Advertisements
Chapter 69 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   69 / 92

204K to 207K   out of 275.8K words

abina sai ji nayi ta nufo
zata kara kai min maka na dago ido waje nace kada ki soma kara tabani don zan rama.
Ko dazun ma arziki kikayi a gaban kawayen kine kada ki matsayi yata na disgaki a
gaban su shiyasa na barki.
Yadda taga na nuna tasan za,a samu matsala sai ta juya tana fada tafice daga
dakin.
Tana fita wayan yaya sadauki takira tana fada mai wai na hana mata abinci taci.
Yace ina ganin bata jin dadin jikin ta nd don tun jiya nake jin ta hakana.
Tace shiyasa ban son zusa gidan nan wallahi sai yarinya tai batun raina maka
wayon ,
Kashe wayan yayi yana mamakin iri wanan hali haka da ta sakd lokaci guda.
Tun daga wanan rana ban kara girka komai ba koma nayi iya cikina nake girkawa
naci



ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


A LOKACIN MU KE,,,,


Tashin hankali a gidan su sadauki haka aka kai dare a cikin shi sai da kyat ya
shiga dakin ya lalashi Nafisa dake ta faman hauka aka samu tai barci bayan irin
tonon asirin da take zubawa umma da mama kawai tana kiran su da munafakai masu bin
boka da malam.
Haka ya dawo gida ranan rashi a bace ina daki naji shigowan shi musalin takwas da
aani abu na dare.
Nafito daga dakina saye cikin wasu kananan kayan da ya sawo min a cikin tsaraban
daya zo min dashi.
Ina fitowa ya sako min mayan idanuwan shi har sai da naji kunyan hakan da yai min
din.
Sannu da zuwa nai mashi idon shi na akaina ga damuwa karara a duskan shi.
Gefen hannun kujeran da yake zaune akai na zauna tare da cewa yayana may kuma ya
faru ne naga kamar kana cikin damuwa.
Murmushi yayi a fili amma a zuciyar mamaki yake yadda nake saurin fahintar halin
da yake ciki ko yaushe.
Yace ba komai Fatima dan matsalane kawai aka samu a gida da sauri nace
subbahanallahi injin bada mama ba.
Yai murmushi ya jawoni zuwa jikin shi yana cewa don mamace kadai taki a gidan
ko ?
Nace cikin murmushi ba hakana bane yaya ban dai son ace wani abu ya samu mama din
ne kawai.
Yace yana sauke numfashi, Umma ce dai da Nafisa kawai ta dan shawo ne tazo gida
tana hauka har ta jin ma umma din ciwo a kafan ta.
Nace innalillahi wa inna alaihim rajjiun Allah yai muna sauki wanan al,amarin
kawai.
Oo ita anty Nafisa bata da ranan gyara rayuwan ta ne wai bata ganin cewa ita mace
al,amarinta daban yake dana maza.
Ajiyan zuciya naji yayi yace zan samu lokaci ai na zauna da ita don na dan
fahintar da ita ko Allah zaisa ta gyara halin ta amma gaskiya abin baiyi ba
wallahi.
Allah ya kyauta nace tare da numfasawa na fara tunanen aanan halin rayuwan na
shaye shaye gamu da acikin ta don ban sani ba ko wani hali shi mutumin nawa yake
yanzu ko ya daina ko yana ciki tsunbul.
Jinayi yaja min hanci na shiyasa na sake sauke numfashi ji nayi yace kina tunanen
naki mijin ko?
Murmushi nayi nace aini nawa mijin Allah ya,kawo mai sauki da sauyi a rayuwan shi
Nafisa dai nake tausayawa kawai da sauran al,umma masu hali irin nata.
Idan kin gama tunanen ki nima sai ki taimaka min da dan ruwan wanka na watsa ko
zanji dadin jikina.
Mikewa nayi sai naji ya kara jawoni na koma jikin nashi yake cewa amma fa zaki
