna.
Ana jiran da garin Allah ya waye kai wani abin asha asakaka ga faifai a tallata
ka.
Yaya sadauki ne yashigo yana ce min sai ki shirya don muna da bakin da zasu duba
gurin da za, a gina kamfanin shimkafa a garin nan
Gashi sunce min ba, a hotel zasu sauka ba anan gidan zasuyi masauki don haka sai
ki samo wanda zasu yi aikin abinci idan kuma bayarwa zakiyi ai masu duka daya.
Kafin ma ya karasa zancen shi sai cewa Raiha tayi bagamu ba yaya aikin may mukeyi
dabaza mu yi ba mu.
Baiyi magana ba don na lura hankalinshi bai kwanta da al, amarin Raiha din ba
wanda shine bai fahince ta ba sauki kaine da ita sosai.
Amma shi yana ganin sune suke jefa yar uwarshi a cikin wanan mumunan harkan da
sukeyi tare.
Bai san tafi su zama shedaniya ba don ita ta hure fitillar ta sosai ma fiye dasu.
Mun jima dasu muna tatauna abinda ya dace muyi da wanda zamu saya na bukatun mu.
Har sai bayan sallah magariba suka tafi mukai sallah suna cewa idan an shirya na
kirasu.
Bayan yashigo gidane yake fada akan cewa may zaisa na yarje ma wa yan nan
mashiririta suyi mai aikin abincin bakin shi yaushe ma suka zauna balle su san
yadda ake girki su.
Nace haba yaya sai kace ba mata ba su gani kuma ga iyya a gurin ai zamu taimaka
masu da wani abin.
Yace da sauri No no kada ki soma cewa zakiyi aikin komai kin dai san yadda
condition din ki yake please kada ki fara ki taba komai idan ma bazasu iya ba sai a
kira wasu suyi final nace ballema insha Allahu zasu iya duk abinda suka lissafo
zasuyi din.
Bai kara magana ba haka muka bar zancen don yaga na aminta dasu sosai yasa ya
kyale badon yaso ba.
Izuwa yanzu alherin da sadauki yaiwa iyayyena bazan iya lisfoshi ba don muna waje
sun tafi sun sauke farali ga gyaran gida da abin sana, a da ya sayawa kowan su a
sanadiya na iyayyena da yan uwana sun fita a cikin talauci yanzu wanda hakkurina da
biyayyana ne yajawo muna wanan alherin haka.
H
Yan uwa dama yan garin mu sukan zo neman alheri a gurina wanda nakan yi masu shi
gwargwadon halina.
Lokacin zuwan bakin shi yayi bayan sati ya zagayo yabani kudi masu yawa akan
abubuwan bukatan su.
Ban masu kyata ba na ba kudi fiye da wanda za, a kashe sosai suma su karu daga
ciki suka shiga kasuwa saywn abubuwan bukata duk da wasu muna dasu a gida.
Ranan har anty maryam da Rukaiya sai da suka zo da mummy tare akai aikin komai
dasu na fita kunyan baki yadda ya dace sai da aka hada abinci kusan kala goma sha
biyu nau,i daban daban suka kara gyara katon falon muna na baki an saka kamshi da
komai a falon yadda ya dace ayi.
Bakin basu shigo gida ba sai misalin karfe uku na rana dirin motocin da mukajine
yasa muka gane cewa gidan mu ya dauki manyan baki yau don har dasu jiya da alaman
akwa wasu manyan kusa a cikin su ke nan.
Nan aka shiga fito da kayan ci dasha bayan wanda aka kai masu da farko wa
drivobin su.
Gida ya rude da hayaniya sai kai da komo su Anty Nafisa sukeyi a gurin ana yaba
aikin da sukayi.
Allah da ikon shi a wanan sanadin Allah ya hada su da masu son su a gurin sukai
wa yayan su magana kan ya basu kannen shi din nan yace yabasu.
Wasa wasa magana ya zama babba don ita Nafisa ta hadu da wani ustazune manager
din wani babban company dake garin Abuja.
Ita ko Raiha wani sojane babba wanda gwaunati ta turo shi as a security guard na
kasa ya kyasa mata.
Amira da mama tace tazo ta taya mu aiki tace ita ba yar aikin kowa bane ba inda
zata tafi nan mama ta ganta ta kyaleta.
Amma daga baya da taji sun ba da tukwaicin dubu dari biyar wa masu aiki sai kuma
ta shiga fada tana ganin laifina
Wai dama ni yar bakin cikine shiyasa na gaiyato yan iska su cika min gida shiyasa
ita bata tafi ba.
Karshe kuma sai ga zancen auren Nafisa da Raiha da taji Allah ya hadasu da wasu
manya sai dai ba yara bane su.
Nan kuma ta shiga zage zage kamar mahaukaciya wai ta yarda ni yar bakin cikine ta
karshe sosai don ban son ta da arziki nafi bukatan komai sai a gani a gurina kawai.

