Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
Kai tun abin yana damuna har yakai yanzu na daina damuwa da rashin dawowan shi
wanda wata biyu.ke nan rabon shi da gida.
Sai yaya bashar mijin maryam abokin shi shine kawai ke dawainiya da mu tako wani
fanni duk da,ban taba cewa muna bukatan wani abuba a gidan na rayuwa.
Maryan yanzu cikin ta yakai wata biyar ke nan a jikin ta don har ya turo sosai
mutum zai iya gane haka atare da ita duk cikin mu ita kadaice Allah yabawa haihuwa.
Da kafa takan tako daga gidan ta zuwa gidan mu don motsa jikin ta idan zata koma
tare muke fita har Iya mu taka mata mu rakata gidan ta don bamu da nisa sosai.
Da dare muna cikin falo zaune ni da Iyan Rabi muna hira waja jen karfe tara na
dare a lokacin .
Sai jin sallama mukayi kamar daga sama muka ganshi har ya shigo tsakiyan falon a
lokacin.
Sadauki ne ya shigo muna gidan da sallaman shi ya murje yayi wani kyau yayi haske
kamar wani dan kwara dashi.
Cikin fara,an shi da walwala ya shigo muna a lokacin daga ni har Iya sai sannu da
zuwa muke mashi a lokacin.
Ganin da nayi fuskan shi a sake yake, yasani nima taron shi a cikin farin ciki
kamar babu komai a tsakanin mu can baya.
Zama yayi saman kujera tare da fadin wassh Allah Iya tace sannu na wurina da
kokari andawo yaya hanya yaya aiki da sauran jaman can.
Na,dawo daga,kai jakar kayan shi daki na nufo shi tare da dan dukawa na rugumoshi
ban damu da wai iya tana gurin ba shima dai rungumoni yayi zuwa jikin shi.
Iya dai kunya taji ta juya zuwa kitchen abinta tana murmushin yadda taga mun
burge ta sosai a yanayin mu.
Zauna da ni yayi saman cinyan shi yana sauke numfashi tare da kai hannun shi a
saman wuyana a hankali yana dan shafawa cikin lumshe idanuwan shi.
Daga inda Iyatake a tsaye take cewa uwar dakina nace ko sabon girki zamu dorawa
yaron nawa ne ?
Itace tadawo muna da hankalin mu muka tuna a inda muke zaune a lokacin.
Da,sauri yace a,a kubar shi kawai zan sa,akawo abinda zanci yanzunan kafin nai
wanka.
Mikewa nayi daga cinyan shi nake cewa Iya zo zauna ki huta abinki ai dan naki bai
faye danuwa da abinci ba idan bashi yaso ci ba kuma bama komai ne yake ci ba shi
dole yanzun sallon abincin mu ya canza ai .
Maimakon tazo ta zauna sai ta shiga dakin ta yana tambayana yaya muke yazaman mu
da Rabin dan musa nace bata da wani matsala wallahi ita ai mutum ce mai dadin zama
ga tsabta ga aiki bata gajiya wallahi.
Sai ganin Iya mukayi da dan jakar bakon ta tafito daga daki tana fadin uwar
dakina nikan zan tafi tunda maigidan yadawo yanzu.
Da sauri dani dashi muke hada baki cewa haba dai ina kuma zaki kuma iya yace Rabi
ina kike nufin zaki kuma ina anan zaki zauna gaba daya kina debe muna kewa kuma.
Tace a,a haba nawa ina zan zauna a tsakanin ku na hanaku shakakatawa kuna sabbin
ma,aurata da ku.
Iya bafa inda zaki idan kika tafi dawa kike son na zauna a gidan nan idan ya fita
shi ko baya garin ?
Ba sai na dawo ba idan yai tafiya din amma zan zauna na hanaku hutawa a tsakanin
ku ?
