Advertisements
Chapter 40 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   40 / 92

117K to 120K   out of 275.8K words

yaro ya shiga yai masu iso akace a
shigo daga zauren.
Maji ce tafara shiga taiwa mutumin bayanin komai yace to a shigo babu komai dama
irin matsalan nan sai anyi wa mashi dabara.
Dattijone fari dogo dashi baida jiki sosai sai dai yana da fatin gemu mu bamu
shiga ba muna zaune a bayan mota.
Sai Bashar dake tagaba sosai bai shiga ba har sun shiga sadauki ya fito yai mashi
hannu daya biyo su mana.
Sun zauna aka gaisa yake tambayan shi yaya jama,a ya aiki ya amsa tare da bin
zauren da kallon irin littafan dake tare a cikin zauren da ido.
Malam ga yaron kamar yadda kai umurnin nakawo maka shi yace nagan shi hjy.
Hannu ya mikawa sadauki inda shima ya mika mai azaton shi gaisawa zasuyi sai yaji
ya rike hannun nashi idanuwan shi ya lunshe yana fadin ikon Allah.
Can yace umm,umm Allah mai iko, aida sun barka da sun sha alheri fiye da
tsanmanin su.
Sai ya sake hannun sadaukin yana girgiza kai yace mutane basu da imani yanzu
duniya tai nisa wallahi.
Agida akwai matsala sosai hjy hakama a,waje akwaishi.
Sai dai ita matsalar ta waje ba wani matsala bane akan harkan samun shi ne.
Nan ya dago kai yacewa sadauki ka na iya gane wani bakin mutum daga cikin ku mai
dan saje a fuska sai dai ma naga kaman ba musulmi bane.
Yace akwai ranan da yaba wani abu a cikin leda fari kai kadai baiba kowa ba.
Sai dai anyi sa,a kana zuwa gida ka manta bakaci ba sai bayan kwana biyu kaga
ledan ka bude amma sai kaga abin ya zama baki.
Shiru yayi yana son ya tuno wanan ranan sai zuwa can yanisa yace anyi haka malam,
Amma Daniel ne abokin wasa na ne saida iyamurine shi ba musulmi bane.
Yace nagani ai .
Yace Allah ya kareka da kaci yadda wanan anin ya koma baki da haka jikin ka zai
koma ayi maganin duniyan nan sai dai Allah gaskiya.
Yace amma idan baka yarda ba abinda zan baka yanzu idan ka gwada zakaga insha
Allahu ba yin mu ba da yardan ubangiji bazai yarda ko hannu ya kara hadawa dakai
ba.
Burin shi shine saboda kaine bai daga ba kakai mashi ko ina don yana ganin kaine
ka,tare mashi wuri.
Ikon Allah inji maji tace ko ina da matsalan dai, malam yace yanzu muna A LOKACIN
NE,
Ai yanzu duniya ba,ai mata hawan kawara sai dashiri ake shigan ta don mutum yana
barci ana mashi nasari ne.
Bashar yace kaji abinda nake fada maka kullun amma kai baka ganewa ne shiyasa.
Shi dai nisawa kawai yayi.
Hankalin shi na gurin tunanen Daneal kawai yasan bai kaunan shi tun farkon
haduwan su suka fara samun matsala amma daga baya sai ya daina tsanar shi.
Yace hjy sai zancen gidan ku gaskiya bazan boye maki ba akwai matsala sosai a
gidan.
Nan ya fara basu bayani tiryan tiryan amma bai fada masu sunayen masu wanan aikin
ba kamar yadda yaiwa gwago bayani a baya dama kuma,shirin da suke a yanzu.
Har kan yaranta mata da aka,asirce mata su akan suyi ta zama ko kare bai kaunan su
balle mutum.
Nan kan ran sadauki yai matukar baci cikin bacin rai yake fafin wai Maji may
mukaiwa wa yan nan mutane ne haka a duniya.
