Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
ashe ke Bintu yaya sadauki ne yaje har kauye ya dauko ki da zaki dawo?
Da sauri na dago kaina kalle ta cikin mamaki sai banyi magana ba don ina mamakin
ina taji wanan zancen ita.
Amirah tace ke kan Maryam wallahi uwar sheri ne wata Bintu ne can yaya zai je
har kauye daukowa?
Maryam tace au kina nufin karya nakeyi ke nan ko,ai ga Bintu nan shi in ba shi
yaje tun daga nan ya daukota ba wallahi.
Kin ma raina yaya Allah shine zai tafi har kauyen nan mai uban nisa akan Bintu.
Don in nunawa Anty Amira na kai nace to anty maryam don ya dauko ni wani abune
halan ni nace yazo ?
Ni da ban ko shirya dawowa ba amma yasa ni tasowa ba shiri saboda zuwan shi.
Bintu da gaske yaya ya dauko ki wai ko may?
Nace su sukaje sukazo dani ban ko shirya ba amma ya matsa min wallahi saida mama
tace na shirya su zo dani.
O lalai ma yayana shine yai pretending kamar ma bai san komai ba a ranan da ta
dawo.
Bake ne ba idan ana magana akan yaya da Bintu sai ki wani kakarw ki hana a fadi
ni dai ban kara magana ba ina mamakin yadda maryam taji zancen ga kunya mama duk ya
kamani lokaci guda.
Nace dama,na,sani kawai tun ranan in fada mata tare dasu nadawo da yafi min yanzu
gashi anji ko.
Amirah bata bar zancen ba sai da ya shigo gida har kowa ya manta ashe ita abin
yana ranta.
Yashigo cikin yar fara,an shi bayan ya zube saman kujera yake, cewa maji yau naga
wanan kawar taki da tun muna tsohon gida kuke tare.
Maji ta dago kai tace wata kawana kuma ke nan yace ko yar Rabin isha ake ce mata
ba ?
Au kace uwar goyon ka dai ai itace tai giyon ka lokacin tana amarya a unguwar na
mu da anyi maka wanka sai gidan ta.
A ina kagan ta yace can wani unguwa naje duba wani tsohon gida da akai min talla
tun kwanaki ban samu zuwa ba sai yau din nan.
Naji ance wai ba sadauki maji bane nan yace wallahi ban gane taba maji ta tsufa
duk ta lalace sosai dagani tana cikin wahala.
Tace Allah sarki, tun lokacin da mijin ta ya dauke ta suka koma kauye ban kara
jin duriyan taba.
Yace lalai na gan ta yau kan maji tace inji ka samu abinda ka bata ?
Yace dubu goma kawai na samu na bata banda kudi ga aljihuna a lokacin amma nai
mata kwatancen gidan nan ai tace zata zo.
Yauwa yayana wai ashe kai ka dauko Bintu daga kauyen su ranan da ta dawo ?
Da sauri ya daure fuskan shi kaman bashi ke fara,a ba yan dakikoki kadan da suka
wuce.
Yaba ta amsa da eh mu muka dauko ta wani abin ne akayi kuma ?
Inda nake ya kalla fuska a daure nima na daure nawa tare da dukar da kaina kasa.
Amirah tace da nace karyanr wallahi da maryam ke fadi dazun ban yarda ba wallahi.
Yace naga bata da niyan dawowa school ne gashi ankoma shiyada naje nazo da ita
ai.
Daga haka yai shiru maji najin su batace kallaba ko wanan lokacin ban da cewa da
tayi Allah yasa yar Rabi dai tazo gidan nan wallahi na dade ina tuna ta sosai
wallahi.
Mikewa yayi yana cewa zan shiga daki maji duk nagaji yau wallahi zan dan huta.
Yana fita na sauke ajiyan zuciya a hankali don nasan nawa ya samay ni kuma tunda
yai min gargadi kada na fadi.
Ban taba sanin yaya yana da nombana ba sai yau ina daki ina shirin sallah naji
wayana na ruri.
Ina dauka naji yace ke ashe baki da hankali gulman ki hae yakai can ban sani ba
dana ce kada ki fadi sai da gulman ki yakai kika fadawa maryam abinda na hana ki.
Na marairaice nace wallahi Allah yaya bani na fada mata ba ban san inda tajiba
wallahi ko.
Sai naji ya kashe wayan dip nabi wayan da kallon mamaki tare da sauke ajiyan
zuciya.
Kwanana biyu da dawowa ya sa kai ya tafi zuwa kashen waje gurin wasan su don can
yafi dawowa a jike idan ya tafi.
Tafiyan shi, na dawo normal kullun ina cikin yan uwana muna mu,amulan mu yadda
muka saba dasu.