Murmushi yayi tare da mikewa ya nufi inda take tare da karban ledan hannun ta
yana cewa wai maji bata fada maki cewa zama zakiyi muna a gidan nan ba.
Tace zama Alhaji yace ai babu inda zaki don kinzo kenan nan zamu zauna dake gashi
kuma nayi sa,a uwar dakin naki naku yazo daya da ita yanzin .
Murmushin jin dadi iyan Rabi tayi tace ai Alhamdullahi don kayi sa,an mace tagari
da kowani namiji ke bukatan samu a rayuwan shi.
Murmushi yayi ya shiga dakinta ya aje mata jakar kayan ta yafito bayan yabi
dakin da kallo yaga komai akwai shi dakin na rayuwa yafito bai zauna ba don ya
fahinci zaman shi zai takura mata sai ya wuce zuwa cikin dakin shi direct.
Cewa iya nayi bari naje na hada mai ruwan wanka ya dan watsa yaji dadin jikin
shi.
Tace afiti lafiya hajiya nabi bayan shi zuwa dakin yana duke yana cire takalman
cover shoes bakaken dake kafan shi da safa.
Da sallama na shiga ya ansa min yana dagowa daga duken da yake yadda ya ansa min
a cikin sakin fuska yasa na karasa gurin shi.
Cikin kwarin gwiwa ya zuba min idanuwan shi na ce yaya hanya ya gajiya kuma?
Kalau yabani amsa da hakan nakai gare shi tare da kokarin fara balle mai aninin
rigan shi ta gaba.
Cikin sanyin murya naji yana cewa kin huce ke nan da mijin naki Fatima ?
Nace don girman Allah yaya ka daina wanan maganan adai gyara gaba please ?
Wallahi yaya yadda kasan mama bata kaunan wanan abinda kake yi haka zalika nima
bani kaunan ganin ka cikin wanan irin yanayin don kwata kwata ban iya controlling
din kaina a hakan.
Nakan jini ne kamar wata mara sa,a acikin mata don sai nake ganin kamar dunuya
zata zageni a dinga nuna ni.
Wata uwar harara ne ya balla min bashiri na kama bakina na kasa cigaba da
maganata.
Cikin maganan tausayi yace min don kina son na daina Fatima shine zaki dinga
nisanta kanki dani ?
Saboda kin mayar dani shasha haka kike zaton kowa yana dauka na a idon shi ko ?
Na katse shi da cewa kasan halin mutane yanzu yaya bazasu iya fada maka gaskiya
ba a gaban ka don abin hannun ka.
Yana da kyau kai nazari akan zance na zaka gane manufata a gare ka ba don na
rainaka bane ko wani abu a,a yaya gani nayi idan ban fada maka gaskiya ba a yanzu
waye zai fada maka shi.
Tsaki naji yaja yace kinga malama idan kin zo ne ki taimaka min kiyi abinda ya
kawo ki .
Idan kuma har yanzu raina manin wayyo ko hankali zakiyi ki fice min daga daki
rainin hankalin naki yana son yai min yawa.
Ke yarince dake zaki min wa,azin da mahaifana basuyi min ba ko may ?
Naga baki son mu zauna lafiya a gidan nan dake don nafahinci kina son ki wuce
matsayinki a gare ni.
Raina ya baci nace amma yaya dama inaga dai ka yadda ka auri ni ne don ka dinga
ci min mutunci ko ?
Kiyi wa Allah idan kasan bada zuciya daya kake zaune dani ba baka sona ne ka
sallamay ni na tafi gidan mu ka huta dani.
Wani irin kallo yai min yace Fatima ke da bakin ki kike fadar na sallamay ki
kikoma gidan ku?
Shiru nai mashi yace ok idan haka kike so sai kikoma ki fadawa wanda suka hada mu
sai su raba mi tunda shi kike bukata ke ?
Naga idan na biye mai daga dawowan shi zamu sake samun matsala kuma again.
