Advertisements
Chapter 10 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   10 / 92

27K to 30K   out of 275.8K words

zancen ne taji shi kamar da,tsawo a zuciyan ta.
Mai masa ina,sauraren ki kinji rabu da mara kunyar nan futsarara.
A,a hajiya barta don Allah duk ba yin kan su bane ai ,abinda ke tafe dani shine.
Yaran ki gaba daya wallahi an sa masu hannu, duk yadda kike fatan samun su
gaskiya a yanzu abin zaiyi matukar wuya.
Don gaba daya an lalata masu rayuwan su ta inda ma baki zata ba wallahi.
Kai ni wallahi ban son irin wannan spercition believe din na,anyiwa wani wani abu
wanan ai duk shirka ne.
Hmm kawai mai masa tace tare da fadin kaiyya bazaki gane ba ke yar nan sai an
makara ko?
Tiryan tiryan yadda malam ya fada wa gwago haka ta fadawa Maji bata boye masu
komai ba don taga basu da niyar yarda yaran.
Tabbas kuwa hajiyan masa na tuna anyi hakan don abin nima ya tsaya min arai
sosai.
Don wata rana yaya babba ta ce wai kifine ta dafa wa yaran ta zaunar da sadauki
wai ga nishi da ta aje mai saida ya cinye shi tas,
Ya kusa gama cine sai ga babangida dan ta ya,shigo yana cew sadauki ya,raga
mashi amma,babu kunya a gaban mu yaya take cewa wai a,shi kadai tayi kada yaba
yaron,
Amma dashi sadaukin ya mikawa dan uwan sauran da ya,raga sai tai wa yaron nata
jan ido akan idan yaci sai ta bata mashi rai sosai wallahi.
Daga baya ne tunane yazo min cewa may zai sa yaya ta hana babangida cin kifin
bayan tace a tare ta dafa masu shi.
Wallahi ko anyi haka don ba,a fi watanni ba yaron nan yafara birkice min na rasa
gane rayuwan shi gaba daya a gidan nan.
Shagon da suke fita gaba daya ma ya daina fita duk fadan Alhaji dole yasa mai ido
ya bar shi don ba yadda za,a yi dashi.
To kinji ke mai cewa wai duk sharce ne na malaman tsubo kawai ko ku din ai baku
tsira ba nan ta fada masu abin da su ma suke ciki a rayuwan su.
Haba gaskiya abin kan da ban mamaki inji maryam don cewa fa su Lawisa basu kai
mutu. Komai ba amma kullun gidan nan sune da sabbin samari kai gaka zaune ko tsoho
bai zuwa yace yana son mutum.
Amma gaskiya duk wace tai muna wanan abin inji Amira sai Allah ya saka muna
wallahi ko.
Ai ko baki ce Allah zai saka maku don zai koma kan mai shi da yardan Allah.
Yanzu dai ga,wanan yace na kawo maku ku fara sha nan da,sati biyu zan koma na
karbo maku sauran hadin insha Allahu.tana kokarin sance ledan dake a hannun ta.
Kuma yace da hannunki zakiba ko wani yaro yasha wanan rubutun, shikuma sadauki
idan da hali yace nazo mashi da kashin shi akwai abinda zai yi dashi wanda zai sa
ko warin kwaya bazai so ya sake ji ba a,rayuwan shi.
Cabdi aikuma shine babban magana wallahi don nasan ba zai yarda ba ya bani
saboda shegen tauri kai ne dashi inji Maji.
Lalai nima nayi tunanen hakan tun a can amma dai yanzu yi kokari ba,shi wanan.
Ta kara fito da wani kulli yace da nonon akuya zaki hada ki bashi ya,shanye yace
idan har abin yai aiki zakiga kwana biyu yana yawan barci ki kyale shi maganin ne
yake aiki a kan shi.
Nan dai taba da harda wanda su Amira zasuyi wanka da hayaki dashi don makarun
asirin da ke kan su harda shi gaiyar aikin.
