Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
da nayi tsaye na kwashi kayana zuwa cikin wardrobe
dina dasu.
Ina ajewa na juyo ban san yana tsaye a bayana ba sai ji nayi ya rike ni kawai na
dago idanuwa na da sukai ja don bacin rai nace may ye haka malam.
Oh tambaya ma kikeyi don na taba mata ta ko may ?
Zan wuce daga gefen shi sai naji ya kamoni yace ina zaki sai kin fada min may ye
wai matsalar ki ne a gidan nan.
Nace cikin kukan da ya kubce min kai yaya kai kaiyaya sadauki kaine matsalata
yaya.
Murmushi yayi ya jawo ni zuwa jikin shi duk kubce kubcen danakeyi sai saman gado
na ya dire ne.
Nan ya shiga kokarin cire min kayan dake jikina har yai nasara rabani dakayana.
Nan ya shiga sarafani yadda yake so raina yai matukar baci tankar da dutse yake
amfani a lokacin .
Har yagama abinda zaiyi ya koma gefe daya yana mayar da nufashi a hankali.
Kuka nake sosai don abinda ya aiwatar min a yanzu yai matukar bata min rai.
Nace cikin kuka abin yakai kuma har da fyede ka koma yi min kasani wallahi idan
ka zalunce ni sai Allah ya isar min.
Dagowa yayi da mamaki don bai taba jin makamancin wanan kalman ba a gare shi
yace.
Fatima nikike jawa Allah ya isa don na taba ki kawai ko may ?
Nace bayan na dan daga ina kallon shi da idanuwa da sukai ja nace kai bakaji
kunyan tabani ba kana cikin rashin tsarki?
Nine banda tsarki Fatima nace ina kaga tsarki mutumin da ya mayar da sabon Allah
abin yin shi.
Mutumin da bai tsoron haduwan shi da Allah cikin ko wani irin halin zai riske shi
ko a maye ko a kalau.
Mutumin da baida mu da halinda na tare dashi suke ciki ba akan mugun halinda yasa
wa kan shi don son zuciya.
Ni wallahi yanzun ko da ake cewa wai yimaka akayi kake halin nan ban yarda ba har
da hali ma.
Ka cuce ni wallahi daka kusance ni a cikin rashin tsarkin zuciyan ka wama yasani
ko ka shawo ne kazo min a haka tunda ba imani ke gare ku ba.
Idan kace wanan halin baza ka daina ba nima wallahi bazan iya zama da mashayi ba
tubur na haifi diya ana masu gori na fita gidan buki ana zunde na nashiga mutane
ana nunani.
Kuma wallahi,,,,
Ke ya ishe ki hakana nagaji da jin mugun kalamin ki a kaina haka na ko don kinga na
damu dake ne zaki tsaya kina fada min magana son ranki.
Damuwa damuwa fakace yaya da kadamu dani dabakai haka ba wallahi dakaso abinda
nake so maka a ranka.
Ni dana damu dakai aina fahinci abinda kake so da wanda baka so kuma na kiyayye su
don azauna lafiya.
Yadda kake ganin an tursasa maka aurena wallahi nima haka aka tursasa min auren
ka badon ina so ba.
Amma nai hakkuri na zauna ina maka addua a kullun na Allah ya shiryaka kamar
yadda mahaifan ka suke maka a kullun.
Amma kassh kai yaya baka sawa ranka daina wanan halin mayen ba kaduba fa yadda
kainan ka Nafisa maye ya mayar da rayuwan ta.
Idan badon Allah ya nufa mamatana tsaye da addua ba akan ka da yanzun ka fita
lalacewa a hakan.
Nikan gaskiya ba zan zauna da dan maye ba don idan akwai abinda na tsana shine
maye a rayuwana amma kuma ina kaddara ta riga fata yau gani Allah ya nufe da mai
shaye shayen da baida ranan barin shi a rayuwan shi.
Yana sauraren maganan da nake fadi sai dai baiyi magana ba har lokacin karshe ji
nayi barci ya dauke shi.
Har na mike na shiga bathroom nai wanka nafito nai nafila na zauna ina kara kai
kukana ga Allah akan al,amarin nashi.
Nagaji na taso daga inda nake na kwanta daga gefen gadon nan nima barci ya dauke
ni ban sani ba ina cikin tunane.
Da safe ko da na falka na samu yafita daga dakin bai kuma tadani ba don ganin da
yayi ina barci a lokacin saboda yasan ban samu barci ba a daren jiya din.
Bayan na sallah na kimtsa jikina na shiga kitchen na hada abin karyawa na jera su
atable na shige daki abina na kwanta.
Har ya gama abinda yake ba alama na a falon haka yasa shi leka dakin kwance nake
rub da ciki kamar mai barci sai dai yasan ba barci nakeyi ba a lokacin.