Sai nai amfani da shawaran yaya bashar da anty maryam na wuce shi zuwa bathroom na
hada mai ruwan wanka tare da,aje mai duk wani abinda zai bukata na amfanin shi
ciki.
Yana shiga nafita daga dakin raina a bace da yan maganganun da mukayi da shi
yanzu na koma dakina na zauna a bakin gadona ina tunane.
Shima dai yana can yana wanka tunanen maganganun da mukayi dashi ne yasan ina da
gaskiya na amma bai bukatan na shiga harkan shi har takai na takurawa zamantakewar
mu dashi haka.
Yafito ya shiya cikin rigar barcin shi falon ya dawo sai dai babu kowa a falon
sai tv dake aiki shi kadai a lokacin.
Kamar ya shiga dakina amma sai yadake kawai ya zauna tare da canza tashan zuwa na
kwallon kafa.
Jin motsin shi afalo danayi na sauke ajiyan zuciya maganganun su yaya Bashar da
suka fada min na dole ne sai na kwanta mashi sosai zan iya,aiwatar da,shiri na akan
shi yasa na sauke ajiyan zuciya tare da mikewa na fita.
Rigan barci ke jikina alokacin sai faman kamshi ke tashi a jikina dan na gyara
jikina bayan fitowa daga gurin shi nima.
Murya na yaji a bazata daga bayan shi don baiyi tsanmanin zan kula shi bakuma har
yadan shiga dan damu akan yaya akayi ya bari muka dan sake samun sabani bayan yaga
na sauka daga fushin da nakeyi da farko dashi.
Cewa nakeyi abincin da kace za,a kawo maka kaci fa kuma gashi baka bari mun dafa
maka ba ?
Ya dan dago kai inda nake yana cewa No ki barshi kawai banjin cin komai yanzun ma
zai sha drinks da tea na sai na kwanta.
Nace lokacin dana karaso inda yake a zaune yaya drinks kuma shi zai sa ka koshi
yace is ok kawai.
Zan zauna yace dauko min laptop dina na duba wani abu a daki please ?
Juyawa nayi zuwa dakin nashi na dauko mai system din nashi maishegen kyau da
tsada.
Mika mashi nayi na juya zuwa kitchen tare da dora ruwan tea din nashi sai dai na
faki idon shi na barbada garin maganin da,akabani in bashi yasha din a ciki.
Najuyo mai tare da dauko drinks da cup har dan flaska din shayin nakawo mai.
Yace inji lemon baida sanyi don kinsan mutum bai shan ruwan zafi dana sanyi a
lokaci daya don gudun cancer.
Nace baida sanyi sosai amma dai bari na zuba ma a cup sai ya huce kafi ka sha.
Dakin Iya na wuce don jinta shiru danayi yau ba hira ke nan ta boye a dakin ta
don ganin shi a gida da tayi.
Na samay ta tayi barci sai rufo mata kofa tare da kashe mata wutan dakin dake a
kunne lokacin.
Na samu har ya bude system din shi ya fara aiki da zaiyi dashi a kan three seat
yake zaune nima saman na zauna tare da kaiwa kwance ina kallon tv dake aiki.
Can na dan ja tsaki tare da mika hannu na daga kwance na dauko remote zan canza
chanel din naji yace baki son wasan ball ke nan dai ko ?
Murmushi nayi tare da kai kaina saman cinyan shi nai filo dashi nace wallahi ni
ban taba fahintar may ake ba a cikin shi don ban san komai ba akai.
Dariya naji tayi yace kai amma shame on you matar dan kwallon duniya kuma bata
san ball ba aiko kinji kunya wallahi.
To yaya kunyan may tunda badani ake zuwa yin ball din ba can nan kuma ina diyan
hausawa yaya zan san wani ball can a rayuna.
Yace aiko ya zama dole ki sani don kada wata rana a tambaye ki mijinki dan lanba
nawa ne ki kasa bada amsa naji kunya.
