Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
da baba Sani take fada mashi indai ita ta haifi sadauki wallahi
ba,a auren nan sai dai in bayan ranta za,ayi shi.
Tace yanzu kasan suna da zumunci kamanta lokacin da kaiwa mutane cin mutunci kace
dan shaye shaye ne shi baka aura mashi yar ka naje cikin dangina na nema mashi.
To na nema mashi din kuma yanzun sai hassada da kyashi ya biyo baya nace ba ayin
auren idan kuma ka isa sai ayi mu gani.
Yace ke wallahi hauwa baki isa ki raba muna zumuncin ba sai dai ki mutu amma sai
anyi wanan auren muddin ina raye kuwa .
Mama tace to ayi mugani idan kaika haifa min dan dakace na bari ya baci da shaye
shaye saboda sakaci na a baya.
Sai da baba ya tsawa ta masu yace subar zancen zai yi tunane yaga mai yadace
yasan maji na da gaskiya kuma baitaba ganin ta rufe ido tayi sa,insa da wani ba
haka sai ranan.
Takira sadauki tun a waya ta falfalleshi so sai har hankalin shi ya daga tace
katatake mutanen da basu kaunar ka da alheri su shiga cikin jikin ka.
Yar matar ka kuna zaune lafiya za,a shigo a tarwatsa maku farincikin ku da
tsagumi yace wallahi maji ni wanan magana ma bai gabana don na riga na fada mai
gaskiya ko.
Ana haka ma tafiya wasan su ya taso ban tashi ji ba sai bayan tafiyan shi da
Nafisa tazo take ce min .
Ke ashe wanan munafukan wai yanzun kuma yayana suke so ya auri Rahama bayan sun
gama ciwa mutane mutunci.
Gaba na ya fadi nace wata Rahama kuma ?
Nan dai tabani labarin abinda ya faru da Baba Sani da mama ranan a gidan su tace
wallahi maji tabani sha,awa yanda ta mayar mai da amsa son ranta.
Munafukin mutum ne fa tare suke makircin su dasu Umma kullun akan yayana ko yanzun
ma kila wani makirci ne suka kulla suke son ayi hadin.
Duk da hankalina ya tashi ban nuna mata ba sai cewan da nayi kai anty baba
kikecewa muna fuki kuma ?
Au ke baki san munafuki bane dama mugune wallahi duk shi ya cinyewa baba kudin
shi haka suke so kuma yanzu su shigawa yaya su cuce shi shida yaya Imirana kuma fa
duk su Umma ke turasu don basu da tausayi dakika gan su nan.
Tausayi tabani nan ta kwanta tai barci ta tashi tace tana son shan tea ni da
kaina ba hado mata tea din da nai mata hadin da bata sani ba acikin shi.
Tana gama sha tace zata tafi nakawo alheri dana saba mata idan tazo nabata dubu
biyar da su man shafa da turare tai min godiya ta tafi nace Allah yasa a dace .
Aiko da dare tafara gala baita hankalin uwar ta yai matukar tashi sosai a ka
kwasheta sai asibiti ranan can aka kwana da ita hankali a tashe.
Sai da tai kwana biyar tana abu guda a asibiti aka gaji aka sallamota.
Ko yaushe muna makale da waya da yaya muna hira akan dai zancen ciki yake min
surutun shi sai nagaji nace zan kwanta.
Da safe ma,shi zai kirani ya tayar dani yana min yaya jikin haka na zan shirya na
tafi makaranta da alolayi .
Ranan nakewa maryam magana kan zancen Rahama tai mamaki inda na samu labari tunda
mama tace kada abaru na san zancen ina cikin lalura haka.
Ban fada mata inda naji ba sai dai cewa danayi ni ba wai shigowan ta nakewa tsoro
ba wullakanci nake gudu tunda ita yar gida ce ni bare.
Tace yar gidan wa Fatima don Allah ki daina kiran kan ki da bare a cikin mu
please.
Tace balle ma may yaya zaiyi da,wata Rahama can bakiga yadda takoma bane yanzu fa
yan wahala wai harda ranon anko sukeyi fa.
Nan naji hankalina yai matukar tashi sosai ranan har saida jikina ya tashi cikin
dare dole aka kaini asibiti a can na kwana kwanana biyu Allah ya taimakeni anyi
hutu sai mama tace a wuto dani gidan ta tunda dai jikin yakiya kuma shi bai gari.
Daga ni har Iyya da Sa,ade muka koma gurin mama can gidan su amma ina matular jin
jiki.
Maryam ke fadawa mijinta har da zancen Rahama da nasawa raina ke kara damuna.
Yakira sadauki ya fada mashi suna kashe waya sai ga kiran shi yake cewa uban wa
ya fada maki zan auri wata Rahana can da zaki tayar da hankalin ki haka kina batun
kashe kanki Fatima ?
