Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
hannun ta
daga rikon da yai mata din.
Mamaki sosai abin yaba Nasir din don dai shi yasan lafiya suka dawo da ita daga
tafiya.
Look baby Raiha ki fada min idan wani abu ya faru ne please don ban san laifin
da nai maki ba ni.
Kawai ra,ayina ne hakan na nisan ta kaina dake don bakai min ba ni, maganar ta
yasa shi murmushi yace to ni kin min ai.
Ko ba shike nan ba ki tsaya please muyi magana mu fahinci juna kada ki tara min
mutane please.
Da,wasa ya dauki zancen amma sai yaga finfirin Raiha ta shige mota ta tafi abinta
tabar shi nan tsaye.
Gurin Brosha ta tafi don dama kayan aikinta sun kare gashi kuma tana son jinta a
network sosai don kwana biyun da tayi bata sha ba duk wani kala take jin kanta.
Shiko Nasir nan ta tafi tabar shi da mamaki don ya kasa fahintar abinda yai
mata, saidai tunanen shi ya tsaya ne kodai yadda yai mata a lagos ne yasa tai
hating din shi.
Wanan yatinyar may take nufi sai da tafiya tai nisa take son ta bata min show
dina wallahi bata isa ba.
Don na riga da na fara shirin fita da ita waje gashi shegiya nasan ba karamin
kudi zan samu a kanta ba don shegen dadi ke gareta.
Koni don dai son kudine kawai da ya rufe min ido aida bazan iya rabuwa da ita
ba.
Gidan mahaifan shi ya nufa inda yan kannen shi suna ganin shi suka taso da murna
suna mashi sannu da zuwa.
Duk cikin subabu sa,an Raiha don suna girmay mata da shekara biyar ko hudu.
Bayan ya gama gaisawa dasu ne yake tambayan
Gaban hajiyan shi dake zaune saman kushin ya zauna yana mata ina kwana.
Ta amsa cikin dakewa tana ce mashi lafiya yakara da tambayan ta ya gida da sauran
al,amuran gidan, nan ma ta bashi amsa da Alhamdullahi.
Sai dan shiru, can uwar tace ashe kadawo ban sani ba yace eh inna ai yau kwanana
biyu da dawowa.
Wani kallo tai mashi tace bayan Abdul yau kusan kwana biyar ke nan da yace min
kun hadu dashi, zakace wai kwanan ka biyu da dawowa.
Nasir ko kana son mayar da kanka mutumin kwarai kuwa ?
Ka saki matar ka kakuma ki aure sai yawon kwasan yan mata kake a mota baka nan
baka can dasu.
Wallahi kayi hattara da cutan zamani don yawa gare su ko ba wanan akwai wancan.
Dukar da kai yayi kamar wani mutumin kirki yana cewa Inna ai zanyi bandai samu
wadda namu yazo daya bane har yanzu.
Don ina gudun kada akara maimaita irin na wancan karon aza kuma ba,a dace ba.
Kai din ma ai ba halin kwarai ke gare ka ba tunda baka iya zama kurum.
Ga shaye shayen da ka sawa kanka don ban tsan manin ka daina yi yanzu.
Girma dai ya kama ka in kanawa kan ka,fada kayi wallahi ni zan fitane kada kazo
ka tare ni da surutun banza.
Yace Inna ina zaki sai na sauke ki dayani tunda gani na shigo.
Tace da sauri wa aganni da kai ace may ace har alfahari nake da irin halinka ina
shiga mota da kai darana cikin gari.
Murmushi kawai nasir din yayi duk da,zancen mahaifiyar tashi ya soshi zuciyar
shi.
Ya mike yana mata a dawo lafiya yafita inda kannen shi suke ya basu dubu goma wai
su raba don yasan ko yaba inna ba karba zatayi ba don tace kudin da yake sayar da
kwaya ne ita bata ci.
Duk yadda yaso ya fada mata matar shi da suka rabu kazafi take mashi amma inna
taki yarda da ba gaskiya bane.
Abu daya tasan yana masu shine biyan kudin wuta da na ruwan fanfon gidan nasu
tun bayan da mahaifin shi ya rasu.
****** ********* ******
Ranan da matan gidan suka samu labarin tafiyan da sadauki zaiyi zuwa kasan waje
sunyi ta zuba bakar magana kamar tashin hankali.
Inda suke cewa lalai maji bata san ciwon kan ta ba da har zata yarda ta barshi
yafita zuwa wani guri wai ma kwallin kafa.
Itako mama Asiya cewa tayi sai dai a kare da hakan a lalace wai wasan kwallo don
tambadewa kawai.