Daga kofa yake ce min shi zai fita sai yadawo ban dago ba kuma banyi magana ba
haka yasake labule yafice daga gidan.
Jin fitan shi yasani fitowa daga daki na gyara ko ina nagidan tsab na dora muna
abincin rana again.
Bai shigo ba sai bayan la,asar naji shigowan shi ya shige dakin shi ina zaune ya
shigo cikin shirin shi yana cewa ni zan tafi ga wanan ki rike a gannun ki sai
badawo.
Da kyat na iya bude bakina nai mashi adawo lafiya yafita daga gidan ranan ban
rakashi ba yadda na saba yi mai wanan abin ya kara bata mai rai.
Sai washe garine yaya Bashar suka zo gidan da maryam mun gaisa da su muna zaune
tana min sheri wai na kore mata yaya a gari saboda halina.
Idona ya kawo kwalla nace cikin wata murya ta mai kararen zuciya haba anty don
kawai baison a fada mashi gaskiya kawai.
Muryan bashar ne yake cewa Fatima kiyi hakkuri shi kan shi yasan bai kyauta maki
ba kuma yaji nauyi da kunya da ya sani.
Hakan da kikai mai kin kyauta gara da kika rufe idon ki kikanuna mashi abinda yayi
ba alheri bane.
Don idan mutum yana aikata barna a doron kasa bai samu wanda zai rufe ido ya fada
mai gaskiya ba komai dacin shi sunan wanan mutum din tabbabe wallahi don baida
ranan daina a rayuwan shi.
Amma kuma ke kuma kin tauye shi da yawa Fatima kin hana mashi hakkin shi bayan
kin saba farauta mashi.
Kunyan maganan shi naji na saddada kaina akasa yace gaskiya kin hora min abokina
wallahi.
Yace ko yar kwaliyan da kike mai da taro haba haba duk kin daina yi mashi su haba
Fatima adai dan sasauta mashi mana.
Maryam tai tsagal tace akan may zatai mashi tunda shi baisan ciwon kan shi ba har
yanzu ba gara ta kama kan ta ba.
Yace to gama dama ai yace shawaran ku daya da ita kece coordinater din ta.
Dariya mukayi nace babu ruwan anty kada yaga laifin ta a banza bataci batasha ba
halin shi daine bai min ba yaya.
Yace to kiyi hakkuri Fatima tinda dashi Allah ya hada ki zama nifa ina ji ajikina
insha Allahu zai daina nan gaba.
Tinda kinga yanzu yarage sosai inda dane ai abin ba dama wallahi don baku san irin
halin da na shiga dashi bane a baya kafin ya aure ki.
Amma aikinyi sa,a ma yana shayin ki yana tsoron yayi ki gane ko ranan ina ganin
akasi aka samu kawai.
Duk wanda yai mai asiri bai fasa ba mai shi yana kan yi har yanzu don dai suga ya
lalace kawai a rayuwan shi.
Maryam tace ina fa suka fasa kwanaki da nafisa tai shaye shayen ta ai ta fadi
amma aka mayar da abin haukan tane kawai yatashi take fadin hakan.
Bashar yace ai zan koma gur8n mutumin nan da muka taba zuwa don wallahi Alokacin
ya daina kwatakwata dawowa abin yayi.
Kuma zan fada maki wani sirin shi idan yana son sha zagiga idon shi sun rine
sunyi ja jajir dasu yana dafe kan shi yana dan murzawa to yana sin yasha ke nan.
Kuma ko a gidan yana da kayan maye har na shayin su da yake sa kina dafa mashi da
hannunki amma ke baki sani ba.
Nazaro ido nace wallahi ko duk dare yaya sai na dafa mashi bakin shayi mara sugar
da madara yasha.
Yace to sune yake sha yanzun dai kafin ya dawo insha Allahu zan koma kauyen nan
naji may ke ciki akan al,amarin don idan akwai wanda zaki bashi yaci batare da
yasani ba sai ki hada mai.
Nace nagode kwarai yaya yace kiyi hakkuri kinji ban son mama taji wanan zancen ko
kadan don kada ciwon ta ya tashi.
Nace nima shine wallahi amma badon mama ba ranan wallahi dana gudu gidan nan yaya.
Yace no no don Allah kada kije ko ina kefa haske ne a gare shi Fatima.
Zamaki tare da Sadauki wani falala ne ga kowa ga masu gadinku suna fada min irin
alherin da yake masu akan ki.
Idan kinyi haka mama bazata ji dadi ba masu hassada akan auren ku kuma zasuyi
farin ciki sosai.
Maryam tace ai bata ma zuwa ko ina mutu ka raba ita da yaya sadauki sai dai yan
bakin ciki su mutu.
