Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
mu yai muna rana muna zuwa aka kaita emergency don sunga
yadda muka shigo da ita.
Bayan yan aune aunen da,sukai matane likitan yake cewa ke yarta ce na amsa mashi
da eh,
Yace to ina manyan ku suke aka bari ke karama dake kika kawo mara lafiya haka
acikin wanan yanayin asibiti ?
Nace, Baban mu baya gari shi da yayan mu sunyi tafiya yace alright yanzun dai
zamu bata gado tare da bata taimakon gagawa tukun kafin mu auna ta muga may ke
damun ta haka?
Sai da na,tabbatar da cewa an bamu gado anyi komai har an saka mata ruwa na dauki
waya na kira Amirah wace cikin gigin barci take min magana.
Nace Anty gamu fa asibiti da mama an saka mata ruwa ma ko.
But tamike da mamaki azaton ta wasa ne don shirmay ta amma tana dubawa dakin Maji
sai taga wayau har falo taje babu mu.
Bayan kiranta kamar kada na kira yaya sai dai nace bari na kirashi dai yasan
halin da uwarshi take ciki.
Babana ta rubuta wajen sunan shi na danna kiran layin baifi ringing uku ba ya
dauka yana cewa,
Maji yanzu nake son kiranki naji ya jikin don jiya Amirah ta fada min kina jin
jiki sosai.
Nace ba mama bace nice Bintu gamunan asibiti da mama an bata gado.
Yace cikin wani irin murya what, anba Maji gado a,wani asibitine kuke?
Nace na,gawon nama watau Usman dan fodio teaching hospital.
Yace ke ba Amirah wayan please nace Amirah tana gida bata iso ba tukun
To wa ya kawo ta,assibitin ita Amirah tana mayye nace ta tsaya hada break ne.
Tsuki yaja tare da kashe wayan ashe bayan ya kashe Amirah yakira yace yaya jikin
na maji wai may ke faruwa ne.
Tace wallahi yaya ban masan sun tafi Asibiti ba Bintu ce ta kirani take fada min
yanzu wai suna asibiti.
Yace you are very stupid Amira yanzun saboda shegen barci tsiya har aka fita da
Maji gida baki sani ba ke kina may ye har wanan yar kauyen yarinyar ta kaita
asibiti.
Tas yai mata tare da umartan ta duk abinda take tai maza ta samay mu asibiti
kafin ya bata mata rai.
Ina zaune na tasa maji da ta samu barci a gaba sai ga Amirah da maryam a gagauce.
Sun wani fuske sun dauki zafi dani ban damuba don nasan ni don Allah nayi masu.
Don danabita nasu sai dai ta halaka a gida saboda sanyin jikin su da narkewa.
Muna nan zaune sai ga likita yazo da takarda magani a rubuce yace suna bukatan
wa yan nan.
Karba Amirah tayi tare da ficewa dakin dagani sai maryam ke kan mama din.
Ajima kadan sai gata tadawo da takardan tana fadin ke Bintu nifa ban san inda ake
sayar da maganin su ba.
Nace a tambaya mana take cewa wai wa zata tambaya amsa nayi tare da daukan kudi
ga post nafita.
Da tambaya,na gane gurin sai gani da maganin cike da leda nashigo dakin nan na
mikawa nurse din dana samu tana gyara ruwan dake tafiya a jikin maji din nayi.
Shiko sadauki yana gama waya da Amirah mahaifin shi ya kira yake sheda mashi
abinda ya faru da uwar su.
A gagauce Baba ke tambayan shi yanzu maijidda tana ina wai?
Yace tana asibiti an bata gado ita da wanan bakuwar yarinyar Fatima dake dakin
ta.
Su su Amira fa suna inane da sauran mutanwn gidan da har za,a bar Fatima karamar
yarinya takai ta asibiti da kanta duk an rasa wanda zai dubaran daukan ta zuwa
asibiti sai Fatima karamar yarinya haka da ita.
Sadauki yace yanzu nakira su Amira ga,waya mazasu tafi asibitin suga halin da ake
ciki don dai tace wai an daura mata ruwa a,jiki ko.
Allah ya sauwaka insha Allahu gobe zan dawo nazo naga abinda ke faruwa hakanan.
Suna kashe wayan sadauki ya dab furzo iska daga bakin shi kadan tare da dan gyara
tsayin shi.
Agogon shi ya fara dubawa ya san idan yace zai taso daga anambara zuwa sokoto ba
karamin tafiya bane don haka ya yanke shawaran samun jirgi zuwa abuja daga abuja
koda da motane sai ya karaso.
Karfe, Biyun rana yana garin Abuja bai bata lokaci ba ya samu shatan mota sai
sokoto,.
Suna zaune sai nice ke ta faman zirga zirga wai su yan gaye a hankali maji ta
bude idanuwan ta da ta kusa yini tana barci.
