Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
min a idona nace Yaya love tunanen bayane yazo
min kawai.
Maganan tawa ta doke shi har ciki ranshi yace tare da riko min hannayena duka
biyu.
Yace kiyi hakkuri Fatima nasan cewa na bata maku rayukan ku sosai a baya dake da
iyayyena wanda nima a yanzu idan na tuna wanna rayuwan bana jin dadin shi a raina
ko kadan.
Ki daina damuwan kanki da yawa don sai ma ince ki godewa Allah saboda na San kece
sillar daina duk wani mugun rayuwan da nayi a baya Fatima.
Ni kaina nasan har abinda ke kanki baki san kina yi ba akaina don wanna rayuwan
da nayi a baya yana bata maki Rai sosai da sakaku kunya ga jama,a.
Fatima nasan kina son na fiye da son da Maji take min a baya wanda a baya nake
ganin babu wani mai sona bayan maji da mahaifina da yan uwana biyu da Allah ya
bani.
Amma sai haduwana dake Fatima na fahinci cewa Allah kan jefo wasu mutane a
rayuwan bawan shi don kawai su taimakawa bawan shi a wani halin taimakon dayake
bukata a rayuwan shi.
Hakane Fatima ke alheri ce a rayuwan mu gaba daya don a sanadin ki Abubuwa da dama
nawa sun gyaru Fatima ta sanadin ki a rayuwana.
Most especially zan iya ce maki ibadana gaba daya a sanadinki Allah ya nufa na
gyara shi.
Kin min Abubuwa da dama wanda ke baki San na San dasu ba a rayuwana Kuma bawai
kina son na sani din bane kinyi ne kawai don ki taimaka min kawai.
Wanna maganan da yayi itace mafi girma da tsoro danaji don ban San may yasani
wanda nai mashi a rayuwan shi ba.
Nace Yaya love idan abin da naima ya bata ma rai a lokacin ka yafe min don Allah
don ba a cikin hankalina nai maka ba.
Ya langabe kan shi tare da girgizawa yace Fatima bata taba yi min abinda ba
daidai da rayuwana ba dana sani.
A lokacin motar mu ta tsaya a kofan hotel din da muka sauka a ciki ya karbi Amir
daga hannuna muka fito daga motan.
A gajiye muke don ba karamin gajiya muka kwaso ba daga inda muka fito nace ya
kawo Amir din na kama mai don nasan shi ba gwanin rikon yara bane sosai.
Yace ki barshi don nima in son ya saba dani ko kin manta da sunan wanda yaci ne a
gurina.
Ya ce don haka ke kuma sai ki dinga kokarin kina Sanya mu a cikin farin ciki da
ni,imar ki.
Kina kashe Muna kishin ruwan sha,awan mu daga ni,imar da Allah ya tana dar muna a
gareki.
Kunya ya kamani daga maganan da yayi haka yasani dan murmusawa kawai Ina biye a
bayan shi.
Duk da gajiyan da muka debo Bai hana mu kasancewa a tare ba a daren wanda sai
faman sanbatu yake akan irin ni,imar da Allah yai min a jikina.
Har muka bar kasar na yoghuslabea bai barni na huta daga jikin shi ba ga sabon
kasalan da ke yawan taso min wanda nake gani sabon yanayin jin dadin da na samu ne
hakan.
****** ********* ******
Watan mu cikin na uku ke nan yanzu rabon mu da gida ga wani irin mahaukacin
soyayya da so da kaunan da yake gwada muna ni da Amir din.
Abin har yana bani tsoro irin yadda ya ke kashe muna kudi haka har sai da yakai
nace mai yayana kayan nan fa sun Isa haka.
Sai dai ya girgizawa min Kai kawai yace Queen idan ban kashe maku ba na kashewa
wasu wa kudi haka a rayuwana.
Nikan ban da tacewa dole na saka mai Ido na bishi da kallon mamaki don sai nake
gani kamar ba Yaya sadauki dana sani a baya bane .
Wanda tsaraba ma idan ya sayo babu rabo na a cikin sa sai idan mamana tai min ci
da karfi nake samu daga gare shi.
Allah mai iko sai gashi yau nice dungurungun a gurin sayan kayan baki daya.
Haka Amir yasha kayan wasan yara su kekuna da jirage teddy ga abin koyon haruffa
na English da Arab kala kala ko wani da kalan sautin sa.
Bayan yasan cewa akwai su a gida wanda ya sayo tun yaron yana cikin ciki.
Kafin mu bar kasan ya turo da kayan gida ta hannun Yaya Bashar kayan zasu fada .
Wayanda na sani kenan wanda ban sani ba sai idan mun Isa zan gansu a can idan
Allah ya Kai mu.
