Advertisements
Chapter 20 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   20 / 92

57K to 60K   out of 275.8K words

akwai wata a kasa ke nan ko ya tambaye ta don son
jin may zatace.
Tace gaskiya kasan halin dan yau fa kada ya yaudare ku da,wasan kwallo ya fada
wani harka na tir da Allah waddai.
Cikin mamakin jin abinda ta fadi yace assha kubura ban zaci jin wanan magana daga
bakin kiba wallahi.
Sai lokacin ta tuna tayi barambarama fa don mahaifi mahaifine ai,da sauri ta
gyara zancen tana cewa a,a ba wani abu nake nufi ba kasan halin dan yau ne shi yasa
na ce a dai bincika kawai ba wani abu ba.
Nan dai taita kamay kamay ta tafita shi dai yana jin ta kawai baice mata komai.
Kwana biyu sai gashi zance na yawo a gari da unguwa wai ya samu kudi ba,a san
inda yasamo ba sai facali yake iyayyen shi suna jin dadi.
Wasu suce wai ba kwallo aka dauke shi ba zuwa akayi dasu suka fita da kwaya kasan
waje shine aka fake da kwallo kafa.
Maji dai da zancen yazo kunnen ta da farko ta so tayar da hankalin ta don sai da
ta tsure sadauki a dakin ta take tambayan shi gaskiyan zancen abinda taji.
Murmushi shi na rabin fuska kawai yayi mata yace haba Maji idan wani ya fadi an
yarda aike bai kamata ki yarda da wanan zancen ba don kin fi kowa sanin halina.
Ban son raini da wullakanci shiya sa na roki Allah yai min mafita na dogara da
kaina.
Nan dai hankalin ta ya kwanta tace koma,waye yai muna wanan sherin mun barshi da
Allah shikw nan.
Takara ja mashi kunne akan ya futar da ita da yan uwan shi daga kunyan duniya don
mutane yanzu ake kiwo ba dabbobi ba.
Bata hakkura ba ranan da take da girki ma saida ta samu maigidan su da wanan
zancen.
Yace au kema ashe zancen yazo kunnen ki amma ya kamata ace kin san halin abinda
kika haifa.
Ni ban ji ko dar ba akan maganan nasan kawai hassada ne irin ta mutanen yanzu
kawai.
Amma ai watarana gaskiya zatai halin ta don shi kwallo ba,sanar boye bace duniya
tana sanin mutum a lokaci guda.
Ki dai yi mashi fada yai tanadi kada yaga kudi suna shigo mashi haka dayawa
lokaci guda yace zai bullo da shashanci cikin rayuwan shi.
Haka yasa tattara zancen ta watsar tabar masu hassada akan danta suna zuba mashi
taki.

****** ********* ******
Sadauki yana zaune a cikin falon Maji duk kannen shi sun tafi makaranta sai ita
dake final exam din ta yanzu.
Wayan shi yake dakila ta hanyar yin game da ita,Bintu tafito daga cikin dakin
kwanan su bata san da yana falon zaune ba a lokacin.
Tana saye da da dogon riga na atamfa a jikin ta, style din dinkin da akaiwa rigar
yai matukar mata kyau a jikin ta.
Tunda ta sanyo kai falon ta gashin a zaune sai taji gaban ta ya fadi don a
rayuwan ta ta tsani ta gan shi a falon zaune don yawan takuran da takeyi.
Jin motsin da yayi a zaton shi ko Maji ce tafito daga cikin dakin yasa shi daga
kai ya kalleta.
Bintu ce ya gani tana kokarin komawa cikin dakin da tafito din,cikin sauri.
Yace cikin daure fuska ke zo nan kina abu kamar muna fuka dake, cak taja ta tsaya
tare da juyowa inda yake zaune.
Yace ina Maji take ne ban ji motsinta ba ya tambaya cikin ci gaba da latsan wayar
shi .
Tana dakin Baba tana gyarawa amma yanzun zata dawo,,,
Hannu ya daga mata yana fadin ban tambayeki ba bani abinci na naci yace cikin
gadara da daure fuskan shi.
