Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
can ta yi sa,a har ta samu galaba a kaina, don nasan kowan wansu ba wai
ta zauna bane.
Duk yadda za,ayi gobe ki je min gurin nan ya kasance duk abinda ma taje garin su
ta kullo a lalata min shi baki daya.
Bintu bata tsaya ta karasa jin komai ba ta juya a hankali ta koma dak8n da take
ciki kwance,
Jin motsin mummy tayi don haka tamike zuwa dakin da Binta take kwance a ciki
tagani in itace take sauraren hiran ta,
Jin motsin mummy tafito daga dakin ta yasa Bintu lafewa tankar mai barcin da yai
nisa sosai.
Mummy ta,dan duba da kyautaga barci takeyi abinta hankali kwance,tai wani irin
sauke ajiyan zuciya tare da dafe goshin ta tana fadi Allah ya soni yau da kashina
ya bushe wallahi.
Komawa tayi taci gaba da wayan ta wanda babu wani abin arziki da take kullawa a
cikin wayan sai kishi irin na kishiyoyin lokaci.
Imani da tsoro duk sun rufe Bintu a lokaci daya na irin maganan da,taji mummy
tanayi a,waya akan uwar dakin ta, Maji ke nan.
Gaba daya kara tsanar gidan taji a ran ta kwata kwata babu mai imani da,tsoron
Allah kowa kan sa yasani yanzu.
Idabn da a hira wani kefada mata abubuwan da taji Mummy tana fadi akan Maji da
sai inda karfinta ya kare gurin karyata maishi.
Matar da duk gidan tafi nuna tausayin ta a kan Maj da yaranta yau kuma itace
take wanan sake maganan a bayan idon mutane don tsaban iya kisisina na,zamani.
Washegari haka Bintu ta,tashi ta kasa sake jikin ta,ga yunwan da ta kwana dashi
harsafe tare da,bacin rai na abinda taji mummy na fadi.
Ita ma dai yanzu gaba daya jin gidan takeyi duk yafita mata a,rai baki daya ba
wanda ta yarda dashi dan dama maman ta watau maji ke nan.
Don in ba kazafi zatai mata,ba,zata iya cewa tunda ta,zo zama dasu bataga wani
anin assha ba daga gurin maji har yaranta sai dai matsalan shaye shayen sadauki
shine kawai abin da zata ce tagani na assha a gurin su.
Bintu tafito daga daki inda ta samu mummy zaune ta gaida ita acikin ladabi da
biyayya.
Sai ta mike tana cewa cikin kwantar da murya zan tafi na gyarawa mama gurin ta
don ina,ganin yau zasu dawo.
Kallon mamaki Mummy take mata tace Bintu yaki nan zo zauna muyi magana ta fahinta
dake.
Komawa tayi ta zauna kamar yadda aka bukace ta da yi din.
Mummy sai da ta dan ja lokaci tace ba komai yasa na ce zanyi magana dake
ba,Bintu sai ganin ki yarinya mai saurin fahinta,da sanin ya kamata.
Ina,fatan maganan da zan gaya maki zaki fahince ni ba,tare da,wani manufa ba
a,ranki.
Murmushi Bintu tayiwa mummy kawai a lokacin sai da Mummy ta,dan yi shiru tace
gaskiya Bintu a dan zaman da nayi dake na fahinci cewa ke yarinya ce mai mutumci da
sanin yakamata.
Irin yarinyar da,na,dade ina gurin samu a,raina a gidan nan na rike ta.
Sai dai kuma,gashi kin zo min a ta,wani babban yanayi mai daure kai sosai, don
zaman da hajiya maijidda zai ita kawo min akasi akan bukatana.
Don haka nake neman hadin kai a gurin ki idan ta,dawo don Allah ki jajirce kice a
gurina na zaki ci gaba da zaman ki.
