Advertisements
Chapter 64 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   64 / 92

189K to 192K   out of 275.8K words

Na dan bata fuska tare da turo bakina nace ni anan zan kwanta murmushi naji yayi
tare da riko min hannuwa na ya mikar dani tsaye.
Look at me yace, sai na dan dago kaina kadan na kalle shi amma ban iya jure
kallon shi ido da ido dole na dukar da kan nawa, kasa.
Yace daga yau ban son sai na kara biyu ki a dakin ki don ko zo guri na ke baki
san right din ki ba ne a gare ni.
To bari kiji bazan biya kudin sadaki na ya tafi a banza ba ni ina gabas kina
yanma kudi nabiya dole kuma a bani hakkina.
Jin abinda yace yasa ni watso mashi harara au harara na ma ki keyi ko ba biya nayi
ba ne ?
Cak ya daukeni kamar ya dauki babyn roba sai dakin shi ya dire ni saman gadon shi
yana cewa this where you support to belong every night.
Rankwafo wa yayi tare da raba hannaye shi yasani tsakiyan shi kokari yake sai mun
hada ido dashi amma na kasa lumshe idanuwa na nayi.
Yayin da naji yafara canza min sallon wasan shi a hankali yafara bin sassan
jikina da wani irin romacig.
Tun ina iya daurewa har na fara dan nishi, kadan kadan cikin neman agaji sosai
yake gwada min wani irin mahaukacin kauna wanda ni kaina ban iya cewa ga inda nake
a lokacin.
Mun dauki tsawon lokaci dashi sai da ya gaji dan kan shi ya sarara min tare da
rugumay ni a jikin shi yana sauke numfashi a hankali.
Al,amarin yau da dan sauki bisa ga daren farkon mu dashi don banyi mugun jikita
irin na wancan ranan ba.
Gaba dayan mu shiru mukayi kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi a lokacin.
Ni dai tunane nakeyi anya kuwa zan iya da yaya sadauki ashe mutum haka bai da
tausayin mace ko kadan.
Ko dai dama haka yake ne wai yana mu,amula da wasu matan ne acan baya.
Da sauri nai istigifari don ance zato zunubi ne koda ya zama gaskiya don haka nai
saurin janye wanan tunanen a raina.
Shiko tunane yakeyi wai dama ashe abinda Bashar ke ta fihintar dashi ke nan akan
mace.
Tabas yanzu ya yarda da zancen bashar da yake cewa dan hakin daka raina shike
tsone ma ido ashe ni,ima da baiwane tattare da wannan yar kara mar yarinyar da ya
raina a idon shi.
Bai tsan mani a rayuwa zaa samu mace haka mai tarin ni,ima da baiwa ba irin na
Fatima ba yarinyar da bai taba samun wani jindadin rayuwa ba irin wanda yake tsinta
yanzu a jikin Fatima ba.
A hankali ya kai hannun shi saman kaina naji yana shafa a hankali ban san lokacin
da na saukw wani irin ajiyan zuciya ba mai karfi.
Ji nayi yakira sunana a hankali yana fadin FATIMA na amsa a hankali da fadin naam
.
Sai naji ya rugumay kamar wani zai kwace mashi ni a lokacin yace.
Don Allah ina son kiyi hakkuri da halina kizama mai dauriya acikin duk wani
al,amari na zaman takewan mu nidake.
Idan har kin min haka kin gama min komai bazan taba son na samu matsala ba daidai
da rana daya da mahaifiya na koke don rayuwa a yanzu akwai akasi a cikin shi kala
da kala.
Shiru nayi ina sauraren shi, yayin da idanuwana suka ciko da hawaye wanda ba zan
iya fadin ga dalilin zubowan su ba a gare ni.
Kukane ya kubuce min jin yadda nake kuka yasa shi kara manna jikin shi sosai da
nawa shi bai lalashe ni ba kuma bai iya furta komai ba .
A haka barci ya daukeni ban san manayi barci ba sai dai dana falko nagani a saman
chest din shi kwance nayi filo dashi.
Gyara kwanciya na nayi dakyau abinda yasa shi dan motsawa ke nan ya kara jawoni
zuwa jikin shi.
Da safe da kyat na mike na nufi dakina can na gasa,jikina sosai da,ruwa masu
zafi haka yasa na dan samu saukin ciwon jikin da nake ji dana tashi.
Nai matukar mamaki kwarai da naga yaya yana sallah jam,i bai wuce shi duk asubahi
sai naji fitan daga gidan zuwa masallacin uguwan sallah.
Ya dawo daga motsa jiki ya samay ni tsaye ina hada table din cin abinci a cikin
kunyan abinda ya faru a tsakanin mu daren jiya yasani dukar da idanuwa nakd gaishe
shi da kwana.