****** ********* ******
Bukin anty Amira ya taso sosai ba kama hannun yaro don haka muke ta zirga zirga
ba hutu don mu ke gudanar da komai akan bukin duk da gwatsale ni da takeyi tana
nuna bata bukatan saka hannuna acikin al, amarinta sam.
Hakan bai sa na daina duk wani abinda nake da niyar yi ba don ba don itace nakeyi
ba dama don Allah nakeyi da mijina da kuma mahaifan su.
Bata san ina da rana a gare ta ba sai da masu zuwa ganin dakin da za, a saka mata
kaya sukaje suka dawo da labari mara dadi don ashe a family house za, a aje ta.
Kuma ga dakunan ba wasu dakuna bane maigirma a jere suke ita da uwargidan ta
wace yar uwace ga mutumin da zata aura.
Da labarin yazo ba karamin tayar da hankalin ta tayi ba sosai nan ta tuburewa
mutane akan Ibrahim ya cuce ta don cewa yayi gida zai kama mata haya don may yazu
zaice a gidan su zai aje ta.
Sosai ta tayar da hankalinta akan bazatayi auren ba ta fasa hankalin mama yai
matukar tashi gashi an gama komai akan shirin buki ga yan uwa na nesa har sun fara
hallara a gurin bukin.
Kuka wiwi takeyi akan ita kan wallahi ta fasa sai dai akai wata ba ita ba don
bazata wanan gidan da ake bada labarin shi ba babu tsari.
Mama kuma da yan uwa sun kafe kan lalai sai anyi auren nan sai dai ta mutu idan
an kaita don bazata basu kunya ba.
Ganin matsalan yai yawa ga tashin hankali ga fuskan kowa idan ka duba ya sa na
tashi daga inda nake zaune lokacin cikina yai girma sosai wata bakwai saura kwana
goma nake.
Dakin da take na shiga na samay ta ta kifa kai ga filo ita kadai a cikin dakin
tayi buji buji da ita kanta duk a hargitse dashi.
Zama nayi bakin gadon don bazan iya tsayi tsaye ba a yadda nake lokacin don karfi
hali kawai nakeyi da kaina.
Duk da taji anshigo dakin bai sa ta dago daga yadda take a kwance ba cikin
yanayin tashin hankali.
Cikin yar siriryar murya nace Anty Amira ki tashi muyi magana musan mafita akan
wanan al, amarin don kuka ba shine mafita yanzu tunda kinga mama ta kafe akan sai
anyi auren nan ba fashi.
Jin muryana yasa ta dago kai a cikin fushi tace Bintu for god sake ki barni naji
da abinda ya damay ni please ke har wani taimako zaki iya yi min ?
Wani matsayi ke gare ki da har zaki dauka zaki iya taimaka min dashi a matsayinki
ko don kawai kinga kina auren dan uwana kina juya shi yadda kike so to ni ba shi
bane ko maji ki sani.
Murmushi nayi kawai nasan ban taba fari a gurin ta amma ni don Allah kawai nai
niyar taimaka mata.
Nace a fili ba matsala anty ni don Allah nazo gurin ki don mu san mafita kawai
idan kina da lokaci ki tashi muyi magana dake mu san abinyi tun ba, a kai maki
kayan ki ba a wancan gidan yawan.
Wani kallo ta watso min kafin tace ina sauraren ki nace nagode naci gaba da
fadin nasan bawai baki son Ibrahim bane a yadda nasan kun dade tare dashi kuna
soyayya.
Kawai dai wanan matsalace ta gurin zama yasaki bacin rai irin haka sai nake gani
idan yace zai canza maki gurin zama duk wanan matsalan zai iya wuce a tsakanin ku
tunda soyayya ce ta hada ku ba kiyayya ba.
May kike fadi mutumin da ya kafe akan shi baida kudin da zai karasa ginan shi
kuma baida wanda zai iya kama min hayan irin gidan da nake so a yanzu.
Nace insha Allahu anty idan don gurin zamane na rokeki Allah ki kwantar da
hankalinki ayi wanan bukin cikin farinciki.
Yadda kowa yazo lafiya don farin ciki ya koma gida da farinciki a ranshi anty
baku gaji yin kunya ba a rayuwan ku balle kuji kunya don Allah ni dai yanzu abinda
nake so shine ki kwantar da hankalinki ki koma kamar babu abinda ya faru a baya don
marasa da suyi kunya don yanzu kinga ido aka sakawa mama aga yaya zata kaya ana
farin ciki zaki shiga gida mai kuntatawa.
Wani kallone takara watso min tare da cewa wanan shine dama maganan da zaki fada
min din.
Nace eh anty don Allah tunda kuna son juna da Ibrahim kiyi hakkuri ki daure ayi
wanan abin cikin rufin asiri insha Allahu bazaki zauna a wanan gidan ba.
Tsuki taja tare da marya da kanta a saman filo tace na zaci wani shawaran arziki
kikazo min dashi har na bata lokacina a kanki haka.