Kin daiga ni da ita,ba daya bane,don haka ki zabarwa kanki inda zaki zauna ki
samu karuwa iyayyen ki, su ma su samu ta gareki,
Don kinga ni kudi zan dinga baki duk karshen wata sabanin yadda maijidda ta aje
ki sai bauta mata kikeyi bata baki komai dake da gwagon ki.
Wani irin mumunan faduwan gaba ne ya daki zuciyar ta na wani dan lokaci inda
tsoro da firgici suka ziyarce ta
Kanta ta,dukar kasa inda mummy take cewa ke nake saurate fa,
Murya kasa kasa take cewa mummy ai da nan da can duk dayane ni a gareni. Don duk
mutunci ne ya hadani da kowan ku.
Ok tau yanzu zabi ya rage naki sai naji shawaran da kika yanke wa kan ki.
A cikin gatse tabata zuwa zabi don ta san bazata bar kudi ba da jin dadi ta koma
inda uwa tsugunne diya a kwance ba dole zata dawo nan gurin ta inda ga dadi ga
sutura masu kyau, ba second hand ba. Tasan dole ne ta dawo gare ta ma don ta kashe
mata zuciya ko.
Haka ta mike ta nufi part din Maji tana tafe tana nazarin maganan mummy matar da
a da take matukar ganin ta da daraja da sanin ya kamata tana tausayin uwar rikon ta
maji fiye da ma mijin da ya hadasu zama tare a gidan.
Haka ta shiga gurin na maji tana aiki tana tunanen irin rayuwan wanan zamanin
namu da muke cikin sa yanzu.
Har girki sai da taiwa maji tare da kamsashe masu ko ina na gidan.
Sai yamma Maji ta iso gidan da yaranta suna daukin ganin Bintu wace itama haka
da murna suka tari junan su cikin jin dadi tsakanin su.
Tun fitan da Bintu tayi part din mummy zuwa,taron su Maji bata kara leko part din
mummy din ba har zuwa dare takwas saura sosai.
Dan, ta mai bi ma na biyu ta tura wai a kira mata Bintu zata rufe part din ta.
Sai ga yaron ya shigo duk muka juya gurin shi inda ya nufo gurin da Bintu take
zaune direct yana cewa,
Mummy tace nace ki zo zamu rufe kofan part din mu dare yayi wai.
Kafin Bintu tai magana Amira ta,watso ma yaron wani fitinaneniyar harara yaron
ya,noke yana cewa mummy ce tace nazo na kirata ya juya yabar dakin zuwa,part din
su.
Muryan Maji sukaji tana cewa,a,a Fatima tashi kije ku kwanta ko har kin gudo ne
zaki mata halin yan duniya yau yau da dawowan mu.
Tashi ki dan tafi tunda ta aiko maki da sako bai kamata ace baki je ba kinji
diyata ta fadi cikin dan kwantar da,muryan ta.
Shima yaron ai iyayi tsiyane dashi mai makon ya tsaya tun can yai sallama shine
ya fado wa mutane daki haka.
Ai shi yaro dan auke ne baida laifi, an aiko shi kuma ya fada ya tafi a binshi
yanzu shawara ya rage namu.
Maji takara yiwa Bintu magana da ta tashi taje ai yaune kawai gobe ta dawo dakin
su.
A zuciyar ta take cewa Allah sarki Maji da kin san abinda ke nan da,baki barni na
tafi ba ko yau din nan ma.
Ita ko mummy tana can dakin ta saikallon kofa take a kai akai tagani ko Bintu
zata zo tabar Maji akan tayin da tai mata.
Zuwa can sai ga Bintu saye da,dan hijjabin ta tashigo gurin mummy a,bisa Umurnin
Maji.
Sai dai ita kuma mummy tana ganin ai tayi nasara saye zuciyar Bintu da abin
duniya shi yasa ta,dawo gareta.
Bintu na fita Amira tace maji da ma kin bar Bintu don naga bada son ranta ta
tafi ba wallahi.
