Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
mu a
haka.
Dara daya idan Allah yaso sai a wayi gari si gan mu yadda ba su zata ba,a,rayuwan
su yace hakane maji.
Tace amma fa hakan ba,zai samu ba gare mu sadauki sai ka mayar da kan ka abin
kwarai a,gurin Allah.
Don kai yanzu kamar uba kake agare mu baki dayan, mu ni da yaran nan, sai dai
kuma hakan ba,zau samu gare mu ba,sai ka,zama kamili, mai addini, gujewa sherin
shedan akoda yaushe.
Haka,zai sa mu cin wa manufar mu da muke fatan samu a,gare ka.
Don Allah sadauki ka,tausaya min ka,taysayawa rayuwanka,ka mayar da kanka
tsarkaken mumuni dan albarka a cikin al,umma idan kai haka,ni wallahi ka gama min
komai wallahi.
Yana zaune yai shiru yana sauraren hudubar da mahaifiyar tashi take mashi akan
sanadiyar irin sake maganan da,ake ta,mata daga kishiyoyin ta,a,tsakar gida har da
yaran su ma.
Wanan nasihan na maji da tai mashi yasa shi jin wani irin sauki a zuciyar shi
kodon kalman Allah yai maka,albarkan dataita nanata mashi ne tare da neman masu
shiryuwa na,alherin a rayuwan shi da,daukaka mai albarka.
Da,dare ba karamin farin ciki sadauki ya tsinci kan shi a ciki ba don duk wani abin
da yake ji cikin zuciyar shi yanzu ya,kau mashi aran shi.
Hakane ma ya bashi dama,daga kwance yake kasafin irin abinda yake son yaiwa
mahaifan shi don su fara,alfahari dashi a,rayuwan su.
Su dai mahaifan shi murnan su kawai suke da,farin ciki akan dan su yaje lafiya ya
kuma,dawo masu lafiya yadda suke fata.
Fatan kawai dama Allah yasa wanan wasan da Allah ya,nufe shi da,zaiyi ta
nisanta,shi daga,akidar shi ta,shaye shayen da ya,fara nisa a cikin sa.
Gashi kuma,da,alama Allah ya taimake su akan haka don dai ko bai bari ba ya dai
rage kan don yanzu ya,dawo kamili salihi dashi ba kamar da can baya,ba da ko su sai
sunyi da gaske akan shi zaiji.
Wanan rashin nuna,damuwa da,abin duniyan da,ake tsanmani daga masu irin fita
wanan wasan kwallin da mahaifan shi suka,nuna mai ya kara sa,shi sanin cewa shi din
dan gatane na kwarai.
Sabon halin da,ya,tsinci kanshi aciki ma shaye shaye shi ya kawar mai da gatan
shi a gare su .
Adinin mu da,al,adan mu duk sun kyamaci mai wanan irin halaiyar tashi ta shaye
shaye.
Wasu hawaye masu dumi ne suka dan zubu mashi daga idon shi yai saurin mayar dasu
a inda suka fito.
Nan dai ya yanke hukuncin duk wasu tdare tsaren da ya dade yana planning din su a
ran shi yana ganin komai ya tafi mashi yadda ya dace.
Kwanan shi biyar da,dawowa yafita daga gida tun safe bai ko shigo ya karya,ba.
Haka yasa hankalin Maji ya dan tashi don tasan yanzu yana gida ko yaushe bai fita
waje.
Amma yau ga abin karyawan shi bai shigo yaci ba ga kuma na rana har ana batun
kare girkin dare kuma again.
Haka yasa ta kasa daurewa tana jin shigowan Imirah gida don shi ke fara dawowa
daga kasuwa ko yaushe, da kayan cefane da dan abubuwan da,suka sayo na gida.
Maji tafito inda yake tsaye yana,ba Umma sako tace a Imirana an dawo lafiya yaya
kasuwan?
Ya amsa da Alhamdullahi a takaice kawai,
Maji tace don Allah Imirah ko dan uwan ka yana kasuwa ne tare da ku don bai
shigo gida ba tun dazun da safe .
