Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
bashi yanzu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA MUN BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,,
A LOKACIN MUKE,,,,
Yau ya shirya unexpected ya samay ni daki bayan na dawo daga school yakw ce min
zaiyi tafiya ne zuwa Mexico gurin wani taron yar kwallo da za,ayi kuma yana cikin
wa yan da aka gaiytata su tafi taron.
Shiru nayi sai jin zuciyana kawai nayi ba dadi ban san har hakan ya fito a
fuskana ba saida naji yana fadin baki son in tafi ke nan don engine din ko?
Ban fahinci may yake nufi ba da gakan cikin mamaki na dago kaina nake tambayan
shi engine kuma ?
Yace eh mana ko karya nake yanzun ba kullun kike bukatan service ba na fahinci
may yake nufi yanzu don haka najuya baya ina fadin wallahi, ni kan Allah ya kiyayye
min abinda ake min a dole zaka wani ce can wai na saba ko nafiso indon tani ce
wallahi mu zauna a hakana mana aga wanda zai sha wahala cikin mu.
Jinayi ya rugumoni ta baya yana fadin anki a zauna hakan sallon kijewa maman ki
da kuka kice anki yi maki service kwana biyu kuma.
Allah dai ya kiyayye min wallahi kai wanan ya dama ni bai a gabana wallahi yace
to tsaya mugani idan bai gaban ki da gaske din.
Gudu naje yi amma na makara nan ya samu sa,a na ya shiga aika min da sallon sakon
shi.
A cikin mamakina sai gashi na zake nima yau ina mayar mashi da martani yadda yake
bukata.
Mun dauki tsawon lokaci a dakin muna abu guda har sai da magariba ya kusanto
sosai ya sarara min.
Rugomo ni yayi zuwa jikin shi tare da dan sinsinan wuya na yana fadin zan dauki
tsawon lokaci a wanan tafiyan da zan yi don haka ki kula min da kan ki please .
Lumshe idanuwa na nayi ina sai dai a fili cewa nayi Allah ya kai lafiya ya bada
sa,an tafiya.
Mun dauki lokaci ba wanda ya iya yi wa dan uwa magana a cikin mu sai can yadan
min peck goshina naga ya mike ya fita daga dakin.
Maimakon na tashi daga kwancin ga lokacin sallah yayi amma sai kawai na lumshe
idanuwa wani zurfafan tunane na shiga yi na yadda zan zauna kwana biyu bashi a
gidan.
Irin yadda muka dan saba da juna a yanzu dashi.
Da kyat na iya mikewa na shiga bathroom don nai wanka nai sallah don har lokaci
ya shige gashi takwasa zai tafi.
Ina idar da sallah namike da sauri na nufi dakin shi na samay shi tsaye yana
gyara aninin gaban rigar shi.
Jin nashigo yasa shi dan juyowa gare ni cikin sakin fuska yau yake ce min ai na
zata bazaki iya tasowo bane.
Karasowa nayi nake ce mashi mai za,a shirya mane wai?
Kinga ina tafiya da shirgine ni acan ina da kayan da nake amfani dasu ba sai na
tafi da wani abuba daga nan.
Miko min yar hand bag dina na rataya kawai natafi don bashar yace min gashi ya
taso zuwa kaini airport.
Na duka zan dauki jakar naji yana fadin wanan karon ma da Amira ke nan zaku zauna
ko?
Murmushi yake nayi na karaso gaban shi nace duk yadda kace haka za,ayi yace ok
zan fadawa maji ta turo ta idan nafita.
Ki dai dinga cin abinci ko zaki kara cikowa kafin na dawo nace idan haka bai maka
ba sai ka karani mana.
Murde bakina yayi yana fadin wanan bakin wai yaushe ne zai mutu da bakar magana
ne bari dai Allah ya dawo dani lafiya nasan maganin ki ai.
A tare muka fito falo dashi sai ga yaya Bashar ya shigo gidan nan muka gaisa
dashi yana tambayana yaya kwana biyu.
Dago kai yaya sadauki yayi yace min tau ni zan tafi ke nan sai na dawo Allah
yakai lafiya Allah ya sa ai nasara ga abinda akaje nema Allah ya tsare muna kai ya
dawo muna da kai lafiya.
Yaji dadi matuka da addu,ana yake ce amin nagode bashar yace bakani dadin auren
ba riba biyu mama tai maka ga kuma Fatima na sharto maka addua haka.
Dan bugo yakai ma bashar daga haka suka fita daga gidan ina tsaye rakube daga
kofan shigowa falon mu.