Mun kai wani lokaci dasu suna bani shawaran yadda zan kara bullowa al,amarin.
Sukace zasu tafi don zasu shiga gaida Inna gidan ta a lokacin nai masu rakiya
har waje suka tafi yaya bashar yace yace akawo maki kayan abinci sai gobe za,a
shigo dasu don ina ganin zai dade a can ne.
Har ya shiga mota yake cewa kin ko kirashi kinji saukan shi na dukar da kaina ina
dariya yace don Allah ki kirashi nace mashi to kawai .
Amma bazan kiraba nace a cikin zuciyata indan yadamu yakirani in kuma bai kira ba
ajira har ranan da ya dawo din.
Jin za,a kawo min wasu kayan abinci na shiga kitchen na auna shinkafa da taliya don
tun na garan mu sunanan ba ai komai dasu ba na kira malam Atiku na bashi kowan su
leda guda guda da dubu uku uku na cefane akan Allah ya yaye mai wanan lurar tashi.
Suna ta godiya suka fice kowa yakai nashi gida don dama a bukace suke a lokacin
don abin sai shukaran kawai.
Na idar da sallah la,asar naji anata kwada sallama daga kofa nafito ina karba
sallah ma.
Na so sheda matar amma na manta ida na san ta a baya muka gaisa da ita cikin
sakin fuska take ce min baki gane ni ba ko hajiya ?
Nace na dai so na gane ki tace Allah sarki yanzu maji tai min waya wai nazo na
zauna dake don maigidan bayanan kuma tace ma zata bugo maki waya ai.
Nine Rabin dan musa uwar goyon sadauki a baya nace cikin sakin fuska Allah sarki
wallahi mama ban gane ki ba saudaya na taba ganin ki ranan da kika zo gaida mama
ina gida lokacin.
Na mike tare da amsan ledan bakon dake a hannun ta na shiga mata dashi dayan
dakin da anty Amira ke sauka a cikin shi.
Nace mata ga daki nan inda zaki zauna mama tana washe baki tace ai da ko nan kika
barni ma yayi min wallahi ko.
Nace kai haba dai nan a waje mama tace ina wajen yake nan na je na kawo mata
abincin mai yawa taci sai da ta koshi tana godiya.
Mun dayi hira sai da magariba ya gabato muka shiga daki don yin alwala da
sallah.
Da dare ma mun dan taba hira da ita take ta bani labarin irin zaman da akayi a
baya a gidan su sadauki yadda maji tasha wuyan su Umma da mama a baya.
Sai zuwa goma mukaiwa juna sai da safe kowa yanufi dakin shi ya kwanta.
Washegari kafin duk ince nafito na samu ta gyara gidan tas ta goge ko ina tai
wanke wanke nace bayan mun gaisa haba mama baki huta ba kuma wanan aikin haka tace
min haba to may yakawo ni gurin ki ba don na taimaka maki ba na zauna kuma ina
kallon ki haka uwar dakina.
Tun ranan itace mai gyara gida iyakata nai muna girki kawai wanda zamuci ko girkin
ma tace bata iya ba da abinda mukeyi sai da icce amma in koya mata don watarana.
Shine dalin idan zanyi girki muke shiga kitchen da ita tana kallon yadda nake
aiyuka na.
Yau satin shi daya da tafiya baikirani ba ban kirashi ba muna zaune a falo da Iya
take ce min wai ke yar nan ni banji kuna waya da maigidan ba mana.
Sai da na kakaro murmushi a fuskana don tambayan nata yazo min a bazata lokacin .
Narasa may zance mata sai nace cikin murmushi lah iya ai shi sai tsakandare yake
bugo waya kin san lokacin mu ba daya bane dasu can namuna rana sukuma suna dare ne.
Tace Allah sarki ni kan dai ince yaran yanzu baku wasa da waya da mazajen ku
shiyasa na tambaya ai.
Takara cewa ba dai dan nawa yana lafiya ba dai ko nace lafiya yake yana ma yawan
tambayan ki na ce mai kalau ki ke.
Tun da na fadawa Iya Rabi haka shikenan bata sake tambayana komai a kan shi ba
kuma.
Abu kamar wasa yau satin sadauki biyu rabon shi da gida amma ba waya daga gare
shi da farko abin bai damuna amma daga baya sai abin ya fara ci min rai kuma.
Mun shiga daki kenan munyi sallama da iya Rabi sai naji wayana yana ringing da
sauri na isa furin don na dauka murja ce wata course mate dina da muka dan shaku da
ita.
Nobar kasar waje ne daga US na dauka da sallama a bakina naji ya amsa sallaman
nawa cikin wani murya.
