Advertisements
Chapter 35 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   35 / 92

102K to 105K   out of 275.8K words

yana min
kwankwanto ga abinda na gani.
Take naji raina ya baci nace ni wallahi yaya Kabir har ka bata min rai ko na
rasa miji may zanyi da wanan mugun mara imani.
Dariya yayi yace shike nan tun da naji haka ga bakin ki da zaran an sallami baba
zan turo da kaya a kawo wa mama kamar yadda nace don komai an hada kawowa kawai ya
rage.
Nace ni dai yaya Kabir da dai zakayi hakkuri har na kare karatuna da zaifi sauki
wallahi.
Yace wa ni ance abari ya huce shi ke kawo rabon wani don haka akarashi a gidana
na san na kama abina a hannu kafin ai min sakiyar da ba ruwa.
Yabude motan shi ya shiga har ya zauna sai kuma yafito yace wallahi ina ji kamar
kada na wuce nabarki da wannan mayen dana hango nai dariya nace kai zuciya mai
nashe nashe wallahi.
Ni ai wanan da kakw gani yafi karfin aure na don shi ba kalana bane ka bar wanan
zancen kawai don Allah.
Yace to tunda kince hakana na gamsu yanzu sosai sai mun yi waya ke nan idan na
isa gida nace Allah ya tsare idan kaje a gayar min da su Antyna da yaran.
Yace zasu ji insha Allahu yatayar da mota tare da yi min horn na daga mai hannu
yafice daga harabar asibitin, saida naga security sun daga mai kofa fita daga get
din na juya zuwa ciki.

****** ********* ******
Kwana biyu bayan haka aka sallami babana daga asibiti sai dai sunce bayan sati
biyu ya dawo a kara duba lafiyan shi da aikin jikin shi.
A zatona zasu wuce gida amma sai Baba yace ba zai bari su koma ba ya tsaya gari
har sati biyun ya cika gidan gwagona aka gyara mashi nan suka zauna da mama tabawa.
Komai sadauki yana masu duk da baya gari amma bashar abokin shi yana zuwa kai da
kai yana duba lafiyan su.
Hakan yaiwa Maji dadi sosai da yadawo ranan ina jin tana mashi godiya sai cewa
yayi haba Maji ai taimako kamar yiwa kaine abinda ka taimaki wani dashi shine
rabonka.
Ban mata da yadda yarinyar nan itama ta taimaka maki ba da kike asibiti wanan ne
kawai zamuyi mata mu saka mata da abinda tai muna muma.
Allah yai maka albarka, sadauki halinka na alheri ya bika duk inda kake Allah
ubangiji yasa kafi haka a rayuwan ka.
Yaji dadin wanan adduan sosai don ya kasa boye farinciki sai cewa yayi Maji ina
jin dadin adduan ki akaina ko yaushe tace ba dole na ba baba na .
Kaine farin cikin rayuwan mu ni da yan uwanka dama,wasu al,umma dake ci daga
gareka.
Yace mata zai fita akwai inda yake son zuwa don akwai wani da suke son hada
business dashi na mai.
Tace to Allah yaba da sa,a har yakai kofa zai fita take ce mai ai na manta za,afa
kawo kayan lefen Fatima nan da kwana uku insha Allahu.
Don haka nake son kudi don nai shirye shiryen taron su.
Yace maji wanan ai maganan ku ne, ni dai bana son ki zauna ba kudi a hannun ki
bani jin dadin irin haka.
Idan na fita zan ciro maki kudi, sai na kawo maki idan bai isa ba sai akara maku.
Har ya juya sai yake cewa amma maji wai sauri may wanan yarinyar takeyi, hakane
da take son aure.
Wani kallo ta,watso mashi, tace shi aure ga yarinyar da takai sha biyar zuwa sama
har wani abu ne yanzu.
Fita yayi kawai bai tsaya ba don yasan fadan zai kawo kan shi idan har baiyi
hankali ba.
