Advertisements
Chapter 53 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   53 / 92

156K to 159K   out of 275.8K words

yi mata tsinanen duka don taga a
tsaye suke su ma.

****** ********* ******
Haka kawai ranan na tsiro da tafiya kauye ba,shiri nacewa mama dake shirin zuwa
gidan buki zan tafi garin mu yau.
Da sauri ta juyo ta fasa daurin dan kwalin da takeyi tace zaki kauye Fatima ?
Na dukar da kaina a kasa nace eh mama mamana ce bata da lafiya jiya ake fada min
a waya da dare.
Tace assha amma gaskiya ban son tafiyan ki a motan kasuwa yanzu da zaki bari zuwa
jibi idan angama bukin nan sai nasa a kaiki.
Nace mama yau nake son zuwa don na dawo da wuri insha Allahu ba abinda zai samay
ni mama ki kwantar da hankalin ki.
Ta je gun jakkan ta na hannu ta dauko min kudi sun kai dubu goma tace gashi kiyi
kudin mota dashi idan min tafi yadda kika samu jikin nata sai ki min waya nace
nagode mama.
Sai da na gama shiri na tsab na fito falon lokacin su Amira ne kawai a falon
ganina da jakka kamar may shirin tafiya suke tambayana.
A,a gaki kamar may shirin tafiya mana Bintu ?
Nace eh anty zani kauyen mu ne yau, gurin mamana har ma gurin babana zan leka na
kara dubo shi insha Allahu.
Maryam tace yaushe zaki dawo nace sai na kwana biyu gaskiya to Allah ya kiyayye
hanya.
Har kofan gida inda zan hau Napep din da zai kai ni tasha maryam ta rako ni na
tafi.
Sai dai a cikin ranta bawai ta yarda da zanyi tafiya bane don ganin mahaifiyata
kawai dai na gudu ne don kaucewa yayan su sadauki.
Amma sai ta sa a ranta zata saka ido taga shi wani reaction zai yi akan tafiyan
nawa.
Takira Bashar din ta take fada mashi da kuma abinda itama take kullawa yace haka
daidai zan tayi saka ido nima insha Allahu.
Ban isa gida ba sai da yamma don ban fito da wuri ba kuma motan bata tashi da
guri ba.
Ina isa gida sai ganina mama tayi kwatsam tace a,a ke kina hanya ne ashe nan muka
gaisa nafito da dan tsaraban da na kawo masu aka shiga rabawa.
Dakin da bakowa suna aje tarkace a cikin shi sai wani dayan kani na da ya dan
tasa ya dan girma.
Nan na gyara na kai yar jakata a ciki tare da shimfida tabarman kaba sabo da mama
ta bani na dinga kwantawa akai.
Ranan haka na kwana ina juyuyi don yaushe rabona da kwana saman tabar ma, zaman
birni ya fara bata ni yanzu.
Sai tunane nakeyi ko may su maryam suke yanzu don nasan dai basu kwanta ba saboda
a can dare baiyi ba sosai kila suna can suna kallon season film din da muke bi a
zeecilmer .
Miskili jarababbe mugu azzalumi na furta a fili nace yanzu ai sai ka samu wata ka
lalata ba dai ni Fatima Binta ba kuma.
Nace ko hutu ya kare ban dawowa sai naji ka tafi kabar kasan zan dawo macuci
kawai.
Allah kadai yasan irin iskancin da yakeyi can bariki idan ya tafi babu kowa nan
ma gida ya yi shaye shayen shi balle can inda babu kowa tare dashi.
Mazina ci kawai mai boye kama ashe shiyasa yake wani kallon mutane duk shakiyai
ne irin shi gashi kirkiri ya rabani da Usman ba wai ban son usman bane amma saboda
bakin zargin shi dole na rabu da Usman din ba don naso haka araina ba.
A haka har barci ya dauke ni ban sani ba sai washe gari kiran sallah da ya tayar
dani a lokacin.
Bayan na idar da salla ban kwanta fitowa nayi na gyara gidan ko ina don yana
bukatan gyara.
Ga karan gidan da akai danni duk ya tsufa har ya dan dadare daga yadda aka jera
shi da farko.
Makewayin su ma haka tsufin tsumane na wani tsohon babban riga aka tare bayin
dashi.
Ga kwata ya taru sai diyan sauro da kuda da gurin ya tara ya wani canza launi duk
da kasa ne yashi amma rashin samun gyara yasa gurin ya canza launin shi.
Nan ma sai dana gyara nasa musa kanina ya debo tsakuwa da yashi muka zuba ya
dauko wani falalen dutse muka kara dagwarawa a saman gurin don mutum ya samu gurin
hawa yai wanka.