A lokacin bani daki sai Amira ce zaune mun fita da maryam zuwa wani guri tace
na,rakata.
Bayan ta bude ido tafara bin dakin da,kallo can tace, Fatima, Fatima, sai Amira
ta mike tazo inda take kwance.
Maji kin tashi ne tace wa uwar ta, sai uwar ta ce mata eh ina Fatima ne ?, bata
nan tabata amsa.
Sai ta mayar da idanuwan ta takara rufe su a hankali, kuma again.
Muna,shigowa take fada muna mama,ta,falka tana tambayan ki Bintu da sauri na isa
gurin ina,fadin wani abin take so ne Anty tace batace komai ba sai ta koma barcin
ta.
Ana maggariba ya iso garin a lokacin hajiya kubura ce kawai tazo duba mama sauran
basu zo ba har lokacin.
Ban san da zuwan shi ba don natafi dauko kayan da za,a bukata a gida.
Ina dawowa daga gida na sauka mashi sai naji ana cewa ke pretty, Fatima,
Jin fatima yasani dan dakatawa na waiga inga mai kirana haka nan don ban sheda
sunan mai shi ba.
Ya karaso gurina da murmushin shi yana wasa da key din motan shi a hannun shi.
Yace ai tun gida na,biyo bayan ki dama na dade ina son in samu time nai maki
magana.
Kin gane ne wallahi kinyi min irin tsarin macen da nake son ke nan ba wani bata
lokaci ki yarda dani kawai muji dadin juna dake zan maki komai wallahi koma may
kike so idan kinyarda dani zan dinga saya maki anything, anything just kawai ki
bani hadin kai mu more junan mu muji dadi idan gida akwai idon mutane zan sama muna
wani scret place da zamu dinga hadu ehy kin gane ko.
Wani irin bakin ciki da taikacin shi suka rufe ni ban kai karshen tunane na
ba,sai ji nayi yana fadi dibki don Allah wanan idan na samayki nagama neman mata
wallahi.
Yana kokarin kai hannun shi ya taba min wuya ban son lokacin da nayar da pillow
dake hannu na ba nakai mashi mari fayauuu,
Daga inda saudaki yake tsaye tun saukana a mashin da tareni dayayi duk akan idon
shine da marin da na kaiwa yayan nashi.
Take ya dafe wurin yana cewa ke ashe baki da kunya ashe ke yar iskan yarinya ce
ban sani ba.
Har ya fara takowa daga inda yake zuwa gurin da muke don yana ganin kamar Imirana
zai iya dukana.
Sai yaga na daga hannu ina fadin dan iska kawai mara mutunci masu gadon iskanci
kaje ai kana da kauna Nafisa ka huta da ita ni ba karuwa bace .
Imirana yace wallahi sai kin gane baki da wayau don sai kin bargidan mu wallahi
shegiya yar ci rani kawai.
Ke Fatima dauki kayan ki, kishige ciki kinji da sauri najuya don jin muryan wanda
ban zata ba a lokacin duk kan mu kallon shi muke yi.
Imirana yace jimun wanan yar iskan yar kauyen fa waini zata raina wa hankali haka
ji mun ita.
Hannu ya daga wa dan uwan shi yace please Imirana is OK naga komai tun saukanta
mashi ina tsaye gaban ku ai.
Daga haka ya kama bina a,baya ina gaba yana biye dani har zuwa cikin female ward
da aka kwantar da maji aciki.
Amirah na ganin na dawo take cewa yauwa Bintu dauki kayan can da akaci abinci ki
wanke su.
Sai ganin yayan su tayi a bayana da sauri tace lah yayana ka iso ashe yace eh na
tsaya yin sallah ne da na iso.
Ban zauna ba na kwashi kayan na,wanko su kamar yadda tace ina dawowa kuma duk
suna tsaye suna magana Amira tace Bintu zoki sayo ruwa mu aje kada dare yayi ba
ruwa a gurin.
Kai haba haba Amirah why komai Bintu, Bintu dai Bintu ku kuna may ye wai please.
Nace ina kudin yake na sayo yace ke maryam jeki ku sayo a tare da ita kuna zaune
sai faman bada intruction kuke kamar wasu tsufi.
Maji da ta farka tace ai basauyi ba sai dai su bada odar yi don su sarakaine.
Sai yanzun yagane abinda yasa yarinyar ta,shiga ran maji sosai yarinyar bata da
kiuyuya kuma bata fushi.
Yace ina son a sake mata daki yanzu zan tafi nai magana gurin nurse yatafi tai
mashi bayanin yadda za,ayi.
Muna dawiwa muka samu har ya karbo takardan canza daki ko nan muka kwasa sai
sabon dakin da aka canza mu.
