Advertisements
Chapter 11 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   11 / 92

30K to 33K   out of 275.8K words

shi sai yaji Uban na cewa Allah yasa haka yafi zama maka alheri gare ka
da ma muma iyayyenka.
Ya amsa a sanyaye da Amin baba insha,Allahu alheri ne ma hakan da yardan Allah.
Kadaikula don Allah ka kula,da rayuwan ka don mu shine adduan mu a gareka ko
yaushe Allah yasa ayi a cikin sa,a Allah ya tsare ya kare.
Yakara amsawa da fadi a sanyaye cikin farin ciki da jin dadi nagode baba yace
tare da mikewa yabar dakin cikin farin ciki.
Ya shiga dakin mahaifiyar shi da murna yana fada mata duk yadda sukayi da uban
nashi.
Yace maji don Allah ke ma ki samin albarka don in baki yarda ba gaskiya babu inda
zan tafi ni kan.
Sadauki Allah yai maka,albarka Allah yasa a,tafi a sa,a adawo lafiya cikin
nasara.
Har kasa ya kai yana fadin Maji nagode nagode maku dake da baba nagode ma Allah
baiko tsaya cin abinci ba yafita daga dakin zuwa club din su ya,sheda masu yardan
mahaifan shi akan tafiyan shi.
Maji tabi bayan shi cikin tausaya mashi irin na da da mahaifi, tasan kwanaki
akan bakin cikin rashin yardan su yasa shi zuwa ya sha manyan kwayoyi yazo masu gid
a buge

Yau tasan cewa duk abinda yaro ke ra,ayin yi indai babu illa acikin sa tauka
kyale shi yayi sai dai kai naka kabishi da,adduan da fatan alheri shine mafita.
Amma idan ka hana sai suga ba,a kaunar su bari kawsi su sha abin kawar da
hankalin su ko zasu samu relief akan maganan.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


Ganin yanzu bata samun kasuwar sana,anta irin farko da Mud al,majiri ke mata talla
yasa hankalinta ya tashi sosai.
Saboda a yanzu ta saba da rike yan canji a hannun ta tana kadawa a bankinta na
gida.
Sai gashi yanzu da kyata zata hada naira dari daya ta kada a ciki ga wuni.
Hakan yasa duk hankalin maria ya yai matukar tashi ga fridge yai ta haukan
kankara shi kadai amma babu kasuwan saye kamar farko.
Gurin mahaifiyarta taje da zanjen, budar bakin uwar tace shi,Aliyu ba zai iya
dan fita maki dashi ba koda a cikin uguwar ku ne yana yawata maki dashi.
Da sauri tace ,a,a,a Umma wallahi mahaifin su bai yarda sam idan yaji nasan ba
karamin tashi hankali zamuyi va dashi.
Ashe ke wawiya ce maria ke zaki bari yaji ne cewa yana talla.
Mutumin dan in ya sa kafa yafita tun safe dai yamma yake dawowa, lokacin ai har
kunci kasuwan ku ko kungama.
Lalai Umma haka za,ayi nagode da wanan shawaran insha Allahu gobe zan fara aza
mashi talla kuwa.
Kafinta shigo gida,saida ta tsaya ta sayo ma yaron farin roban ruwa dan
madaidaici irin wanda zai iya dauka.
Washegari tun safe ta tsaya shininiki bata shirya yaran zuwa makaranta ba yadda
ta saba tashi da wuri ta shirya su su karya su fita tare da mahaufin su, ya aje su
islamiya sai ya,wuce gurin sana,ar shi.
Da maigidan nata yai magana sai cewa tayi yau bata jindadin jikin tane shiyasa.
Shi dai ya shirya yafita abin shi amma yana mata mitar tayi ta shirya yaran su
tafi islamiya kafin su makara.
Daga wanan ranan ta fara,azawa yaron talla duk da Aliyu kara mine sai da yai kuka
yana fadin mama makaranta fa kada a wuce ni gurin bita fa.
Amma sai hawan shi tayi da fada cewa indan baije mata tallaba wa yake son ta
azawa.
Ya dai ga duk almajirin da ta kira sai yace malam ya hana su yin talla yanzu.
Kuma gashi yasan da dan kudin take samu tayi masu dan lalurori a gidan wa yake
son ta azawa talla.
Yaron haka ya dauka ranshi bai so ba ya tafi tallan ruwan yana turo baki harda
kwalla a idon shi.
Da yake bai iya tallan ba shiga farko da kyat ya samu yayi dan ciniki yadawo da
saura gida duk yayi zafi wasu ma duk sun yoye a roba.
Nan maria ta hau yaron da masifa da fitina har tana kirarin idan bai mayar da
hankali ba yai mata, bazata sayi mashi komai ba da kudin ta.
Dole yaron ya dan kara dagewa ya mayar da hankali gurin tallan duk da ba,wani
girma yayi sosai ba.
Ita uwar ganin yaron ya mayar da hankalin shi yanzu sai dadi take ji don har tana
wa makwabciyar ta da ta rike almajirinta na farko habaici wai in an maka bakin ciki
sai ka fashe haushi da naka tunda Allah bai hana maka,ba.
Hakana yaron tin bai saba ba yana fita da kuka har yazo ya sake jikin shi yana
shiga mutane talla.
Ito ba abin da ya shille ta sai jin dadi take yi yana kawo mata kudi tana kadawa
a bankin ta na gida kawai.