Haka ta karasa fitowa ta gaban shi ta wuce ba don taso ba inda yabi bayan ta da
dan tsuki yana fadi a ranshi jita dan Allah kamar zata kare, mace haka ba kiba ko
kadan.
Tafito da abincin cikin sabon kulan shi da ake saka mai abinci ta aje a gaban shi
ta juya zata dauko ruwa ya kara binta da kallon haushi.
Yadan kara jan guntun tsuki wanda yai daidai da shigowan Maji falon, tace, a,a
Baba na kai dawa kuma ke wanan tsuki haka kai kadai?
Yace kai tsaye ni da wanan yar kauyen mana tafito taganni shine kuma wai zata
gudu anya maji yarinyar nan kuwa tana da gaskiya ya fadi tare da,dago kan shi yana
kallon Maji.
Wani kallon da yaga tana mashi yasa shi shan jinin jikin shi ta,wuce zuwa ciki ta
aje kayan dake hannunta.
Jima kadan tafito ta zauna tana fuskantar shi tace gaskiya banjin dadin irin yadda
kakewa yarinyar nan,
Ko banza taci albarkaci na nida na ajeta a gurina bawai bata da gata bane a,a
itama tana da gatan ta rayuwane kawai yasa ka ganta anan din.
Amma yarinya tana tsaye tana iya kokarinta a kan mu kai kuma,sai binta da hattara
kakeyi da wani zataji na rashin iyayyenta kusa da ita ko kuwa da halinka zataji.
Ban son karatun yarinyar nan ya tsaya ne shiyasa kaga ana ajeta a gurina don
itama watarana iyayyenta suyi alfahari da ita.
Ashe ba dadin ku bane yau ace a sanafin mu ta zama wani abu a duniya, ban rokeka
komai don na tallafa mata ba.
Amma kasa yar mutane gaba haka da tsangwama tare da hattara ba yau ba ina lura
balain tsoron ka fatima takeyi wallahi.
Wani kunci ne yaji ya rufe shi a ranshi ya mike ba tare da ya gama cin abincin da
yake ci ba ya bar falon cikin fushi.
Maju da tabishi da kallo ta,tsuki tace sha sha kawai mara hankali mutane suna
bakin cikin zaman ta anan kaikuma kace zaka tsiro min da naka kalar tsiyar a kanta.
Tsayin sati daya sadauki yana fushi a kan maganan gashi ya hana Bintu sakat a
sashin nasu don da ya shigo ya kama hararan ta ke nan da kuma tsuki.
Allah Allah Bintu keyi ta gama exam tabi gwagonta kauyen su don dama zaman dole
take a gidan.
Hankalinta yana gurin iyayyen ta da yan uwan ta don tunda tazo bataje gida
ba,bata kuma ga kowa ba cikin su sai gwago dakan dan zo ta kwana biyu ta koma.
Allah ya taimaketa kafin su gama exam aka kirasu Abuja inda ya kwashi komatsen
shi yanufi gurin kiran da akai masu.
Hakan ya,dan ba Bintu daman sake jikin ta har maji ta fahince ta tafi sake jikin
ta idan baya nan ke nan.
Amma tana gama exam ta fito da zancen son zuwa gida don tagano yan uwanta.
Hankalin Maji yai matukar tashi a lokacin inda take tambayan ta cikin lalashi ko
an mata wani abine take son zuwa gida.
Bintu tace cikin sanyi murya da,sauri a,a mama ba ai min komai ba ina dai son
zuwa,nagan su ne tunda nazo banje gida ba shiyasa nake son zuwa nagano babana da
yan uwana.
Maji ta sauke ajiyan zuciya tare da,tambayan idan kin tafi yaushe zaki dawo
Fatima?
Don nasan ko kwana,nawa zakiyi acan saboda na tura a dauko ki in lokaci yayi.
Bintu tana,wasa da yan tsunta,da,harde su guri guda tana cewa mama sai na tafi
tukun don ban san hukuncin da mahaifina zai yanke a kaina ba yanzu tunda na gama
karatu na ko.