cika ladan ki don ke ce zaki min wankan don banjin lakkan yin da kaina ko kadan.
Da sauri na dan juyo ina kallon shi sai yake cewa eh haka na fadi ko baki ji ba
nace amma yaya gaskiya sai kuma nai shiru yace to shike nan barni hakana na kwana
da dauda.
Jin abinda ya fadi yasa jikina yai sanyi hakka na mike na nufi dakin nashi
murmyshi ya sake tare da bin bayana da kallo kawai.
Sai da na hada ruwan wankan na aje brush din dana matsawa maclean da soso da
sabulun wankan shi na fito daga bayin.
Yana zaune a ida na barshi a falon na ce a sanyaye na hada yaya yace ok sai naga
ya miko min hannayen shi alaman na kama shi ya daga ke nan.
Murmushi nayi nace ni ina zan iya tayar da kato dan kwallo haka kulun cikin motsa
jiki.
Dariya nabashi ya kara mika hannayen shi inda nima na kama hannayen nashi na
mikar dashi din kamar yadda ya bukata din gare ni.
Amma kuma kamar ina daga dutse gashi na saka duk karfina na dago shi amma na kasa
jawoni yayi na fada a jikin shi tsab ya mike tsaye dani a hannayen shi.
Bai dire dani ko ina ba sai tsakiyan dakin shi kawai ya tsaye kimkam yace sai ki
fara aikin ko?
Kallon shi nayi yace uhumm bissimilah ki cire min kaya ko ?
Kallon shi nayi fuskan shi a daure dole na fara kokarin cire mashi rigan dake
jikin shi.
Nakai ga wandon shi ina kokarin cire ina kawar da kaina a gefe tsaya yake kimkam
dashi sai murmushin abinda yaga ina yi na kawar da kaina gefe daya.
Ina na cire wandon na kara dukar da kaina kasa, ashe akwai wani gajeren wandon
maza daga ciki jin bai motsa ba yasani dan dago kaina.
Kai ya gyada min tare da kashe min ido alaman saura wanda ya rage daga ciki din .
A hankali kaina a duke na karasa cire mai wandon sai naji ya sauke ajiyan zuciya
da sauri na mike na nufi inda towel yake na dauko ina mika mashi tare da kawar da
kaina gefe daya.
Hannu naji yariko da kyat na iya dago kai tare da juyowa na dan kalle shi kai ya
gyada min alaman bai bukatan towel din yau.
Nashiga uku na furta a raina ashe har a fili na fadi hakan ban sani ba sai naji
yace akan may kika shiga uku fatima ko rabi ban bari ki shiga balle har uku.
Muje kiyi min wanka please da sauri na shige gaba tana bina a bayana sai faman
kawar da kai kawai nakeyi gefe daya don ban son dago kai na kalle shi, don wani
irin mugun kunyan da nake ji a lokacin.
Zama yayi a cikin bahon ruwan inda na fara yi mashi brush sai na hau yi mashi
wankan idona a rufe har muka gama muka fito.
Dan towel na dauka ina goge mai jiki dashi sai faman lumshe idanuwan shi kawai
yakeyi a lokacin.
Kayan da zai saka na dauko mai wani dan riga daga cikin kayan barcin shi sai
wando gajere don nasan ba zai fita zuwa ko ina ba kuma.
Falo muka dawo ya ci abincin shi da ya kare ya koma saman kujera two seater ya
zauna ni kuma na kama kwashe kayan nagyara ko ina tsab.
Inda yake a zaune na dawo na zauna a dayan kujeran dake daga gefen shi waya yake
amma sai ya yafito ni da hannu alaman na dawo gare shi.
Abin da ya buka ta nayi inda na dawo daga gaban shi na zauna a hankali ya fara
kai hanayen shi saman jikina yana aiwatar da wasu abubuwa can na ma,aurata.
Tun ina lumshw idanuwana har nima na dan fara mayar mai da martanin abinda yake,