****** ********* ******
Raiha tun bata kula wayan Michael dake damun ta, da kiran akai akai har tazo tana
daukan wayan shi.
Da farko tana ganin kamar hada kai sukayi da Nasir a kanta si da ga baya ta
fahinci bada sanin Nasir din yake kiran ta ba.
Don yakan ce kada tai serving din nomban shi yadda Nasir zai fahinci cewa shine.
Don baya son Nasir yasan shine ya rusa mashi plain din shi a kanta.
Da lalashi da komai yasamu ta yarda ta tra mai da account number din da yasa ta
ta,bude.
Tashin farko kudin da ya turo mata saida hankalin ta ya daga don dubu dari biyu
ya turo mata ga account din ta.
Ta rasa yadda zata boye wanan kudin don haka ta fadawa mahaifiyan ta amma bata
fada masu cewa ba musulmi bane shi,
Ta daice a waya suka hadu dashi yace a lagos yake aiki hankalin mahaifinta ya
tashi amma da sukai waya da Michael yace ba komai yadai bata ne kyauta don ya
fahinci ita diyar tallakawa ne.
Abinka ga kudi masu shiga rai sai mahaifin nata bai tsaya wani dogo n bincike ba
kawai aka shiga harka dasu harda tayar da katangangidan shi daya zube badi guda.
Bai san cewa katanga mai muhinman ci agare shine ya mugun zubewa ba kan kudin.
Shiko Nasir ganin Raiha bazata samu ba yasa shi canza akalar sa zuwa gurin
cigiyar wata sabuwar kamu da,zatayi daidai dashi.
Sai dai Raiha ta riga ta rusa mashi plain din shi na,wanan shekaran kamar yadda
ya tsara al,amarin nashi.
Wata yammaci yafito ne daga ma,aikatar su sai ya hangi ra yarinya tsaye a,bakin
titi daganin shigarta yar hannun ce don ta dan waye a fuska.
Daidai inda take tsaye yai farkin din motar shi inda ya bude yafito har inda
take a tsaye.
Sun gaisa zakace ko yasan ta a bayane yake ce mata daga ina take haka ta tsaya
rana yana bugun ta duk haduwan ta.
Amsan da ta bashi yass shi gane cewa tana da,wayo don sai yayi da gaske idan har
tafiyan su zaiyi daidai.
Tun daga wanan ranan yafara dawai niya da yarinyar yana kashe mata masu gidan
rana yadda ya kamata.
Yarinyar irin wanda idon su ya riga da ya bude da kudi da maza ne sosai ya sa shi
fara ganin indan baiyi da gaske ba ba zai samu yadda yake so ba.
Tashin farko ya taya mata zuwa lagos kamar yadda yake a duk bayan wata uku don
yin assignment din company su.
Ba wahala ta yarda zata bishi su tafi amma sai ya bata wasu kudin da zata sai
wasu abubuwan bukatun ta da zata da su.
Kusan tare dashi suka tafi tasayo abubuwan da take so wa ranta a kasu da wani
shago.
Daga baya suka shirya zuwa lagos kamar yadda ya bukaci suyi tare dashi.
Yaso yai mata irin yadda ya,saba yiwa mata don ya horar dasu amma sai ya fahinci
kamar matafishi sanin bariki sosai.
Ya samu Michael yana fada mashi irin matsalar da ya samu akan sabuwar kamun da
yayi yanzu.
Nan ya bashi shawara akan yabi yarinyar a sannu don mata yanzu suma sun yi wayo
sosai.
Haka suka dawo bai samu yadda yake son bata training ba don in ya tura ta turai
kada a samu matsala sosai da ita.
Bayan sun bar Michael ne ya bugo waya yana fadawa Raiha sabuwar yarinyar da
abokin shi ya samu kuma yana son ya aiwatar da nufin shi a kan ta.
Raiha taji a ranta yarinyar ta bata tausayi don haka dole ne ta taimakawa ko
wacece.
Sai bayan sun dawo ne ta samu wani abokin shaye shayen ta bashi kudi don yanzun
bata da matsalar su ta ce yai mata bincike akan sabuwar yarinyar da Nasir yake
target ga fitawar waje wurin safarar matan da yake a boye.