Kagin tai magana malamin yace hassadane kawai don sun san kokai waye shiya kawo
haka kawai..
Maji tace yaran suna nan nazo dasu ai yace na sani don nagan su su uku ko?
Sai dai dayar bataki bace Allah daine yakawo maki ita cikin hikima irin na ubangi
wanda duk abinda kaga ya tsara ba,a banza yake tsara shi ba.
Zaman ta gareki alheri ne sosai koda yake bama sai na fada maki ba ai kema kin
sani.
Sai dai zatai aure amma dai auren yanzu gaskiya sai Allah don banga yuyuwan shi a
halin yanzu.
Malam daga gurin mijin ne ko kuwa yace Allahu,a,a lamu sai gaibu sai lillahi
gaskiya.
Cikin ran sadauki yace aidama nasan wanan mutumin yaudaran tane zaiyi sai yaji
malamin na fadin amma akwai abinda zanba kowan su insha Allahu komai zai walwale da
yardan Allah.
Sauran ma insha Allahu mazajen su zasu fito bada dadewa ba ai.
Nan dai yaba yaya sadauki abubuwan da,suka dace tare da kara jaddada mai yadda
zaiyi amfani dasu.
Sai yace ace mu shigo idan mun fito sadauki ya shigo shi kadai sai uwarshi akwai
maganan da zai yi dasu wanda siri ne.
Nan dai yai muna duk abindaya dace da kowan mu muka fito da yan ledojin kulin
maganin daya bamu daga zauren.
Ni a lokaci duk a galabace ma nake don ni ban san wai ina da matsala ba,su dai ne
na dauka masu matsala kawai.
Muna fita sukai magana ta siri sosai da mana ta fada mashi damuwan ta yai kuma
alkawarin taimaka mata.
Sadauki ya shigo ya zauna mutumin ya kalle shi yace kai babban mutum ne watarana
zaka tuna da magana na matsalan ka dayane shine wanan shaye shayen da kakeyi.
Duk da naga abinda sauki yanzu sosai akan ka don abin yarage maka fiye da baya
can.
Yace sai kuma ka kara da hakkuri don ko yaushe biyayya na iyayye yana kai mutum
ga alheri.
Yai mashi nasiha sosai akan duniya tare da kara mai wasu yan abubuwa irin nasu.
Inda yace ya tabbatar kagin ya tafi gurin neman shi yayi abinda ya bashi din.
Kudi masu yawa ya ba mutumin sai yai dariya yace ba haka nake ba ni dari biyar
kawai zaku bani ko shi kada kuce naki karba ne da ban karba ba wallahi.
Sunyi mamaki sosai muka kama hanya sai sokoto koda zamu dawo naita kakarin amai
saidai da yake cikina ba komai sai kumfa kawai nake zubowa.
Bashar dasu mama suna ta faman yi min sannu amma,shi ko kallo ban ishe shi ba.
Da la,asar muka iso gida tun lokacin kowa ya fara abinda aka bashi yayi daga
gurin bawan Allah.
Don har bashar saida ya anso nashi shima don mutimin shi da kan shi ya bashi
taimakon.
Tun dawiwan mu nikan ina dunkule saman dogon kujera harda barcin wahala saida
nayi.
Anty maryam ce ta dafo min liptop da lemun tsami na dan sha shine na dan ji dama
sosai.
Ya shigo falon yayi wanka ya,sauya kayan jikin shi a lokacin yasa wando da rigan
na maza mai dogon hannu.
Gani a kwance na dunkule yasa ya dan tsura min ido sai yaji na bashi tausayi
sosai.
Yace ke may ke damun kine yanzu kuma?
A sanyaye nace cikin bata fuska kaina ke min ciwo.
Bari in nafita sai a sayo maki magani kisha.
Nace nagode.
Wanan gidiyan da nakan yi mai idan yai min alheri yakan ji matukar dadi a,ran shi
don shi mutum ne mai son yaji ana godiya gare shi.