Kafin dan wani lokaci gidan ya koma tsab dashi kaman bashi kaca kaca da farko na
dora ruwa muka dama kunu ina gamawa na dora sauran tuwo na gyara ma ma yaran don
dashi suka saba karyawa.
Sai dana gama nai wanka na shirya tsab dani dakin da nake na gyara kafin lokacin
sa girkin rana yayi.
Sai da mijin mamana naji ya fita daga gidan don bai tashi sai rana ya raba wani
lokaci ma alokacin zaiyi sallah.
Na shiga gurin ta na samu tana nade kayan wankin da na samu tayi jiya da na zo.
Nace ta bari dakin na zo na gyara mata dama nan kuma na shiga gyara nafito da
tulin shara daga dakin don irin gyaran da ake mai na sama sama ba,a kwakwalo komai
da kyau.
Dakin sai gashi yafito tsab dashi kamar dakin mace nace mata may za,a girka ne da
rana
Tai murmushi tace ai bamu girki rana sai dai da yamma idan ya dan samo muna sai
mu girka jiya ma da kikazo ai sa,a ki kayi yasayo muna dawa shine nan nai muna
tuwon shi har kika samu.
Haushi ne ko tausayin ta zai kamani na rasa may mama ta zaunayi gidan wanan
mashayin har lokacin nan.
Yanzu gashi har sun kai ga tara yara har shidda dashi babu zancen fita gare ta
kuma ke nan.
Bance mata komai ba nafita na kira musa ya sayo muna rogo da zogala a bakin yar
kasuwan su.
Nai zaune na gyara shi kowa yaci ya koshi muka sha ruwa abin mu nayi hakane don
mu kyale mugun mijin ta da baida katabus ga iyalin shi ko yaushe.
Dan na lura yanzun idan nazo komai bai saye in an tabaye shi sai yace a tambayi
Bintu ko tana da canji a sayo.
Yana ko dawowa yake tambayan ba,a gika komai bane a gidan mamana tace ka kawo
abin girki ne halan ?
Yace baga Bintu tazo ba bata sayo bane a girka din ?
Naga idan tazo takan dan yo muna dabara yanzun aci shiyasa yanzun nake farin
cikin zuwan ta furin mu ai don nasan idan tazo hankali na a kwance yake da kayan
bani banin ki.
Tace to bata sayo ba yau don haka sai ka canza tunanen ka kafita kasamo muna.
Yace kin tambaye tane tace maki babu a gun ta da zaki ce na fita in na fita ina
zan samo tunda ba sana,a nakeyi ba ni.
Sai kawai naji yana kirana ke Bintu Bintu fa na amsa daga dakin da nake nace
na,am Baba na fito.
Yace cewa nayi baki zo muna da komai bane wanan tafiyan don naji shiru har yanzu
bakice muna komai ba?
Nace ban zo da shi ba a takaice.
Kallona yake don jin yadda na bashi amsa duk nima ban so bashi amsa a haka ba don
ko banza mijin mahaifiya na ne shi.
Ina fafin haka na juya ban tsaya ba balle naji may zai kara fadi kuma tunda ba
ta ido ne dashi ba.
Yanzun kai bakaji kunyan tambayan ta wanan magana ba haka wani sana,a takeyi ne a
can kokuwa itama ba karshin wasu take bane wai ?
Yace na dai fahinci abin akwai rainin hankali watay kin hada baki da uwar ki kada
ku taimaka ko to oho akan ku zai kare ai munafukai kawai.
Idan naga abin rainin wayo ne sai yarinya ta koma gidan uban ta wallahi tunda nan
ba gidan su bane ?
Zance ke nan kake fadi ai matsawan ina gidan nan dole ne yarinyar nan ta zauna a
gidan nan ita ma.
Yafita yana fadin oya shege ka fasa ni daku kuwa a gidan nan mama tace ai ni
wallahi dana huta ta wanan wahalan.
Ni dai ina jin su nace mashayin banza kawai a raina a haka zaka kare har girma
yazo maka baka bar tabara ba har yanzu.
Muryan kani na musa dake zaune ta waje naji yana fadin ni wallahi mama da ma kin
gudu din mu huta da halin baba mu koma can birni gurin yaya Bintu muma mu huta
kawai.
Daga daki nace kai musa baka da hankali ne ina ruwan ka da saka baki ga maganan
man ya ne wai ?
Da yamma muka shirya nace su rakani unguwa duk da ban fadi inda zan tafi ba sai
gidan su marigayi Kabir naje gaida mahaifiyan shi.
Matan bata gane mu ba sai da muka shiga har dakin ta muka gaisa da ita, sai dan
shiru can tace ban ko gane ki ba.
Nai dan murmushi nace Fatima ce diyar Hausin dan Amo, tace Allah sarki Fatima kuwa
haka akayi gaskiya ban gane ki ba wallahi.