Allah ko ai ban san bata son zuwa ba da ban tura ta dole ba amma kuma,sai naga
in munyi wa Kubura haka bamu kyauta,ba tunda har ta aikomata.
ko da,ta shigo falon Mummy tabita da kallo tare da,sauke ajiyan zuciya a fili,
har ta karaso tsakiyan falon nasu.
Mummy ke cewa k8n wa kanki kiyamallaini yarinya don ba mai son wahala yanzu.
Bintu da bata ce uffan ba tashige dakin da take kwana abinta tabar mommy da
yaranta suna kallo zaune a falo.
Tun shigan ta bata fito ba sai washe gari ta farka kafin kowa ya,fito tai ma
mummy duk aiki kamar yadda ta,saba yi a kullun tare da,dafa ma,yan makaranta
abinci.
Bada,sanin kowa ba ta kwashe yan kayanta zuwa dakin maji tunda farar safiya.
Koda Mummy ta tashiga gurin ta ta samay ta zaune sai cewa tayi kinga Bintu nasan
kina jin kunyar Maijidda ne ki barni da ita zan san yadda nayi da zancen ta.
Fitan mummy daga gidan Bintu ta kwashe sai part din Maji da farko taso ta boye
damuwarta amma sai su Amira suka fahinci da damuwa a tare da ita.
Da suka tambaye ta sai take cewa babu komai kanta ne kawai ke mata ciwo.
Sai zuwa rana kowa na sha,anin gaban shi Kubura ta dan fakaici ifon su ta kwashe
komai nata sai dan gidan gwagon ta ta bude ta shiga.
Shiga da fitan ta duk akan idon sadauki wanda yake zaune kofan dakin shi sai dai
furannin gurin sun boye shi ba za,a iya ganin shi ba.
Sai bayan fitan ta ne daga gidan shikuma yamike yabi bayan sai yaga gidan su ta
shiga.
Nan yakoma ya zauna a inda yake zaune cikin tunanen irin nasihan da yasha gurin
kamilin kakan shi dan matashin dattijo mai dan farin gemu a fuskan shi.
Kubura ta gyara ko ina tsab tunda dakin kwanan su har tsakar gidan nasu ita
kadai a gidan.
Sai da Maji taji shiru bata ga fitowan yar amanan ta ba ta ce Maryam ta diba
mata ita taga may takeyi.
Da sauri Maryam ta,dawo tana fadin Maji Bintu fa bata gidan nan nake gani.
Da sauri Maji tace kodai tana bandakine ki koma ki duba min mugani.
Aikuwa har bandakin ta duba ta kuma duba gurin kayan ta babu komai nata a gidan.
Da sauri ta dawo gurin Maji tana fada mata Maji har kayan Bintu babu a gidan nan
fa.
Hakali a tashe Maji ta mike zuwa dakin hajiya kubura sai dai a rufe dakin yake
shima.
Ikon Allah ta dawo dakinta nan ta samu yaran ta duk a cikin damuwa Maji tacewa
Amira jeki gidan mai masa ki duba min ita da sauri.
Shigowan sadauki yayi daidai da jan hijjab din Amira ganin yanayin su yasa shi
kalkon su cikin mamaki yana tambayan su may ya faru ne wai.
Bintu ce bami gani ba shine zan tafi na duba gidan su.
Ke zauna naga fitan ts tana cikin gidan su don nan naga tashiga dazun da rana.
A jiyan zuciya Maji ta sauke tare da cewa akwai matsala ke nan tunda yarinyar nan
tai muna haka.
Haba Maji wai may yasa kika damu da zancen wanan yarinyar ne haka bayan ita bata
damu da ku haka ba.
Kai ban son rashin mutunci Fatima a dan zaman da tayi damu ni nasan irin karuwar
da nasamu da zaman ta nan din.
To may akai mata da zata gudu bata fadawa mutane ba har zata kwashe tabar gida.