Yace waye dan uwa na Maji?
Duk da tambayan ya bata mata rai amma sai ta share ta,dake a ran ta tace mashi
Sadauki.
Kafin yaba da amsa Umma tace, dan uwan shi don Allah gyara hausan ki mana.
Kada ki sa mashi bakin jini da zargi ga mutane, ace ko tare suke shaye shaye
dashi.
Imirah yace haba Maji, may kuma zai kai Sadauki gurin ni tunda harkan mu ba
daya,ba dashi.
Maji tace Allah sarki ai zatona yana tare da kune a can kasuwan, kasuwan kan ba
gidan yan maye bane ai.
Ba ta dai juyo ba ta koma part din ta inda dama daga itace sai Bintu su Maryam
basu dawo ba tukun.
Ba,a jima ba suka shigo dawowan su ke nan daga makarant alokacin, sai suka shiga
neman abinci.
Maryam da tafita waje ta samo ruwan sanyi don sai sun saye basu da fridge a part
din su.
Nan ta samu Umma nata fada dan may za,ace wai Sadauki dan uwan Imirah ne ganin
maryam bai hana ta fadan da takeyi ba.
Maryam na dawowa take cewa halan anyi wani abin ne wai naji Umma na tafada wai
dan shaye shaye don rainin wayo za,ace dan uwan tane.
Bintu ce tabata amsa tace kin san basu da tunane da mama take fada wai don ta
tambayi yaya imiranah yaya sadauki da,bai shigo gida,ba tun da safe yau.
Ikon Allah shine kuma abin fada inji Amirah cikin nuna mamaki karara a fuskan ta.
Komai fadan su dai ai ba,a raba anta da jini ko? Don basu san cewa wata rana suma
abin zai iya shafan su ba ko,
Nan Amira take ta fada ran ta a bace basu san shigowan shi ba sai ji sukayi ana
cewa wai kedawa ke fada haka ne Mira,
Tace hmmm ashe ma ka dawo yaya nida su Umma mana da basu so a zauna lafiya.
Nan take fada mai abinda ya faru shiru yayi baice komai ba suma dai din hakan ne.
Maji tafito da alwala tana mashi kallin mamaki tace kai ina ka,shige yau haka ne.
Yace maji wallahi ina cikin gari kayan mune ya iso shine naje nai clearing din su
a gurin da ake saukewa.
Kaya kuma wasu irin kaya ne haka yace cikin wasa yana wuce kayan yan kwallo mana
maji.
Kai kan da kwallo Allah ya inganta kawai, don ya zama maka jinin jiki ko?
Fatima kawo mashi abinci kinji tun safe mutum bai karya ba yana gurin zancen
kwallo kawai aranshi.
No Maji gaskiya,abar abincin nan don sha dan drinks a can kada naji yunwa
saidai anjima da dare zanci.
Yaro ke fadin wai ana sallama da Umar UF a waje, inji wani mutum.
Mikewa yayi yafita saida Maji tai mamaki take cewa a ranta yau kuma Sadauki akewa
sallama a gidan nan.
Allah dai yasa mutumin kirki ne ba abokan shashancin shi bane suka fara biyo shi
su mayar dashi ruwa.
Amira ce ta sako zancen abinda Umma takeyi na kokarin raba su da yan uwan su don
ganin su basu da komai wanda yakai ace sun hada alaka dasu.
To koma maye ai dai ai su yan uwanku ne kuma duniya ta sani to may ye abin
damuwan kai a ciki uwar ta,basu amsa.
Kafin tai magana sai ga sadauki ya shigo yana zama yake cewa Amirah gobe zaku
shiga school ne da safe.
Wani abin kake so ne yaya, ya na,gyara zama yake cewa bani amsa mana kafinki min
halinku na yan Nigeria.
Tace idan da abinda zanyi sai na bari sai jibi ko na shiga yace dana gode sai yai
shiru daga haka bai kara magana ba suke tahiran su kan wata yar uguwar su.