Sai da naga subar haraban gidan najuya na shigo gida zuciyana a cunkushe min,
fadawa nayi a saman kujera na dade zaune a guri, ina ta faman tunane kala kala ni
kadai can dai ganin dare ya soma namike tare da rufo kofan gidan don ban tsan mani
anty Amira zata shigo ba har wanan lokacin.
Ina shiga daki naji wayan na yana ringin da sauri na isa gurin, da wayan take shi
ya kirani na dauka a kasalance ina fadin Assalamu Alaikum.
Yace wa alaikis sallam baki barci bane Fatima nace yanzun dai nake shirin yi.
To may ya hanaki yin barcin har wanan lokaci sai nace a raina kaine mana ka
hanani a fili kuma sai naji yace nine ko?
Nace ni karatu na tsaya yi kawai shine ba makara don ina test da zamuyi satin nan
insha Allahu
Murmushi yayi yace to ki kwanta hakana ki huta don nasan kina da gajiya a tare
dake.
****** ********* ******
Ya sauka lafiya don yana isa Abuja da safe suka daga sai Mexico gurin taron su.
Yakira wayana kafin su tafi tana kashe ina cikin class ban samu magana da shi ba.
Yinin daya da sadauki yayi batare da Fatima haka yayi shi a cikin tunanen ta.
Sai a lokacin yake sanin cewa akwai wani babbban alamari a zaman ta kusa dashi ji
yake tankar itace jagoran duk wani farin cikin rayuwan shi a halin yanzu.
Bai samu lokacin kiran ta ba,sai da ya dawo masaukin shi a lokacin dare yayi a
can.
Yana kwance dakin shi saman gado tunane Fatima kawai ke cikin zuciyar shi har
zuwa wanan lokacin.
A nan ya fara tina abubuwan da sukai ta faruwa a tsakanin su abaya.
Irin yadda yake yawan mata tsanani da hattaran ta cikin gidan su yana daukan ta a
matsayin itace mai mashi gulma a gurin maji.
Sai yanzun ne yake gane cewa bata fadawa maji komai a gamay dashi sai dai nata
kokarin da takeyi gurin ganin cewa ta saka mai ido ya daina shaye shayen daya ke yi
kawai.
Wani irin bacin rai ne yaji sai yanzu yake gane cewa ashe son shi takeyi
da,alheri take hakan gare shi.
Yana jin ciwon irin abin da yai ta aikatawa yar mutane a baya a bisa gaskiyan ta.
Haka yasa yamike ya fara dan zagaye dakin a hankali yana zargin kanshi da aikata
abinda ba daidai ba akan Fatima din.
Lalai dole ne ya gyara tsakanin shi da Fatima yadda zata fahince shi ta yadda
zata daina mai kallon mugun da take mai koda yaushe.
Yace in har bai gyara tsajanin su ba baiyi wa kan su adalci ba don haka zasu
dinga zama suna samun matsala a tsakanin su ko yaushe.
Gurin tagan dakin ya koma tare da budewa yana shakan fresh ai dake fitowa daga
window.
Ya daga wayan shi da ke a hannun shi ya kira nomban Fatima bugon farko da,wayan
yayi sai da yaji wani iri a zuciyan shi .
Ina hanya zan dawo gida naji wayana na ringing, hakali na dauka na duba yaya
sadauki ne a layin.
A hankali cikin wani murya bayan nayi receive din call din nace hello yaya.
Ya dan rikice da jin muryana yana cewa Fatima kina inane haka naji dan hayaniya.
Nan dan ajiyan zuciya sai nace ina hanyane yaya nafito school zan koma gida ne
yanzu.
Sai nace kana lafiya yaya yaya gajiyan hanya da taro sai da yai wani lunshe idon
shi ya amsa da taro Alhamdullahi Fatima mun fara yau din nan.
Allah ya bada sa,a nace mashi ya amsa da amin fatima.
Yace kiyi tuki a hankali don nasan yanzu titi ya cika da motoci yamma yayi nace
mai insha Allahu.
Yace nakiraki ne naji muryan ki don na kira ki da safe wayan ki baya shiga.
Nace ina class alokacin na rufe wayana ne ya sake cewa gashi na kasa barci sai
naji muryan yar kauyen matata yaya zanyi da raina dole na kira ki naji ki don mu
nan yanzu daryayi sosai .
Nace shine kaki bari da safe ka kirani yace abinda ya dace ke nan nayi don na
kasa samun natsuwa rashin jinki .
Kwata kwata rashin jinki a tare dani ya hanani sukuni Fatima yaya zanyi dole ne
na kiraki ai.
Take zuciyana ya narke sai naji kamar na shige cikin wayan na isa inda yake din
naga kyakyawan suran mijina da nai missing.