min nan muka shagalar da junan mu a falon .
Lokaci mai tsawo muka dauka a hakan cikin wani irin yanayi mai shagalar da mutun
a inda yake.
Sai da ya tabbatar da kowan mu ya gamsu da dan uwa sannan ya sarara min.
Dakina na koma nai wanka na gyara jikina tare da saka rigan barci na na nufi
dakin shi don nasan dai duk wani abinda zaiyi a ranan yariga yayi shi a falo ko sai
dai kawai mu kwanta kawai mu huta.
Shima dai na samu yayi wanka ya kwanta a hankali na hawo gadon ta bayan shi tare
da rugoma shi daga bayan shi.
Murmushi naji yayi tare da juyowa gare ni yana jawoni jikin shi nai mamaki dana
ji kan shi da bakin shi a saman kirjina again.
Sai da gabana ya fadi nan ya shagala a saman kirjina tun ina rutse idanuwana har
yakai nima ina jin dadin abinda yake min.
Sosai muka tsotse junan mu a karshe ta shigeni yadda ranshi ke so sai barci mai
nauyi yai gaba damu.
Washe gari bamu tashi da wuri ba sai after nine na safe don haka mukai sallah a
makare .
Ya ce kada na girka komai na koma na kwanta idan mun tashi zaifita ya samo muna
abin karyawa.
Nan muka koma barci sai to one muka tashi wanka kowan mu yayi lokacin duk muna
bukatan abinci.
Nafito falo naji ana sallama na nufi kofa naga ko waye yaya Bashar ne tafe dauke
basket dauke da abinci daga gurin maryam.
Nai sauri na karba ina gaishe shi tare da bashi hanya ya shigo ciki lokacin
sadauki ya fito daga daki shar dashi kayan da yasa sunyi matukar yi mashi kyau
sosai.
Nan suka zauna suna hira na nufi dining da kayan na fara had gurin yadda ya
kamata bayan na bude ne naga tuwo semo ne da miyan yauki.
Nace mai ga abincin can na hada mashi, a dining yace ok bari na dan ci abinci
bassh.
Yace bari dai naje gida nima jirana ake muci nafito zuwa gurin ka kasan maryam
yanzun ba ita kadai bace.
Ita da waye ya tambaye shi yace a anfada maka ni irin kane raggo sai iya jefa
kwallo fa raga kawai amma ba ka iya jefa shi inda ya dace a jefashi ya shige.
Dariya yayi tare da kaimai nashi ya gwauce mashi yana fadin baka da kunya,wallahi
wai ka manta cewa ni surukin ka ne.
Har zai fita yace kuna ko da labarin Umma bata da lafiya idan kaje ka fada mata
please.
May kuma ya samay ya tambaya cikin son ji hankalin shi a tashe ya bata fuskan shi
yace kawai dai dan matsalane ita da Nafisa shine ta gwauce kafan ta.
Yace mashayiyar ta shawo ke nan tazo tana hauka a gida ko yace raban ma acan na
gane ta ta bugu a hanya duk dan taxes din ta tsare sai yaki tsayawa ni na daukota
zuwa gida tana min tanbele a hanya.
Yafita yana maijin haushin halin rayuwa irin na Nafisa da ta jefa kan ta a ciki
yanzu.
Sai wani dukar da kaina keyi don balain nauyin shi da kuyan shi nakeji yau din
sam ban iya hada idona dashi.
Can yace ke na ce naam yace dago idon ki ki dube ni nan da kyat na iya daga kaina
kalleshi sai nai saurin dukar da kaina kasa kawai.
Murmushi yayi yace wai wanan kunyan na may ye kuma haka ko abin bai sheki bane na
kara maimata maki fiye dana jiyan ko?
Da sauri nace don Allah dai yaya kayi hakkuri kawai dai ban san yadda zan kalle
ka bane dai.
Ok yanzu zan kawar da kunyan nan ai daga yau bazaki kara jin shi ba aiko da gudu
na kwasa sai cikin dakina harda saka key na rufe daga ciki.