Sosai ya mayar da hankali shi ga maganin shi da mutumin ya bashi don yai matukar
yarda da zancen mutumin ba din komai ba,rashin amsan kudin su da mutumin baiyi ba.
Ya dawo ya,sayo min magani harda na amai da kuma drinks mai sanyi na kwali.
Ina kwance na na dunkule a saman kujera su na kallo ni kuma gani kwance a dunkule
sai dai ba barci nakeyi ba idona biyu.
Muryan shi naji yana tambayan su ita wanan barcin takeyi har yanzun ne ko jikin
ne ke damun ta?
Maryam tace tace kanta kawai ke ciwo yanzu yace ke tashi ga magani ki sha ko zai
lafa maki.
A hankali na mike zaune daga kwancen da nake sai dai still ina dunkule ga hijjab
ga kuna blanket dana yafa ajikina.
Na karba tare da bare maganin na kai abakina saida na dago kai naga ya tsura min
ido ashe ni yake kallo daga inda yake zaune.
Da sauri na dukar da kaina kasa bban tsaya shan drinks din ba yake cewa bazaki
sha juice din ba ne?
Nace a,a ban iya sha yanzu sai nakai kwance daga inda na tashi yamike zai bar
falon yana cewa idan bai bari ba sai akaiki asibiti ke nan.
Ya fice daga dakin na lumshe idanuwana tare da komawa barci a lokaci guda.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,


IDAN KIN TURA WANDA BAI BIYA,BA BA MU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAN MUNA AKAN
KI,,,,,,,


Sadauki bai koma ba sai dai yayi duk yadda malamin nan ya umurce shi da yi a baya.
Ya kama hanya yatafi an muna E,passport na batayi tare da duk wani clearing din
da ya dace aiwa masu tafiya.
Na kira kabir nai mashi albishir kamar yadda ya dace nan fada mai don ya,sani .
Sai na fahinci bai yi farin ciki ba da hakan take naji raina ya naci nace, amma
ka bani mamaki yayana da zakaji alheri haka ya samay ni ka kasa tayani farin ciki.
Yace umma gaskiya Fatima ban iya munafunci ba don haka idan nace maki nayi farin
ciki to na munafunce ki giskiya.
Cikin mamaki nace Yaya Kabir lafiya kake kuwa ?
Yace lafiya ta kalau Fatima ,
Wanda dai ya kaiki saudiyane ban yi naam dashi ba gaskiya.
Kana nufin wai yaya sadauki ke nan?.
Yace shi nake nufi Fatima ya,fadi a takaice kawai ba shakkan komai
Yace ina matukar kishin zaman ki da yaron nan gida guda Fatima, a duk lokacin da
na tuna cewa a guri daya kuke sai naji banjin dadi wallahi.
Don ni mutum ne mai matukar kishin iyalin shi sosai ina kokarin ganin matata bata
mu,amula da wasu maza koda yan uwanta ne ko nawa.
Nace amma dai kasan ni ba,watsa,tsa bace haka shima wanda kace baka kauna din ba
dan iska bane hakana.
No Fatima baki fahinci magana ta bane don haka mubar zancen haka nan Allah ya
kaiku lafiya ya dawo daku lafiya ba shike nan ba.
Nai fushi na kashe wayan ba yadda na,saba yi mashi shagwaba ba idan zan kashe
wayan.
Ni kadai maganan tai ta cina a,rai har na gaji na sake don kaina.
Nai fushi da yaya Kabir da kyat ya shawo kaina muka shirya dashi yana ta kamay
kamay, wai shi ba wani abu yake nufi ba,
Hakalin shi, bai kwanta bane don kada yaya sadauki ya kwace mashi ni yahana ya
aure ni ace yar gida gida za,ayi.
Jin maganan nayi cikin haushi da takaici, don may zai hada ni da yaya sadauki
mutumin da yake a matsayin yayana yake a gareni.
Nan na nuna mashi ban ji dadin yadda yake min ba a matsayin yaya fa,sadauki
yake gareni.