Umma sai da ta samu maigidan su da zancen tana cewa wai da gaske ne zancen da
taji yara suna fadin sadauki zaifita waje wasan ball.
Yace da gaske ne mana akwai illa ne ga hakan ko yaya ?
Tace haba Alhaji yanzu kamarka da kimar ka da darajan ka,za,ace wai danka ne ke
wanan abin.
Shi kwallon kafan kuma yanzu mugun abune, da na barshi nan zaune gida yana
tambadewa ai gara na san ya kama wani abun.
Tace amma gaskiya Alhaji,,, ke yafa isa haka Rakiya don nasan abinda nakeyi
sarai wallahi don haka na fada maki da yardana zai tafi.
Cabdi ashe akwaita gidan nan ke nan don sunan ka bai lalace ba yanzun ne ake
shirin yin ta.
Ta fito fuuu, daga dakin tana zuba bakaken maganganu itakadai har zuwa dakin ta.
Ba su hakkura ba sai washegari kuma suka kara,tayar da zancen.
Lokacin haniya kubura tana kusa sai cewa tayi maye cikin wasan kuma ai wanan idan
Allah yasa mashi hannu sai kiga an take akai.
A sawan kwallon ko a shaye shaye wanan dai kawai an kara turashi ne yaje ya kara
yin cos kan shaye,shayen shi kawai.
Nikan wallahi idan ya dawo naga yakara haukacewa sai dai na bar ma su gidan shida
uwar shi kawai don dama haka sukd so.
Allah dai ya shirya muna shi amma ai ba kai wa dan wani mugun fatan mugun abu ya
samay shi.
Daya samay shi da farko ni nai mashi fata ko may kada fa mace ta daure ni da
raina.
Ni yanzun ma gani nake kamar ya koma ga shaye shayen shi ne don ko yaushe yana
gida kwance kamar wani malalaci sai aukin barci kawai.
Duk a kunnen maryam dake zaune a falon suke wanan hira da dane kafin maji ta hore
su da rashin kunya da,tabasu amsa daidai da maganan su.
Sai da ta,dawo daki take fadawa maji abinda taji suna fadi kan tafiyan na
sadauki.
Maji tace Allah ya sauwaka ai Allah yafi su ni dai ban wa dan kowa mugun nufi
akan shi.
Amira tace ai ba zasu so suga ya zama abin kwarai ba tunda ba haka suke son
ganin shi ba dama.
Ke kubar wanan magana duk ma abinda su ke nufi ni dai ga Allah na dogora.
Sai lokacin Bintu da bata faye shiga maganan su ba ta sa baki tace ai in ba abin
mutum ba ba mai son yaga nashi ya lalace su dai suyi mashi fatan alheri kawai.
Ke kika san wanan amma ai su basu sani ba sunfi son ko yaushe su ganshi a hakanan
inji Amira.
Amma maji kafin ya tafi da ki sa ai masa saukan alkur,ani maigirma Allah ya kare
shi a can inji Bintu .
Ina da niyar yin hakan sai dai ban san wanda zan sa yai min ba tunda ba, baga
hajiyan masa ba maji Amira tace mata da sauri.
Lalaifa haka za,ayi zan mata magana da ta san yadda zata samu na Allah da zasuyi
min.
Amira tace ashe su ma wai har sun farga da wanan yawan barcin da yaya yake yi
kwanakin nan
Ba sa ido bane duk abinda mutum yakeyi idon su yana a kai kamar wasu mayyu can
Mutane suce basu son suga dan uwan su a farin ciki ko kadan sai dai kullun aga
kana wahalan tsiya kawai
Ai yanzun haka duniya ya koma hassada da bakin ciki yai wa mutane yawa a rayuwan
su inji maryam.
Allah ai yafisu don duk abinda zasuyi Allah ya dai yana ganin su.
Uwar dai tana zaune tana jin su kala bata kare ce masu ba ga hiran nasu.
Duk zuciyar ta a jagule yake akan tafiyan da dan nata zaiyi a cijin wanan halin
da ake ciki dashi.
A kullun, zancen Maji kan sadauki shine ya taimaka idan ya tafi ya kama kan shi
da rayuwan shi acan.
Don Allah Baba na kada ka bamu kunya ni da mahaifin ka, sadauki yakan yi mata
murmshi ne kawai yace kada ki damu maji insha Allah zan tsare kaina danan dacan
kamar kuna tare da nine ai.
Mai masa ta tafi kamar yadda Maji ta bukaci da ta taimaka mata akan ai mashi
addua kafin yatafi inda tabada kudi cikin asiri ko yaran ta basu san da zancen ba.