****** ********* ******
Tsaye ta hango wani guy a kofan gidan su kafar shi daya a cikin mota daya kuma
ya daga waje ga waya a hannun shi.
Ganin Amira da,zata shigo gidan yasa shi saurin samun ta ya tsare ta yana fadin,
barka dai.
Don Allah idan gidan nan zaki shiga ina son ki sallamo min Nafisat ne, wani kallo
Amira tai mashi kamar zatai magana amma sai tace mashi kawai taji.
Tana shiga gida ta fara haduwa da Bintu wacce ta sheko ta rugumay ta cikin so da
kauna zakace yar uwarta ce tajini tana cewa Anty Amira sannu da dawowa ya makarata
ya hanya tare da karbar wa Amira school bag din da ke rataye a hannun ta zuwa cikin
dakin su.
Mama Asiya suna waje da yaran ta sai tsaki suka ja suna fadin sai kace diyar
wata,
Harda zuwa don kisisinar yarinyar nan yar kauye zuwa yi mata sanni da zuwa.
Wai ma mama may wanan yarinyar takeyi a gidan nan ne har yanzu, wallahi ban son
ganin ta shegiya gata yar kauye amma ta iya ba mutun haushi da takaici gata aiki
baya isan ta.
Uwarta ce ina ga kamar a nan take zaune yanzu tare da su kin san su da shegen
kwashe, kwashen tsiya ai da son asani komai basu aje ba.
Dayar yar mama dake yankan akaifa tace may zasu bata banda wahala suma ta kan su
sukeyi ai.
Ni Alhaji ma yafi bani mamaki don da watace cikin mu ta ajeta da yanzu ya fara
fada za,a kawo mashi bakuwa a gida cikin yaran shi ta bata mashi tarbiyan ta.
Can kuma cikin daki da Bintu ta shiga da murnan ta tana fadin Mama Anty ta dawo.
To yar gidan Anty sai kace wace ta dawo daga wani guri haka kina ta wani farin
ciki dake.
Mama ai duk wanda yafita ta dawo lafiya ai masa barka da arziki inji Bintu, kai
Fatima ke kan halin ki sai ke wallahi.
Amma a ran Maji dadi taji irin yadda taga Bintu tana matukar son diyan ta wanda a
da can baya ba ruwan su da juna a dakin kowa kan shi daban basu damu da junan su
ba.
Amma zuwan Bintu cikin su yasa koda maryam bata kusa zata bita tana fara,a tana
fafin Anty maryan antyn mu ta dawo.dole ta fito
Idan kuma maryam ce ta dawo sai ta nemo Amira tana fada mata cikin jin dadi har
takai suna barin abinda sukeyi suzo su tari junan su cikin nuna jin dadin su.
Yau ma hakan ne don har baya taje tana fadawa maryam dawowan Amira inda maryam
tazo da murna tana wa yar uwar ta sannu da zuwa Anty don ita bata fita ba.
Nan suka zauna a falo Amira bayan ta cire kayan jikin ta tafito Bintu ta aje mata
abincin da ruwa tafara ci suna hira a tsakanin su.
Tana fadin kai yau wallahi akwai rana ga zafi duk dama na matsu na dawo na cire
wanan kayan nasamu ruwan sanyi nasha.
Maji tace aiko mu dake gida wanan zafin ya ishe mutun Allah dai yai muna Rahama
kawai.
Yaran suka amsa da Ameen ya Allah.
Amma kila an kusa fara ruwan sama ne don zafin yau yai yawa mama Bintu ke fadi.
Sai suka sa dariya gaba dayan su maryam tana kokarin cewa ke Bintu ai haka garin
nan yake da shegen zafi walla,,,,
Sai gani sukayi an daga labulen dakin kawai ashe Nafisa ce gaba daya suka juya
don ganin waye haka bako sallama zai fado masu kai tsaye.
Tau yar bakin ciki ashe anzo nemana shine don bakin ciki irin naku na gado kika
ki fada min, to Allah bata ku ba.
Wai dawa kike yi ne inji Amira take tambayan ta a cikin daga murya.
Ke mana yar bakin ciki mai shegen kishin tsiya kamar na uwarta ni bani na hana
azo a soki ba balle ki gwada bin bakin ciki karara a fili.
Nafisa niba sa,arki bace balle don kin kwaso dan rashin mutunci irin ki yace wai
ni na kiri mashi ke don rainin wayo.
Ji yar rainin hankali oho sai yanzu ai na kara gane bakin cikin ki a fili wallahi
don naga aikin hassada yau,
To wallahi a haka zaku kare tanbade lalace sai bakin kitifi ku da uwar ku a daki
dangin yan caca da shaye shaye.
Kafin tace wani abu ba,wanda ya san Maryam har takai inda take tako shako wuyanta