Dawowan Alhaji yasa Maji fita tabar su don zuwa gaidashi kamar yadda ta saba, Sai
da ya mike, tsaye bayan fitar mahaifiyar su, yake cewa don Allah Amira gobe ku
kwashe kayanan gaba daya kufita dashi kafin nine na safe.
Amma kada ki fadawa maji yau sai goben kawai taga kuna kwasa please angama yaya
tace mashi do ita kadaice a falon lokacin su maryam da Bintu suna ciki.
Maji na,shigowa bata ga sadauki ba take cewa,a,a shi kuma wanan din ina,ya tafi
ne wai,?
Bai faci abinci ba yau gaba daya Amirah tace yako fita ina ganin saida safe ke
nan, nan Maji tasawa maryam da Bintu kira tace su zo sukaiwa yayan su abincin shi a
dakin shi.
Tai hakane don tagani idan yana gidan ko yafita don in fita yayi to gaskiya
zancen ya fara baci ke nan kuma.
Zun dauki abincin zuwa part din samarin gidan tun daga,nesa,suka gane yana cikin
dakin nashi don wutan dakin da yake kunne a lokacin.
A hankali ta kwankwasa kofan don itace a gaba maryam hankalinta yana kan wayan
ta.
Sadauki wanda yake zaune dakin shi yana karatun wani littafi mai ban tausayi yaji
nocking din kofan shi mamakine ya kama,shi don dama har ya rufe daki ko.
Don haka ya taso ya bude don yaga wanda ke kwankwasa mai kofa a wanan lokacin
haka.
Daga shi sai yar singileti da gajeren wando irin da maza ke kwanci dashi da dare
idan zasu shiga kwana.
Bintu ce yagani da kayan abinci a hannun ta ya zuba mata ido baice mata komai ba.
Ganin yadda yake yasata dukar da idon ta kasa tana cewa Mama ce tace mu kawo maka
abincika nan.
Dan guntun tsuki yaja yace banace na koshi ba shine sai an biyoni dashi har nan
kuma.
Bai sanda maryam suke ba,saida taimagana daga bayan Bintu tace kasan maji in
bakaci ba hankalinta bai kwanci ai.
Maryam na koshi wallahi yanzun na,rage yawan cin abincin nan sosai don gudun kada
nai nauyi da yawa na,kasa yin wasa kuma.
Yace shiga ki aje min daga ciki, yadan jaye mata a hanya Bintu ta shiga ta aje
mai a bakin katifan shi da sauri tafito bata sab yana gap da ita ba sai ji tayi
tayi karo dashi.
Tsaki yaja yana fadin ke dai yar kauye ce wallahi ko baki ganine zaki tureni haka
kamar baki da ido.
Yi hannkuri ta fadi cikin dan muryanta kamar zatayi kuka shi dai ya kauce mata
ta,wuce ta gaban shi yai tsaki yace yar kauye kawai da ita.
Maryam dariya take take cewa kai Bintu ke dai matsoraciyace wallahi kamar wace
za,a kama ko tai laifi.
Har suka shigo gida Maryam tana mata dariya take basu Maji labarin abinda ya
faru.
Maji tace wallahi in yana kiramin yarinya da yar kauye sai na bata mashi rai
Allah, duk wanan kokarin da yarinya ke mashi baya gani.
Washegari kamar yadda ya umurci Amirah dayi haka,tayi don ta,tayar da Bintu
suka,fara aiki don ita a,zaton ta fenti zai sa ai ma,shiyan nasu.
Matan gidan kowa tana fita daga gidan daya bayan daya zuw gurin aikin su inda
suke gulma a ran su cewa, kullun sharan daki kamar wani tsiyane cikin shi.
Mani dai a zaton ta gyara kawai yaran keson yiwa shiyan don karan kan su kawai.
Tara da yan mintina sukaji muryan sadauki yana cewa wasu mutane ku shigo dashi
nan.