Ya kara so tare da dan rike ni daga bayan na yana cewa, ke baki gaji bane har
kika tashi ki aiki haka mai yawa?
Kunyan shi nake ji ban yi magana ba sai dan murmusawan da nayi nace yanzu zakaci
abinci ne?
Ba abinci nake son ci ba ke dai nake so yanzu ya bani amsa fuskan shi a daure
tamau kamar ba wani magana yayi ba a lokacin.
Da sauri na kalli agogon ban gon dake falon sai na ji ya furzi iska yace zan
makarar dake ke nan kike nufi ko?
Ya juya ya fara tafiya yana ffadin ok a dawo lafiya sai dai kafin ki dawo zan kai
musa school din su sai kuyi sallama dashi.
Daga haka ya shige dakin shi ya barni gur8n tsaye koda na shirya nashiga yi mashi
sallama na samu ya shiga wanka a lokacin.
Don haka na cire mai kaya daga cikin wardrobe din shi haka zai sa yagane na shigo
dakin na juya nafita da sauri don na kusa makara ranan.
Bayan yafito kayan da ya samu na fitar ma saman gado don yasa yasa shi gane cewa
na shigo dakin a lokacin sai daya gama shirin shi yafitone musa ke fada mashi nace
na tafi don na makara yau.
Yana gamawa dama musa duk ya kagu su wuce don haka,basu bata lokaci ba suka fita
zuwa school din da za,a kai shi na kwana.

****** ********* ******
Haka muka kasance da yaya kullun a tare muke kwana dashi yana yadda yaso dani tun
ina jin nauyi da kunyan shi har na dan fara rage kunyashi da nakeyi sosai.
Yanzu yakai basai yace nazo dakin ba don kaina nake shiryawa naje don ma inhar
banje ba shida kanshine zaizo ya dauke ni cak yatafi dani.
Ya gama binda yake ya koma gefe daya yana sauke numfashi a hankali tare da furzo
iska daga bakin shi.
A raina nace wai dama maza basu da kunyane haka wai kamar ba shine mutumin da ke
ta cika bakin shi ba abaya akan dole ne maji ta lakaka mashini.
Yanzun gashi shine harda wasu irin kalamai da ina ganin ba a hayacin shi yake
fadar su ba idan mun kasance a dukule tare.
Idan kuma weekend ne zan iya cewa kusan a tare muke zama muyi shi agidan bai son
fita nan da can yana nan ciki ya hanani shakat a gidan sai yayi yadda ranshi ke so
zai sarara,min.
Watan shi daya cur a garin da dawowa bai fita zuwa koda Abuja bane yanan cikin
gari.
Ranan ya shigo da yamma yake ce min na shirya zamu fita zuwa gida mu gaida su
baba don baba bai jin dadi jikin shi ya tashi.
Na dan rude ina fadin subbahanallahi may kuma ya faru da,baba ni dai Allah yasa
ba wani mugun abin aka aikata ba har ciwon shi ya tashi.
Tun karfe bakwai na fara shiryawa na saka wani atamfan super exclusive, mai ruwan
yellow da zanen ganye kore zani da rigane sai gyalen da na yafa karo na farko a
gidan aure na.
Takalma da handbag duk na fitar da zan saka sai wani irin mayen kamshi dake tashi
ajikina na dade ina bata lokaci gurin gyara jikina kamar wacce zata gidan wani
shugaban kasa.
Nasan idan na samu matsala ga shigana ba su Umma da mama ba har Amira sai na samu
musguna daga gare ta.
Sai gashi ya shigo dakin yana wani kamshi dashi yai mugun haduwa don shadda ce
gezenah a jikin dark blue sai wani maiko da yauki takeyi har hulla sai da ya saka
yau nace dankari a raina wani abu ko sai mahaifa.
Yadda yake kallon shigana nima haka nake satan kallin nashi shigan don duk wanda
ta fan mu komai bakin cikin mutum dole ya kyasa muna.
Karasowa yayi har inda nake zaune a gaban mirror ya kura min ido can naji ya
numfasa yace wai ke ashe haka kike dama kike ta faman boye kanki cikin mugun hujjib
kullun kamar wata munafuka can.
Nace ai dama sunana ke na a bakin ka kuma boyewan danakeyi ai ba kaina naiwa
hakan ba don da baka samay ni ba kai.
Namike ina cewa dama nasani na dinga kwalliya irin na anty Nafisa tunda shina ga
yafi burge mutane yanzu.
Yace dako na halakaki tun lokacin don ba zaki jawa maji zagi ba, nace ai naga
shine ra,ayin ku ku.
Murmushi yayi tare da kamoni yana mikar dani tsaye yace ki tabbatar da kin rufe
min wanan jikin naki da kyau don kinsa akwai kardawa a gidan .