Bamu da matsalan komai a gidan yanzu don gaskiya Alhamdullahi, mota kowan su na
dashi, haka ma sutura duk muna dasu matsu tsada, waya kowacen mu babba take riko a
hannun ta duk shi ta saya muna, gurin abinci sai wanda ran mu yake so zamuci, ga
uwa uba makka da muka tafi kowan mu da hakoran makka a bakinta irin na adon mata
yana walkiya.
Matsala guda yanzu shine matsalan gidan su maji na fitina a tsakani kullun ga
Nafisa yanzun abinta yai kamari sosai gwanin ban tausayi da ita.
Idan iskancin ta ya ishi Baba haka zaifito tsakar gida yai masu tas ita xa
uwarta, sai in Umma ta gajine takan tanka itama tace.
Ba kan diyana aka fara lalacewa ba ai a gidan kan suyi ai wasu sunyi kuma nasan
hannu aka samin suka lalace.
Don haka koma waye na sani kada maishi yaga kamar yaci bulus wallahi indai nice
bashi akaci wallahi.
Don sheri saboda mutum yaga nashi ya lalace sai ya mayar da dan kowa lalatace a
gida.
Badai na su kawai duniya zata fada ba sai an fadi na mutum tukun.
Mummy tafito daga dakin ta tace kai amma dai hjy Atika tauhidi bai sheki ba
wallahi.
Ashe shi wanda kike nufi hannu aka saka mashi ke nan a lokacin yazama haka bamu
sani ba ko sai yanzu da yakawo akanki ne kika san haka ne.
Kada ki manta iskancin namiji ado ne a gare shi duk yadda ya iya lalacewa bai
rasa macen aure a duniya itako diya mace fa ?
Ke tsohuwar kilakiya kada ki manta mun san komai wallahi, nan kikagama tambadewan
ki ba mashinshine in bashi alhajin dayazo yatara ba ya dauko muna masifa a gida.
Kin ishe mu kin ishi diyan mu wai ke adole ga yar bariki to anriga ki indai
barikine a gidan nan don gidan kikazo.
A haka cure ake barikin don shifa bariki iyawa ne dama don kinga ashe nafiki
iyawa ke nan tunda kika fadi.
Dariya mummy tayi tace wai a haka ashe ke bariki kikeyi ke nan ba,a sani ba ko ?
Nafisa dake daki tayi tatil da ita ta leko tana fadin Umma rabu da wanan gajar
matan mai muna mazuru muna shaho.
A,,,, mu,,mun,,san komai,,,wallahi, ikon Allah ai gara kija yar mayer yar ki daki
kafin wani ya shigo yaga wanga tabaran nata a fita damu waje.
Haushi da takaici ya kama umma da Nafisa ta bude bbaki zatai magana ta wani daka
mata tsawa tace don Allah rufa muna baki kinji kin jawa mutum gori a gida kawai.
Haka sukan ta faman jidalin su ita da mummy da bata iya hakkuri idan tana
habaicin ta.
Maji dai bata kan tanka mata sai dai tai shiru kawai tace tabar ma Allah kuma
Allah ya tsare mata zurian ta.
Irin wanan jidalin yakan tayar wa Baba da ciwon shi wani lokaci sai ya kwanta
asibiti saboda bakin ciki dake damun shi gashi duk wanda ya sanshi sai yai mashi
korafi akan Nafisa abinda takeyi baida kyau a gari.
Ranan dai ya tara iyalin shi yai masu fada sosai yace da mazan da suka isa aure
da matan kowa ya fiddo da miji da mata aure duk aurar dasu zaiyi gaba daya kowa ya
huta a gidan dasu.
Yace kai Imirah na fada maka ka kawo mace kafin na zaba ma da kaina wallahi kaji
na fada maka.
Ya juya gurin mama Asiya yace danki yace min muje gidan yarinyar da yake so aiyi
zancen auren su.
Mama tace ba dai wanan yar iskan ba da ta tsohe mashi ga shekaru da komai yace
shi din maye inba halin su daya ba a ina suka hadu da ita?
Tunda yace ita yake so kuma shi zai zauna da abin shi ke ina ruwan ki da zancen
su ne wai?
Zan tura iyayyen shi suje nema mashi auren ta nan dagobe insha Allahu.
Mama ta tubure tana fada tana zagin Ahmad tace badai ya auri wanan karuwan
yarinyar ba agidan nan.
Baba yace ai sai mu zuba mu gani tunda kece zaki zauna mashi da ita ai kina bani
mamaki wallahi.
Ki fara tambayan danki yaya ya hadu da ita kafin ki fara zagin yar mutane haka
nan.
Ya juya gurin mamana yace idan danki ya dawo ina son ko fada mashi sakona yafito
da mata na da karshen sabon wata duk aure zasuyi muddin ina raye a duniyan nan.
