Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
a cikin ruwan sannan nai wanka tsarki na fito da kyat na
tayar da sallah.
Haka na daure nafito na hada abin karyawa wanda dakyat nagama hadawo don zazzabin
da ya rufe min jikina a lokacin.
Dakina na koma na kwanta ke nan wayana dake gefe na yai kara a lokaci daya da
kwanciyana.
Maryam ce ina dauka take cewa banga kin shigo school bane yau madam.
Da kyat na iya bude bakina nace banda lafiya ne yau anty tace subbahanallahi may
ke damunki Bintu?
Maimakon na bata amsa sai na sa mata kukan takaici kawai hankalinta a tashe tace
kashe wayan gani nan zuwa yanzu.
Zazzabine mai karfi ya rufe ni a lokaci daya ina dunkule a cikin bargo idanuwa a
rufe naji an shigo dakin.
Bai min magana ba sai tsayawan da yayi yana kallon yadda nake kaduwa a cikin
bargo kawai.
Takawa yayi har bakin gadon tare da yanen bargon a hankali dunkule nake idanuwa
na a rufe hannun shi yakai a saman wuyana a hankali.
Zanfin da yaji a jikina yasa shi faduwan gaba don shi kanshi yasan yadda yai min
bai kyauta min ba a daren jiya din.
Dan tsuki yayi tare da daure fuskan yace ke nasan idon ki biyu may ke damun ki ne
haka ?
Nikan gyara kwanciya nayi tare da kara dunkulewa dakyau guri guda.
Muryan maryam ce dakw ta kwada sallama daga kofa yashi amsawa tare da fitowa daga
dakin suka gaisa yana tambayan lafiyan ta.
Tace ina Bintu take ?
Ya bata amsa da tana ciki ya wuce baiso shigowan maryam gidan ba a lokacin.
Da sauri ta karaso gareni tana cewa Bintu subbahanallahi ashe serious ne haka
may ke samunki ne wai haka ?
Banda lafiya kawai na bata amsa dashi tare da kara dunkulewa kawai.
Fita tayi ta samay shi zaune yana cin abincin breakfast tace yaya an ashe Bintu
bata da lafiya ne naje school ban ganta ba shine na biyo ta nagani.
Yace mata Umm kawai yaci gaba da kurba shayin shi kawai.
Ta sake cewa tasha magani ne to ?
Yace may tace maki yana damuntane ?
Batai magana ba sai dai hawayen da naga tanayi kawai a idanuwan ta.
Bari yanzu zan fita na sayo mata magani yabata amsa tace ba,a zuwa asibiti naji
zafin jikin sosai ne fa.
Yace fir god sake ki barni da surutun nan kamar wata yar jarida can nace maki zan
sayo mata magani yanzu idan na karya ko?
Shiru tayi ta mike zata koma dakin yaks cewa ba barci takeyi ba ki barta kawai ki
tafi ai ina gida bazan tafi nisa ba .
Kallon mamaki tai mashi kamar mara gaskiya kodai yaiwa yar mutane wani mugun
abune wai.
Bari nai sallama da ita na tafito ke zo ki fice min a gida ban son gulman tsiya
ya fadi cikin daure fuskan shi.
Da mamaki take kallon shi batai magana ba ta juya zata fita yace ke dakata sai
taja ta tsaya guri daya yace idan naji kin fadawa wani Fatima bata da lafiya
wallahi sai na saba maki harda munafukin mijin ki kuwa.
Fita tayi daga gidan kamar yadda ya umurce ta gida ta koma bata koma school ba
ranan.
Bashar yai mamakin ganin ta a gida yake tambayan ta ko lafiya ta dawo a lokacin .
Tace lafiya sai dai Bintu ce wallahi bata da lafiya sosai naje gidan kuma yaya ya
koreni harda gargadina idan na fadawa wani sai yaci mutunci na.
Dariya taga Bashar din nayi mata yace ai maganin ki ke nan ina ke ina zuwa gidan
mutane gulma kuma.
Shima fa haka yace min yace kingani tace wallahi yace kokai na fadawa sai ya saba
min .
Dariya yayi yace mugu yasan abinda yaiwa yar mutane shine yake jin kunya mana
kada aji.
Kallon shi tayi cikin mamaki tace may yai mata yaya yace auke kin manta da naki
ke nan ko abinda akai maki da kikazo gidan nan kika lamay muna ahine shima nake
ganin yau yai mata.
Sai wani shu,umin murmushi ta sake tace Allah sarki Bintu har tabani tausayi
wallahi.
Amma kuma shine don keta zai hana a taimaka mata wallahi yaya sadauki mugune
Allah, bakaga yadda ya sha min toka ba wai na fita na bar mashi gidan shi.