Amma shine zai ce, wai sadauki na iya kwaceni daga gareshi, ya aureni wanan
maganan tai min zafi yadai bani hakkuri aka zauna lafiya.
Munsha magana gurin mutanen gidan mu da,ma,wasu yan sa ido akan zancen tafiyan
mu,

****** ********* ******
Mun isa kasa mai tsarki, saukan asuba mukayi a garin kafin agama muna screening
har anyi kiran sallah asuba ko.
Wasu motoci muka samu suna jiran mu su suka kwashe mu sai masaukin mu a cikin
garin madina.
Bamu dauki tsawon lokaci ba muka fita zuwa masallaci don muyi sallah da ziyara
kamar yadda yazo ga sunah.
Ibada muke sosai ba kama hannun yaro daga mu har uwar mu da yayan mu sai
yaya,Bashar da muka zo dashi.
Aiki tukuru komai bamu da matsalan shi sai mura da ya kama mu kawai a garin don
sanyin Ac da ruwan sanyi da yai muna yawa.
Yaya ke sayo muna duk wani abinda zamu bukata sai ya tambaye mu ko may zamuci
daga haka har ya gane favorite abincin da kowan mu ke so.
Kwanan mu tara a na goma muka kama hanya sai garin makka nan ma mun samu anyi
muna masauki inda zamu sauka .
Bamu kwana ba sai da muka je mukai dawafi a can muka kwana sai safe muka dawo
masaukin mu.
Barcin gajiya mukayi bayan munyi wanka muka kwanta, mun tashi mun samu har mama
ta farka tana zaune tana waya a gida.
Zaune muke a falon dagani sai ita su Amirah ana can an baje ana barci a cikin
A,C.
Bashar da yaya sadaukine suka shigo dauke da abincin rana da zamuci.
Ganin da sukai min zaune a kasa gap da kafan mama nake zaune kamar wace zata koma
ciki .
Fatima ke har k8n farka ke nab baki gajiya dai, mama ta karbe da cewa ai kai dai
Bashar wanan yarinyar har mamaki takw bani karama da ita amma yawan ibadan ta kamar
wata babban mace can wallahi.
Daga inda yake zama idon shi ya na a kaina yake cewa, addu,a takeyi wa mijinta
kila ko kuma maman ta.
Ai na gode da Allah ya ban diya irin Fatima mai ibada ga sanin ya kama ta a tare
da ita ko yaushe.
Kai maji kina da fasawa wanan yar kauyen yar taki kai koda yake yanzu naga,ta
fara wayewa,ai don ina Allah Allah kada,tai muna,kauyancin ta, ta,bayar damu a
cikin mutane muji kunya.
Nace cikin dan jin nauyi da kunya kai haba yaya wai kai kullun dai a bakauya
nake a idon ka ne?
Kyaleshi Fatima ba abinda zai gwada maki yanzu na wayewa jirgine dai kin haushi
don kin gama sanin komai.
Kai mama don Allah bari kada ta dauka ko jirgi shine karshen kauyanci a duniya.
Kada fa ka,zabo matar da tafi Fatima zama yar kauye muga tsiya wallahi don dai
yanzu kasan Fatima ko kai sai kayi da gaske zaka gwada mata wayewa.
Aiko cikin auri yace don Allah MAN ka bari ka fa san a kasa mai tsarki muke kada
yan amin su karba muna.
Nan suka dinga mashi sheri suna ta dariya yace aiko da na karkarya yar kauyen
banza da duka.
Dariya nima na kama nace ni yanzu yaya idan ,al,amarinka ne bana jin haushi balle
nayi kuka akan zancen ka.
Da can bayane da ban san halinka ba nake kuka yanzu ko kin waye ko?
Ya tambaya cikin son jin amsata daga bakina amma sai nai shiru don maji tace na
kyale shi duk abinda zai fadi na dai fishi ne yasa yake jin haushi na kawai.