Daga can bamu nufi Dubai din ba wai suna da meeting a US da zasuyi acan na yan
kwallo.
Sai da muka share wata daya a kasan inda ya kara hada business da wasu turawa na
kasan don ya saka hannun jari atare da su.
Nan ma bai barmu hakana ba sai da yai min sayayya kamar wanda zai hada kayan
lefe.
Suturu na alfarma da atamfofi masu tsadan gaske ya saya muna anan kasan.
Ni kaina a lokacin nasan na zama wata daga cikin matan manya a kasata ke nan.
Gashi nai wani irin kyau fatana yai wani irin lub lub dashi tankar dai irin
matan, larabawan Pakistan din nan hakan ni da kaina nasan na samu canji a rayuwana.
Mun shiga kasar Dubai wanda a lokacin watan mu hudu rabon mu da gida kenan har na
Fara kewan gida da yan uwana.
Duk da Ina waya da duk wanda nai kewan shi a raina amma duk da haka Ina son gani
na a gida.
A kasan Dubai naga mata kasa she masu ji da kansu duk da na taba zuwa amma sai
wanan zuwan ya zama min kamar na farko a rayuwana.
Ga matan Nigeria Nan zakace tankar a gida Nigeria kake Nan na Dan sake jiki naji
Dan sauki shaukin gida da nakeyi a raina duk da irin kullan da muke samu a gurin
shi.
Sam sadauki baya yarda nai hurda da matan hausawan da muke haduwa dasu a can
acewan shi Bai yarda da hurda da irin wa ya Nan matan ba dake baro gida su zuwa
wata uwar duniya da sunan neman kudi ba.
Gashi suna son yin hurda dani amma sai yace masu ni matata boye ta nakeyi don
matar kulle ce ita.
Mutum zai yi mamaki yadda matan manyan kasar mu suke acan birjit dasu zakace a
gida Nigeria ne mutum yake ganin su ba wani boyewa ba ne kamar nan da ba,a ganin su
sai da ticket.
Gashi da farin jinin jama, a a tare dashi duk kowa na son shi wanda hakan ne muma
iyalinshi ya shafe mu don mutane suna haba haba da mu a can.
A nan nuna min halarci so sai a kasan don sun it's taron bakin su dake zuwa masu
ko yaushe. wani buki da aka shirya na yan kasan Nigeria inda akai ma Naira kaca
kaca a gurin.
Don ko a can sai wanda ya Isa zai halarci wanna taron da aka shirya ida yan
bussines din kasan mu suka baje nairan su a gurin.
Shiga sosai ta alfarma mukayi wanda nan ma wani dogon riga na saka mai balain
kyau kamar alkyabba rigan take.
Bayan na saka wani English wear daga ciki na kawo rigan daga sama na dora akai.
Alkyaban irin mai tsananin tsadan nan ce ta matan manyan ko manyan ma sai wace
ta isa take saka ta don yakai jarin wata a kudi.
Hular rigan yai min wani irin rufi yana rike da wani dan mayafi da yake like a
jikin rigan Idan kinga dama zaki iya Dan zarga shi akai shi ma.
Sai ki koma kamar kin yafa idan kuma baki ra,ayin haka zaki sake shi ya biyo
bayan alkyaban ne.
Haka na dan yafo shi yai min matukar kyau sosai ajikina kamar wata yar labawa
masu fada aji.
Wuyana Kuma diamond necklace dan Kiran Dubai sai su awarwaro da zubbuna masu
tsada na saka.
Yaya sadauki yake cewa gaskiya da nasan haka rigan nan yake da kyau da akwati
daya zan saya maki nashi.
Nace Kai haba dai Yaya har guda biyar fa ka saya min su duk da tsadan dake gare
su.
Yace Queen ba tsada ba shagarki na fada maki shine mutunci na a idon jama,a da
kuma matan abokaina.
Ina amfani mijin ki yana rike makudan dollars haka amma babu fitan kwarai ga
iyalin shi ai sai duniya ta zage ni kamar ban godewa Allah ba ke nan.
Nafi son duniya su San cewa ke mai tsadace dariya ya bani nace to nagodewa Allah
da irin baiwan mijin da ya bani yace to ke fa.
Isowan mu yaja hankalina mutanen dake gurin fitowan mu ya mayar da hankalin
mutane sosai a kan mu don shigan mu ko makiyi dole ya kyasa muna ga Dan mu a hannun
shi ya dauka a kafanshi Wanda barci yakeyi shi yaron duk da yasha kwaliyan shi
sosai.
Matan da basu San mu ba sai tambayan sukeyi halan matar waye wai shin wanna guy
din dan Nigeria ne wai ?