Ina wanki duk ina jin hiran su nace tunda kowa irin kane da bai tsoron Allah
zauna har mutuwa ta riske ka ahaka.
Kamar yadda Kabir yace ranan laraba za,a kawo kayan lefena a gurin mama hakan ne
kuwa,don ranan mama da,su Amirah basu huta ba sai aikin abincin masu kawo kaya
sukeyi.
Maji ta,gaiyaci abokan arzikin ta daga ko ina a cikin gari kamar yadda akeyi.
Karfe hudu na yamma gida ya cika da abokan arzikin mama masu zuwa mata karan
karban kayan lefen diyar ta.
Nayi kwalliya cikin wani swiss lace kore anyi min dinkin riga da siket Amira ta
daura min dan kwali gashina ya zubo daga baya.
Sai dai ban fito ba ina dakin mu zaune don kunya daga cikin kawayen mama wasu ke
fadin basu gane ni ba nan mama ta,tura Maryam data kirani nazo na gaida mutanen ta.
Maryam ta shigo cikin dakin ta samayni zaune nayi shiru tace Amarsu ta ango may
ye haka kuma ranan farinciki kin zauna kinyi wani tagumi dake.
Nace kai anty maryam ni wallahi ina tunanen wanan kokarin na mamana ne kawai .
Tace ke taso su hajiya Larai na son ganin ki wai sunce basu san ki ba shine maji
tace na kiraki ku gaisa.
Nai wani iri nace walkahi Anty maryam kunya nakw ji tajawo min gyale na dake gefe
na fari ta dora min akai amma can bayan tuntun kaina ya tsaya.
Tare muka fito fallon dasu duk a kunyace nake idona yana kasa sai da nakai kasa na
tsugun na a tsakiyan falon nace masu mama ina wunin ku?
Tubarkallah masha Allahu suke fadi hajiya maijidda wanan yar taki haka kamar ita
tai kan ta dayar matan tace may ma sunan ta maryam na dariya na yadda duk na
tsorace tace masu Fatima Bintu.
Sukace diyar ma,aikin Allah sai lokacin na daga kai na dan kalle su sake rudewa
nayi da ganin su manyan mata ne hamshakai ban taba sanin mama tana da kawaye haka
ba don banga tafaye fita,ba ita.
Naje gurin matar na zauna tace Allah yasa angon naki shima haka yake kamar ki
zama nayi daidai kafar matan tace kaji arziki ba yarinyar da kunyanta yaushe za,a
samu yara masu kunya haka wanan nan zamani aida yanzu muna nan dasu suna rawan kai.
Matar ta dan duko tana ce min kina karatu kuwa na ce eh tace a ina ?
Nace a hankali nan state university nake two hundred level.
Masha Allahu duk a kunyace nake zaune cikin su sai hiran duniya sukeyi.
Dayar matar take ce min jeki kin ji diyata don naga kinki sakin jikin ki namike
cikin natsuwa nabar falon .
Ban karasa shiga ba naji wata na cewa kai amma hjy maijidda kin ban mamaki yaushe
zaki bari wanan daman ya,wuce ki haka, aida kawai kin kamawa danki wanan zukekiyar
yarinyar haka ga yarinya da kunya da sanin ya kamata.
Ban fi minti goma ba da shiga masu kawo kaya,suka iso da gudan su yan uwan shi
ne mata su shidda suka shigo da,akwatina set biyu masu kyau da daukan ido.
Nan nake jin an shiga guda da yabon kaya basu dade ba suka ce zasu tafi aka bisu
da kayan da aka hada masu drinks, kajin da aka soya, da su snacks.
Sai kudi tukwici dubu hamsin har mota aka kai masu nan aka dawo falo akabaje
aka,shiga bude kayan ana yabawa.
Naji wata na fadin inji bata da ciwon kai dai ko da sauri maryam tace har biyu
kuwa.