A,a Fatima idan hakane ki bari mu tafi tare sai mu kwana daya mu dawo, tare.
Da sauri Bintu ta dago kai tana fadin mama har gurin mahaifiyata nake son zuwa
don mun dade bamu ga juna,ba da ita.
Eh to gaskiya hakan yana da kyau kuma ina ga,dai kila zakiyi sati biyu zuwa uku
ke nan eh mama Bintu ta bata ansa da hakan wanda ta dai fadi ne don su rabu lafiya
da maman nata sabuwa.
Amma yadda tajeji bata sa ran cewa zata dawo wanan gidan ba kuma da sunan zama
duk da dai ba ai mata komai ba amma gidan ya fita ranta don tana gudun kada sanadin
ta mama tai fada da dan ta daya shiryu yanzu.
Tsaraba sosai Maji ta hadawa Bintu na gidan mahaufinta da yan uwan ta daban wanda
zata kaiwa mahaifiyarta daban.
Mota akai mata shata ita kadai Alhaji yabiya tare da bata kudi da zata rike don
amfanin ta a can.
Kamar yadda akai alkawari da driver hakan yayi har kofan gida su Bintu ya kaita
inda aka,ganta a bazata don ba wanda yasan da zuwan ta.
Irin kayan da,akaga a na,shigowa dashine yasa hankalin matar uban ta ya tashi,
har ta kasa boyewa da zuwan Bintu din.
Nan dai kowa ya,wayance sai sannu da zuwa ake mata ana kallon yadda a lokaci
daya ta canza kamanin ta gaba daya ta koma wata yar Birni da ita.
Kafin wani lokaci har zancen dawowanta ya zagaye dan kauyen nasu kowa na fadin
Bintu ta dawo ta koma yar Birni da ita.
Saida dare ta samu ganawa da mahaifinta wanda ya dawo daga gona a lokacin ana
gabanin magariba.
Nan suka kebe tana bashi labarin zaman ta a burni da kuma mutanen arzikin da
gwagon ta,tabarta gurin su.
Takawo sakon da maji tabata na,tsaraba ta bashi yana ta murna da farin ciki.
Bintu ta sheda mai ta kare karatun ta har matar dake rikon ta tace zata ci gaba
da karatun ta idan jerabawan ta ya fito.
Mahaifinta yai farin ciki da jin wanan albishir din da tai mashi sai dai kuma
yasan abune mai wuya yadda ta girma haka yan uwan shi su barta taci gaba da karatu
sai dai in Allah ya nufa zatayi din.
Washegari Bintu kamar yadda ta,saba zuwa daukan karatu a lokacin da take gida
hakan ta shirya zuwa islamiyan su.
Sai dai ta samu yawanci yan matan da suke karatun tare sunyi aure a lokaci, dan
kauye basu bari yarinya tagirma sosai suke mata aure.
Malamin nasu yai farin ciki daganin hazikan daliban shi ta dawo kuma bata
watsar da karatun ta ba don taje birni.
Taso ta fara a inda ta,tsaya da karatu a gurin shi amma da,tafara biyawa sai
yaji ta,wuce tsanmanin shi.
Don haka yace ta dauka a inda,take can birni haka yasa taci gaba don ta sauka
bita take yanzu.
Ganin duk idon sauran dalibai yana kanta kuma suna sauraren yadda sabon sallon
karatun ta yake fita.
Duk sai sha,awan ta ya kama su nan suke zuwa wai ta koya masu yadda take fitar da
haruffa cikin kara harshe.
Nan fa samarin kauyen masu jin sun isa suka fara kawo kan su gareta da,sunan sun
gani suna so.
Itako mama ta,bawa matar ubanta tunda ta kyala ido taga kayan maihaifiyan Bintu
da maji ta bata ta sa a ranta su take so.
Bayan nata da,takawo mata da yaran ta duk sai da Maji ta ba kowan su tsaraban da
zata basu in tazo.