ji kake tas,tas, mari biyu masu lafiya ta kwashe ta dasu.
Umma fito wallahi gasu Amira can sun tarar wa Anty Nafisa da duka inji karamar
kaunarta take fadawa uwarsu.
Haba gaba daya sukayo part din Maji hankali a tashe daidai duk su kuma sunyo waje
inda Nafisa take tsaye da maryam.
Maji tana fadin ke Inna Isa kyale ta haka na barta taitayi ita kadai.
Daga nesa Umma ke fadin wallahi idan kuka kara dukan ta yau sai dai duk akai mu
asibiti gidan nan .
Kaji man marasa mutunci haukan ashe ba,a kan sadauki kawai ya tsaya du, dukan ku
kenan ya shafa.
Ke Nafisa may yakawo ki gurin wa yan nan matsiya ta ki jawa kanki tsiyan su irin
ta gado ya shafe ki ke ma.
Nan take fadawa uwarta duk abinda yafaru uwar take cewa barsu tsiyane da talauci
yai masu katutu a kai shine bakin cikin su gare ki.
Hassada ko sai dai su mutu dashi a gidan nan don babu mai kama kafar mu don mun
riga mun masu nisa ko.
A haka zasu kare daki tsiya tsiya kamar madallacin malam ba komai sai tarin
raggaduda kawai ciki.
Saurayi kuma sai sun ga har dan gidan gwauna a gidan nan gurin ku.
Sai lokacin sadauki dake tsaye daga kofa shigowa gidan tun farkon fitina yana
tsaye yana sauraren su.
Ran shi yai matukar baci irin yadda yake jin ana zagin mahaifiyar shi da yan uwan
shi a kan talauci.
Su madai su Amira duk da Maji tana masu fada bai sa sun fasa mayar masu da amsan
zagin da suke masu ba don harda mama Asiya ta shige tsagal cikin fitinan tana cewa
ai wanan mutanen kune baku san sherin su ba dama da kowa bakin ciki sukeyi a gidan
nan.
Ke Amira shige daga ciki kada na kara jin muryan kowan ku yai tsaye yana nuna
masu kofan dakin su da hannun shi.
Ranshi a bace idanuwan shi sun kada saura kiris ya fashe irin yadda ya hasala.
Yaran suka bi bayan uwar su da tafara shiga ciki ranta a bace yayin da ya juya
inda taron mutanen gidan suke tsaye ya watsa masu jajayen idanuwan shi akan su.
Zo mutafi kinji don wanan mahaukacin yanzu yana iya muna haukan shi akai.
Gaba daya suka watse zuwa shiyan su a can suka yada zangon su yana jin sunci gaba
da fitinar su ya shiga dakin mahaifiyar tasu.
Tsawa yadaka wa su Amira akan suyi shiru hakana bai son hayaniya ya isa.
To amma yaya don kawai an raina mu shine kowa ya kwaso sharan shi a kan mu zai
yaba tsiyar shi.
Nace ya isa haka ya fadi cikin tsawa hakan yasa gaba daya sukai shiru da
maganan.
Nan yakai zaune saman dayan kujeran da ya saba zama idan yashigo gidan, maimakon
ya zauna yadda ya saba sai kawai yayi kwance tare da dora hannun shi daya saman kan
shi daya na saman kijin shi.
Ya kai wasu mintina a hakan gaba daya dakin ba wanda yai magana daga cikin su.
Bintu ce ta mike don shigewa don dai ita gaskiya zaman ta a dakin duk a
tsorace take dashi.
Don gani take cewa kiris ya rage ya kamasu da dukan tsiya a dakin.
Takai gaf da kofan zata shiga taji yana cewa "Ke kawo min abinci na na fita.
Da,sauri ta juya zuwa kitchen inda ta hado mashi abinci kamar yadda ya saba hada
mashi wanan karon har da spoon din da yace dashi yake ci.
Bai masu magana ba ya mike zaune kamar zai dauki abinci sai kuma ya bude a,nan
falon ya fara ci a hankali.
Maji ki yace daidai zaikai spoon din shi a baki batare da ya kalleta ba kiwa
yaran nan magana su daina shiga harkan mutanen gidan nan ana zagin ki a banza.
Don bazan iya hakkurin wanan mugun zagin da ake maki ba a gidan nan haka.
Talauci dai ba mune muka azawa kan mu ba Allah ne yayi mu a haka ba yin kan mu
bane ai.
Amma mutanen nan da,sun tashi da,wanan zasu zage ki ke da yaran ki, don tun ina
karami nake jin wanan kalman daga bakin mama da Umma a gidan nan.
Sai kuma ni da na ja maki wanan gorin na dan shaye shaye da kuma cacan da suka ce
ina yi wai.
To amma ba komai Allah na gani shida ya dora min wanan lalurar shine zai yaya min
shi dakan

11 / 92