Murmushi nayi nace haba yaya akan Rahama zan kashe kaina don may zanyi kishin yar
uwar ka ce fa ba,a aure ka aure ni ni ?
Yace waya fada maki auren Rahama zanyi ne wai Rahama may ce ni bata ko a cikin
lissafina wallahi.
Sai da ya gama fadan shi yake tambayan jikina nace mai naji sauki yace kina cin
abinci kuwa nace eh mama tana saka ni gaba na sha koko.
Yace kokon may kuma can Fatima koko abinci ne da zakice kina cin abinci.
Zan wa maji magana ta saka ki gaba sai kin dinga cin abinci sosai na dan
marauraice nace ko naci wallahi bai zama a cikina wahala kuma yake sakani.
Ya kashe wayan nace namiji ke nan kamar badashi ake wanan zancen ba ji wau
Rahaman may can kamar ba a baya sun sha soyayya tare ba.
Yadda ma nake jin labari duk abinda ya samu su yake kaiwa ita da uwarta shi yasa
bai kawowa maji komai a lokacin.
Amma da suka tashi bashi baya suka rufe ido sukai mashi cin mutunci ta uwa ta
uba.
Baba da kan shi yake zuwa har dakin maji da safe ya duba lafiyata wanan abin yana
matukar ciwa su Umma da mama rai sosai.
Sunyi gulma har sun gaji sun kyale shi suna zunde wai don ina matar dan son shi
ne yake min haka.
Ya bugo min waya muna zaune da mama da Iyya yake ce min gashi wani shago yazo
shopping din kayan jarirai wani iri zai zabo antambaye shi yace a bari ya tambaya.
Sai naji yace Fatima mace ce ko namiji a cikin ki innalillahi na furta da sauri
suka kallo ni mama taju tsoro ta karbi wayan a hannu na lokacin da ya kara tambaya
yana cewa fada min mana please.
Mace ne ko namiji ba ance kuna ganewa ba idan mace tana da ciki don in san wanda
za zaba.
Mama tace to mara kunya ita ba irin ka bane mara ta ido kai kasan wanan ita
batasan shi ba kada Allah yasa ka sayo din insai tafada maka abinda ta kumsa.
Kaida kaicikin bakasan ko wani iri bane ka saka mata a cikin sai itace zata sani
mara hankali kawai.
Amira da ke zaune ko kallo bamu ishe ta ba tai tsuki tace maji tambaya fa kawai
yakeyi killa yana son sayo kayane a can.
Shidai yana jin fadan mama ya kashe wayan yana dariya kawai.
Wani irin mahaukacin sayayya yayi kamar bai san zafin kudi ba yadda ya kashe su
akan kayan baby kawai.
Har su kayan wasan yara saida ya sayo sukekuna da gadaje ya hada da kayan uwar
jego gaba daya, ya sako su a jirgi kaya guda dasu.
Sai da dare ya kirani yana cewa watau dazun kika hadani da maji ko don kina
muguwa na dauka abin siri ne tsakani dake amma kika mika mata waya don keta.
Nace to naga sune manya su suka san abinda ya dacs asaya shiyasa nabata wayan ta
fada maka abindake cikin.
Kai dan kwallo dai bai jin wahalan kashin kudi kodan samun shi sukeyi any howa
balle shi dayake ya,shara dan kwallon duniya ne shi yanzu kasa kasa ana hayan shi
ya buga masu wasa.
Don nan yanzu sun dauko sheri wa yaran musulman mu sai su hana su buga masu wasa
idan za,a tafi.
Haka yasa yanzu yai watsi da yan Nigeria yake bugawa wasu kashe she sai daga baya
kuma suke son wai ya dawo masu yanzu ya dinga buga masu.
Amma shima yaja masu aji ayace yabarsu can inda yake sunfi sanin darajan su suna
biyan su da tsada fiye da nan da,ake masu kyat.
Yayi kudii fiye da tsanmani don dai yana,bogon kurwa ne ba,a gane yawan kudin shi
sai wanda yasan kan abin.
Yana can yana gina gida a abuja wani irin maithigh house na gani na fada ba wanda
ya sani sai yaya bashar da Baba kawai da mama.
Don gudun yan baki irin su Umma don gujewa sherin su da munafunci don zasu
iyacyin komai suga bayan shi.
Zaman mu gurin mama yakaiwa Anty Amira ko ina don yadda mama take ririta sai take
jin haushin hakan a ranta.
Cewa takeyi wai shagwabane nakeyi ba wani ciwo dake damuna don dai naga kawai ana
kulla min ne.