Bai da rowa ko kadan sai da,wanan tafiyan ya hada mu na tabbatar da hakan don duk
abin da kannen shi sukace suna so shi zai masu ko nawane.
Munyi ibada munyi rokon Allah sosai ba dare ba rana muka kammala aikin mu muka
fara shirin dawowa gida.
Naiwa iyayyena da yan uwana tsaraba haka naiwa Kabir shima nashi kalar tsaraban da
ya dace da shi.
Munyi mamakin dawowan mu, gida muka samu an gyara ma mama part din ta gyara sosai
na gaske akai mata na zamani mai kyau,.
Tafita daban daga sauran part din matan gidan an sauya mata komai nata ya koma
side din ta daban yake a cikin sauran sai dai still a gida guda ake kuma farfajiya
guda.
Mun shiga gida mun zama wasu abin sha,awa gurin mutanen gida sai sabon hassada ya
kunno kai kuma.
Kishi kumallon mata nan zance yafara yaduwa cewa ba kudin halas bane shine muke
tin kahon mun tafi saudiya wa mutane.
Wasu su, ce ai shi kan shi sadauki baya taimakon kowa,sai uwarshi da yan uwan shi
ya sani kawai.
Sun manta duk irin taimakon da yake masu a cikin gida yanzu komai shine yake
kawowa ayi amfani dashi a gidan don yanzu Baba yai sanyi sosai ga arzikin shi.
Ya rage saura wata biyu kacal buki na da Kabir, don haka bayan mun dawo su Baba
sun shigo taron mu shida mama tabawa da wata kawar ta da tazo gulmq taga inda nake.
Nan Baba Alhaji yake bawa babana shawara kan kada ya tayar da hankalin shi akan
zancen aurena.
Duk wani abinda za,ayi agurin bukin shi zai dauki nauyin yi da shi da matar shi
Maji.
Baba na yace amma Alhaji auren ta na farko ke nan ya kamata ace a dan bari nima
na taima a wani gurin inda ya dace dani na kauye.
Babu komai ai duk yiwa kaine don Fatima ta cancanci ai mata komai a rayuwa ai.
Sun dan yini muna sukai sallama na basu tsaraban su suka kama hanya sai gida suka
koma, inda nace masu zan shigo karshen wata don nazo naga mahaifiyata .
A bangaren Kabir kuwa ji yake tankar ya lashe ni don irin so da kaunan da yake
nuna min abi yai yawa sosai.
Duk da lokacin ya matso sosai amma shi gurin shi shine yadai ga an daura muna
aure ace ni mallakinsa ce.
Sai kuma gashi ya dan bijiro da wani zance, wai yana son a dan kara matso da
bukin don yana son zuwa wani course a lagos na wata daya.
Da zancen yazo wa Maji sai cewa tayi ace yayi hakkuri tunda an fadawa kowa sai
wanan lokacin za,ayi bukin.
Da kyay dai na samu na shawo kan shi ya hakkura sai lokacin za,a daura aure daga
baya sai na tare idan ya dawo.
Maryam itace ke shirya komai a kan sha anin bukin sai dariya mama da Amira suke
muna.
Shiko yaya,sadauki yabi ya koma wani silent dashi koda yaushe fuskan shi a daure
take bai wani walwala,
Shi kan shi din ma ba zai iya cewa ga matsalan shi kawai dai haka yake jin jikin
shi ba dadi.
Haka ya daure yana yan al,amururinshi cikin rashin kuzari da walwala a tare
dashi.
Kumshi da kitso da gyaran jiki duk su akai min zan fara zuwa na hadu da Kabir
da,zai shigo inga mahaifiyana sai na,dawo sokoto sai gobe daurin auren mu zai dawo
garin don suna,aiyuka yanzu sosai.
A gidan mahaifiya na ya iso da yamma na fito na sanay shi yana tsaye jikin motar
shi nafito daga cikin gidan namu.
Murmushi a fuskan shi har na karaso gare shi yake

40 / 92