Advertisements
Chapter 15 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   15 / 92

42K to 45K   out of 275.8K words

da taimin magana akan zaman yarinyar gidana shine ma
dalilin da yasa na barta kowan ku bai sani ba.
Amma kubura kin bani mamaki wallahi yardane fa yasa maijidda ta barta a gurinki.
Yau ina wayon ki da iliminki ya tafi ina suka shiga da zaki turawa yar mutane
wanan akidar na bijerewa.
Alhaji nifa ba,a kyauta zan dauketa ba kudi zan bata ita da iyayyen ta don ina
bukatan taimako.
Wani irin tsuki yaja ya dauki wayan shi nomban Amira ya kira tare da babban
dan,shi yace su zo yanzun falon shi.
Ba,a dade ba sai gasu yake cewa ya raka Amira tazo da Bintu yanzun nan suce inji
shi.
Bintu har ta rufe gida da daki ammajin da tayi anata bugawa tare da kiran sunan
ta yasa ta bude kofan tafito.
Duk ta fyde ta ramay lokaci guda da ita ta canza don fitinan daya samay ta.
A tsiwance Amira tace da yaya Imirana muke Baba ne yace muzo dake yanzun nan.
Daga haka Amira bata sake cewa komai ba ta tsaya jiran ta ta shirya su tafi.
Jin Alhaji da kanshi ke nemanta yasata dauko hijjab dinta zuwa amsa kiran inda
tabiyo bayan su simi simi har falon Alhajin.
Shikan Imirana bai san komaiba ya na cewa gata nan yajuya abinshi ya fita falon
shida Amirah.
Guri ta samu ta zauna a makure duk ta kode lokaci guda da ita fuskan ta duk ya
wani kode mata.
Gaba dayan su kallonta sukeyi take taba Alhaji tausayi yace Fatima may ke faruwa
ne.
Sai tai shiru ta dukar da kanta kasa tare da sako wasu hawaye masu dumi daga
idon ta.
Ganin bazatai magana ba tasa Alhaji cewa may kike a gidan ku ke kadai baki tsoron
dare wasu miyagu bata gari su shigo maki ke kadai a gida karamar yarinya dake.
Nan ma Bintu sautin kukanta takara batare da tai magana ba sai tsoron da ya
kamata a cikin ran ta lokaci guda don ita batai ko tunanen hakan ba.
Yace kin fadawa maijjida abinda ya faru tsakanin ki da hajiya kubura ne.
Da sauri ta dago kai tare da cewa cikin kuka ban fadawa kowa ba Baba.
Baki kyauta ba Fatima don kinga amana kike a gurinta agurin mu ma baki daya idan
wani abu ya samay ki damu uwarki zatai kuka.
Baba kuyi hakkuri amma ni na guji hafin hasumi ne akaina shiyasa na kona gida.
Baki kyauta backe nan baki rike maijida a matsayin uwaba gareki tunda har zaki
iya boye mata maganan ki.
Da sauri tadago kai ta dan kalli maji tace ba hakana bane Baba ban son wani abu
ya faru ne a tsakanin su don naga akwai yarda a tsakanin su.
Inda mummy take zaune ya dan kalla yace kinga karamar yarinya ma tafiki tunane
wai mai ya samay kine kubura da zaki wanan danyen hukunci wa kanki haka.
Maganan nan ba abin kunya ne gare ku abokan zaman ku suji shi an yarda dake abaki
amanan yarinya sai kuma ki mata wanan danyen aikin haka.
Kituna fa kema kin haihu idan wani yaiwa yaranki haka zaki ji dadi bafa rashi
gatane yasa kika ganta nan ba lalurace takawo ta gurin mu.
To amma Alhaji aini naga ,,,,, dakata don Allah wallahi baki kyauta ba kuma kin
bani kunya yau ace kece kikawai maijida haka a gidan nan.
Ke tashi ki koma dakin ku kuma na kashe wanan zancen a gurin nan kada naji shi
wani guri don ranku zai baci.
Daga yau ke maijjida nabar maki rikon yarinyar nan a hannunki koda uwarta tadawo
zanyi magana da ita kada na kara jin zancen nan ko nan gaba.
Bintu ta mike jiki ba karfi tana fadin nagode baba cikin kuka tana fita taji yana
cewa ke kuma kubura wallahi duk naji kin wa yarinyar nan wani muvun kallo gidan nan
sai na saba maki ta yadda baki zata ba.
Bintu tana shiga dakin da dan muryan sallama duk su Amira suka kalleta a
wulakance bata gane masu ba.
Bata jima da shiga ba saiga maji tashigo tana cewa Amira hado mata tea mai zafi
tasha tasha magani.
Nan taje mayar masu da yadda maganan yake sai ko suka shiga zagin hajiya kubura
sai da ta tsawata masu.
Ta juta kan Bintu tanacewa Fatima ashe baki dauke ni uwa ba da gar zaki iya biye
min magana irin haka tunda badawo.
Cikin kuka tace mama ban so kuyi fitina ne shiyasa naga gara kawai nabar gidan
gaba daya.
Nan maji tai mata fada sosai tare da kara bata shawara akan mutanen gidan gaba
dayan su.
Bintu a ranta tace nafiki sani komai yanzu ai mama nan dai su Amira ma sukai
mata magana sosai akan zaman duniya.
Duk yadda suka yi da mummy ta kwashe ta fada masu komai suka shiga tsinarta da
kwashe mata,,,,