Haka ta,bawa tasa Bintu da mahaifinta gaba da masifan kan lalai sai dai ta dauki
turmin wajen ina da aka bata takai mata.
Har abin yaso yakawo sabani a tsakanin ta da mininta watau mahaifin Bintu.
Don haka Bintu ta tsiri tafiya garin da mahaifiyarta take bashiri don tabawa sai
fada takeyi wai bayan tagama wahala da ita yanzun anga dadi yazo shine zatace tasan
uwar ta.
Bintu dai murmushi tayi kawai tana hada kayanta tare da tunanen yadda zata zauna
gida da wanan masifanna matar mahaifin ta kulun.
Ta hada duk dan abinda tasan tana so tana bukata a cikin kayan ta tafito tare
da,yi masu sallama ta tafi abinta badon ta tashi zuwa ba.
Ganin ta kawai mahaifiyarta tayi a bazata don rabin ta da ita tun tana aji hudu
na primary bata sake zuwa ba don maigidan ta baida dadi ko kadan.
Bai son yaga Bintu tazo wajen uwarta ya shiga fitina da mitan shi baison zuwanta
tana zuwa tana hure mata kunne don ta koma gidan mahaufinta.
Ta,samu mahaifiyarta da tsohon ciki a jikin ta kuma yana bata wahala don haka tun
zuwan ta bata huta ba.
Da maigidan ta ya dawo daga Kasuwan kauye ya samu Bintu tazo ya dan fara daure
fuskan shi.
Saida yaga abin arzikin da tazo masu dashi don har shima ya samu shadda yadi
goma.
Shine har ya dan sake fuskan shi, yazo har dakin su fuska a sake yana cewa ,a,a
Bintu harda tsaraba muka samu haka mai yawa.
Har yana tambaya ko taci abinci da tazo nan dai ya karaci surutin shi ita dai
Bintu kai kawai ta gyada mashi har ya fita.
Washe gari tun da safe Bintu ta tashi ta gyara ko ina na gidan nan gidan yakoma
wani fes dashi.
Sai zuwa rana ta fahinci ko abinci basu dashi a gidan nan ta saka katon hijjab
din ta har kasa ta fita can sai gata da kayan cefanen ta niki niki mai mashin ya
kawota gida.
Bata tsaya ba ta girka masu abinci suka zauna ita da yan kannen ta suka ci suka
koshi harda mahaifiyarta dake auren wahala.
Maigidan sai zuwa rana ya dawo yana yan kamay kamay shi wai tunda ya fita ko
sisu bai samu ba sai dan fura da akabashi da nono yace a dama,mashi,
Matarshi ta mike da kyat ta shiga daki sai gata dauke da kwanon abinci yana
mamakin ina tasamu kudi har tai masu girki.
Bayan ta aje yake tambayan ta don ya zaci taciwo mashi bashine don diyarta tazo
ta girka masu abinci.
Matar tace mashi yaringa ce ta sayo ta girka muna nan ya wani washe baki yana
bude kwanon yai tozali da shimkafa da miya harda nama a ciki.
Yashiga ci yana sakawa Bintu Albarka tare dakai lomar abinci a bakin shi.
Bintu da ke daki tausayin mahaifiyarta ya kamata don tasan wanan susun mijin nata
bai aje komai ba sai bakin shaye shayen da yakeyi kawai.
Abu tun bata da,wayo yake haka har yanzu data girma ta zo ta samay shi a hakana.
Dalilin da yasa ke nan take matukar tausayawa Maji akan shaye shayen da dan ta
yakeyi don tasa mugun abune mawuyacin abune mutum ya daina shi a rayuwan shi.
Da yamma sai gashi da dan kunshin a leda yana wargale baki yana fadin ina,diyata
ne gashi ba,sayo mata dan abin mu na kauye taci don nasan can birni basu samun shi.
Bintu najin haka tafito daga dakin tana gyara daurin dan kwalinta ta nacewa gani
Baba.
Ya mika mata ledan ta,karba batare da,tasan abinda ke cikin ledan ba yana fadin
ki gyara kici abin marmari ne gare ku.