Yayyen nawa ne kuma gardawa ashe kardawan yawa gare su bamu sani ba masu kalle
surar kannen su .
Yagane maganata sai yai murmushi kawai yace ai ban kalle ba sai dai ina shirin
kallo don gada wani ya bani labarin abinda ban sani ba nida abina.
Da sauri na dago kaina nace may kake nufi da hakan ya wani lumshe idon tare da
furzo iska yace ma,ana har yau ban san komai ba akan matata da rana ganin dare
kawai nake mata koshi ma a,wahalce ga cizo ga yakusa da zagi.
Murmushi nayi na dukar da kaina kawai don natuna first night din mu dashi yadda
naitakiran shi azzalumi macuci mazina ci kawai.
Isan kin shirya sai ki tashi mu tafi kada ki bata muna lokaci don ina da abinyi
ni idan mun dawo don ba wani dadewa zamuyi ba can.
Kallon mararaicewa naimashi nace tare da turo baki, ni wallahi kullun abu kullun
abu ba tausayawa mutum.
Yace wani abu kuma cikin kasheni da idanuwan shi don son jin amsa na.
Banyi magana ba sai gyalena da ke tashin kamshi kawai dana yafa akaina nan na
kara fitowa wata shar dani nai marukar kyau har ya kasa dauke idon shi akaina.
Yarinya ke kikace kina so dabakice kina so ba da ba,abaki ni ba, yasani gaba muna
tafiya yana min waka a baya na.
Wata landdrove jeep nagani a waje dark blue sai shaki takeyi van san da ita,ba a
gidan sai wanan lokaci ko ba afada nasan ansha miliyoyi a waban gurin .
Ita muka shiga shike driving kamar bai son tukin motan nace amma ya kamata mu dan
sayi wani abinda zamu shigawa baba da su Umma dashi kada mu je masu hannu a sake.
Kamar baiji mai nake cewa ba yai banza dani a raina nace bahagon mutum kawai
wanda ba,a gane kallan shi kaman ba shine yanzu yake min waka ba gashi mintina
kadan ya wani sha toka ya murde fusaka tamau dashi.
Gaban wani katon shago ya tsayar da motar shi sai da ya kashe motan ya juyo yana
ce min fito mu tafi.
Har mun fara tafiya yace gyara rufe jikin ki dak yau don kinga an fara binki da
kallo kiyi shiga kamar wata budurwa can.
Gyara tsayin gyalena nayi da kyau tare da bin bayan shi munyi sayayya sosai a
shagon har sai da nai mamaki leda kusan bakwai akayo muna muka nufo gida dasu.
Ina ganin get din gidan nai wani lumshe idanuwana don jin dadin ganina a gidan da
nai rabin rayuwana a cikin shi cikin jin dadi.
Muna fita gab da zamu shiga gidan sai naji ya riko min hannu na kallon hashi nayi
ba tare da ya kalle ni ba yace eh haka nake son maman ki ta ganmu don tasan na rike
mata amana.
A haka muka shiga gidan mun fara cin karo da yaya Abdul yace tun daga nesa a,a,a
Allah yayi hadi a gurin nan sai kace kuka hallici kan ku haka.
Murmushi ya sauke kawai tare da kara rike min hannu da kya yaya Abdul yace kaga
zabe gaskiya kan nan ba irin wa yancan da suka zabo mata ba kamar suna barci.
Muna shiga cikin gida Rukaiyya diyar mama Asiya tana waje tsaye tana waya tana
ganin mu ta wani watso muna idanuwan ta gaba daya a kan mu.
Dakin maji yace a fara shiga da kayan bayan ya cire wasu leda guda uku daga cikin
ledojin da,muka shigo dasu yace min a hankali kiba wa su Umma kowa guda guda nace
angode.
Dakin Umma muka faea zuwa tana zaune da yaran ta sai jin sallaman mu tayi har mun
kawo kofan shiga ko duk sai ta daburce da ganin mu.
Zama yayi kan kushi na zauna kasan carpet daidai kafan shi muna gaida ita .
Cikin hali irin nata na shan kamshi take amsa muna kallo daya tai muna wani mugun
hassada da bakin ciki ya darsu a zuciyar ta tace kina nan kina ta hakkuri da halin
mijin naki ko don ba fasawa zaiyi ba na sani.
Murmushi kawai mukai mata don duk mun fahinci nufita amma muka kyale ta
Bamu dade ba muka mike na karasa gaban ta ina cewa mama ga wanan ba yawa dan
tsara bane ta amsa a wullakance tana tabe baki tana fadin angode.
Na juya har na fara rafiya sai najuyo ina cewa yaya sagir fa idon ta nagani tana
kallin kasan zanina da harara tabini ta tabe baki tace yafita dazun nan.