Da dare sadauki ya shigo gida inda ya samu maryam kaunan shi a tsaye gaban
tsohon TV dakin su tana kwalan shi don ya tashi yai aiki don saboda tsufa ya gaji
ya na tsayawa don kan shi.
Sai yake cewa ke Maryam kina ta faman kwalan Tv haka idan ya fashe fa?
Yaya idan ba dukan shi mukayi ba baya tashi sabofa ya tsufa da yawa sosai shi
yasa muke dukan shi gashi za,ai program da karfe tara muna son muyi kallo.
Wani irin ba dadi yaji a,ran shi inda ya kara jin tausayin uwar shi sosai a ran
shi . sai ya tuna yadda yaga dakin hajiya Kubura a ranan,
Komai akwaishi na,zamani a dakin amma su ga dakin uwar su kamar zaure ba komai a
cikin shi sai yan tsofafafin kujeru da wanan tshon TV da maryam take kwalla.
Wani dogon huci yaja a fili har yasa su dago kai su kalle shi kan shi ya mayar
saman makarin kujera ta baya yana shafo fuskan shi kawai.
Bintu tafito cikin wani dogon rigan atamfa wanda akaiwa dinki budade daga kasan
shi.
Maji tafara sallah ishai a lokacin don haka ta waiga inda yake kwance saman
kujera taso share shi amma tsoron shi take matukar ji.
Don haka takara waigawa still yana a yadda yake kamar mai barci, tace cikin
daurewa yaya sadauki ina wuni.
Tankar a cikin mafarki ya tsinkayi zazzakan
muryan ta da take gaishe shi.
Batare da ya,sauke hannun shi daya kare fuskan shi dashi ba ya amsa mata da kyat
da lafiya.
Tace akawo maka abincin ka ne yanzu kamar ba zai amsa mata ba sai can yace kawo
min kawai.
Ta juya zuwa kitchen don ta dauko mata yai daidai da ya dago fuskan shi sai ganin
bayan ta yayi tana tafiyan ta a cikin natsuwa.
Yace ke idan zaki fito ki zo min da ruwan sha daga nan, ta amsa mashi da tau
kawai ta shige abinta.
Tana kitchen sai faman tunane take barkatai tana cewa, shi wanan haka Allah yayi
shi da mudaden hali ne wai.
Girman kan shi da share mutane gami da nuna isa sunyi yawa don isa ma da izza
wai ke yake ce mata.
Shigowan da Amira tayi kitchen din shi ya tsayar mata da tunanen zuccin da
takeyi.
Amira tace abincin yaya sadauki ne zaki hada mai ta bata amsa a cikin ladabi da
fadin eh nagan shi zaune nako san abinci ne ya kawo shi amma bai iya tambaya.
Amira tai dariya tace kin san shi magana ma matsalace a gurin shi kafin kiji yai
magana aiki ne gare shi, dan dama idan da maji suke magana zai iya dan kai lokaci
yanayi.
Tana hada abincin suke magana da Amira inda ta dauki abincin zuwa falon su inda
yake zaune.
Wanan karon ta samay shi a,zaune ya dauki kafa daya ya dora ga dayan kafan shi
yana kallon yadda maryam ke bugun TV nasu da karfi.
Daidai ta kusa karasowa inda yake taji yana cewa Please maryam kibar TV nan
hakana idan ba zaiyi ba mana.
Bintu ta,kawo abincin a gaban shi ta dire mai zata juya yakw cewa ke mai aka
dafa don banga cibi ba.
A tsorace tace mai tuwo ne shi yasa ban hado da cibi ba cikin jin tsoron shi take
magana.
Da hanzari ta juya zata bar gurin yace ke dauko min cibi dan Allah ko tuwo ne
ba,aci da cibine akace maki bakauyar banza kawai.
Simi simi Bintu ta juya zuwa kitchen din duk da zagin da yai mata yaci mata rai
akan tai mashi abin arzikine kuma zakirata da bakauya.
Kai inji Maji da data idar da nafila take cewa kada na karajin kakirata da
bakauyan nan don ba gurin ka tazo ba.
Ina laufin ta ta hado ma abinci don kai miskilancin ka bai bari ka tambayi mutane
abincin ka.
Mikewa yayi tare da dauka abincin nashi yana kokarin barin falon don bazai yarda
a raina shi ba akan bakuwar yarinyar Maji da bai san inda tafito ba.
A lokacin ita kuma Bintu tafito daga kitchen din dauke da cibin a hannun ta tana
mika mai.
Yace ke barshi dan Allah ya fice daga falon Maji taja tsaki tace shiyasa ake ce
ma mahaukaci yaji ta amma bai tsaya ba yafice kawai abin shi daga gidan zuwa part
din su ranshi a bace.
Don shi bai son ai mashi fada a gaban yara kada su raina shi.