Mai masa nagode nagode kwarai wallahi, ban ma,san kalar godiyan da zanyi maki ba
ni wallahi.
Wai yanzu don Allah shi mutumin bai fadi wanda yai muna wanan irin aikin ba ne
don mu sani.
Yafadi bai fadi ba yadai ce min mata biyu ne sai namiji guda kuma ba,atare suke
aikin ba kowa tashi tafishe shi ne.
Yace shi bsi son tonon asiri bukatar shi dai aiki yayi kyau asamu biyan bukata
don fadin zai kawo hadin hasumi.
Ikon Allah yanzun ni mai na tarewa mutane har na samu makiya daga cikin su
haka..
Mai masa may nakd dashi a gidan nan daya tsone wa mutane ido dashi har za aimin
haka wai ?
Nuna yaran mai masa tayi tace gasu kuwa abinda kika raina,shine ya dami wasu ai.
Wallahi Maji nafi zargin su mama da Umma don sune basu kaunan mu a gidan nan.
Kada kuyi zaton haka ya kasance basu bane din don zato zunubi ne koda ya zama
gaskiya.
Kada azo ana zaton wuta a masaka,asmay shi a makera.
Hakane fa to amma gaskiya su sunfi nuna basu kaunan mu sam wallahi tun muna yara
mun san da hakan.
Yanzun dai abar wanan zancen don koma waye mu barshi ga Allah shi zai saka muna.
Yanzu mai masa nawa zanba wanan bawan Allah ke nan don ni har ma na rude wallahi.
Dole ki rude ai don wanan magan ba karamar magana bace saboda yanzu a lokacin
muke kana barci ana maka nasari a kai.
Nan dai suka dan taba huran lokaci tsakanin su tai masu sallama tabar su nan suna
jimamay.

****** ********* ******
Da farko maganan bai so damuwan Maji ba amma da,dare yayi kasa barci tayi tana
nazari akan irin zaman da take da abokan zaman ta a gidan.
Wanda dai ita taga babu ruwanta da,hassadan ko dayan su balle zurian su , bata
taba tunanen wai ta aikatawa wa dan ko dayan su wani mugin abu ba koda a,baki ne.
Amma yau gashi ita an sakata gaba har yan yaran da ta haifa a gida ba,a barsu
ba don hassada kawai.
Ita dake da yara uku kawsi kacal amma wai sun tsone idon masu bakwai tara da
hudu.
Haba jama,a kishi haukane wai da har zaka salwantar da dan kishiyan ka kan bakar
kishin da iyakar shi nan duniya sai kuma lahira inda,za,ai hisabi.
Lalai yanzu lokaci yayi da kowa zai kama taka tsantsan da dan abinda Allah
yaba,shi don gujewa sherin shedanu mutane.
Gaskiya sai yanzu tasan tayi mugin sakaci akan yaran ta don ita ko goro bata taba
basu ba da,sunan wai tsarin jiki.
Musan ma ma,shi sadauki wanda ya tashi tun yana yaro da shiga idon jama,a.
Don haka yake kamar dan larabawa ga kyau ga ilimi ga kunya gashi da miskilanci.
Bai shiga harkan kowa ba,agida ba har gari baki daya, bazata iya cewa ga,ainihin
abokin shi na kurciya ba balle ma yanzu da ya koma hakan.
Tayi tayi ta san ko da wa yake hurda da har ya fara wanan shaye shayen amma ta
rasa aini hin abokin shi.
Dan dama dama,ma,yaron malamin da,sukai karatu a gurin shi na islamiya ana ce
dashi Manir shi manir hae yanzu yana zama da mahaifin shi yana koyawa yara karatu a
kofan gidan su.
Don haka bata zargin Manir da wani harkan sha,shanci ko kadan sai ma jin dadin
shi na aminin shi da take yi.
Don tasan ko banza zai dan dinga mashi nasiha akan sabon halin da ya dauko ma
rayuwan shi.