Kai tana da kishiya fa a,a,a yarinya kinko debo da zafi kamar wanan yar yarinyar
ce za,ta shiga cikin mata biyu.
To Allah ya tsare ya kare ai sai ku tashi tsaye do dai kema gaki kina fama danaki
a gida.
Zuwa yamma kowa ya watse gidan aka barmu iyamu hajiya kubura ce zance naji
muryanta lokacin da aka kawo kayan har aka tafi tana falon tana yaba kyaun kayan .
Sai dare muka samu kan mu sai kuma a lokacin nafito ban kai minti biyar da zama
ba yaya sadauki yashigo falon.
Ina cikin kwalliya na ban cire ba idon shi suka kai ga,akwatinan yazauna yana
cewa har bakin naku zun tafi ke nan.
Amira tace su wuce sunzo wallahi kagama kayan da,suka kawo muna can.
Maryann tace kai yaya,wallahi kabir yai kokari sosai wallahi yana nuna yana
matukar son Bintu ji wanan uban kaya haka haddadu dasu bari na,dauko maka kagani
sai ta mike zuwa gurin kayan.
Yace ke ina wasa da kene ni mace ce da zan tsaya kallon wasu tarkacen banza can.
Da sauri nadago kai ina kallon shi don jin abinda yace, ya watso min harara tare
da jan tsuki yace karamar yarinya sai shegen son aure haka.
Wanan tarkace kikewa rawan kan aure jekiyi ke kika sani indai wanan tsohon ne
dana ga kina rawan kai akan shi.
Nace a hankali adaibar min abina ko yafi duniya tsufa ina son shi hakana .
Baki da kunya wallahi nike fadawa hakan na juya ina magana kasa kasa nikadai inda
nake zaune.
Wai sadauki ban san wanan abinba yanzu shi Kabir din ne tsoho kuma koma dai may ye
haka take son abinta sai kaje can kaji dashi.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


IDAN KIN TURAWA WA WANDA BAI BIYA BA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MUNA AKAN
KI,,,,,

Maji ne zaune falon Alhaji dake cin abincin da takawo mashi, abincin yai mashi dadi
sosai kullun yana son cin girkin da maji da yaranta ke hada mashi idan itace da
girki.
Tv daga bangon falon da ka shigo dashi zakai arba ya na aiki yakai tashan CNN
yana kallon news da akeyi.
Ahmad ne ya shigo falon da wani takarda a hannun shi, yana cewa uban ga takardun
an karbo sai ka saka hannu a mayar masu gobe.
Imirana kun dawo yaya kasuwan amma kaman baiji gaisuwan da maji take mashi ba
alokacin.
Saida ya gama bin takardan ya dago yana fadin, bakaji ana maka sannu ne ka kyale
ta.
Ya dan juya inda maji ke zaune ya watsa mata wani kallo mai kama da harara.
Duk a idon mahaifin shi Alhaji yace yanzu kai da girman ka kana namiji kake shiga
harka irin ta mata.
Imirah yace may kuma nayi baba gaisuwa ce taimin kuma na ansa a rai na ai.
Yace to lalai ashe da sauran ka kuma ka bani kunya kai da yau idan na kwanta
dama, kaine zaka zama min jigo a gidana.
Ashe hasashen na ba haka bane yanzu nasan ko bani Umar zai iya hada ku ya rike
min don shi banga ya banbanta wata daga cikin gidan nan ba.
Ni dama baba ai nasan baka daukan mu yanzu da wani matsayi tunda mu bamu ,,,,
Cikin tsawa Alhaji yace ashe rashin kunyan naka Imirah har yakai haka ban sani
ba ?
Yau ni kake kallo ina fadu kana fadi haka kai tsaye babu jin kunya.
Imrah baiyi magana ba ya juya yafita daga dakin rai a bace sai dakin uwar shi.
Maji tace Alhaji da baka biye mashi ba ai, don ni wanan halin na riga na saba
dashi ko a gidan nan .