Duk hiran da mukeyi hankalin shi na,wurin abinda yake acikin laptop din shi
lokacin baidago kan shi ba.
Muryan shi na kara ji again yana fadi amma ki saka a,ranki kulba dade kul ba
jima akwai ranan da,zaji hade da yan jarida zasuyi mako inter view akaona da kan ki
don har sai ki fara shitleya basu amsa da zaki fada masu.
Da sauri tare da dan dagowa daga kafan shi ina kall9n shi nace ni nidai din yaya.
Yace cijin murmushi kekuwa Fatima din nan rana da lokaci sina tafe muddin muna
araye zasu tambaye ki.
Komaqa nayi na kwanta kamar yadda nake da farko tare da ajiyan zuciya nace ashe
akwai aiki kuwa ke nan.
Dariya sosai na bashi yadda yake dariyan yana ci gaba da,aikin ya ban sha,awa ban
san lokacin da nakai hannuna ga fuskan shi ba na shafo a hankali.
Wani irin irin ajiyan zuciya ne naji ya sauke tare da lumahe indanuwan sho gyaea
kwanciya nayi akan jikin shi nace.
Basai ka fada min abinda zan fada masu ba ko kuma nace ni ban san duk wani
tambayan da sukai min ba ma.
Ban san har ya rufe laptop din nashi ba sai ji nayi ya mike ya nufi gyrin tv ya
kashe tare da kashe sauran na,urorin falon inda nake yazo ya dauke ni cak ya hada
da computer din shi sai dakin shi.
Saman kado ya dire mu ya jaye laptop din ta fado min saman jikina yana fadin
barin fada maki abinda zaki fada masu tunda shine kawai kika sani a gamay dani.
Bakina ya lalabo ya fara kai min kiss mun dade a haka can ona jin dadin abinda
hannayen shi suke min sai kuma naji ya tsaya tare da zare bakin shi a cikin nawa a
hankali
Ya juya yana mayar da numfashi a hankali can yake cewa sorry fa kada kuma na
sake maki fyede again .
Ban san lokacin da dariya ya kamani ba nace yaushe kuma ai kasaba min yanzun ma
gashi kayi min din again.
Auto ashe bari ma na karasa tinda har nayi maki ma waida kada nai lefi nake gudu
nace cikin dariya ai kaf8n kai min wallahi sai na rama nima don yau nice zan maka
fyede da kaina.
Kafin yasan may zanyi har na juya na haye mai ruwan cikin shi ko a hakali na cire
mai rigar jikin shi bai hanani ba nan nashi ga nuna mai wani sallon da ni kaina ban
ban san ina dashi ba.
Sosai muka gwadawa wa junan mu how far we miss each other a lokacin, tsawon
lokaci muka shayar da junan mu zuman ma,aurata ranan masha godiya ba adadi a gurin
shi kamar ba yaya sadauki bane mai izzigilancin nan.
Bayan komai ya lafa a tsakanin mu sai zancen shayin dana hada mai da magani
yafado min a raina.
Gabana ya fadi kada yazo baisha ba ai hasaran maganin gashi yaya bashar ya jadda
min na tabarar da yasha ahi sosai fa.
Ikon Allah sai naji yace ni wallahi har kin sani jin yunwa ma sosai wallahi nace
ai ruwan shayinka na nan baka sha ba.
Yace anya yadda nake ji din shayin nan kuwa zai dauke ni a yanzu gaba na ya kara
faduwa kada yazo bai sha ba fa.
Muryan shi ne yake fadin tsiyayo min insha kada kice zaki fita yin wani dahuwa da
daren nan kuma.
Don keta sai da na zuba mai da yawa kuma nai sa,a duk ya shanye cup din gaba
daya.
Sai da ya shanye yake cewa amma sai naji shayin ya dan canza test yau ko ya fara
expire ne dai nace ko kuma don ya dade a bude yai sanyi yasa shi canza test ba yace
indai a bude yake shi ya kawo hakan gaskiya.