Mama tace shi sadauki yana da mata kuma na yaba da tarbiyan ta kwarai yace mashs
Allahu haka nake son ji dama.
Duk gurin sun so sanin wacece matar don su sani ko yar gidan maikudine ko wani
kusan gwaunati can.
Don kada yazo yafi diyan su zaben yar gidan mai kudi azo ana mazu feleke a gida.
Haka dai akabar falon kowa da abinda ke cikin ranshi manya da yaran su na gidan
da aka kira.
Ina daki a zaune suka shigo kowa sai gunaguni takeyi maji dai ta shige tabar mu
nan zaune muna hira.
Amirah ce takira yayan ta da waya take fada mashi hukuncin da Baba ya yanke akan
su.
Yai dariya yace Amirah kice mun kusa shan buki ke nan yan kanne na sun kusa zama
amare.
Tace bamu ba ai harku yaya don yace wa su Maji wallahi duk fito da matan aure a
aura maku dariya yai mata kawai.
Tace yaya kai kaga abin dariya ma ni wallahi duk na rude na rasa may nake ciki ma
aallahi.
Yace ina samarinki ba sai ki fitar da daya ba kawai a zarga maki dashi, tace yaya
ni duk fa basuyi min bane na ma rasa wa zan tsayar a cikin su ni wallahi komai ma
ya jagule min yayana.
Yai dan murmushi yace kibari zandawo month end sai mu san abin yi tace ni dai da
Baba zai min hakkuri ne har faba dayafi min.
Yace No Amirah ki godewa Allah fa gaki har kin gama karatunki ma may kuma kioe so
yanzu inba aure ba kuma.
Tace yaya ke nan bazaka bashi hakkuri ba har zuwa gaba yace wa ni rufa min asiri
please bari mu rabu lafiya da Baba don Alla dai.
Tace yaya naji maji tace wa Baba wai kai kana da mata shine mu bamu san wanan
lucky girl din ba da tai wanan sa,an haka?
Yace No,No Amira maji ta dai fadawa Baba hakane kawai don ta kare ni gare shi
ammani for nowa ban da kowa a kasa tukun na.
A kwai da wata wadda nake son fada masu akan ta don yar kasar ghana ce sai dai
akwai matsala gaskiya.
Matsala kuma yaya ?
Yace eh don ba musulma bace Christian ce ita sunan ta Linda.
Yaya kafira kuma ?
Yace eh amma ai idan munyi aure zata musulun ta ne insha Allahu.
Tace ashe kuwa akwai case ke nan nasan maji da wuya ta yarda gaskiya don yadda
bata kaunan kafirai ko kadan.
Ni dai daka jaye zancen ko zaka samu wata nan gaba ku shirya yar asali yar gari.
Yace ban ma san ni may yasa suke son mutum yai aure bane yanzu wallahi.
Amirah tace kasan maji kance ita dai muyi aure don yanzu Life is to short
knowadays.
Hakane kuma fa Amirah gaskiyan maji ne rayuwan yanzu dan kalilan ne gaskiya.
Yace ni nasan zamu kwasa da parents din mu dama both don ko ita parents din ta
takw ji yanzu.
Shiyasa tace zata zo Nigeria sai muyi auren mu kawai sai daga baya iyayyen ta su
sani.
Amma ban yarda da wanan ba ni don ban son ni ai min haka gaskiya.
Tace yaya ai matsala shine yaran da zaku haifa zasu zama ruwa biyu ke nan fa?
Yace kai Amirah akwaiki da shirmay wallahi ni fa ban ko tunanen yin aure yanzu
balle wasu iyali can .
Yaya kadai yi tunane kafin kazo da maganan nan gida don za,a samu matsala sosai
wallahi.
Ki bari kawai idan nazo sai mu san yadda zamu bullo wa zancen cikin sauki haka
zaifi ai.
Tace ni wallahi maji nakejiwa akan zancen nan don nasan halinta akan abinda bai
mata ba.
Yace ke dai kawai kiyi shiru ban son kowa ya ji wanan zancen a bakin ki sai nazo
tace shike nan .
Nan sukai sallama,dashi yace ta kwantar da hankalin ta yana nan zuwa month end
insha Allahu.
Suna gama waya gulma yaci Amirah ta kasa barin zancen a ranta tace wata sabuwa
wai yaya kafira zai aura fa ashe?
Muna hada baki da maryam gurin cewa kafirah fa kika ce antu ?
Tace wallahi yanzu yake fada min wallahi wai yar kasar ghana ce ita
Sunan wai ko Linda ?
Nace wayaga Leather ke nan kuma ?
Kai baima yuyuwa gaskiya kafira arniya mai fitsari a tsaye zai ce zai dauko muna.
Muji da wani irin gori da habaici gidan nan kuma ba,a gama wani ba har yau a fada
wani ke nan kuma.