Sai kuma mukai shiru gaba dayan mu can yake cewa Fatima yanzun kan na sheda dole
akai maki a kaina don yadda kika nuna baki damu ba dani.
Nace dole dai akai muna da juna aikama kasan kabar mai gadi gidan ka baka damu
dani ba.
Hmm naji yace yace wanan kuma mafanan ki na rasa ke wata irin yarinyace haka mai
taurin kai dake.
Kina nufin idan munzuba ni dake waye zai sha wuya a cikin mu ne wai kefa mace ce
ba kowa ba.
Nace oh don ina mace shine akace ban san right dina ba ko komay ?
Idan kina ganin halin da kika dauko yi min zai sa na daina abinda kike ganin zan
daina sai ki matsayi ai gafili ga mai doki.
Nace ban ma son ka bari don ni ai nafison kabari don Allah da iyayyen ka da
zurian ka masu zuwa.
Yace oh ashe kin sani kik matsawa wa kanki nace ni ban matsawa kaina da komai ba
sai dai kawai ina tsoron mu,amulane da wanda baida tsoron Allah kawai.
Yace na gode nima haka nabashi amsa sai naji ya furzo iska yake cewa ance Rabin
dan musa na gurin ki ko ?
Nace oh iyaba tananan yanzun ma ta kwanta don muna tare yace ok ina son ki kula da
ita sosai don tana da mutunci sosai nace insha Allahu zanyi yadda kace.
Bashar ta kawo maki kayan abinci nace eh amma kasa akwai su dama kuma ka karo
wasu shiya sa na diba wanda muke dashi na ba su maigadin ka su ma yace ok haka yana
da kyau idan kuna da wani matsala dai bashar yana nan sai ki fada mai ko ma may ye.
Nace bamu da matsalan komai don iya tana da kirki matuka kuma tana debe min kewa
sosai a zaman kadaici.
Murmushi naji yadan yi yace akwaita da,son hira ai sai kingaji kintashi inda Rabi
ce.
Na katse shi da cewa ina fatan kana wa kanka adalci acan ka daina wanan shan
mugun abin mai bata maka tunanen ka akan komai.
Tsaki naji yaja yace yacd ai da kika damu da hakan da sai ki shigo jirgi ki gani
don gulma ko ?
Yace kin ga malama idan kikace zaki saka min ido haka arayuwa na wahala zakisha
wallahi.
Raina ya baci da kalamin shi nace dama ai zaman wahalan aka kawo ni yi don raina
yai ta baci a banza tunda ba fasawa zakayi ba kai.
Amma kin san ko ni waye kika yarda aka daura ni dake haka na ko don kin ga ban
maki yadda na kulla ba shine har kike jin dadin samun gurin ke ki cutata min ko ?
Naga idan ban kashe watan ba haka zamuyi sa insa dashi akan zancen yasani kashe
wayan dip na ji dul jikina ya mutu a lokaci guda.
Mikewa nayi na ahiga wanka na dauro alwala raina duk abace ina ta faman tune
watau shi wanan dai bazai daina halin nashi ba ke nan yake nufi tinda da anyi
zancen fitina yazo ke nan dashi.
Washe gari da safe yaya bashar ya samay mu da iya mun gaisa da yake iya mace mai
fahinta sai taba guri dashi.
Wasu kulin magani ya ciro daga aljihun shi ya kashe murya yana min bayani yadda
zan yi da maganin idan yadawo sosai nai mashi godiya da fatan Allah yasa mu dace
gare shi yace amin ya kara jadda mi na tabbatar da na zuba mashi fa yaci sosai
nace insha Allahu nai murna kwarai sai nake gani kamar har maganin yaci ko a
lokacin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA,BARKI GA ALLAH,ALLAH SHI ZAI KARBA
MIN HAKKINA A GARE KI ,,,,,
Saura yan kwanaki a fara azumin watan ramadan ko ina,kasa shen musulmai sai shirye
shiryen taron wanan wata mai alfarma da albarka dake tafe a,wanan lokacin aketayi
manya da yara da,tsofi duk farin ciki suke da wanan wata mai albarka .
Zan iya cewa rashi dawowan sadauki a cikin lokacin da nake gani kamar har za a
kama a azumi bai dawo ba garin a lokacin.
Babu wani abin da na rasa,a gidan daga na ci da,sha da sauran abubuwa amma kuma
sai na kasa gane may ke yawan haddasa min bacin rai haka na rasa ganewa.
Gidan baba sai abin arziki yake samu daga diya da sarakain shi da,abokan arziki
na gari.
Ba kunya mama take habaici wa baba wai gashi dan na shi bai kawo ba amma fa wa
yanda ba,a so sun kawo don sune ,ba,a so da alheri gashi Allah ya hore masu sin
kawo mashi ya karba yana washe baki .