Yaci gaba da cewa Fatima ina kewan bakar maganan ki ina kewan wanan fadan namu da
muka kwana bamuyi shi ba.
Murmushi nayi yace kin dauka ina wasa ne ko sai idan kinga nadawo maki don kawai
muyi shi zaki gane.
Nace a hankali ina murmushi haba yaya don fada kawai zaka dawo na rokeka kayi
hamkuri ka zauna har kagama abi da yakai ka.
Har nakai gida muna waya dashi inda na ke ce mai na iso gida sai da zanyi sallah
mukai sallama dashi yakashe wayan.
Wayan dake hannu na dan kalla na ce ikon Allah yau kuma mai ya samu yaya haka
ne ya sauya min gaba daya.
****** ********* ******
Yau kwana yaya uku da,tafiya amma Amira shiru batazo ba tun ina saka rai da zuwan
ta har nagaji na,fara fitar da rai ga zuwan ta gidan.
Yaya da yakirani ya tambaye ni Amira bata zo bane nake ce mai bata iso ba tukun.
Ranan Na dawo gida da yamma a gajiye neke a lokacin sai dai ina shigowa get din
gidan na hango motan anty Amira a kofan gidan namu.
Nashigo gidan da yar fara,a na a fuskana don ganin ta tazo tana zaune saman
kujera tayi daidai da ita sai waya take yi abin ta.
A sanyaye nai sallama ta dago kai ta kalleni a dan wullakace nace Anty sannu da
zuwa.
Hannu kawai ta daga min ba tare da ta amsa min ba taci gaba da wayan ta da
takeyi.
Ido nabi ga yadda ta kaca kaca da falon da yake a gyara tas kafin na wuce da
safe.
Ganun bata da niyan gama waya yasani na nufi daki na don rage kayan dake ajikina
a lokacin.
Sai d nai wanka nai sallah nafito falon har lokacin tana zaune a inda na samay ta
da farko.
Ina batun na zauna take cewa ke ina key din daki na yake na bude naga a rufe
yake.
Nace au yana gurina anty bari na dauko maki taja uban tsuki tana fadin don isa
da sa.un guri zaki kulle ma mutane daki wai ke ga matar gida ko.
Nace fita zanyi ai shiyasa na kulle ko ina na gidan kuma ma ban san kina tafe ba
yau ai.
Dalla Bintu ki dauko min key ni bani son yawan zuba haka kinji.
Kallon mamaki nake mata nace yau kuma nice mai zuba anty ki dai gyara maganan ki.
Au to abin har yakai kuma zaki min rashin kunyane Bintu ?
Wanan ba halina bane anty kinfikowa kuma sanin hakan don ban tabayiwa kowa rashin
kunya ba.
Kai ta gyada tare da kutawa ta dauki jakar ta bayan na bata key din ta wuce zuwa
ciki ran ta a bace.
Kitchen dama a rufe yake na dauki abincin dana aje zanci idan na dawo tunda
safe na shige daki da abina nace can nafito nasawa gidan key na shige abina na
kwanta.
Ban fito ba sai da safe na hada breakfast na bar gidan ko fitowa batayi ba tana
dakin ta kwance.
Bayan fita data gaji da barcin ta tafito ta zauna taci abincin da ta samu na aje
mata.
Inda taci anan tabar min kayan sai dana dawo na kwashe su na wanke na gyara
gurin.
Ban fito na girka na dare ba don a gajiye nake nashige kawai abina nai kwanciya
na kawai.
Amira tafito tasamu babu komai saman tabld din tai mamakin hakan ta nufi dakina
lokacin ina bathroom ban maji tana buga kofan ba har tagaji ta,wuce.
Tunda safe ina kitchen sai gata ta shigo daga kofa taja ta tsaya tace ke Bintu
wai may kike daukan kanki ne halan.
Nace namay kuma anty?
May ya hana jiya ki girka muna abinci da kika dawo ki ka barni da yunwa na kwana.
Nace kiyi hakkuri anty wallahi na gajine jiya sosai kuma ga yamma yayi dana dawo.
Eyye samun guri ke nan ke ashe har kinga gurin hutu ke nan to wallahi ki kama
kanki da ni.
Murmushi nayi kawai naci gaba da aiki har ta fara tafiya ta juyo ki girka abinci
dasu salma don sunce anan zasuyi breakfast yau.
Yadda tace haka nayi mata na sauri na fita yadda na dawo daga gajiya da yamma
haka na samu gidan sai da raina ya baci.
Ban fito ba haka nabar falon sai da safe na tashi na shiga gyaran gidan sai da
nai ko ina tas har bayin falo duk sun bata shi .