Aka fada masu Dan wasan kwallon duniya ne da ake Kira UF Dan jahar sokoto din nan
da matar shi.
Lalai yayi abinshi don su keda lokaci gaskiya inji wasu Mata dake zaune saman
wasu kujeru dayan tace matar shi yar wanene a Nigeria ita Kuma ?
Dayan tace ba yar kowa bace diyar tallkawa ne auren hadi ne ma akai masu shi ya
mayar da ita haka da kike gani.
Kalleta cikin shigan matan manyan duniya kamar diyan wani hamshaki can da ita.
Matar dayan tace gaskiya ba laifi don first class ce gurin gwadawa tsara wanna
don bata da makusa ta ko Ina gaskiya dubi dan data haifa mai mai dan karen kyau da
shi don Allah.
Wata daga ciki taja tsuki tace kalli yadda yake wani tarairayan ta kamar diyan
wani can.
Dayan matar tace ke ko aita isa yai Mata haka don gaskiya ba laifi akanta gara
yai haba haba da abinshi don akwai muggan tsofi a gurin nan kema kin sani.
Gaskiyan shi kan gara ya kula da abinshi don tsofin nan da kike gani basu da dama
gurin mace maikyau balle suna ganin ta haka yarinya danya da ita.
Dayan kuma tace ke ko ai mace rahamace fa ga mijinta gara yaji da abinshi kowa ya
gani a fili.
A gaban matan dake gulman mu muka karaso suka shiga daga muna hannu muma hakan
mukai masu muka wuce zuwa inda aka tanadar muna mazauni.
Sun bimu da kallon rigan dake jikina yasha jinin jikin su sosai wanda ko shagon
sayar da irin su basu iya shiga don tsadan gurin.
Amma gashi a jikina Kuma mai high quality din na saka a jikina a lokacin.
Sai yatsune fuska suke su na rayawa a ransu dama sune a wanna matsayin haka ko
diyan su a haka.
Don haka aka shi ga girmama ni a gurin don matsayin baiwan da Allah yaiwa mijina
kawai don sun san ni din nashiga cikin sahun matan manyan yanzu.
Ganin saukin kan dake gare ni yasa wasu suka sauke girman kansu suna zuwa muna
gaisawa dasu cikin mutunci.
Bamu wani jima agurin sosai ba don dare ya soma yi muka koma masaukin mu sai dai
nayi kawaye da suka nuna ra,ayin su akan hurda dani duk da Yaya ya hade rai bai son
hakan dani.
Washegari a masaukin mu sabbin kawayena suka kawo min ziyara nan muka sha hira
dasu suna ta yaba irin kyawon da nayi a daren jiya gurin waliman da akayi.
Tare dasu da wasu abokan Yaya mutum uku muka Kai ziya gurin Abu sufiyanu daya
gaiyace shi da kan shi.
Karban girma akai muna a gidan nashi inda muka samay shi don suna da appointment
da Yaya da suka aje kan tana son ya dora shi jagorantan wani company da yake son yi
a Nigeria na mai.
Da sunan zuwa yini muka shiga gidan sai gashi munyi kwana buy a tare dasu cikin
kullawa da mutunci.
Ya dankawa Yaya duk wani abinda ya dace na mallakan company da yake son yi a
Nigeria din.
Don ya zamo masu babban wakili a can idan min koma gida Nigeria don samun nasaran
shi.
Taron nasu ya samu halartan wasu manyan engineers yan Nigeria wanda wanda shi
halinshi ne ya daukaka matasa na kasashen duniya don ci gaban su da kasan su.
Mutane sunyi murna da wanna anin alherin da sadauki ya jawo wakasan mu Nigeria.
Gashi matashi mai tashen zamani sun San matasa zasu samu aiki da dama a wanna
harkan insha Allahu.
Ga kyauta na alfarma da sukai muna nagani a fada bamu ba harda su Salma kawayena
dasu ka raka mu sun samu alheri sosai a gurin su.
Haka yasa na tuna da masoyiyata yar uwata Maryam wace nai alkawari a raina duk
abinda na samu nima tare da ita zan raba shi.
Don Maryam ta nuna min so da kaina da bazan iya mantawa dashi ba a rayuwana don
itace silar komai da nake ciki a yanzu.
Ba don ta gwada min so da kaunan ba da ban Kai haka a gidan su ba da tuni na gudu
na koma kauyen mu duk da halarcin da mama itama take nuna min.
Idan da ban jin dadin zama da Maryam indon ta Amirace kawai ba zan iya zama na
tsawon lokaci ba a gidan.
Na samu kyautar mota daga matar maigidan irin da matan su ke yayi a lokacin.