Ta dauko kwanon ta bude ledan zogalane da rogo dafafe da zafin shi ya sayo mata
harda kulikulin da zata gyara shi ya hado mata.
Bintu ta zauna ta gyara tasamo wani kwanon silver na miya ta zuba mashi azaton
ta,bazai karba ba sai gashi ya karba har ya riga su cinyewa ko.
Sai faman santi yake zubawa sosai taji dadin ganyen don ta dade bataci ganye ba
haka mai yawa.
Kamar yadda tai masu girkin rana haka ta girka mazu na dare inda tai tuwon garin
masara data sayo da miyar kuka yaji daddawa da kayan yaji sai kamshi ke tashi ciki.
Haka ta zauna gidan mahaufiyan ta don yafi mata dadin zama gidan mahaifinta da
matar uban ta ke sakata gaba da fitina kyashi kishi da hassafa duk ta dagwara mata
shi.
Satin ta biyu a kauyen bata fita ko ina kulun tana gida da yan kannen ta suna
hira ko tana koya masu karatu.
Ranan dai mahaifiyarta ta matsa mata akan tafita taje gidan yan uwan ta,su
gaisa.
Ba don Bintu taso ba ta shirya tare da yan kannen ta mata biyu suka fita zuwa
gidajen dangin su.
Suna gap da zasu dawone suka hadu da,wani matashi daganin shi kasan bako ne a
garin ko kuma dai yazo ne ba,a nan yake zama ba.
Saboda yanayin shigar shi jikin shi da suturun shi ya banbanta da na mutanen da
yake tare dasu a gurin.
Tun da su Bintu suka tunkaro idon mutimin yake kanta duk da katon hijjab din dake
jikinta bai hanashi kallon ta ba.
Sun kawo daidai inda suke Bintu tai masu ina wuni gaba daya suka amsa cikin washe
baki, a hankali mutumin ya tambayi wanda suke tare wanan a garin nan take ne ?
Har zasu wuce sai dayan mutumin yace wa dayar kaunan Bintu a,a Dije bakuwa
kukayine yarinyar ta tsaya tana cewa eh yayan mu dage Birni ne tazo.
Su dai suka wuce zuwa gidajen da Inna ta tsara masu sutafi sukai Bintu ta gaida
su.
Agajiye suka dawo gida lokacin yanma tayi ko gashi batai sallah la,asar ba don
haka ta shuri buta ta nufi gurin alwala don kada lokaci ya shige.
Inda ta idar da sallah tana zaune mahaifiyarta take tambayan ta kawo mata
abincine tace sun koshi tasha fura a gidan kakanta.
Sai ga,yaro yana sallama yace wai ance ana sallama da bakuwar gidan nan.
Bintu dake daki a ran ta tace ai kaji matsalar wallahi shiyasa ban son fita ko
ina wallahi.
Bata so fita ba amma mahaifiyarta ta takura mata akan sai tafita badon taso ba
haka ta shirya tafita cikin katon hijjab din ta kamar kullun.
Wanan mutumin da tagani a cikin gari dazun shine tsaye a kofan gidan nasu ya
jingina jikin shi da motar shi baka henixe,
Yana dan kada makulin motar dake hannun shi a hankali, yana ganin fitowan ta ya
dan fadada murmushin shi.
Yana cewa barka da fitowa gimbiya sai kika gannin kwasan kofan gidan ku babu
tsanmani kuma ko?
Murmushi tayi tana fadin ina wuni yace shaf kinga na manta bamu ko gaisa ba ko ya
kuke ya garin kuma?
Ta amsa da Alhamdullahi,
Yace ko da yake nasan ke bakuwa ce a wanan garin don ban sanki ba a garin namu.
To nidai sunana Mohammed Kabir kuma ni haifafen wanan garin ne ina aiki a abuja
ne ina da mata biyu da yara biyar.
Jin haka Bintu ta dago kai tadan saci kallon shi yace yes kwari kina

20 / 92