Sun kai wani lokaci da Bashar suna maganan cikin tausaya min ya fita yabar gidan.
Kiran wayan Sadauki yayi yana ina yace yana gida kuma bai samun fitowa yace gashi
tafe kafin yace kada kazo har Bashar din ya kashe wayan shi ko.
Ina kwance naji yana tabani cikin barci na bude idanuwa na da kyat shine tsaye da
cup din ruwa da magani a hannun shi.
Yace cikin daure fuska tashi kisha magani nace a hankali naji sauki ban sha sai
ya tuna ban son shan magani dama yace idan baki sha ba wallahi zan kira ai maki
allura yanzu ragguwan banza kawai.
Jin za ai min allura yasa namike da sauri ina hararan shi na karbi maganin nasha
da kyat na iya hadewa.
Na koma na kwanta ina wai wai tare da kara rufe kaina gyara min kwanciya yayi ya
kashe A C dake aiki a dakin.
Yafita falo ya koma ya zaina shida musa yana fada ma musa wai yau banda lafiya ne
shiyasa nake kwance.
Can yaji anshigo gidan ya daga kai Bashar ne ya gani yace cikin daure fuska kai
kuma may yakawo ka ne wai nace ma yau hutu nake so fa.
Yace au don nazo nayi laifi ke nan ko yace dana sani na wuce school wajen madam
dina yafi min zuwa nan ai min wulakanci haka.
Ya zauna yana fafin kaunata tana school ita ma ko ?
Yace bataje bata jin dafin jikin ta yau da sauri bashar yace subbahanallahi may
yasa may ta kuma ?
Sai da yai dan tsuki yake cewa fever ne kawai ke dan damun ta.
Kallon yadda sadauki ya daure fuska yayi ga dariya nadon kamashi amma ya dake
inda ya yakushe shi a wuya da gefen fuska dana wuya yace subbahanallahi may kuma ya
yakushe ma fuska haka kamar kayi dabe da mussa haka?
Yace kai dan iska ban sani ba mutune kaman yan jarida dakai da matarka ban san
wanda yafi gulma ba wallahi.
Don Allah daka ta man kaman fa kasha yakusa nake gani jiya dakata mu gani mana.
Filon kujera dake gefwn shi ya dauka ya jefa mashi a fuska ya cabe yana cewa oho
yanzu nagane kace min ka shigo gari kawai mutumina.
Fita min gida kaima watau munafukan matar ka taje ta fada maka shine kazo don ka
karas da idon ka ko ?
No kadain kiramin da mata munafuka ni Maryam bata dawo gida ba tana makaranta
kuma ba abinda ta fada min zuwa nayi mutafi illela gurin zancen kayan nan da zasu
shigo muna.
Yace cikin taba baki ni yau ba inda zan tafi don wanan raguwar banzan ta kawo min
cikas sai shegen rakin tsiya kamar wata jaririya can da ita.
Kai man wallahi ka fadi gaskiya abinda ake lalashin mace kodai kai kai mata may
gaba daya ne wai ka illanta masu yarinya ga banza saboda alluran ku na yan kwallo
na maka caji ko ?
Kaidai dan iska ne wallahi bashar kashe ta ma nayi ba illantawa ba bar gida don
Allah naji da abindake damuna ni please.
Sai yaja tsuki yace ni wallahi maji ce bani ma son taji zancen nan Allah, bashar
yace a ina zataji shi.
Gurin maryam mana bashar yace haba kai ina tana ma fara fadin wan nan magana ina
bazata fadi ba zanyi warning din ta ai.
Amma sai dai sun makara don suna magan har maryam takira wayan mama tana fada
mata cewa maji yaufa sai ki dafawa yarki bagaruwa don komai zam wallahi.
Murmushi maji tayi tace masha Allahu nan take cewa sai dai bata da lafiya tana
can nade kuma na tafi yaya ya kore ni.
Suna gama waya mama tashirya sai gidan mu wanan ne karo na farko da tazo gidan
namu tun bayan gama bukin mu.
Suna hiran su a falo suna dariya sai jin sallaman ta sukayi a falon kawai.
Damm gaban shi ya fadi ya dukar da kanshi a kasa haka kawai yaji yau ba zai iya
hada ido da maji din ba karo na farko kenan a rayuwan shi.
Suna gaishe ta bata tsaya amsa masu ba da dadi take fadin ina dakin fatiman yake
ne da hannu ya nuna mata.
A hankali tasa hannu ta daga bargon da nake ciki a rufe a lokacin saboda maganin
da nasha har na fara zufan jin sauki fever ya dan sauka min sai dai jikin nawa
akwai sauran zafi still.
Jin an tabani yasa na dan bude idona a hankali mamace na gani tsaye a kaina tace
Fatima yaya jikin naki ina kokarin tashi take ce min koma ki kwanta abinki.