Nan ta,rasa inda zata sani don murnan gani na tace yaushe kika zo garin namu
nace mata jiya nazo Inna.
Nan muka zauna muka kara gaisuwa dasu da sauran matan gidan suna kara jajanta min
mutuwan Kabir din.
Nan suke fada min iyalin shi yanzu suna sokoto zaune don karatun yaran shi daya
bari.
Nace Allah sarki aiko ban sani ba dana shiga inda suke tace min dama ai a uguwar
GRA yake da gida an raba gado anba kowa nashi shind ita Saude da yaran ta suka samu
gidan .
Nan dai nan dan zauna har zuwa dan wani lokaci nai mata sallama muka bargida bamu
ratse ko ina ba sai gida.
Mun shigo bamu dade ba sai ga yaron gidan ya biyo mu da sakon wai inji
mahaifiyan su.
Ana wata ga wata sai ga wani dan kanin Kabir da suke uwa daya dashi ya aiko wai
yana so na da aure yana son ya maye gurbin yayan shi da ni.

****** ********* ******
An wuni an kwana har dare duk shigowan da yakeyi a gidan baiga Bintu ba a ran shi
yake tambayan wanan ko lafiya take ne ban gan ta ba duk kwanakin nan ?.
Yana son ya tambaya sai daibai son raini ko tuhuman wani abu ga tambayan da
zaiyi na ina nake kwana biyu baya gani na.
Da yamma ya shigo gidan baiko shiga part, din shi ya wuto cikin gida direct nan
ya zube a falon mahaifiyan shi.
Wayan shi ya jawo daga aljihun shi, bayan sun gaisa dasu rasa may ke mai dadi
shine ya ciro waya.
Ya fara yin game da ita sukosai hiran su suke suna kallo hankalin su a kwance
abin su sabanin shi dake a cikin damuwa.
Can yace maryam
Ta amsa da na,am yayan mu .
Yace wai ina wanan yarinyar take ne kwana biyu bana ganin ta ?
Tace yaya sadauki Fatima kake nufi ?
Yace ita din mana.
Tace ta tafi kauyen su yau kwana uku ke nan taje gun mahaifan ta ne wai zata kwana
biyu a can.
Wani irin faduwan gaba yaji a lokaci guda, yace a ran shi kodai saboda abinda ya
faru ne a tsakanin mu ta bar gidan nan don ni.
Duk sanyin AC dana gari da akeyi bai hana ahi feso wani irin zufa ba a lokaci
guda.
Take kamannin shi ya sauya a cikin, lokaci guda, idanuwan shi sun sauya kala zuwa
ja a lokaci guda.
Tankar wanda aka watsa wa barkono yace a kasale yaushe tace zata dawo ne wai ?
Tace zata kwana biyu a can don haka ba rana ke nan sai dai idan mun ganta kawai.
Yace ba kun kusa komawa school ba shine zatai tafiya taje ta zauna har wani
lokaci.
Maryam tace ai muna da sauran lokaci ga hutun mu yaya kila sai hutun ya kare zata
dawo ai?
Maryam tace lafiya kuwa yaya kake tambayan ta cikin son kara tuhuman ta akan shi.
Yace No babu komai dama zanyi bakine shine nake son ta hada min wanan abin dama
yan wasu abubuwa.
Daga haka yaja tsaki ya mike tsaye yabar falon a lokacin maryam ta dan matsa
gurin Amira bakin ta tab da gulma tace a hankali.
Cikin yanayi irin ta mai rada tace wai anty may kika fahin ta ga yayan mu da yake
tambayan Bintu.
Tace eh nima nai mamakin jin yana tambayan Bintu don naga shi bai damu da kowa ba
ai.
Hmm baki fahinci komai ba,wallahi amma ni nasan yaya yafara kamuwa da son Bintu
wallahi.
Kai haba wata Bintu can wanda ke shiga duniya yana ganin mata kala kala shine zai
tsaya son wata Bintu can.
A ganin ki ba tunda ke baki san so ba har yanzu kina nan zaune a na soyewa a gida
baki sani ba.
Ke dai wallahi akwai ki da shirmay tsiya maryam may zaiyi da Bintu wace kullun
cikin fada suke a gidan nan .
Mugun takaicin ta fa yake ji shine ke ko yar kayan soyayya kike ganin kamar shi
suke yi.
Maji da tasamu suna firan tace waye wai,?
Amirah tace wai yaya sadauki take cewa wai soyayya suke da Bintu kila a boye haba
may zaiyi da Bintu ga yan mata yan gayu iri iri a gari ko ina.
Eh tun da ita Fatiman ba mutum bace ko ke kin fita kama mai kyau ba da zakice
hakana.