Sai da dare ya shigo gidan har zuwa yanzu inka gan shi kamar natsatse yake sai
dai gaskiya bai bari ba don bai jin zai iya barin sha gaskiya da,wuya.
Amma dai yanzu shan da yakeyi na,tsanaki ne a ganin shi yana wayo ne don kada a
gane shi.
Abinda bai sani ba shine karfin adduan mahaifane ke tasiri a kan shi lokacin.
Don Alhaji yaba bada kudi ana mashi addua yanzu sosai sabanin da can da yake
daukan abin da,wasa.
Ya fadawa wani amin shi a kasuwa irin halin da yaron na shi sadauki yake ciki.
Mutumin yai murmushi yace Alhaji ke nan kai kama yi arziki yaro daya ke wanan
halin.
Ni wallahi har da yarana mata suka fada cikin wanan mugun rayuwan nayi nayi abin
yafi karfina dole nasa wa sarautar Allah ido.
Kasan sai mutum ya,daga hammatan shi ake jin wari amma yanzu duk wanda kagani
yana da matsala akan iyalin shi sai dai mutum ya rufe kawai.
Don abubuwane gasu nan ba iyaka da lokaci ya kawo muna,sai dai Allah ya kyauta
kawai.
Akwai wani malamina zan kaika gurin shi onda abinda abinda zai iya maka sai ya
taimaka muna dashi.
Don kasan kowa da irin abinda ya karbe shi mai yuyuwa ni banci nasaraba kai kaci.
Abubuwa da dama Alhaji keyi akan Sadauki amma ba wanda yasani a gidan har ita
mahaifiyar yaron ma kanta batasan yanayi ba.
Don ita gani take ita kadai ce keda damuwa akan yaron kawai shi ai yana da,wasu.
Bata san cewa shima abin kamar yafi damun shi ba, don shi ke fita yana ganin duk
gari kowa yasan da dan shi mashayi ne.
Yazama mutumin banza ke nan a idon mutanin gari ai.
Suna hanyar su dawowa ne, wani abokin shi ya tare shi hanya yana ce mai bayan sun
gaisa.
Alhaji yaya akayine yaronnka ya samu abin arziki, amma kuma kukai sakaci da
hakan.
Ban fahince kaba ai wani dan nawa ke nan kake nufi daga cikin su.
Yace U, F mana dan kwallon nan dake gidan ka ance an zo sayen shi yafita zuwa
ghana buga kwallo amma baku yarda ba.
Kana nufin Umar Faruq ke nan ko sadauki muke kiran shi ai shifa shi.
Wallahi yaron ya iya kwallo sosai don hakane ma couch din su yai mashi hanyar
fita amma wai baku yarda ba.
Sai abokin tafiyan Alhajin ke cewa kai amma kuwa Alhaji baku kyata ba da kuka
hana shi zuwa ai wani hanyane na samu nan ma.
Abinda muke ganin yan kudu kawai keyin sa yau gashi ya kawo ga yaran mu.
Don Allah kubar yaron nan yaci gaba da,wasan shi kada ku lalata mashi hanyar
samun shi.
Shiru Alhaji habu yayi don shi bai ma san da zancen ba a rayuwan shi don ba,wanda
ya taba fada mai hakan.
Yace cikin mamaki gaskiya banda masaniya,akan wannan magan ni in ba yanzu ba din
bai taba samuna da,wanan zancen ba gaskiya.
Amma zan bincika naji ko mahaifiyar shi ta san da zancen ita.
Gaskiya a bincika don kaga har team din farko sun shiga gasu sun dawo da abin
arziki mai yawa wallahi.
Don Allah Alhaji kubar yaron nan ya tafi don akwai alheri so sai ga,wanan harkan
don ba harkan banza bane gaskiya.
Ga yaron naka yana samun yabo sosai a gurin abokan shi dama mutanen gari don
haka abarshi kawai yatafi ko zai zama alheri a nan.
Sunyi sallama da mutumin bayan sun kama hanya da abokin shine mutumin ke cewa
kaga ikon Allah ko kai duk ka damu kanka gashi ashe mutane kallon mutumin kirki ma
suke wa yaron.