Kinsha magani ko nace mata cikin karfin hali eh mama ta kara min sannu da jikin
na amsa da kyat tare da dan mikewa zaune na dukar da idona sam ban iya hada ido da
mama din yau.
Bathroom naga ta nufa saida ta cika kwamin wankan da ruwa ta kawo wani gari ta
zuba tace na tashi nashiga ciki na zauna zan dan ji daman jiki na taimin sallama ta
fita abinta.
A falo ta samay sunyi zaune zugun da su sai jira yake yaji fadan da zatai mai
sai dai tanafito ta dan zauna tana cewa nashigo ban tsaya mu gausa ba hankalina ya
daga naga hakin da diyata take ciki.
Tace sai ai ta hakkuri da mata Allah yai maku albarka yabaku zuria dayyaba na
gari masu albarka irin ku.
Ni zan koma sai anjima kazo ka dauko maku abinci kazo dashi tunda nasan bazata
iya komai ba ita.
Mama ta mike ta fita tana masu sallama ta wuce zuwa gida nan ta barsu zaune cikin
kunya.
Yace sai na batawa maryam rai wallahi haba dai akan may kuma may taimaka zaka
saba mata kuma daga taimako
Kwarai naji dadin abinda mama ta taimaka min dashi haka yasa dana fito ban kwanta
ba sai yunwan da nake ji kawai.
Shigowan shi dakin yasani saurin dukar da kaina yace yaya jikin naki da sauki
nace mashi kawai.
Kin karya kuwa ya tambaye ni cikin son sani ko na karya sa safe nace a,a a
hankali juyawa yayi yafita daga dakin.
Zuwa can sai gashi ya shigo dauke da cup din tea mai kauri a hannun shi daga gefe
na ya zauna tare da mika min cup din.
Yana fadin ki shaye shi don ki dan kara samun saukin jikin naki wayan shi ce tai
kara ya dauka sai da suke magana na fahinci da mama suke magana .
Yadda suke magana na fahinci mama tana cikin matukar farin ciki da walwala a tare
da ita tana cewa ka fara ganin al,amarin Allah ko.
Nikan raina kamar an fasa min guduma tsakiyan shi nake ji don nasan dada shike
nan ni tawa ta kare ke nan.
Shiko sai wani lumshe idanuwan shi kawai yake abu ya taru yai mai yawa a zuciyar
shi.
Na farko tunanen irin ni,iman da ya diba daga jikin yarinyar da yake ma kallon
kitse saman ruwa don bai taba zaton haka zai samu ba daga gurin Fatiman daya raina
da farko .
Suranta sai gizo yake mashi a idanuwan shi ya kasa mantawa da abubuwan da suka
faru a tsakanin a daren jiya din.
Idon shi ya sauke ga dogayen yatsuna dake rike da kufin da nake kurban shayi a
hankali bai san lokacin da ya sauke wani irin ajiyan zuciya ba wanda har yasa na
dago kai ina duban shi.
Sai kuma nauyi da kunyan yadda ya kasa sarara min har takai yai min rauni a jiki
ance dama dan hakin da ka raina shikw tsona maka ido.
Nauyi da kunyan maji sun rufe mai zucita don bai taba tsanmanin cewa akwai wani
rana da zaiji nauyi da kunya maji ba sai ya din nan.
Kofin nake kokarin ajewa a gefe ya kura min ido cikin daure fuska yake cewa kin
shanye ne.
Na dan marairaice ina cewa, nasha yaya hannu ya miko min yana karban cup din gani
sauran tea a ciki yake cewa wanan fa ?
Na dan marairai ce nace na koshi yaya please tausayi na bashi ya dauki cup din ya
fita dashi.
Ba,a dauki wani lokaci ba saiga sako daga mama ferfesu ne na kaji da kayan cikin
rago sunji kayan kamshi na gargajiya, sai kuma gassan naman rago mai zafi .
Da kanta ta bugo min waya akan na tashi na ci abin da akakawo tare kuma da
jaddawa yaya akan ya tsare ni naci sosai.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
IDAN KUMA KIN BIYA KIKA TURAWA WANDA BAI BIYA BA NA BARKI GA ALLAH YAR UWA,,,,
Zama muke na zaman kwari tsakanina da Amira don iyanzu takai ni inda bani son mukai
tun farko da ita.
Ina zaune a dakina naui zugun ina tunanen irin wanan halin takuran da Amira take
kawo min har a cikin gidana.
Sai hakkuri nake tayi ina hadiyewa don ban son mahaifiyar su su sami labarin
halin da muke aciki.
Amma ranan da maryam tazo gurina ta fahinci akwai matsala a zaman mu da Amira.