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


A LOKACIN MUKE,,,,,,


Nocking din kofan take a hankali yayin da take jin sautin kida ya na tashi daga
dakin, sai dai ba a da niyan bude dakin a lokacin.
Kara sautin nocking din da takeyi tayi sai ji tayi ana cewa wai waye please ke
damuna haka.
Mai dakin tana bude daki sai suka fara kallon kallo a tsakanin su don ba wanda
yasan wani a cikin su.
Kina neman wani please ?
Har lokacin tana tsaye ta tare kofan dakin nata ta inda mutum zai iya shiga
dakin.
A,a gurin ki dai nazo.
Ni kuma ta fadi cikin dan mamaki a fuskan ta tare da dan sake fuska tana dan kada
idanuwan ta cikin mamaki.
Eh duk da dai nasan baki sanni ba amma dai gurin ki din ne nazo ai.
Ok tau shigo daga ciki mana ko ?
A tare suka shiga dakin a lokaci guda suna nuna a jere da junan su.
Kujeran dake dakin ta nunawa Raiha ta zauna inda Raihan ta gane nufinta ta ta
zauna kamar yadda ta bukace ta da yi.
Juyawa tayi zuwa ciki sai gata dauke da kwalin juice da cup a hannunta inda
Raiha take zaune tazo ta aje drinks din tana cewa bisimillah.
Raiha ko sai bin dakin take da kallo wanda dakin yai mata kama da ta mai zaman
kanta ko kuma wace tazo karatu a garin.
Idon ta ya kai akan kwalaben syrup din maye dake saman wani dan table can gefe
guda.
Kisha mana bisimillah ko sai takai idon ta akan kwalaben da Raiha take kallo,
tace,
Ko kema dai yar hannu ce na miko maki ki surka dasu ne?
A,a barshi kawai ni sai dare nake sha idan zan kwanta yafi min caji don ina gudun
mutane su gane ina wanan harkan.
Dariya Nura tayi har fararen hakoranta suka haska daga bakin ta tana cewa.
Kai har kin bani dariya wallahi ashe da sauran ki ke har yanzu dasha da rana da
dare ai ni duk daya na dauke su a gurina.
Haka dai kika ce amma akwai banbanci gaskiya baki dai ganewa ne kowa da nashi
irin ra,ayin nake gani.
Kurba biyu Raiha taiwa juice din sai ta aje cup din tana kallon Nura cikin
murmushi.
Nura tace ni kin barni a duhu ban fa gane kiba gaskiya har yanzu gashi kuma kince
guri na kika zo.
Raiha tace eh gaskiya baki sanni ba nima haka Sunana dai Raiha amma mutane suna
kirana da Raihanatu musanman ma iyayyena.
Ok ni Nura nake karatu ne yakawo ni wanan garin ina karatu a dan fodio university
ne.
A ran Raiha tace shikan karatu kikazo kika buge da harka ke nan a garin da ba,a
sanki ba.
Raiha tace cikin murmushi ko kin san Nasir Habbib mai aiki a sokoto cement ?
Nura tace a ranta au budurwan Nasir ke nan ta biyoni don nai mata snatching din
shi a gurin ta ko?
Aiko yarinya kinzo gida wallahi don zan maki wankin babban bargo yanzun nan kuwa.
Amma sai ta kyale a fili tana cewa nasan shi kuwa kwarai da gaske anjima kadan ma
zaki ga yazo nan ai idan ya taso daga gurin aiki.
Raiha tace good zan iya kiranki da Anty Nura don ko ba,a fada ba nasan kin girmay
ni.
Dafatan zaki saurari maganan da nazo maki da ita da kunnen basira batare da kin
fassara min zance na ba da wani abu.
Ok ke nake saurare ina jinki ai.
Da farko dai kamar yadda na fada maki sunana Raiha kuma ni haifafan wNan gari ne
muna zama a uguwar arkilla ne nida iyayyena.
Sai kuma tai shiru tare da dan kallon saman silin din dakin zuwa dan wani lokaci,
Nura tace ke nake saurare fa kada mu bata lokaci.
Ba zancen bata lokaci ai don magana ce mai muhinmanci da zata amfane ki nazo
dashi.
Tace ok ai ina sauraren ki ko?
Raiha tace kafin Nasir ya nemay ki ni Raiha ya fara nema amma sai Allah ya
tsallakar dani daga mugun nufin shi a kaina.
Kamar ya mugun nufi kuma Nura ta tambaya a cikin mamaki da son karin bayani ga
Raiha din
Raiha tace niyar shi na shigewa yan mata ya sace zuciyar su da so da kauna kamar
yadda yake maki a yanzun haka.