A haka muna dan hira naji yayi shiru barci ya kwashe shi lokacin ga gajiya ga
aikin magani ke nan.
Mikewa nayi nashiga bathroom nai wanka tare da dauro alwala nazo nai sallah
raka,a hudu ina rokon Allah yasa mu dace ga maganin.
Muna barci can shiyoyin asuba naji cikin barci yana wani irin nishi sosai
abinda ya falkan dani ke nan a dan firgice cikin tsoro yadda naga ya dunkule guri
daya ya dafe cikin shi.
Cikin tsoro nake magana yayana may ya samay kane may ke damun ka kuma ?
Cikin shi ya nuna min da hannu nace a dan razane subbahanallahi ciwon ciki kuma
ko may ya gyada min kan shi da kyat .
Nacw daure mu shiga bathroom kadan yi wanka ko zakaji dama sai na fita na hada ma
abinci ko yunwane don kaga jiya bakaci komai ba ka kwanta hakana sai ruwan shayi .
Ban samu amsa ba sai murde murden da yakeyi a lokacin kawai na ciwon ciki na mike
na shiga na hada mai ruwa na dawo ina yake kwance.
A hankali na duka cikin kunnuwan shi ina rada mai ya tashi mu shiga bathroom din
yai wanka hannun shi ya miko min da taimakona muka shiga har bandakin .
Ranan dole yanayin da yake ciki na cire kunya na hada mai ruwa da kaina nai mashi
wanka wankan tsarki ne kawai ya daure yayi da kan shi lokacin.
Ba laifin wankan ya sa yaji dan sauki ana kiran sallah mukai sallah ya koma ya
kwanta nafito zuwa sama mai abinda zaici inayi ina lekashi dakin shi.
Ranan a daki nakai mai ya dan daure ya tsakura kadan yaci yace baijin dadin
bakin shi ko kadan.
Koda Iya tafito ta samu na hada abin karyawa ko sai gyaran gida kawai tayi
nafito daga dakin a cikin shirina na samay ta tana aiki muka gaisa da ita.
Tana tambayana kwanan dan ta nake fada mata wallahi Iyya yau dannnan naki ciwon
ciki ne ya hana shi barci .
Tace da sauri subbahanallahi ciwon ciki kuma da sauki dai ko nace da sauki don ya
ci abinci yace idan ya tashi zai sha magani .
Dakin na koma sai dai bai saman gado yana bayi ina na tsaye har zan juya sai naji
yana kakar8n amai daga cikin bandakin .
Da sauri na isa gurin amai yake shekawa wani irin bakin amai ba dadin gani.
Wasa wasa amaiko yaki tsayawa sai faman sheka amai yakeyi hankalina yai matukar
tashi sosai na fita na kira wayan yaya bashar na fada mai sadauki fa ba lafiya
ciwon ciki da amai ya damay shi.
Yace subbahanallahi gani nan zuwa yanzun nan muna gama waya dashi nake shawaran
kiran mama na fada mata .
Itama kiran ta nayi don kada taji daga baya taimin fada gata tana a cikin gari
kuma.
Tana ganin wayana tunda safe haka gaban ta ya fadi ta dauka take tambayana Fatima
lafiya ko nake fada mata abindake faruwa tace subbahanallahi gamu tafe yanzu.
Yaya bashar ne ya fara shigowa lokacin muna ban daki dashi har bedroom din
yashigo nan yasamay shi yana wanan bakin aman nashi.
Yace subbahanallahi man may ke faruwa ne kuma yadago kai da kyat jin muryan
aminin shi idanuwan shi sun canza launi sosai.
Yace wallahi ban sani ba man ciwon cikine sai kuma amai da ya biyo baya da kyat
yake iya magana a lokacin .
Shi ya kamashi ya