Sai ranan da dare fever ya rufe ni sosai taga an rufa min bargo amma jikina sai
shocking yake ina rawan sanyi
Shine washegari har na samu sannunta take min yaya jiki yaya Sagir ne ya kai mu
asibiti ni da mommy muka tafi akece wa fever ne na masu ciki yakamani.
Kila sauro ya cije ni ne sadauki yana ji yaturo bashar a gyara AC a canza fanka a
saka neat a window mama da kofa.
Amira tace lalai ashe abin nayi ne wai duk a bintu ake wanan abin haka wani aiki
kan sai malam.
Ina jin ta nai murmushi nace lalai kam malam yai aiki saura biya tace Allah dai
na ganin ki wallahi idan ma daure min dan uwa kukayi ke da mai masa dama ta iya
bakar shige shige ai wa mutane balle nata.
Nace ai wanda tayi ma saka ta akayi tayi din ba yinkan ta bane tayi don haka ashe
masu ahige shige suna da yawa.
Aiko tace wai na zage ta nai mata cin mutumci nan tafara min masifa mama tashigo
tasamu tana min zari tace a,a ashe rashin tausayin naki yakai haka yarinya bata da
lafiya mijin ta bai gari kice zakiyi mata rashin mutunci.
Ke na gaji da wanan bakin halin naki wallahi Amira nan gidan su Bintu ne tunda
gidan mijin tane kema kije ki nemi uwar mijin ki can ku karata can da ita.
Amma baki zuwa ki saka min yarinya haka a gaba bata da lafiya kin isheta da
masifan tsiya haka.
Haka taita tunzura ta kwashi fushin ta tashige daki itama maji tafice zuwa waje.
Iyan Rabi tace kinyi daidai wallahi wanan yarinyar kamar ba hajiya ta haifeta ba
wallahi mugun halinta yayi yawa Allah.
Nace haka take ita bara da,son jama,a yaniyin take tunda tace kai dan Allah
wallahi dai halinta baiyi ba.
Mutum bai da lafiya ace kuma bakai mashi sannu ba sai bakar yadiya.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BA KI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN BIYA KADA KI TURAWA WANDA BAI BIYA BA PLEASE DON HAKKA CIN AMANA NE MUN
BARKI GA ALLAH,,,
Zamana a gidan su mama yasa na dan kara walwalewa na dan samu sauki sai dai har
yanzun ba dama naci wani abu a ciki.
Don da zaran naci yanzun zan shiga na mai ke nan sai kunu kawai zan dan sha ya
zauna min a cikina.
Ana cikin haka yaya saudauki ya dawo daga tafiya da tarin abin arziki don kusan
watan shi biyu ke nan a can gurin tafiyan da yayi.
Sai da yaje gida ya,shirya ya tafi inda muke a lokacin ya dawo ya samu matar yaya
Imiran ta haihu ta samu diya mace.
Muna zaune a falo mama gaba dayan mu mama da Iyya suna hira ni kuma ina dunkule
saman kujera na nade kaina har kafa a cikin hijjabina.
Anty Amira da,wayan ta a hannu tana chatting sai Sa,ade da ta kurawa tv ido tana
jallo don ita kallo baya isan ta.
Da,sallama ya shigo falon gaba dayan mu muka mai da hankalin mu a kan shi.
Duk da dare ne mutum zai iya ganin canjin da ya samu a tare dashi sosai a lokacin
daya haka.
Zama yayi suka gaisa da kowa dake cikin falon tare da mashi yaya hanya suna mai
fatan alheri.
Sa,ade ta mike har gurin da yake tana gaida shi yace a a wa nake gani haka kamar
yar kauye don yanzu sunana a kanta ya koma kuma.
Daga inda mama take zaune take cewa ,a,a kabar kira min yarinyata da yar kauye
don yanzun ta waye kai ma nake jira kadawo kakai muna ita makaranta gata sai zama
gida ba karatu.
Yariko hannunta yana cewa mama wanan bakauyan zata iya karatu ne a haka ?
Kaita a gani mana inji mama ta bashi amsa tare da cewa kai yaya akayi ka iya ba
koyo kayi ba kaima.
Ita dai Sa,ade sai murmushi takeyi kawai don bata sake jiki dashi ba har lokacin
duk yana dan mata wasa jefi jefi.
Gurin da nake zaune ya kalla yace madam yaya kuke wai har yanzun dai jikin ne
haka ?
Ya mike zuwa inda nake zaune bai damu da akwai mutane a falon ba ya zauna a bakin
kujeran da nake a kwance tare da dan shafo fuskana a hankali.
Wani irin mugun zafine yaji jikina dashi yace kai maji haka jikin nata yake da
zafi ko yaushe?
Su ka dan kallo mu tare da saurin kawar da idanuwan su don ganin irin zaman da
mukayi dashi a lokacin.