Na dade a zaune ba tare da tajuyo gare ni ba ga wayan ta dake ta verviration taki
dagawa.
Wanda nasan ba kowane ke kiranta ba a lokacin sai angwan ta wanda yake a cikin
tashin hankalin kan cewan da tayi bazatayi auren ba ta fasa.
Nagaji da zama ina batun tashi anty maryam ta shigo dakin kallon mamaki tai min
ganina da tayi a zaune ga maidakin ma kamar bata san ina zaune a gurin ba.
Tace ke kuma may kikeyi anan ina can ina neman ki mama tace wai wanan kayan
kitchen din da aka fitar a mayar dasu a kwali tunda babu inda za, a saka su a
gidan.
Tajuyo cikin zafin rai daga inda take a kwance idanuwan ta sunyi ja jajir dasu
don kukan da tasha sosai.
Tace sai naga iban da akewa shirin auren da har ake maganan rage wasu kayan daki
can akai badai ni ba.
Nikan da kyat na mike tsaye muka fita maryam tana mata dariyar mumuke muka fice.
A gajiye na bar gidan don dare yayi a lokacin yaya Sagir ne ya kaimu gida da kan
shi don ban driving saboda matsalan cikin dake jikina.
Sai da nai wanka nafito falo na samu Iyya tana gyaran abin da zamu karya dashi
tana kwaba abin da zatai muna sanasir dashi.
Ina zama ana kirana ga waya yaya sadauki ne wanda bai ma kasan yai tafiya a
lokacin.
Mun gaisa yake tambayana ko mun dawo gida ko muna can gidan su mama har
lokacin .
Nace mun dawo tun dazun har munyi wanka gani a falo ma zaune zan sha magani na
kwanta.
Yace maji ta kirani tana fada min iskancin da wanan mara hankalin kewa mutane tun
jiya wai ta fasa auren ko ?
Nace yaya bafa fasawa tayi ba kune dai baku fahince ta ba bawai bata son Ibrahim
bane a, a gidan da za, a kaita ne bai bata ba don a cikin family house din su ne
inda uwargidan shi take zaune.
Kaga kasan halin anty Amira da tsandan mutane bata son yawan hayani ita tafi son
ta zauna koda yaushe silent bata son yawan hayaniya.
Ya karba kafin naci gaba da fadin don taita mugun hali ko?
Nace haba yaya ya kamata a taimakawa anty please bai kamata abar rayuwan ta a
haka ba don Allah.
Yace ok yanzi so kike nima na biyewa haukan ta nace a fasa auren taita zaman gida
ko?
Nace ba nufina ke nan ba yaya abinda nike nufi shine ka taimaka da baiwan da
Allah yai ma na falala ka sama mata inda zata zauna don wanan auren nata yai karko
kamar na kowa please ?
Ban fahince ki ba Fatima kima nifin nine zan bada gurin da Amira zata zauna da
mijin ta ko may ?
Nace ai ba mijin ka zakaiwa ba yar uwar haihuwan ka zaka taimaka kamar yadda
Allah ya taimake ka kaima ka sama mata gurin zama yadda take so.
Don yin haka kawai shine shedan dan uwata ya samu kuma mai taimako ne ga jinin
shi don kaga ba Amira ba kawai wallahi har mama hankalinta a tashe yake akan wanan
magana daurewa kawai mama keyi don ta bata karfin gwiwa amma ran mama baiyi dadi ba
ace a wanan gidan za, a kai Amira gaskiya.
Yanzun dai na fahince ki yace nine zan aurar da ita kuma na bata gurin da zata
zauna kamar na matsu da ita a gida ko ?
Nace wallahi yaya ba haka nake nufi ba ni nufi na shine kawai ka taimakawa
rayuwan su tunda Allah ya hore ma abinda zaka iya yin haka din.
Idan kai haka ba karamin lada zaka samu ba har a gurin Allah don shine shedar
zumunci yanzun fa kaine uwar mu kaine uban mu gaba dayan mu har kai.
Amira ba ko Nafisa ce da irin wanan matsala din zaka iya taimaka mata idan kaso
saboda Allah.
Ji nayi ya katse layin tare da jan guntun tsoki haka yasa banji dadi ba a raina
nasan bai yarda da shawaran da nake gani shine a matsayin mafita ba ni.
Bayan mun gama waya nasha magani na mun dan taba hira da Iyya akan zencen tana
fadin ahi yasa ba, a son mutum ya faye bakin hali wallahi don karshen shi baya
kyau.
Yanzu ga irin ta nan ai tace ita tafi kowa bata ganin kowa da daraja kamar ba
mamace ta haife ta ba tafita daban a cikin yan uwa.
Nace Iyya kin san kowa da kalar halin shi ita nata rayuwan ke nan haka Allah yayi
ta daban.
Ai ba za, a biye mata ba idan ana son auren yai karko sai a taimaka mata anyiwa
banza ma balle ita.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

92 / 92