Shi damay yafita ?
Ai da ta taimakawa rayuwan shi wallahi dayayi arziki in ya aure ta.
Ita Bintu din dai maji ?
Oh baki san shi al,amarin aure ba ke nan ashe da sauran ko ke tunda baki da
fahintan komai.
Ni na dade da sanin abinda yakeyi kyaleshi kawai nayi kada najawa yar mutane
matsala.
Kai haba maji don Allah kubar wanan zancen mana kada ku ja wani matsala kuma
yarinya na zaman zaman ta yasa ta agaba.
Kai amma dai anty Amirah nan .
Watarana kice na fada maki ai.
Ita dai Amirah jin su takeyi kawai don tasan haka ma bazai taba yuyuwa ba ai.
Wata Bintu can yar kauye kuma ba diyan kowa ba, a gari.
Sai ma taji ranta ya ba i kawai da zancen don abin haushima ya bata ita a ran
ta.
Yaya sadauki na barin falon dakin shi ya shiga ya fada kan gadon shi yayi lamo
saman gado.
Tan kar wanda yake barci, sai dai ba barcin yake ba yar damuwa ce da bai san
dalili ba ya dami zuciyar shi kawai.
Can ya tambayi kan shi wai may yasa har yake son damun kan shi akan yar karamar
yarinya hakane.
Gashi a yadda ya lura da yarinyar bata ma gama sanin komai ba na rayuwa don akwa
childish a tare da ita har yanzu a rayuwan ta.
Karancin shekaru uwa uba kauyanci bata san ko inaba daga sokoto sai kauyen su
kawai.
Shi dake son mace nagani nafada na gwadawa tsara shima ya faso zai tsaya ga yar
kauye kuma karama haka dako twenty bata cika ba har yanzu.
Sai yaji take wata zuciya tana gargadin shi dacewa kai baba ina kai ina wanan
tunanen kuma wai ?
Washegari tunda safe yashigo yana cewa shi zai tafi Abuja yanzun nan maryam tace
a,a yaya wai ya zancen bakin da kace kuma zakayi har ina shirin masu abinda kace ai
masu din.
Yace No maryam ki barshi kawai sun fasa zuwa din zanyi tafiya ne nima yau din
nan.
Bashar yana jiran shi a kofan gida nan suka samay shi da suka rakashi, Bashar ko
a,gaban kowa bai ita boye kaunan shi ga maryan yanzu sai ya baiyana shi a fili.
Don suna fito tana dauke da yar jakan tafiyan yayan ta, da ta karba ta saba a
kafadan ta.
Daga cikin mota da Bashar yake zaune suna karasowa idon shi akan maryam yake cewa
Madam how far?
Ita ko tai wani shake murya tace bakomai yace ya su mama tace suna lafiya.
Har sadauki ya zauna a mota Bashar sai soyewan shi yake yi hankali a kwance.
Dallah malam ja mota mu tafi da wanan bakin shirmay naka babu kunya da kake min.
Easy man, take it easy bani nakar zomon ba fa, kaga ni fa ban hanaka ba don ni
ba motsoraci bane irin ka.
Wani harara yakai wa Bashar yace wallahi zaka kaini makura Allah da wanan halin
rashin kunyan da ka tsiro wa mutane daga sama.
Bashar dai yaja motan shi yanawa sahiban shi bye bye, suka bar gurin suma suka
juya zuwa cikin gida.
Airport ya kai shi nan ya shiga jirgi da ya tashi da sha biyun rana suka tafi
Abuja, bai so buga wanan wasan ba amma halin da yake ciki yaji kawai gara ya je ya
buga ball din shi ko zai samu sauki a zuciyan shi.
Duk da kwallon da ya buga bai hana shi jin abinda yake ji a zucuyar shi ba har
yanzu.
Suna waya da mutanen gida amma bai, taba jin wani yai zancen yarinyar ba ko yaji
an anbaci sunan ta ko a waya.
Gashi girman kai ba zai iya barin shi ya tambayi kowa labarin ta ba don sai yana
ganin kamar abinda yai mata ne yake ganin bai kyautawa yarinyar ba.
Don yana gani ai kaman zaman kaunan shi yarinyar take a gareshi amma shedan ya
rude shi yai mata haka.
Yace a fili, kai kai gaskiya ban kyauta why don Allah why har haka ya kasance a
tsakanin mu ne wai.
Ya dan kai wa katifan da yake kwance nashi da hannun shi na hagu da karfi sosai
har sai da ya dan jin zafi a hannun shi.
A haka ya kai har sati biyu acan suna da wasan da zasu buga sati mai zuwa amma ya
juyo ya dawo gida haka kawai.

****** ********* ******
Ina gurin mama na

53 / 92