****** ********* ******
Sadauki ya,gayar da Maji a cikin mutunci tare da tambayan ta lafiyan ta?
Maji tabashi amsa a takaice da da sauki, Alhamdullahi dama ai kaine kaso kashe ni
da raina.
Murmushi kawai yayi irin nashi can saman fuska yace ayi hakkuri don Allah, insha
Allahu na daina ai.
Suna nan suna dan hira shi dai yana zaune baice komai ba kuma bai ma sauraren su
hankalin shi na daga maganan Maji.
Ke Amira dauko min ledan nan na,saman TV stand kikawo min ba mussu Amira ta mike
ta dauko ledan take cewa kawo min ludayi a kitchen.
Bayan an kawo ludayin ta bude roban maganin ta,zuba tana mai addua a bakinta cewa
Allah yasa wanan maganin yai muna aiki a jikin mu baki daya.
Babana zo nan tace tana zaune a saman salayan ta bai tsaya ba ya mike zuwa gurin
uwar tashi.
Mika mashi ludayin da maganin ke a ciki tayi tana fadin duko kasha duk da bai so
bai musa mata ba ya karba ya,sha ta shayar dashi da hannun ta kamar yadda aka
umurce ta da tayi.
Haka taiwa Amira da maryam sai ga Bintu tafito daga cikin daki tace yaki ya ta
zo ke maki karba kinji.
Bintu ta karaso kamar yadda suka sha haka itama tasha maganin daga hannun maji
Inda maji ta,shanye sauran maganin gabadayan shi da ludayin.
Sai kuma ta hada wani nasha tace a mikawa sadauki wanda ke zaune ya kurawa Tv
ido kamar yana kallo.
Saida ta tabbatar yasha komai kamar yadda akace tace dauko mashi abincin shi
kinji.
Ana kawowa bai tsaya ba ya karba tare da mikewa maji tana fadin ina kuma zaka
tafine wai ?
ya ce dakin shi zai tafi yaci tace tau kadai ci abinci don naga kana,wani rama
can.
Sai da safe ne taje gaida mijin su yake ce mata ta dagata yana da magana da ita,
haka yasa Hajiya Kubura tafita daga dakin .
Yace dagata ai duk magan ta,shafe ku don ka sadauki ne zancen da zamuyi da ita.
May kuma dan nawa yayi inji hjy kubura take tambayan shi da sauri.
Baiyi komai ba wani magan ce dai aka tare ni da shi akan shi wai zancen kwallan
ball din kafan da yakeyi.
Oho Allah yasa alheri ce ta samay mu akan maganan t
Tau kusan hakane dai don wai ashe sun bukace shi da yatafi ya buga masu ball a
kasar ghana.
Amma sai yace wai gida an hana,shi zuwa shine nace ni dai ban sa zancen ba amma
kila ita uwar shi ta san da zancen?
Eh na sani tabashi amsa amma kuma na fada mai hakan baiyoyuwa.
Kada ma ya kara min zancen shine yake ta faman fushi a kwanaki ai har yaje yai
wanan aika aikan.
Kai amma hajiya maijidda baki kyauta ba gaskiya.
Ai wanan abin alfahari ga kowan mu nan ace an samu haziki daga gidan mu .
Amma may yasa ni ba a shawarce ni ba kika yanke hukunci ke kadai, maji tace
Alhaji naga baka ra,ayin wanan kwallon da yakeyi ne.
Sannan kuma yana nan ma a,tare da mu yaya aka kare ballw yatafi wata uwar
duniya can, inda babu mai kwaba mashi.
Haba kwabo fa daga Allah yake mu itakarmu dashi addua ne a duk inda yake, amma
ai wanan wani babban abin alfaharine idan Allah yasa mashi hannu inji hajiya
kubura.
Nikan gaskiya sai naga kamar hakan zai kara jefashi cikin mugun halin da yasa
kan shi a cikine.