Mama tace aima jikin yai sauki yanzu gata har tana dan fitowa falo yanzu aida ko
yaushe tana daki a dunkule.
An ko koma asibiti da ita kuwa ya tambaya ?
Yau sati daya ke nan da aka kara mata ruwa da magani ai abin yazo mata da akasi
wallahi haka nan nai cikin maryam kusan duk sati biyu uku sai na sha ruwa ga zafin
jiki da ciwon kai duk na kare a lokaci sai dana haihu kamar anzare min kaya naji
komai ya wuce.
Iyya tace hjy ashe maishi ya biyo gwagon shi ke nan da ga jini wani ciki kara
gare shi sosai wallahi.
Ya mayar da hankalin shi gare ni tare da tausa muryan shi yana tambayana may
nakeji ajikina ne wai ?
Nace ba komai yaya ai naji sauki nace mai yaya hanya yace cikin bata rai
Alhamdullahi.
Sannu yaya jikin to yanzun kuma nace da sauki yaya.
Maji ko zan fita da itane waje idan nan basu gane may ke damuwar ta ba ?
Dariya sukayi mama tace ji shirmayn ka ciki may ye bai zuwa wa mace dashi kowa da
kalar daukan cikin ta ai.
Yadda ya mai da hankali akaina muna magana kus kus yasa Anty Amira jin haushi
matuka tana gani idan da dane daya dawo itace yar gaban goshin shi amma yanzu tunda
ya shigo hankalin shi yana a kaina baima ko yi mata wani magana ba bayan gaisuwan
da sukayi kawai.
Mikewa tayi tare da tsuki tabar falon daidai lokacin da yake tambayan ina kuwa
cin abinci yaga duk na ramay gaba daya haka,?
Baima san tanayi ba tashige tana gunguni wai an asirce shi yanzu bai ganin kowa
da gashi sai ni da yan uwana kawai.
Mama tace mai bata cin komai sai ruwan kunu kaganshi nan a gefen ta aje koshi bai
ludayi uku ba idan ma tasha din ke nan ai.
Nan ya fara tambayana zakici abu kaza ko na sayo maki kaza ne nace yaya ban son
komai Iam ok haka ma na koshi.
Ya dan tsuki tare da kura min ido yana tausayawa halin da nake ciki sosai can
mamatace mai.
Matar dan uwanka fa tana gidan nan kasan na fada ma ta haihu banda gobe suna.
Yace au a gidan nan take zaune ne mama tace eh daga asibiti uwar su tace a kawo
ta nan.
Yace amma naga maryam ita a dakin ta ta haihu ai bata dawo gida ba ?
Mama tace kasan kowa da irin ra,ayin shi nata ra,ayin ke nan yin haka din Alhaji
ma ido yasa masu don yasan ba a wanyewa lafiya indai yaya ne.
Sun dan yi hira ya mike zuwa cikin gida dakin Umma idan ya duba jaririya.
Ya samu su umma da uyalin ta a falo yai masu barka suka tambaye shi hanya yace
Alhamdullahi.
Da zai tafi bayan maijego tafito sun gaisa da ita yakawo kudi masu yawa ya bata
yace ta sai wa yarinya sabulu dashi.
Yana fita yaji Umma tana tambaya nawane halan ya basu ta nuna masu raffan yan
dari biyar sabbi tace akawo a kara ga laluran buki dashi.
But Nafisa dake daki tafito tana cewa a,a Umma ki bar mata kudin ta don Allah don
dai ita aka ba itama ai tana da abin da zatayi dasu ko?
Umma tace kada ki kawo min diban albarkan ki da kika saba yiwa mutane wani lalura
gare ta wanda yafi namu kuma ?
Ita dai Shafa,tu mikawa Umma kudin tayi amma sai Nafisa ta rike tana cewa wallahi
ba,a bayarwa tunda ita akaba.
Ai ya ganki baice maki gasu ba ya mika mata idan yabaku naku da ita zaku raba ta
shige cikin daki da kudin a hannun ta umma tana kwalla mata kira amma ta kyale ta.
Nafisa ke kan ke kan wallahi Allah ya waddaran hali ir8n naki na tir da Allah
waddai tace daga ciki ban dai bayarwa wallahi.
Bai dade ba yace zai tafi ya kwanta don a gajiye yake lokacin mukai mai sai da
safe ya fita daga gidan.
Ji nayi kamar na bi bayan shi da zai fita sai dai babu halin yin haka dole na
zauna a gurin mama don nan ya samay mu.
****** ********* ******
Kwanan shi biyu da dawowa sai faman sintiri yakeyi bai gidan mu baya gidan maji
gurin mu.
Yau an tashi da bukin sunan matar yaya Imirana inda yarinya taci sunan Umma kowa
na kiran ta da Ummi don sunan ta na Umma da taci.
Sai naji