Babu wani yaron gidan nan dake kallona da daraja a matsayin uwa sai diyan hjy
Kubura kawai.
Tace don haka don Allah ka daina fadan abinda da duk kaga sunyi min a gaban ka.
Don bazasu daina ba saboda kullun huduban shedan ake masu a kaina.
To Allah ya,sawaka amma gaskiya ba zan lamunci irin haka ba a gidana.
Sai muryan Umma sukaji tana fadin anki agaishe ki din ke waye da sai angaisheki.
Shi da ya mayar dake wata tsiya sai ya zauna yai tayi amma babu mai tirsasawa
diya na akan wata mace can marasa asali da ta cika muna gida da diyan tsiya diyan
taulali da suka zama ma mutane alkakan kafa.
Maji dai ta fito daga dakin maigidan da kayan abincin da,ta kwaso daga gurin shi.
Muna fuka kawai tun shigowan ki gidan nan kan Alhaji ya burge saboda bakin
kilibibin ki wai ke ga,saliha.
Maji tace yaya Allah ya baki hakkuri indai akan zancen nan kike magana ko ni ba da
son raina yai mashi fada ba.
Rufe min baki bakar munafuka sai kinyi annamincin ki kizo kinawa mutane wani
marairaicewa.
Kin iya kitihin da zaki raba miji da matan shi da yaran shi .
To wallahi hawau kiji na fada maki kinyi kadan a gidan nan muddi kikace zaki
shiga tsakanin diyana da uban su.
Ke har ina diyan naki dayake kirarin zasu rike mai gida bayan ran shi?
Ba dai wanan bakin mashayin dan naki ba da duniya tasan da zaman shi yana yawo
cikin gari a wukance yara na kallon shi.
Masu abin fadi har ba iyaka saura wa yan nan muna fukan masu kirarin su kamilai
ne a gida a waje ko tantiran yan iska.
Kuma kin sa Alhaji yaci zarafin imiran a gaban ki, kinji dadi to ki sani indai ni
na haifi Imirah har abada ba zai gaishe ki ba bashi ba duk diyana a gidan nan.
Tsiyan banza duk wani a halina ma bazai taba yin mu,amula da kuba idan kuma kin
insa sai ki sa Alhaji ya sa wuka yai ta yankan su don basu gaidake ba.
Haka zai sa nasan yaji zafin, basu gaida ke ba tun da ke dashi kuka daukan min
nauyin cikin su na haife su.
Banzan bazara dake mai gayyan tsiya gida masu abin fadi tab ga tsuliya kawai.
Allah ya sauwa inji maji ta nufi dakin ta da kayan dake dauke a hannun ta.
Sadauki tagani tsaye a kofan ta ya dafa, dan gishikin dakin da hannun shi daya.
Batai mashi magana ba ta shige dakin ta kawai,ran ta a bace tana mamakin irin
wanan halin na uwargidan su.
Bai shiga ba juyawa yayi ya fita daga gidan ran shi a bace don wanan cin zarafi
da akewa mahaifiyan su yana matukar damun shi a rayuwan shi.
Tun da safe yabar garin don bai iya tsayawa yana ganin irin wanan takaicin haka a
rayuwan shi.

****** ********* ******
Zaman shi a turai yasa ya manta da bakin cikin da ya baro a gida.
Sai dai kusan kullun zai kira mahaifiyan shi su gaisa yakuma tambaye ta yaya suke
da sauran kannen shi.
Yana kiran mahaifin shi shima suna gaisawa har su dan taba dan hira a tsakanin
su.
Bangaren Bashar kuma komai yana tafiya masu daidai don yana da rikon Amana sosai .
Gashi kuma sadauki ya yarda da Bashar din don tun suna kana suke tare dashi,
lokacin mahaifin Bashar na da rai yafi mahaifin su sadauki kudi sosai shine ke yi
masu komai.