Tare da wani dan karamin kit wanda ke dauke da gwalagwalai a cikin sa Kiran
kamfanin su ta alfarma wanda sai wanda ya Isa ne zai saye su a nan Dubai din ma.
Ranan da zamu bar gidan matar tana rike da hannu na tana yabawa da halaiyar mu na
kirki don har su Salma da muke tare da su sai da ta yaba da halinsu.
Kwanan mu biyu a masaukin mu na Dubai din muka dunguma zuwa airport inda zamu
biya kasar saudiya muyi umurah a can kafin mu dawo gida Nigeria.
Mun Isa kasan muyi ziyaran fiyayyen halitta manzon rahama, a Madina muka dan fi
dadewa acan din.
Ranan jumma,a muka shiga garin makka muka fara umarah tare da sallah jumma a.
Adduoin danayi a can sun fi yawa akan samun shiryuwa da kariya na zuria da neman
zaman lafiya a gidan aure na tare da mijina da sauran yan uwan shi.
Muna Shirin dawowa ne zazzabi da nake fama dashi ya tsanata a kaina wanda dole
muka tafi asibiti ganin likita a can din.
Bamu sha wahalan ganin likita ba sosai kasancewa da wani abokin wasan su sadauki
dan kasan muke tare.
Nan a ka shiga min duk wani test da binciken da ya dace ai min a lokacin inda a
take results yafito cikine a jikina Dan wata uku Kuma again.
Ya kara auna ni tare da min wasu binke komai nawa normal yabamu shawara Alan
Amir da zaran ya dan Kara shan nono na wata daya mu cire shi daga nono.
Yabamu magani na yara da zamu dinga bashi Yana sha kafin a yaye shi daga nonon.
Muna barin asibiti masaukin mu muka koma inda sadauki ya rugumoni zuwa jikin shi
yana murna tare da fadin my queen ban San irin godiyan da zan maki ba a rayuwana
ba.
Don kin min komai a rayuwana gashi a Dan kankanin lokaci zaki wadatani da zuria a
gidana kyawawa abin son kowa.
Nan ya nemo bakina muka mannewa junan mu sai kalman godiya yake sako mun tare da
kara manne ni a jikin shi.
Bamu dauki lokaci ba dana ji sauki sosai muka dawo gida Nigeria cikin yan uwan mu
tare da tarin arzikina alheri mai yawa da muka dawo dashi a gidan.
Mun kwana bit a garin Abuja kafin mu Kama hanya zuwa sokoto birnin shehu inda yan
uwa da abokan arziki muka samu suna jiran mu a airport din.
Yawancin masu taron mu yan zuwa taya shi murnan samun wanna babban nasara ne na
shugabancin wanna babban kafanin da zai jagorantan a kasan mu Nigeria.
Mun sauko daga matakalan jirgin cikin shiga irin ta alfarma dana saba yi a yanzu
don fitar kunya.
Idanuwan mutane Cass akan mu wanda nai mamakin ganin wanna taron da akai muna a
gurin.
Yana sabe da dan shi a kafadan shi yayin da nake biye a bayan shi Ina saukowa a
hankali daga matakalan jirgin.
Nan aka shiga watso muna wasu flowers masu kyau da kamshi ana ta muna sannu da
zuwa.
Acikin taron nan haka Maryam ta kutso kai naji ta rungumay ni ta baya take muka
rungumay junan mu a cikin murna da saukin ganin junan mu.
Dan wani lokaci kadan ta sake ni tare da dagowa ta Dan kalle ni tana cewa wai
Fatima kece haka ko dai mafalki nakeyi.
Nace kai haba anty na bagani a gaban ki ba tace kin koga yadda gaba daya Kika
koma kin zama wata irin big madam dake Fatima.
Murmushi nayi na Kara jawo ta nai hugging din ta tare da rada mata cewa aikin
yayan ki ne haka yar uwa.
Muryan shine a cikin taro yana fadin ke uwar surutu agajiye take please ki barta
ta huta tukun kin wani tsare ta da gulman ki.
Nace haba Yaya baka ko tausayin mu yaushe rabon mu da ganin junan mu ne wai?
Ya jawo hannuna tare da watsa mata harara yake cewa kwayi gulman a gida idan kin
hadu a can.
Gaba daya da masu taron mu muka wuce zuwa gidan mu sai dai nai matukar mamaki da
ganin an canza hanyan da na sani zuwa gidan namu.
Inda naga an shiga wani irin mamakeken gida mai wani irin katon get ginin gidan
ba sai na tsaya fadin shi ba don har da bene a gidan.
Nan ma yan uwane Mata dam a gidan a hankali ya rada min cewa welcome to our new
house queen.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE, , ,