Amma fa daga baya zaki zo ki sha mamaki don ba nufin shi ke nan ba a kanki.
Nura tace a gatsale Allah ko ?
Hmmm Raiha ta dauki cup din drinks din da ta aje takara kaiwa a bakin ta tadan
kurba kadan sai ta juya gurin Nura tace.
Wallahi wallahi ifan bakiyi hankali ba a karshe zaiyi safaran ki ne zuwa kasa
shen turawa ya tura ki karuwanci a can ya kuma karbe passport dinki duk gudin da
zaki samu sai dai dila ya turo mashi ta account din shi.
"Ke
Kada ki maisheni karamar yarinya mana kedai kinzo da tsigar nabar maki Nasir don ki
yaudareni da wanan magana naji tsoro nace ban son ki sai ya koma maki ko ?
Allah sarki babu ko daya wallahi don idan da na yarda da yanzu nima nazama tarihi
a gurin iyayyena da yan uwana a nemay ni a gari a rasa inda na shiga.
Amma sai Allah ya kare ni da yake banda rabon wahala nasamu wani abokin shi ya
tausaya min ya fada min ainihin gaskiyan abinda ke nan.
Raiha ta mike tana cewa ni zan tafi tunda naga kamar baki yarda dani ba yanzu
amma nasan watarana zaki tuna da wanan dan zaman da mukayi dake.
Ni zan tafi kuma ban tsoron ki fada mashi cewa nazo gurinki don yanzu a shirye
nake da na tona mashi asiri a harkan da yakeyi .
Ta juya tare da daukan jakarta dake saman kujera tana cewa idan kin shirya
saurarena sai ki nemay ni.
Har Raiha takai kofa zata murda kofan Nura tace kinga dawo ki zauna ai bamu gama
magana ba tukun ko?
Baki da niyar saurare na shiyasa kina ganin kamar kishin Nasir na tare dake
yasani zuwa gurin ki ko?
Ba haka na bane amma akwai wasu yan tambayoyi da zan maki ina bukatan amsa daga
gareki in naji su daidai kinyi gaskiya.
Raiha ta dawo ta zauna tana kallon Nura ido da ido tace ina sauraren ki ko?
Hmm wai ma ta ina zan fara tambayan ki ne duk kin sani a caji wallahi.
Duk ta inda kika fara in na sani zan baki amsa insha Allahu.
Ok tau dan Allah kunkai kamar tsawon wani lokaci dashi Nasir din a tare dashi.
Ummm gaskiya mun kai kamar wata takwas muna tare inda a sannu ya fara koya min
wasu abubuwa na rayuwa.
Kallon ta Nura tayi da kyau tace hmmm lalai ma amma ce min yayi tunda matar shi
suka rabu bai kara neman wata ba bayan ni.
A,a karya yai maki don kafin ni akwai wasu da har yai galaba a kan su yanzun
haka suna waje on behalf of him suna karuwanci a Spain.
Kai wai da gaske kike da zancen ki ni yar uwa wallahi ba karya a magana ta sai
tsabar gaskiya kawai.
Ok ya taba zuwa dake tafiya ne ke dashi kubar garin nan zuwa wani waje?
Tace kwarai mun je lagos da sunan yatafi aiki ashe yakaini ne gurin yan commuty
din su sugan ni idan zan yi sai ya dawo ya shirya tafiya na.
Mikewa tsaye Nura tayi tana fadin ikón Allah na ko yarda da zancen ki don duk
inda muka tafi sai naji ana cewa she is ok,
Very pretty you will get a high level on dis pretty,
Sai da nai mashi magana ya daina kaini ana fada min hakana don ban son jin wanan
kallaman daga bakin arna.
Murmushi Raiha tayi tace a can bai nuna maki true color din shi ba ne ko ?
Kamar yaya Nura ta tambaya.
Murmushin takaici Raiha tayi tare da fara fada mata duk yadda yayi da ita a garin
Iko din.
Mikewa Nura takarayi tsaye tace umm ummm na yarda da zancen ki gaskiya don nima
ya jawo wani abokin shi akan na tarda mu kwana tare dasu su biyu amma bai san ina
jin lokacin da suke maganan haka ba sai na bijire mashi tun kafin dare nace period
yazo min.
Mikewa Raiha tayi tace nasan koke can akayi shiyasa nasa a saka min ido a kan
shi nai alkawarin duk yarinyar da yai niyar batawa sai na kwatota daga halaka
hannun mugu azzalumi mayaudarin banza macuci kawai.
Nan suka zauna sukai ta hira akan yadda zasu dau mataki a kan shi don kada yaci
gaba da abinda yakeyi.
Tun wanan ranan suka kulla kawance da junan su inda ta rako Raiha tana mata
godiya.