Alhaji yace yanzun dai idan ya shigo kafin na fita kice ina magana dashi don
inji yaya zancen yake ne.
Majibata,dade da barin gurin maigidan na suba sai ga sadauki ya,shigo don yau
sammako zaiyi ya fita saboda yana process kan fita service din shi.
Bayan sun gaisa ne maji take cewa yaya akayi Alhaji yasan zancen zuwa kwallon da
kai min bayan na fada maka cewa ban ra,ayin hakan tun farko.
Cikin muryan ahi ta,rowa yace wallahi Maji ban sani ba don bamuyi maganan da
kowa ba a gidan nan.
Ta ka godewa Allah da uwarka hajiya kubura don naga ta dauki abin haikan ita akan
dole sai anbarka.
Na ko san tunda tai magana Alhaji yarda zaiyi ba fashi amma ya,dai ce idan
ka,shigo kasamay shi yana nemanka wai.
Baba ke nema na maji tace eh ba,wanj abu bane wai yana,son jin kan maganan daga
bakin ka ne.
Sadauki bai tsaya ba ya mike don zuwa kiran mahaifin shi da yake mashi,
Yana kaiwa kofa yaji muryan bakuwar yarinyar nan cikjn yar siririyar murya tana
fadin Allah yasa baba ya,yarda yatafi wallahi.
Juyowa yayi ya maka mata harara yafice daga dakin yarinya karama,sai bakin iyayi
ina,ruwan ta dani ne
Yarinyar nan bata,san halina,ba,sai watarana na gwada mata,zata gane kuren ta
gidan nan.
Yafita yana magana,shi kadai a ran shi yana fita hajiya kubura tana kulle kofan
part din ta zata fita ya ke cew mummy ina kwana.
A,a sanda sadauki sabda gagare ashe ana ganinka ni yaushe ma rabo dana saka a
idona ne wai.
Yai yar murmushin shi yace ban zama,sosai ne yanzu shi yasa ba,a gani na,
Tace tau akula dai don Allah a daina rashin ji kaji Umar Allah ya tsare muna ku
Allah kuma yai maka,albarka.
Yace amin yabarta taba,ci gaba da,rufe kofan dakin ta shi dai matar batai mashi
komai ba amma kuma ya kasa sakin jiki da ita,
Dan dama,ma,yau har ya tsaya sundan yi dogon magana dashi ko shi don irin
halarcin da ta nuna mashi ne ranan yasa yadan sake mata yau.
Da Umma ya hadu tafito tana sauri don ta makara kauce mata yai nufin yi don
kada,su hade amma sai cewa tayi wallahi haukan yaro yakawo gareni da,uwar yaro
zanyi a gidan nan.
Bai ko gaisheta ba ya,wuce abinshi gurin mahaifin nasu don amsa kiran da yake
mashi.
Ya samu yana gap da fita ya,shigo falon da,sallaman shi suka gaisa yake cewa
hauwa ta fada maka ke nan ina neman ka ko.
Don nasan inbashiba bazaka zo mu gaisaba ai anya Umar kana kyautawa kanka kuwa?
Baba kayi hskkuri lokacin da nake fitowa sai na samu kafita ko kuma lokacin da
zan fita baka fito ba tukun.
Ba sanan ba idan maka gyara don kanka, yaya zancen dana ji na batun fita kwallon
ku yake ne?
Don ban son abinda zai je ya kara saka sha shan ci kuma a bayan idon mu, anan ma
muna nan kafara haka inaga babu kowan mu.
Baba insha Allahu ba,zanyi wani abinda zai bata maku rai ba ko martaban gidan mu,
Hmm daga baya ke nan amma sadauki yaushe kuma,ai kayi waka an amsa maka ko.
Don tunda harka bari kishiyoyin uwarka suka fahinci halin da kake ciki ai abu ya
baci ko saidai Allah ya kyauta kawai.
Nan dai sadauki cikin dukar da kai yai ma mahaifin shi bayanin komai yadda
abinyake ya kuma fahince shi.
Ga mamaki

10 / 92