Gaba maryam ta sakani sa tambaya iri nata har dai na warware mata duk irin zaman
da mukeyi da kawayen ta da take kwaso wa su zo su dinga min abu isa isa a tsakar
gidana.
Rayuwan maryam yai matukar baci tamike tana fadin wallahi sai tayiwa Amira magana
Amma na sha gaban ta na bata hakkuri tare da fadin idan Allah ya yarda ni da
kaina zan dauki mataki a kan ta.
A kwana atashi ba wuya a gurin Allah sai ga shi yai har wata daya da kwana goma
sha da tafiyan yaya sadauki.
Munan da Anty Amira muna ta kwamawa a cikin gidan don gaba daya yanzu na fitar da
tsoron ta ko shakka da kawaicin ta da na ke ji da farko .
Karatuna nake don yanzu exam mukeyi hutu zamu fara next week banda wani lokaci
sosai na kaina a gida gaba daya.
Tsaye yake idanuwan shi suna a lumshe dan murmushi ne ya sake don tuno da yanayin
Fatima, da murmushin ta da take a boye tsiwanta da fushin ta da takeyi a lokaci
daya ,
Sai dai kuma duk karancin shwkarun Fatima hangen nesa ta da kyakyawan zuciyan ta
da manufan ta akan kowa haka halitta ne a gare ta.
Yana gyara tsayuwan shi yake cewa Fatima ke ba diyan masu hali ba amma kuma kina
da,diyauci irin na masu halarci.
Su iso Lagos da yamma don ta nan jirgin su ya sauka Nigeria a gurin su basu
dauki tafiya a bakin komai ba don haka ya tsaya yai clearing din kayan shi da ya
shigo dasu.
A lokacin mun kammala exam na dawo gida satin nan ba fita duk wani motsi na
da,wani taku na yana kan idon Amira da ta saka min ido a agidan.
A kullun tunanenta shine yadda zata kawo was Fatima cikas din rayuwa ta hanata
jin da dadin rayuwa a gidan Sadauki.
Don ita Amira a watau ta sune yan uwanshi na jikin shi sune ya kamata suci
arzikin shi fiye da,wata mace can da tashigo da sunan zaman auren sai su mamaye
komai na miji ya zama na au suda yan uwan su kawai.
Shiko miji da dangin shi sai yadda akayi dasu kawai a gidan sun zama yan bi ke
nan a dinga juya su yadda rai yaso,
Hakan ke matukar bankan ta mata rai ita bata kaunan ace dan uwanta sai wata ta
bata doka akan shi Amira na cikin irin jinsin mutanen dake adawa da matan yan uwan
su maza a duniya.
So take sai yadda tayi da shi da matar shi sai dai ta dinga bada commad ana bi
kawai shine zaman lafiyan kowa da ita don bakin ran ta da yai yawa.
Takan ce dan uwa dai dan uwan tane babu mai raba shi da ita don a tare aka gan su
don haka sai dai mace ta kare kutin gwilar ta tabar da dan uwan ta saboda babu
wanda zai kawo wani shamaki a tsakanin su.
Haka mukai ta zama da ita a cikin fitina da gori habaici bakar magan cika baki
sai dai wanda ba bu shi don duk nagani ga Amira lokaci guda.
Gashi kuma yadda take samun, gashin kanta yanzu a gidan namu tayi kiba tai fari
ta kara dan girma da ita.
****** ********* ******
Suna zaune falo da kawayen tabar gazan ta wai su wayayyu su salma kubura da
Fauziya sai jin motsin turo kofan shigowa falon gidan sukaji.
Idanuwan su na kan kofan don suga mai shigowa falon a lokacin don yanzu sha daya
saura na safe muke ciki.
Cikin mamaki Amira tace yayana dama yau zaka dawo ashe bai amsa mata ba sai bin
falon yake da kallo cikin mamaki bayan ya gama kallon fuskoki wa yanda ke zaune a
falon lokacin.
Daya bayan daya yake kallon su har ya kai karshe Fatima bata falon.
Hakan yasa shi wuce wa direct dakina yagani don sai yaji zuciyar shi tana mashi
wani irin kuna a lokaci guda.
Yana bude kofan zaune nake na sallamay sallah walha, ina dan jan tasbaha bayana
yana jingine da fadon dakin
Jin an turo min kofa yasani saurin dago kai ina kallon kofan dakin wanda nagani a
tsaye ya harde hannayen shi guri guda yana min murmushi yasani saurin dan sakin
murmushi tare da yunkurawa in tashi.
Na nufoshi a a cikin fara,a ina cewa sannu da zuwa yaya yaya hanya ya can ?
Murmushi yayi tare da,ware hannayen shi na sheko da dan gudu na na shige ciki ya
mayar da hannayen shi ya rufe ni dasu .
Sai da muka dan dauki lokaci a haka muna