Sai bayan kwana biyu ya shigo gidan duk lokacin yana fushi wai maji ta
kunyatashi a gaban kannen shi.
Jin gidan shiru sai maryam dake zaune falo tana karatu yace mata ina Maji tace
mai tana ciki ta kwanta.
Yai kamar zai fita sai kuma ya tsaya ya mayar da hankali ga maryam yace ke,
Wai wanan bakuwar yarinyar da nake gani a nan daga ina tazo tace yaya sadauki
kana nufin Bintu?
Yace ina ruwana da sunan ta nace dai ita din wacece ?
Tace diyar hajiyan masa ce makwaciyar mu Maji tace ta zauna nan don hajiyan
yanzun bata zama tana jiyan yarta a kauye.
Ya koma tambayan ta a nan makwabtan mu suke ke nan shine maji tace ta dawo nan
kuma,?
Tace eh daga kauye tazo karatu take kuma hajiyan masan bata zama yanzu.
Wani irin tsuki yaja yace kai Maji da kwashe kwashe take wallahi shine har zata
disgani a kan ta?
Maryam duk ta kagu da tambayan da yake mata kada itama nata ya samay ta.
Idanuwan shi sun yi ja sun kada sai take tsoron ko ya shawo ne a lokacin.
Yana kokarin fita daga falon Maji tana fitowa tace ina jinka mara kunya dana
kwaso ta akan ka nace ta zauna ko kuwa.
Tana kallon shi ido da ido taga idanuwan shi yadda sukai mai ja sun kade kamar
an watsa mai barkono a cikin su.
Tace mashi kai mai kuma ka,shawo ne naga duk idon ka ya wani sauya haka.
Sai lokacin yace kai haba Maji shike nan ni banda aiki sai sha harda rana haka.
Kuna da lokacin shane tunda kun bushe filar ku baku jin kunyar kowa a wanan
yanayin,
Kamar zaiyi magana sai kuma yace ni ban sha komai ba kaina ne dai tun safe yake
min ciwo.
Ya juya yana fadin yanzun ma magani na sayo bari naje nasha na kwan ta, ya juta
yafita daga dakin.
Yana tafiya Maji ke fadin in ma dai ka koma shane wanan kuma ruwanka.
Amma da yafita hankalin ta bai kwanta ba sai cewa take a ranta ko ya sha din ne
ko kuma barin shan da yayi ne yake haifar mashi da ciwon kan oho.
Maryam ce ta katse da cewa nima wallahi yadda naga ya shigo ya tsare ni da
tambaya tsoro ya bani .
Shiko yana fita sashen su na samari ya shiga kai tsaye ya nufi dakin su don da
gaskiya kan shi din ke masa ciwo don rashin shan da baiyi ba kwana biyu.
Ya fada kan katifan shi batare da yasha maganin da yace ba din, kwance yake
kamar mai barci yana tunanen kodai ya dan hada ne yasha ko zai samu relief.
Yana gurin a kwance sai faman sake sake yake a cikin ran shi kodai yashane ko ya
bari.
Sai wata zuciya tace mai idan kasha shike nan zancen tafiyanka ya lalace.
Don ko kowa ya yarda Mani bazata yarda yatafi ko ina ba tunda ba bari yayi ba.
Amma wata zuciya kuma tana ce mashi yasha koda kadan ne don ya dan samu sauki a
ran shi.
Mikewa yayi ya jawo ledan da yake aje kayan aikin shi a ciki yana kallon su sai
faman sakan zuci yakeyi shi kadai a dakin.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYABA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,,,,
A LOKACI MU KE,,,,,,
Bintu bata da wani matsalar komai tsakanin ta da mummy da take zaune a shiyan ta.
Don mummy dai irin wayyayun matan nan ne masu faraf faraf da mutane ba,a gane
gaskiyan cikin su.
Wata, yammaci da dare, Bintu tana kwance tana barci don yayi saurin kwanciya don
ta gajiya sosai gashi bataci abinci ba da yunwa ta kwanta hakana.
Cikin dare yunwa ya damay ta don haka ta bude idon ta don ta sauko saman gadon da
take kwance akai.
Tana son fitowa zuwa kitchen don dauko abincin ta da bata ci ba a daidai kofan
dakin mummy take jin sautin muryan ta tana waya kamar haka.
Wallahi ina fada maki yau kwanan ta uku bata gidan tana can garin su ana mugun a
bu,
Yanzun haka yarinyar da take gurin ta,da nake fada maki tana dakina ta barta
ba,aje da ita ba.
Wai kin san may wallahi ni kin san ba yarda nayi da su ba matan gidan nan baki
daya.
Kada taje