Sai na dora muna girkin rana ina tsaka da yine sai ga Anty tafito ta ce yau ma su
salma sunce a nan zasu wuni kiyi girki dasu.
Ina gama muna girkin na koma dakina na kwanta can na fara jin hayanin yan su har
da yan ihun su.
Nace yau kuma din nan wai may ke damun anty Amira haka tana son bata rayuwan ta.
Ki fito ki gaida su salma naji muryan Amira daga sama ina kwance na dago ina
kallon ta kawai.
Kamar bazan fito ba sai dai na mike na fito da fara,ana a fuskana nake ce masu
sannun ku da zuwa.
A lalace cikin kallon banza suka amsa min banji dadin haka ba amna na dake na dan
samu guri daga gefe na zauna.
Sai naji dayar na cewa wai ashe musty ya auro wata gajar matace can yar kauye da
ita.
Ke haba inji saura tace wallahi ko kada kiso ki ganta ga gida ga komai ya hada
amma ina ba matar gwadawa tsara don bakauya ce wallahi.
Sai Amira tace anyi biyu ke nan muma ga.unan da irin matsalan ai a gidan mu kin
san yan kauyen nan su iya bakin asiri su mallake miji.
Yanzu bari ki gani kwana biyu idan an aaruce shi zakiga ya fara wani bakin rawan
kafa bai jin kunyan kowa akan ta.
Nagane maganan ta shagube ne amma sai na dake suna sako min magana ina jin su.
Bai mata ba sai cewa tayi ke Bintu kwashe kayan nan ki girka muna indomie kubura
zataci tace.
Kallon mamaki nai mata may anty ta mayar danine yar aiki ko may wai ?
Ina gama kwashe kayan sai dana wanke su na,shiga daki in fito sai naga wace tace
wa Kubura dauke da cup din tambulan yaya da nake mashi amfani dashi tana shan
drinks a cikin.
Kamar na wuce sai na dawo nace anty da kun canza cups don wanan din na amdmfanin
yaya ne shi.
What Bintu may kike nufi lalai ma Bintu kin kai wuyan ki ya isa yanka ashe ?
To baza ,a mayar ba sai kiyi abinda zakiyi don an dauki cups din yaya ko sannu
mai yaya.
May kike gurin yaya din ke nace mata a daure mata mana mai miji kuwa.
O lalai naga alama tunda har kin fara bani ansa to baza a mayar ba din tunda daga
gidan ku kikazo da shi.
Nace may yai zafi haka anty harda giri da zagin gidan mu kuma haka ?
An zaga ko zaki ramane ki nuna min wuyanki yai kauri yanzu.
Nace bazan rama ba amma koda banzo dashi daga gidan mu ba nawane dai ke ma sai ki
jira naki.
Aiko sai saura sukacs iyye gorin aure kuma zaki mata Bintu don ke kin samu an
maki auren hadi ko ?
Nace au haka ta fada maku ashe idan yin hadi banza ne wasu suje ai masu mana
mugani.
Na bada amsa haka sai na juya zan wuce ji nayi an finciko ni ta baya sai kawai
naji mari kyauuu.
Cikin mamaki na dafe kumcina da ta mara nace anty abin har da duka kuma sai sauran
na fadi kyale ta please kada ta kulla maki shiri kin san su da sheri irin matan
nan.
Banyi magana ba na juya kawai idona tab da hawaye na,shigd daki ina mamakin wanan
irin cin zarafin da Amira tai min a gaban kawayen ta haka.
Kiran yaya sadauki ne yashigo min yake kirana na dauki wayan bayan na goge
fuskana.
Na amsa mashi sallama da sauri naji yace Fatima may ya samay ki ko baki da lafiya
ne.
Na daure nace may ka gani babu komai yace please nace may ke damun ki ne wai ba
komai nace mashi.
Baiyarda ba sai dai kawai ya kyaleni tunda nace mai babu komai ina daga kwance
nake tunane dole na dage na futar da kawaici na fara gwadawa Amira nima na iya.
Bayan kaman awa daya sai gata bazaki dafa abinda nace maki kubura tana so bane
ko may ?
Ban bata ansa ba na kyale ta haka suka gaji da zaman su har suka bargidan.
Da safe ma washe gari haka na gyara gidan tea na hada nasha na koma na kwanta
abina.
Can cikin barci naji takai min maka a baya da gigin barci na falka ina kallon ta.
Bazaki muna abin karyawa bane yau gashi har sha daya da,wani abu na rana.
Nace bazanyi ba .
Bazakiyi ba fa kika s tsuki nayi na koma na kwanta