Set ne na kayan gado tare da masu hakawa aka,shigowa Maji din dasu nan masu aiki
sukansuka fara aikin gyaran guri kamar yadda ya dace.
Labule sabbi, kujeri set masu dan karen tsada, fridge sabo dal dashi a kwalin
shi, TV plastama babban size din sai center carpet mai laushi duk a falon.
Dakunan ta duka ukku an saka sabbin gadaje a ciki don shi ana shigo da kayan ya
fita abin shi waje, bai shigo ba,balle maji da imani ya cika ta tambaye shi inda
wanan abinda bata taba mafarki ba ya fito masu.
Kafin karfe biyu masu wanan aikin da yake aikin su ne har sun gama komai ko nan
su Amira suka karasa sauran gyaran da yarage masu.
Sai uku ya shigo gidan da ghana most go manya manya har guda hudu niki niki dasu
aka zube su a falon Maji.
Maji tace Sadauki zonan cikin damuwa da rudani take tambayan shi ina ka,samo
wanan kaya haka.
Ya lura cewa ta,shiga tashin hankali yasa shi zama kasa gap da kujeran da take
yace Maji ko kin manta kin gura danki tilo guda sadaukar da ranshi wa kasanshi ne.
Yace abinda kika yarda shine alherin shi ya fara zuwa maki a yau din nan duk
abinda zan samu ga,wasan da nakeyi Maji nakine ke da yan uwana gasu nan.
Sai mahaifina da kuna kakannina da suka nuna min hanya madaidaiciya da ta dace
dani.
Don haka kwantar da hankalin ki Maji dankine ya,fara kawo karfi lokaci yayi da
zamu fara shiga mutane muma ayi damu.
Maji yau ina matan gidan nan suke?
Duk sun fita gurin neman na kasu da rufin asirin diyan su, amma ke kina gida kina
masu bautan da basu gani har abada.
Idan na samu bakiji dadin ba Maji ai ban haihu ba gare ki.
Wasu hawaye ne masu dumi suka zubo mata don abin kamar a mafarki take ganin shi a
ranta.
Ji yayi ta dafo kan shi abinda ta dade batayi mashi ba tun yana yaro in zasu tafi
makaranta take mashi haka.
Takance Sadauki Allah ya tsare min kai Allah yabada sa,a Allah ya daukaka min kai
Allah ya albarkace ka da arziki ta hanyar alheri.
Yau ma da yaji ta dafa mashi kai yasan maka manci haka za,ayi sai yaji tace.
Allah nagode ma daka azurta min Sadauki ta hayan daka zaba mashi a rayuwan shi.
Ya Allah ka tsare min shi ka kare min shi daga duk wani abincutarwa da kuntatawa
a,rayuwan shi Allah ka albarka ta min wanan yaron fiye da tsamanin mai tsanmani,
Ya Allah ,,,,,,, sai kawai kuka mai karfi ya subce mata ta kasa karasawa abinda
tai niyar fadi daga karshe sai a cikin ranta tafadi Allah ka,azurta shi da zuria
masu albarka.
Bintu ce mai karfin halin amsawa don duk kuka suke adakin gaba dayan su har ita
Bintu din dake kallon ikon Allah.
Saida sukaci kukan shi ne ya,fara yin shiru cikin su yake cewa Amira dauko
jakarcan na baya ki bude.
Tajawoshi dakyat zuwa gaban su inda ta bude turamay zannuwane irin na kasar ghana
ciki makil dasu.
Yacd tajawo dayan kuma shima dogayen riguna ne na yan mata acikin sa su takalma
da hand bags, nan suka,rude suka shiga fitarwa,
Dai dayan shadda ne ciki masu tsada suma dayan kuma kayan kantine nashi da yan
kanneshi kana yasayo masu.
Nan ya,ware wa kowa naahi kason kamar yadda yasayo su tun can ghana din.
Maji tai matukar jin dadin haka a,ranta don yafara da yaddaya dace duk da nagari
yayi yasamu yan uwa su sheda.
Tasan Allah ya hore mata da nagari wanda yasan zafinta da darahan ta a idon
duniya ke nan.