****** ********* ******
Kaya irin na marasa lafiya muka saye sai gidan su mama kwana biyu ke nan da
faruwan abin amma kafan ya hau yai sundum dashi.
Tana ganin mu duk da nishin da takeyi amma bai hanata daure fuskan ta ba a
lokacin.
Mun gaida ita tare da mata yaya jiki cikin daure fuska ta amsa muna Allah ya
sauwaka nai mata tare da mika kayan gaisuwan da muka zo mata dashi.
Na mike na fita na barshi a dakin nasu dakin mummy na shiga na gaida ita na fito
zuwa dakin mu.
Ina fita a dakin umma yaya sadauki yace ina Nafisa take ne wai ?
Umma bata amsa mashi ba sai sagir ne yace mahaukaciya tana ciki mana yar iska
kawai.
Kira min ita yace wa sagir din nan ya mike ya shiga har dakin Nafisa yace tazo
yaya sadauki na magana da ita.
Tafito jikin ta babu ko riga tace cikin wani yamuste fuska yaya sadauki ina wuni
ya amsa mata cikin girgiza kai tare da tausaya mata.
Yace Nafisa ina son ganin ki don Allah gobe a gida na idan babu damuwa.
Tace ina ne gidan naka nema wai ?
Yai mamaki da wai batasan ma gidan shi ba yace sagir zai kawo ki idan kin tashi
goben.
Tace kai tsaye niba zan shiga mota dashi ba ya illanta ni ga banza kawai mugune
kagan shi nan wallahi yaya .
Tausayi tabashi don abin ya fara taba ta sosai dole ne a taimaka mata.
Ya mike yana fafin kada ki manta please sai nagan ki ko ya ciro kudi ga aljihun
shi yana mika mata yace ga kudin mota ko idan zakizo.
Sagir yace kada ka bata yaya wallahi wanan shegiyar maye zata sha dashi don dama
shi take nema kaga ta lafa a gida tana neman na wanda zata ware dashi idan mai shi
yai sakaci.
Yace ka barta dasu ai zata zo din kasan Nafisa akwai cika alkawari tace nagode
babban yaya irinka muke so ko yaushe ba masu hana abamu ba.
Amira ce kawai a falon lokacin mama tana daga ciki na gaida ita tare da mata yaya
kwana biyu.
Banza tayi dani kamar bata san ina gurin ba ma a lokacin sai wayan ta kawai take
dakila a hankali a lokacin.
Nace anty har yanzu kina kallon film din queen of south ko kin daina ne don
shirin yai nisa sosai.
Ke Bintu kikama kanki dani wallahi don idan kikai min tsiya yanzu na lahira
zaifiki jin dadi wallahi ko.
Haba anty daga tambaya kuma shine laifi Allah ya baki hakkuri nacs mata sai ko ta
dago da nufin kai min duka ji tayi daga kofa yace kada ki soma wallahi yanzu zan
bata maki rai sosai wallahi.
Yar kice koko kaunan ki da duk lokacin da kikaga dama zaki dinga dukata son
ranki.
Duka kuma dukan wa kuma wai ban fahinci may kuke magana ba akai wa ake duka ne
wai ?
Bai fasa magana ba yace kin san ina da hayshin marin da kikai mata ranan yau kuma
don samun guri zaki kara dukan ta to bisimillah gaki gata shege ka fasa.
Tambayan ku nake wa ake duka ne wai yace maji rabu da yar rainin wayo yarinyar
nan ban san yaushe ta zama haka ba wallahi.
Har gidana fataje ta samu Fatima da mari ta tara shegun kawayen ta a gida suna
juyata kamar ta samu yar aiki.
Bai isheta ba kuma yanzun daga tambaya shine wai zata duke ta again.
Duka shin Amira ko may dukan Fatima fa akace kinyi ko may ko kin fara shaye shaye
ne kema bamu sani ba?
Bata fara komai sai rainin wayyo kawai ta ji na fada mata duk ta kara dora hannun
ta akan matata ko zagi wallahi sai na bata marai Allah.
Nikan mikewa nayi na cire hijjab din dake a jikina na fara gyarawa mama falon ta
da duk ya wani yamutse kaman bashi ba.
Na gama na koma can uwar dakin da dama nike gyarawa nai mashi kwal na kwaso shara
gudan mai yawa.
Mama tace ki duba ki gani yadda muke zaune a cikin shara haka saboda shegen son
jikin ki kin kasa gyara muna mazaunin mu sai fama da dakilan waya.
Nagama na dawo na zauna yace ke in kin gama tashi mu tafi akwai inda zamu biya in
mun fita.
Tun muna hanya bayan mun baro gidan su mama nake jin marana yana murda min a
hankali alaman period zai zo min ke nan.
A hankali na dan ya mutsa fuska na sai kawai naji yace ba tare da yakallo niba may
nene kuma ya faru.
Sai da na sauke ajiyan zuciya nace ba komai yace shine kike yamutsan fuskan ki
haka kawai.
Murmushi nayi nace bakoma mun tsaya wani shago naga yayi sayaya yafito aka sa mai
a bayan motan shi.
Bamu tsaya ba sai gidan Inna mahaifiyar Bashar naji matukar dadin haka muka shiga
a tare mun samay ta da yaran ta zaune suna hira suna ganin mu suka shiga murna.
Nan muka zube muna gaushe ta ta matsa sai mu tashi mu hau saman kujera bamu dade
ba don yamma yayi a lokacin.
Mun isa gida duk nagaji ga marana yana min ciwo sosai a lokacin daurewa kawai
nakeyi.
Na shiga yin alwala naga har jini yazo min ko nan na dan daureye jikina na fito
ina tunanen yadda zan fadawa yaya ina period yau.
Ban fito falo ba ina kwace rike da marana dake min ciwo yashigo dakin yasamay ni
na kifa kai a filo sai nishi nakeyi.
Yake tambayan wai may ke damun kine haka kinki fada wa mutum ko so kike ki halaka
kanki ne wai?.
Da kyat na iya cewa marana ne ke min ciwo tun dazun, yace shine baki iya fadi na
sai maki magani tun a hanya.
Shiru nayi ba amsa yace ko period zakiyi ne wai a hankali na gyada mashi kai tare
da cewa har ma yazo min ai.
Yace ashe ko da gaskiyan Bashar ni raggo ne tunda na kasa jefa kwallo a wana jan
ragan naki.
Turo baki nayi yai murmushi tare da mikewa har yafara tafiya yace kwana nawa kike
yi dashi ne wai ?
Nace sati daya da karfi naji yace what ?
Sati daya fa ko baki da lafiyane zaki dinga sati kina fitar da abu daya haka
nan ?
Kara kife kaina nayi kawai batare da nai mashi magana ba naji da abinda ke
damuna kawai.
Fita yayi zuwa can ya dawo min da magani da lemo mai bawa da sauran kayan fruits
.
Sai da nasha maganin na samu ya dan lafa min na

69 / 92