Koda sadauki ya fara shaye shaye bai hana bashar yai mu,amula dashi ba duk da
hanashi da mahaifiyar shi tayi da farko.
Amma da taga alakarsu abin daga Allah ne sai takawo ido ta samasu kawai don tasan
shakuwar su daga Allah ne.
Hankali shi sosai yake a kwance yana sha har yanzu sai dai ba irin na can farko
ba irin shan kauyanci da kurciyan da yayi a baya.
Don yanzu ko mutum yafi aula dubara ba zai iya gane cewa ya sha wani abuba.
Haka yasa mutane ke ganin ya daina sha ne kwatakwata a rayuwan shi.
Wani yammaci ya bugowa mahaifin shi waya a yanayin da yaji muryan shi sai baji
dadi ba.
Yake cewa Baba lafiya kake kuwa murmushin manya Alhaji yace lafiyata kalau
sadauki sai dai dan zazzabin da ba,a rasa ba kawai.
Yace to Allah ya sawaka basuyi wani dogon hiraba yai mai sallama ya kashe wayan.
Washegari tun da safe sai yaji bari ya kira Baban yaji lafiyan shi saboda jiya,
yana jin jiki.
Sai dai yana kira hjy Kubura ce ta dauki wayan suka gaisa take ce mai sadauki
Alhaji ba lafiya amma gamu asibiti dashi don jiya anan muka kwana.
Hankalin shi ya tashi cikin rudewa yake tambayan ta komay ya sami mahaifin nasu.
Tace mai hawan jini ne akace kuma har ya fadi jiyan sai dai da sauki don yanzun
ma ya bude idon shi amma dai har yanzu akwai jikin.
Hankalin shi yai matukar tashi yace mata don Allah ayi duk abinda ya dace dashi
kafin ya iso garin.
Sukai sallama da ita hankalin shi a tashe tun a lokacin ne yafara shirin tafiya
dawowa gida don ganin halin da mahaifin shi yake ciki.
Washegari Sai dare ya shigo garin don nisan inda yafito a lokacin.
Kai tsaye bai yo gida ba yace Bashar ya,wuce dashi asibiti nan ya samu yan gidan
su gaba daya a gurin mahaifin shi.
Umma tana zaune a bakin gadon da Alhaji yake kwance ya shigo dakin daga cikin su
wasu sunyi mashi sannu da zuwa.
Wasu ko sai harara shi kawai sukeyi yana saye cikin swoth na maza baki mai guntun
hannu daga ciki yar rigace itama pink mai guntun hannu.
Sai dai bai sa aninin rigan saman ba haka yasa za,a hango tacikin sosai a fili.
Ganin Umma ta babake gaban gadon ba wanda ya isa ya matsa bakin gadon bai hana
shi karasawa gaban mahaifin nashi ba.
Tare da rage tsawon shi ya duka gap da kan mahaifin nashi ya dan rike hannun shi
yana fadin Sannu baba ya jikin naka yanzu.
Alhaji Abubakar ya dan juyo tare da bude idon shi da suke mai a lumshe yace,
Alhamdullahi na samu sauki sadauki ya ya hanya har ka iso ne ?
Yace eh Baba,
Likita yace kada a damay shi da surutu abarshi ya huta kawai, Umma ce ke fadawa
sadauki hakan.
Yasan nufin ta bai biye mata ba yace wa mahaifin nashi Baba amma ya kamata a fita
dakai zuwa wani kasan a dubaka sosai zaifi zama haka anan.
Murmushi yayi tare da rike hannun yaron yace kada ka damu Faruku ai naji sauki
sosai.
Kana dai jin abinda nake fadi likita yace kada asa shi yawan magana ko ?
A hankali ya dago kai ya dan kali inda take zaune tana shimfidawa sauran iyali
ikon ta.
Daga bayan ta hjy Kubura tace haba ki barsu su gana mana yanzun fa ya iso shi.

35 / 92