Nifa na ganta ban yarda da ita ba yasa na tashi na bi bayan ta amma sai naga ta
shiga gidan su.
Yanzun haka ma da zan dawo naga gidan a bude da alaman tana ciki har yanzu.
Amira maza jeki ki jiyo min ko may ke faruwa da ita har ta guje muna hakan nan.
Amira da maryam suka fita zuwa gidan hajiyan masa lokacin Bintu ta idar da sallah
tana zaune ita kadai ta hada kai da kujeran dakin gwagon ta inda tafi zama akoda
yaushe indan tana gidan.
Da sallama suka tura kofan shiga gidan inda tun a tsakar gida suka hango ta a
zaune.
Bintu na ganin su gaban ta ya fadi don in akwai abinda ta tsana shine ta koma
gidan su mai tarin rikici a cikin sa.
Maryam tun bata karaso ba take fadin haba Bintu may akai maki zaki tafo gida
batare da sanin kowa ba kin tayar wa Maji da hankali yau sosai wallahi.
In ba don yaya sadauki ba da ya shigo yana fadin yaga lokacin da kika dawo nan
gidan.
Amira tace Bintu nasan akwai abinda ya faru ki fada muna ba boyewa zakiyi ba a
ranki.
Don in har baki fadi ba ba,a san may yasamay ki ba balle asan ta inda za,a
bullowa maganan.
Maimakon Bintu tayi magana sai kawai ga hawaye sun fara zubo mata shar nan ta
fashe masu da kuka mai tsuma zuciya.
Duk yadda suka so tai magana Bintu taki fada masu komay ye matsalarta da har ta
guje su haka a lokaci guda.
Haka suka koma gida da sanyin gwiwa suna fada wa uwar su yadda suka yi da ita a
can.
Hakalin Maji yai matukar tashi si dai kuma gashi babu halin ta fita zuwa gidan
don maigidan yana kasuwa a lokacin.
Gashi kuma itace zatai girkin gidan ranan nan abu ya taru ya rikice mata akai.
Itako mummy tana can hankalinta a kwance, don tasan yanzu bata da matsala don
Bintu zatai mata komai kafin ta dawo gidan.
Sai yamma lis ta shigo tare da yaranta da takai suka sayo abubuwa a wani shago.
Ganin kofan ta a rufe yasa ta tunanen ko Bintu ta shiga gurin hajiya Maijidda ce
sai take fadi a ranta dole nasan yadda na hana wanan yarinyar shiga gurin matar
nan.
Sai dai tana shiga taga ko ina tsab an gyara amma babu alamar an dafa abinci a
part din.
Don haka tafito da kanta har kofan dakin Maji tana fadin hajiya ina ya ta tashiga
ban samay ta,ba a daki dana,dawo.
Tun lokacin Maji tadan fara tunanen duk yadda akayi akwai wata magana a kasa.
Maji tace hajiya ina yarda da fahinta yasa nabar wanan yarinya a gurin ki da
zanyi tafiya.
Eh haka ne amma kuma ai haka ba yana nufin yarinyar bata da yancin kanta da zata
zabi inda take ra,ayin zama bane ko?
Oho yanzun nagane inda matsala take ke nan ashe akwai abinda ke faruwa a gidan
nan bayan tafiya na ban sani ba.
Babu komai sai alheri inji hjy kubura tace kawai dai mun shirya da yarinyar zata
dinga min aiki ina biyan su, aikin san babu boyo a tsakani na dake.
Hmm tau Bintu dai bata gidan nan yanzun haka don ta kwashe kayan ta tabar gida
ta koma gidan su.
Kai amma ban zaci haka,ba daga gareki hajita maijidda.
Ban taba zaton zaki yi min bakin ciki ba irin haka yanzun don kada yarinyar ta
taimaka min kika kore ta a gidan nan.
Hmm ke ma kin san hakan ba halina,bane ra,ayin kantane takwashe batare da,sanin
kowa ba tabar gidan nan don kanta.