****** ********* ******
Tun daga kofa yake kwala wa mariya kira har zuwa cikin gidan, maria wace ke duke
tana wanke wanke taji kiran a bazata yai mata yawa.
Ta mike tana fadin gani nan babban Abba lafiya dai ko kira haka daga waje babu
kakautawa.
Yace cikin hasala yanzu naga malam a kasuwan mu yake ce min wai yaran nan yanzu
basu zuwa makaran ta ko yaushe.
Shi Abba ma sai ya makara kullun kafin yaxo in ma har yaje din yace yai magana
yan uwan shi suka ce wai talla yake zuwa.
Tace tallafa tallan may wani kallo yai mata na ban yarda dake ba fa.
Tace ba gaskiya bane in zai yi talla ai ban dora mashi ban fada maka ba balle ma
nasan ba yarda zakayi ba.
Shi dai kila yara sunyi mai yawa yanzu bai gane zuwan su da rashin zuwan su
shiyasa ya fadi hakan.
Yanzu ina suke ya tambaye ta tare da tsureta da idanuwan shi tace sun tafi tin da
karfe hudu suna can.
Yace ai zan tafi nagani ko suna makarantan ya mika mata ledan ce fanen da yayo ya
dauki buta zuwa ban daki.
Nan ta samu tafa leken zaure ko Aliyu yana tafe saiko gashi ya sayar rataye da
roban shi na talla a wuyan shi.
Da sauri ta tare shi ta karbi roba da kudi tai mashi magana kuskus a kune yaron
ya juya da sauri yabar gidan.
Kafin maigidan ya fito ta boye roban da kudin da sauri a dakin kayan su ta kama
aikin ta.
Yafito daga ban daki yana fadin yanzu zan tafi nagani idan suna can ko kuma wasa
suke tsayawa yi a hannya.
Yafita tana ce mai a dawo lafiya bai amsa mata ba don a cike yake ran shi ya
baci sosai.
Don shi bai wasa da hakkin iyalin shi a kan shi don haka yake matukar saka ido
akan al,amarin yaran shi dama ita kan ta matar tashi.
Tun daga nesa ya hango su a zaune gaba dayan su don haka sai bai karasa kusa ba
ya juya zuwa kasuwa ko zai dan kara samun wani abin tabawa a can.
Kafin ya dawo yaran sun rigashi dawowa gida Aliyu da yuwan taci ta ishe shi
abinci yafara nema yaci sannan yai wanka zakace bai tafi ko ina ba .
Taja ma yaran kunne akan duk wanda yace Aliyu yana fita talla sai ta yankewa yaro
kauna a gidan.
Bayan maigidan ya dawo ne yake tambayan yaran inda suke tsayawa basu zuwa
makaranta da wuri yanzu.
Sai cewa sukayi suna zuwa andai canza masu ajine malam baiganin su yanzu.
Haka yasa yaja bakin shi yai shiru ya yarda da maganan su tunda ya gansu dazun a
makaranta sabanin yadda malamin ya fada mai.
Haka Aliyu yaci gaba da zuwa tallan ruwan shi batare da mahaifin su ya fahinci
komai ba tunda shi ba mai zaman gida bane ko yaushe.
Haka yaron ke kawo mata dan kudi itako tana bunkasa bankin ta dashi kullun tana
farin ciki.

****** ********* ******
Tun ranan da akai wanan rikicin a gidan hankalin Bintu a tashe yake da mutanen
gidan baki dayan su.
Ance babban gida babban magana ashe har da ita da take ganin ta kama kanta da
kowa a gidan bata tsira ba ga matan gidan.
Don har da zaman ta gurin Maji ya tsone masu ido sai yanzu tagane nufin maji na
bata magani tare da sauran diyan ta a baya.
Gashi yau Alhaji da kan shi yake fadin korafin da sauran matan shi sukayi a gidan
kan zaman ta da Maji.
Wanda ba komai suke wa kishi ba sai basu kaunan suga ta karu da komai kankantan
abu a gidan,
Wanan dalilin gitinan yasa damuwa ya dan fara yiwa Bintu yawa arai sai kafa kafa
take da komai a gidan.
Tun da

15 / 92