****** ********* ******
Dakin kudi muka koma mu kadai ne a dakin yana da tsari sosai harda dan fridge da
kayan kallo a cikin sa.
Maji har lokacin magani bai sake ta ba na kafe ta da idanu sai barci take gashi
duk ta wani ramay sosai da ita.
Ban san lokacin da tausayin ta ya kamani ba sai jin hawaye nayi sun zubo a
idanuwana sai sauka suke a kumatuna.
Ban san ya shigo ba yana tsaye yana kallo na may kikewa kuka haka duk suka juto
gareni kuka kuma Bintu sai maryam itama ta fara kuka.
Tace Tun safe Bintu ke kukan nan idan ta kalli maji nai mata magana taki bari.
Likitane yashigo dakin saye da corth din shi baka duk muka gaishe shi yake cewa
tare dan taba jikin ta har idanun ta.
Zata dan samu sauki idan ta farka amma yaya akayi kuna gari kuka bari har ciwo
yaci ta haka a gida.
Gaskiya data kara awa a lokacin bata samu taimako ba da zamu iya rasata wallahi.
Ya juyo inda nake yana fadin idan ta farka sai ki hada mata tea mai zafi tasha
sai ki bata wanan maganin da aka sayo amma don Allah kada kiyi mata wasa da maganin
don ba abin wasa bane.
Yana fita dakin na mike tare da daukan cup na fita na dauraye shi na,dawo na,saka
acikin wani leda baki.
Yace Amira waya zo daga gida cikin su Umma eh to Bintu tace ina barci wai mommy
ta shigo bayan ita ba,wanda yazo kuma.
Muna zaune dakin kowa yai shiru a cikin mu duk kowa da abinda yakeyi sai ga hjy
Kubura itace a gaba yaranta na bin ta a bayanta.
Suna dauke da kwandon da kuloli a cikin sa da flask din ruwan zafi sai ledojin
da yaran suka riko na kayan fruit.
Tana ganin sadauki take cewa ,a,a sadauki ashe har ka iso yace cikin dagawa daga
saman kujeran da yake zaune kusa da maji don ya bata guri na iso mummy.
Da sauri na mike na karbi kwandon dake hannun ta, nakao saman durowan dakin na
asibiti na aje.
Tace ai natafi wancan dakin na farko sukace min kuna nan ancan guri.
Yace eh mummy gurin can bai min ba mutane sunyi tawa baza,a bar mara lafiya yayi
barci ba da dadi.
Hakane gaskiya amma nan din kaga is ok zata samu hutawa sosai anan din.
Likitan ya shigo ko may yace kafin wata tai magana nace zazzabine wai typhod yai
mata yawa suka ce ta ce wai da sauki ai nazaci suce ciwon zuciyan tane ke batin
tashi.
Nace yama ce bata da ciwon zuciya wancan daya fadi haka bai san aikin shiba.
To Allah ya sauwaka muka amsa mata da Ameen mummy tace zamu koma don dare yayi
sosai gani da yara bandawo da wuri ba shiyasa ban yi girki cikin lokaci ba.
Anwar yana lake jikin yayan shi tun shigowan su dakin yagan shi ya lake mashi sai
hira suke dashi.
Tamike tare da muna sallama tabar dakin muka dan rakata zuwa kofa tace ku koma
abinku zanga wata kawana dake duty acan ward din.
Tana wuce muka dawo ni da maryam nace yaya a zuba ma abincin kaci ne?
Yace No barshi banjin cin abinci yanzu Amira tace yayana bari a zuba maka kaci ko
kadan ne don Allah.
Hakana jawo plate na,soma zuba mai abincin wanda dafa duka ne da kayan lanbu a
cikin shi sai kifi da tai amfani dashi.
Sai dan ferfesun kifi danye da tayi daban ta zuba shi a wani dan kula karami.
Shina zuba mai don nasan bai shiri da dafa duka shi sai dai da miya ko tuwo.
Na koma gefe na zauna maryam tace zuba muna abincin muci mana kin kima zauna.
Nace sai dai na zuba maki ni ba yanzu zanci ba Amira tace kinbsan bafillatace sai
kafa ya dauke taci.
Hmm aini Bintu tabani mamaki jifa yadda tai saurin boye ciwon maji wa mummy harda
cewa ance wanda yace tana dashi bai san aikin shi ba.
Nace eh mana yanzu da anfadi gaskiya sun samu na fadi kena a unguwa cewa
bakinciki ne zai kasheta ai likita yace kaza yace kaza.
Maryam tace wallahi kamar kina zaune kuwa don tana komawa zakiga muna fukancan
sun tambayeta may ke damun ta kamar da gaske da an fada masu shike nan an samu na
fafi ana canza magana.
Sadauki wanda yake zaune yana shan ferfesun shi hankali kwance bai ce muna kala
ba.