Ai da su Umma an samu abin dariya ke nan a gidan nan wallahi don shi za,a aza a
faifai kuma ana talla lungu lungu inji maryam ke ta sababi haka.
Tace ni wallahi har girman shi ya zube min wallahi arniya fa Allah tsare mu da
ita a gidan nan.
Diyan shi sai su girma suma su zama kafirai ke nan ko ?
Nace to shine daidai daahi don shima ai zuben yare ne gare shi baka taba ganin
yaya kace mai dan hausawa ne kullun yana cikin kananan kaya irin nasu.
Ke Bintu inji Amirah yaya din ne mai zubin arna kuma?
Nace rufa min asiri anty kada yajini nawa ya samay ni a gidan nan kuma .
Maryann tace na rasa may yasa mafi yawan yan kwallo suke auren diyan kafirai
wallahi.
A ji anty marayam fa ba,a cikin su suke ba suna ganin su kullun may zai hanasu
fadawa tarkon su.
Shine ai tunda dasu suke mu,amula can suna ganin su fa ko yaushe inji Amirah.
Sai da muka watse ne zancen ya tsaya min a rai na nace cikin zuciya na ai dama
muguntan mutum ke cin shi.
Yaya za,a kana dan musulmai kace arniya zaka aura a haka ma yaya aka iya dakai
balai ka auro kafira mara sallah kuma.
Wanan kan sai yadda Allah yayi dashi kan don ba ranan shiryuwa gare shi ke nan
kuma.
Ai su gasa junan su da mugun hali sune ma daidai da halin shi, ai tunda shi yace
shi mugu ne su karata, can wallahi.
Maji suna waya take ce mai ka sayo kayan da aka taba a cikin kayan lefen ka don a
cika.
Yace cikin murmushi maji ai yanzu angama yayin su kawai a rabawa yaran nan sai na
hado wasu kawai amma kada a taba gold din don akwai wanda na sayo da tsada tun
lokacin.
Mani tace zan dai zabi na kwarai na aje idan ka kawo sai akara ciki kawai yace
duk yadda akayi maji shike nan insha Allahu idan zan dawo zanzo dasu din.
Sukai sallama tana mashi fatan alheri da saka mashi albarka tana rokon Allah ya
tsare mata shi ya shirya su baki dayan su.
****** ********* ******
Kamar yadda yace karshen wata zai dawo hakan ne da yammacin asabar sai gashi a
gida nan aka shiga murna ana zuwa gaidashi.
Nikan tunda muka gaisa na gudu falon na shige don ina tsoron wani disgi kuma ba
wuya gareshi ysi min shi yanzu da dawowan shi.
Sai hira sukeyi maji da bata san bani falon ba tace don Allah Fatima dauko min
jakata a daki na.
Maryam tace wata Fatima maji Bintu kan ai dodon ta ya dawo tashige ciki tun
dazun.
Itace ta shiga ta dauko jakar ta leka ina kwance daki tana min sheri wai yaya
yana kirana nace o,o, ni ya su may zan mashi kuma ne wai ?
Tace ke wasa nake maki dan Allah kwantar kada kiyi fitsari a wandon ki please ?
Ban sake ganin shi ba don bamu hadu ba dashi tun ranan da ya dawo daga tafiyan
shi.
Kwanan shi biyu kawai ya juya ya koma Abuja sai da yai kwana goma sha uku ya dawo
gida a jike da abin arziki.
Ko ni na lasa don ba cikin gidan ba har makwabta sun san sadauki ya dawo garin su
Umma ya canza masu motar shiga don yace yana bakin cikin ya gan su a motan kasuwa
suna shiga.
Ranan munyi kallon kayan lefe mun baza kauyanci bani ba har su Amira yan birni
sai da sukayi kauyanci ga kayan .
Mummy tashigo ta gani sai faman mamaki takeyi da yaba kyan kayan tana cewa kai
wace yar sa,an keda wanan kayan haka.
Ina son naga wanan mai kayan nasan ba karamin gida za,a kai suba haka kan.
Hjy Kubura ai shi kyawon aure albarkan shi kawai yar masu hali da yar tallaka duk
dayane ga Allah Allah dai yasa andace kawai.
Hjy kubura tace gaskiya kan shine magana ai shima mai kayan da dan tallakawane
yanzu baga ikon Allah ba.
Maryam tace mumuy ai sai kinhaji daganin ta gidan nan ke da sarakuwan ki kune fa
yan kai kayan in Allah ya yarda.
Tace hakane fa kedai mairamu sai fa na gaji abuna namu maganin akwabe mu.
Su Umma basu shigo ganin kayan ba wai su ba,a gaiyace su suzo su gani ba don haka
basu zuwa.
Mummy tace kyale yan baki ciki duk hasadane da kyashi ke cin su