Yace ban sayo maki kayan kitchen ba don ban san kayan da kuke so ba sai a saya a
nan kawai.
Maji tace a,a dakata ko wanan ma sun isa haka wallahi.
Saidai banji ka fadi may kaiwa mahaifin ku ba har yanzu don baiyuyuwa ace ni kai
min haka amma shi banji nashiba.
Yace Maji na Baba daban ne nasan ya dade yana son harkan noma don haka noma nake
son yafara bana sosai akwai kudin da zan bashi wanda zai dan isheshi yafara dasu.
Allah yai maka albarka sadauki takara fadi a fil kowa yace amin cikin jin dadi
da farinciki.
Gardama ya fara a tsakanin Amira da maryam gurin rabon kayan su nan ya fitarwa
kowa da wanda ya sayo mata ya mika masu.
Bintu dai tana gefe tana kallon ikon Allah da jin dadin uwayen dakin ta ganin
farin ciki ya sauka masu yau.
Maji tace ban fa gane ba sai duk suka joyo suna kallonta don jin may zatace
dashi.
Tace naga kayan su Amirah amma banga na diyana,ba mana ko ita ba yar uwarka,bace.
Shiru sukayi gaba daya don su sai a lokacin kan su ya kawo wuta ga hakan.
Shiru yayi bai bata amsa ba kamar badashi takeyi ba ma sai da takara tambayan shi
ne yake cewa ban sayo da itaba Maji.
Don may sadauki shiru yayi kawai yana dakilar wayan shi bai bata amsa ba.
Ta juta gurin su Amira tana ffadin ku miko min kayan nan a,kasa uku kowa ya
kwasa.
La Mama don Allah kibar masu watarana idan ina da rabo za,a sayo dani ai.
Ba zaiyuyu ba gaskiya ku miko min nan kawai kunji tafada cikin bacin rai yace
Maji bar masu sai a sayo mata a nan.
Amma maji bata saurare shi tai masu jan ido suka miko kayan inda ta raba daidai
ta cirewa Bintu suna ta bata rai don may za ai masu haka.
Waya ma dole bai basuba saida dare ya shigo da guda hudu sai dai na Bintu baikai
nasu kudi ba.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
A LOKACIN MU KE,,,,,
Yau kwana arbain da,wasu yan kwanaki da tafiyan Sadauki don haka a wani yammaci
Alhaji ya dawo kasu Maji ta tafi gaishe shi yake ce mata.
Maijidda kunyi waya da Umar yau kuwa tace bai kira mu ba don kasan kiran shi
nada wahala ta nan.
Indai ba shine ya kiramu ba ni ban faye kiran shi ba gaskiya, ya dan juyo yana
kallonta ciki kada kai yace haba maijidda ya wuce ki kashe dubu daya da dan kai
gurin jin lafiyan shi kawai.
To Alhaji kudin fa ai yazama cacan kudi kulun gaskiya ace dubu dubu haba dai idan
dai ya kira muji lafiyan shi ai.
Yace tau yace min insha Allahu gobe zai karaso gida don yau jirgin su ya,sauka
Nigeria da safen nan.
Wani irin murmushin jin dadi Maji ta sauke a lokaci guda afili kuma tace Allah ya
kawo muna,shi gida lafiya.
Alhaji ya amsa mata da Ameen yace da farko naji tsoron tafiyan yaron nan amma
kinga da muka,bar ma Allah zabin shi gashi har sunje sun dawo lafiya.
Maji tace a hankali Alhaji nafika jin tsoro don ina gudun yaje ya kara hinjire
muna a can.
Ai kawai al,amarin daga Allah ne maijidda don dai ni san ba wai rashin tarbiya
bane ya jefa yaron nan cikin wanan yanayi.
Jerabawa ne kawai daga Allah ya zo min ta hanyan shi wanda mafi yawan mutane
yanzu kowa da kalar tashi jerabawan da,ake jarabtar shi dashi.
Allah ya sauwaka