Dakin mama Asiya kuwa muna shiga dama Rukaiyya ta riga data fadawa mamata zuwan
mu ko da ta gan mu.
Idon kyam a kaina yadda mukayi dakin mama haka mukayi a dakin ta bamu dade ba
mukafito namika mata ledan tace to har da wani tsaraba can to angode.
A daiyi ta hakkuri don kin san abinda kika aura dama don haka sai a daure da
hakan .
Muna barin gurin sai dakin mummy sai dai a rufe dakin yake yaran ta dai ne kawai
a ciki alaman tana dakin baba a lokacin.
Yaran suka yo kanmu suna muna sannu da zuwa cikin rugumay mu Imirah yace yaya
nace mummy takai mu gidan ka tace wai zamu damay ka kana hutawa .
Muma yaya kazo ka kaimu mu huta tare da kai kaji, ya shakan shi yace zanzo na
dauke ku.
Yaran sukaji dadi suna ta murna yayan su yace zaizo ya dauke su zuwa gidan shi
namika masu ledan tsaraban su wanda daban yake saboda akwai alawan yara acikin shi.
Sai dakin mama muka nufa kuma suna falo zaune da Amira muka shiga da sallama ina
rike a hannun shi kamar wata yar yarinya can dani.
Sannu ku da zuwa mama tai muna Amira tana dago ido kallo daya tai muna naga tai
sauri kawar da kan ta gefe daya tana cewa sannu da zuwa yaya.
Nace anty ina wuni ta ansa a wulakance da lafia kawai ta juya kan ta ya kalle ta
yai murmushi yace sister ke nan yaya gidan gaban mama na tafi na durkusa a gaban ta
nace mama ina wuni ?
Cikin jin dadi da ganin mu haka tace ashe kuna tafe ne yanzun tashi ki zauna
Fatima kinji Allah yai maku albarka ai yanzu yaro yashigo da leda yake cewa kune
kuka shigo.
Sadauki yace maji yaya na barku dazun haka yasa nagane cewa yashigo da rana ashe
nice dai yakawo nagaida Baba da jiki ashe.
Mama tace mai lafiya muke yace to yaya jikin na baba tace a,a Alhamdullahi ai ya
samu sauki sosai har ya tashi yayi sallah ko dazun.
Ta juyo gareni tana cewa Fatima kuna lafiya ko cikin jin kunya nake cewa lafiya
kalau muke mama.
Tace ashe musa an tafi makaran ta saiga babana yazo dashi ya sallamay ni ranan .
Cikin jin kuya nai murmushi tare dukar da kaina kawai nace wallahi mama yaya ne
yai mashi wanan kokari kuma yasaya mai komai da zai bukata acan .
Sai a taya mu godiya gurin shi mama tace ince maki sun gode kwarai Allah ya saka
da alheri.
Mama tace kai haba waban ai yiwa kaine kawai wa yasan abinda zai zama watarana
kuma in Allah ya raya abinshi.
Kina dai waya da su ko don ki dinga jin lafiyan su akai,akai don haka na dakyau.
Gurin da Amira take zaune ya koma ya zauna saman hannun kujera yana cewa may
kikeyi ne wai kin wani fuskewa mutane haka.
Tace cikin da yake yaya kawai dai hakanaji ashe zaka dawo yace eh waccan nakawo
ta gaida baba da jikin shi don dazun ya tambaye ta.
Hummm wanan muba fukar matar taka ai ta iya sace zuciyar kowa da makircin ta
harda ma wanda bamu zata ba duk ta sace munafuka kawai.
Kai Amira Fatima ce kuma muna fuka munafuncin may taimaki kuma haka ne wai .
Sai lokacin ta dago kai tace humm yayya ni wallahi mamaki ma kake bani yanzu dan
ban yarda amma yau na shedawa idanuna gaskiyan zargina.
Yanzu kai yaya har ka iya fito da wanan a gari a matsayin wau matar ka har kana
wani jerawa da ita, kamar wata mai mukami can.
Kasa kasa suke maganan su amma duk zancen su ni yana a kunne na don ina dan kusa
dasu mama ce kawai bazata ji ba a lokacin don ita sai farin ciki da murna takeyi
tagan mu a cikin farin ciki a tare.
Can ya mike don ba zai jure sauraren Amiraba don tana bakanta mashi rai da
zancen ta gap yake da ya dauki matakin da bata zata ba a lokaci guda.
Idan nake a zaune ya kallo yana cewa taso muje gurin baba ki dauko wancan ledan
muje mashi dashi.
Yana gaba ina bayan shi muka tsaya daga kofan falon baba muna mashi sallama.
Aka ansa

64 / 92