Suna cin abincin duk kamshi ya bude dakin sai hira suke kasa kasa kan mummy a
gidan su .
Yana gama wa yadago kai muka hada ido na daure fuska na yace kwashe kayan nan
anan .
Sai da ya sha ruwa yace ke may yasa bazakici abincin ba ke nace sai anjima zanci
yaya nadan sha lemo dazun.
Ya dan kalleni kamar mai nazari can yace su waye zasu kwana anan don dare ya soma
sai nakai sauran gida.
Maryam tace sai dai abar anty Amira tunda itace babba ko da sauri tace a,a
wallahi ban iya tsayawa ni kadai don tsoro nake ji.
Baki da hankali ne idan baki zauna ba wazai zauna dama ke dakike babba wallahi
yayana ban iya zama ni kadai anan gaskiya.
Nace dama ka barsu yaya dama ni anan zan kwana ai tare da mama su tafi gida su
huta su.
Yace don may za,a barki ke kadai dole dayan su ta tsaya tare dake a nan ya wuce
da maryam mukuma muka zauna dakin nan zamu kwana da mama.
Azaton mu ya tafi ke nan can sai gashi ya dawo dauke da ledoji ya sayo muna su
kayan shayi da kwalayen drinks sai naman kaza mai zafi ya kawo muna.
Yamika muna yana cewa kuci naman kubar wa maji idan ta farka kila ta danci
Amira ta jawo ledan gamu tana fadin oya muci Bintu nace fara ci ke, nan tafara
yagan naman tana kaiwa bakin ta.
Zaune yake a saitina yana amfani da wayan shi data dauke mai hankali.
Yace wai may yasa ke bazakici komai bane wai, na dan tsuke fuskana san nan na ce
haka kawai .
Yace amma badon kin ci wani abuba ko kin koshi ba ko?
Nace ban karya ba yaya ban dai iyacin komai ne saboda hankalina daya tashi.
Yaya na fada maka bar Bintu haka take ita bata damu da cin abinci ba fa ita.
Ya dubi Amira yace kina nufin zata iya kwana a haka bata ci komai ba?
Haka take ko agida sai maji tai mata fada take cin abu ita.
Yace tura mata naman da kwalin drink din tasha ban musa musuba na dauki yaka
gudanakai abakina da kyat nake iya taunawa na dauki drinks din nakai abikina sai
naji sanyin shi yai min yawa sosai.
Haka dai na danci naman nasha drinks din kamar wace za,a kama a lokacin
Wayana yai ruri da sauri na nufi side drower dana aje wayan akai.
Ina kokarin duba maikirana a wanan lokacin don dai nasan ba Kabir bane don a
lokacin yana cikin iyalinshi.
Sadauki ya kafe ni da ido don jin waya kirani a wanan lokacin kuma ko zanyi
fitsaran dana saba na waya agaban mutane dayace inayi.
Na daga tare da sallama sai naji muryan gwagona tana tambayana jikin maji nace
gamunan ma asibiti da ita an bata gado.
Nan take ce min insha Allahu gobe tun da safe zata shigo gari don yanzu tafi gane
ma ta dinga kai kaya gari gari.
Ina kashe wayan maji tana,farkawa duk mukayi kanta gaba dayan mu muna mata sannu
da jikin ta.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA,BA
KA DA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,,,
Kudi yabashi har dubu daya,yace yaje yasaya duk abinda yake so dashi yaron bai san
girman kudin ba yadai san ko nawane don yaka,yaje ya fara sayen abinda ke ran shi.
Kayan zaki sai kayan sanyi su ya,kwasa ya sha har yafara kyautawa,abokan shi.
Ya dawo dauke da roban shi dakin sisko nan suka zauna ya sa masu wasan turawa
suna kallo daga,shi sai shi a daki.
Can sai ya sauya tasha inda ake wani wasan shedana zallah.
Yaron sai ya,fara kawar da kan shi gefe sisko ya ja mai kafa yana fadi ji dan
nema kaida wata rana zaka zama boss da wanan harkan kake kawar da fuska ai gara ka
fara koyo tun yanzu.
Nan dai har yaron Aliyu yadan fara tsayawa yana kallo ta gefen idon shi ajima
kadan yake cewa zai tafi gida sisko yace kai tun yanzu yace lokacin zuwan shi
makaranta yayi ne.
Jawo shi yayi kamar wandaya,samu budurwa yana dan wani wasani dashi sai da yaji
dai,dai ya sake shi da zai tafi sai da ya,kara mai dan kudi saboda jan ra,ayi gobe.
Ruwan sai makaranta,wasu, almajirai yakai yace inji wani mutum yace na bayar
sadaka anan.
Shi kuma ya kama hanyan gida yana murna da farinciki ya isa gida ya mika