Ikon Allah inji Mummy kamar zatai magana sai kuma ta juya a fusace tabar gurin
zuwa part din ta ranta a bace wai Maji tai mata hassada.
Kai duniya kan yanzun ba gaskiya babu tsoron Allah a cikin ta,wai ita da za,aiwa
zargin rashin gaskiya amma itace ke ganin hakan akaimata.
Maji nashiga daki Maryam tace amma kuwa Bintu munafuka ce yanzun saboda kwadayin
duniya har ta uya yiwa mutane haka.
Amira tace aini tabani mamaki wallahi.yanzun ita tana ganin taiwa mutane wayo ke
nan ko.
Aitazo indai Mummy ce dan abu kadan zatai mata sai duniya taji su .
Matar da bata da,yarda ko kadan inba diyan taba ita batasan kowa ba aduniya shine
kwadai zaikaita gurin ta.
Maryam tace bataga daki yana kyalli ba kamar aljannan duniya dole ta gudu nan
inda ba komai ai.
Kai ya isa haka dan Allah kubari muga yatinyar muji may ke na kafi ku yanke
hukunci ku fara zaginta.
Da zata zauna da ita aida tun tuni tayarda da zugin da tai mata, ina jiya kince
da kuka taje kwana dakin dana tura ta.
Koma may nene duk nice najawa Bintu din haka don ni nakaita da hannu na cikin
rashin sani.
Maji dama aikin san mummy ba mutunci ne da ita ba don ita kanta kawai ta sani
amma wanan rashin gaskiyan haka ai ya zama cin fuska.
Da yamma da maigidan yadawo maji takai masa abinci lokacin ya tafi sallah sai
tadawo dakin har in ya huta ta samay shi akan ya bari ta shiga gurin Bintu taji may
ke faruwa.
Amma tana zuwa gurin maigidan saita samu hajiya kubura tana mayar mai da magana
akan karya da gaskiya.
Wai taimata bakin ciki akan yarinyar shine har ta koreta bayan tafita daga gidan.
Shigowan Maji ya sashi cewa madalla ga Maijiddan ai ta shigo ma dama yanzun nake
nufin kiran ki.
May ke faruwa ne akan yarinyar nan ta gurinki don hjy kubura ta samay ni da wani
magana sai dai ban fahinta,ba.
Murmushi maji tayi tace nima dai ban fahinci maganan ba sai takai zaune yayin da
mummy tacika ta batse da Maji din.
Nan ya kara tambayan ta ta fara fada mai tun farkon barin yarinyar da tayi a
gurin mummy da kuma yadda jiya akayi kafin ta tafi gurin ta ta kwanta kamar yadda
mummy ta bukata.
Maji tace ni a zatona ko don a jiyadin muka dawo yasata cewa tazo ta kwanta.
Sai yau tun safe yarinyar ke daki tana kuka dana tambaye ta take cewa wai kanta
ke ciwo.
Wallahi Alhaji dafa haka ban sani ba bayan nabata magani ashe ta faki idon mu ta
kwashe duk kayan ta a gidan nan ta sulale ta fita ba wanda ya sani.
Saidana tura yaran ban,suka ce tana gidan su dakin gwagon ta ita kadai a gidan.
Subbahanallahi yanzun dai ina yarinyar take tana gidan su ita kadai a gidan.
Yanzun nake batun na rokeka naje naji ko may ke faruwa da ita tai muna haka amma
kuma sai dazun ga hajita kubura tazo tana wani maganan da ban san dashi ba mani.
Yanzun dai ba,wanan ba ahin kun san hatsari ne abar yarinya karama kamar wanan
ita kadai cikin gida babu kowa a wanan zamanin da muke ciki.
Hakan yasa fa uwarta takawota gurinki don ki rike mata ita har lokacin da zata
dawo.
Don da kanta mai masa sai