Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
zaune na sake raina ba abinda ke damuna yanzun in ba matsalan
mijin ta ba da kulun a cikin tashin hankali suke a tsakanin akan ban kawo masu
komai ba.
Amma nazo ina cinye mashi abincin gidan shi a banza shi gaskiya ba zai zauna da
agola ba a gidan shi.
Naso na bar garin amma sai na dake na tsaya inga iya gudun shi ko zai kore ni ne
ni kuma nasan yadda zan girgiza mashi auren shi.
Sai dai ya shigo yayi haukan shi ya fita babu mai tsinka mashi a cikin mu dan
dama ma ita mama sukan kwasa dashi idan abin ya ishe ta.
Gidan kowa ban zuwa kullun ina gida zaune kamar wata matar aure can dani.
Ganin shi kawai sukayi da yammacin jumma,a ya diro garin nan suka gaisa mama
take tambayan shi yaya akayi kuma ya dawo ba yace suna da wasa wani sati ba sai
satin sama zai dawo gida.
Yace eh maji nadawo ne nai wani abu a garin kuma da akwai wasu takardu dana manta
ban tafi dasu ba da zan tafi.
Yakai wani lokaci a zaune baiga giccina ba hakan yada shi sanin cewa har lokacin
ban dawo ba ke nan garin.
Ya mike ya fita kaman wani mai jin kasala a lokacin, Bashar ya kira yazo idan an
fito sallah su fita.
Ranan Monday maryam tafito a cikin shirin ta zata shiga makaran ta,a waye ta
samay shi ya fito daga gurin exercise .
Sun gaisa yake tambayan ta ita wana har yanzu taki dawowa ba kun koma makaranta
ba tace eh munyi waya da ita tace bata san ranan da zata dawo ba kila ma,
Fuska a daure yace ina ne garin su?
Tace, a yaya baka san garin su Bintu ba kai, duk zaman ta a gidan nan?
Yace don Allah malama fara bani amsan tambayana kafin kiyi min halin ku na yan
kasa tukun na tambaya cikin tambaya.
Tace can rabah take nan dai tai mashi kwatancen yadda ake zuwa garin yace inda
muka tafi gaisuwan wancan mutumin da tatashi aure kenan ya rasu ko tace mashi eh
can ne ya amsa mata da ok good.
Zaka tafi garin ne yaya ta tambaye shi tare da kallon fuskan shi yace ban sani ba
tambayan ki kawai nayi.
Sai batan kamar kwana biyu da tambayan maryam ranan da safe yace wa Bashar ya
shirya zasu tafi wani dan kauye su dawo.
Sam Bashar bai kawo komai ba a ran shi nan yazi ya dauke shi shi yaja mota suka
tafi.
Ban zuwa gidan kowa amma ranan haka kawai nace zan je na gaida kakanin mu kafin
na tafi don saura kwana biyu na tafi.
Mun fita gida da kaman awa biyu suka shigo garin wani mai faci bakin titi suka
tambaya gidan dan Amo shayi akai masu kwantacen gida.
Da farko da suka isa gidan yaso yai gardama ko banan ne gidan ba saboda ganin
yadda gidan kaman ma yafi ko wani gida na uguwar lalacewa a shiyan.
Sallama suka ce ai masu da maigidan yaron da suka tura yace kai mai gidan kan
yanzu ba,a samun shi gida yana can gurin moli.
Basu gane may yaro ke nufi yace yashiga yace wai bakine daga sokoto sun zo ganin
Bintu.
Mamana tanajin haka tace, Bintu bata nan tafita amma ace su waye yace ace yaron
hjy ne yazo tafiya da ita.
Jin haka yasa mama tace ace su shigo daga ciki ai su yan gidane nan ta tura yaron
ya kirani gidan kakan nina, basu so shiga gidan ba amma dole suka shiga.
Shi dai bashar sai kallon ikon Allah yakeyi kawai don abin ba mamaki ba daure mai
kai yayi.
Bin gidan yake da kallo da mamakin yadda dan adam ke rayuwa cikin wanan rubaben
ginan haka da akoda yaushe yana iya rushewa.
Bai san cewa shigina in har akwai mahaluki a cikin shi ba Allah na karewa yadda
yaso.
Tabarma mana ta shimfida masu daga dakin ta nan ma yai matukar mamaki wai dakin
da ake rayuwane, acikin shi haka.
Ruwa ta debo masu acijin wani kufin silver ta sabo ta kawo masu bashar ya karbi
ruwan ya dan kora a cikin shi.
Shikan bai san yaya zai iya kai wanan cup din a bakin shi ba gaskiya don tun
bashar baisha ba yaji kaman yai amai.
Bayan mama ta dan fita dauko masu abin fitara ne Bashar yace wallahi kasha ruwan
nan don ba haka ake neman aure ba.
Cikin tsawa yace Bashar you are very stupid wallahi.
Neman auren wa kuma can sai dai idan kaine kazo neman auren ban sani ba don kai
baka raina mata naga alaman haka ?
May ye abin rainawa ga abinda mutum ke so a ran shi ?
Shiru yayi don mama ta dawo a lokacin tana mika masu abin fitaran tana fadin kuyi
hakkuei akwai zafi wallahi.
Sai ga wata akuya tashigo nan ta hau saman tsadaddun takalman su ta sake mai
fitsari a na shi.
A hankali yace oho shit da ido yaiwa bashar din signal ya kalli kofa abinda akuya
take mashi.
Murmushin keta bashar ya sake mashi, yace don't mind my friend duk ciki ne ai.
Lokacin na shigo gidan da mamakin ko su waye aka ce sun zo nemana a lokacin daga
sokoto.
Sam ban kawo cewa shine ba don sai ina zaton mamace ta turo wani ya dauke ni kila.
Ina bullo daga kofa mukai arba dashi zaune cikin fararen shaddan shi yaci starch.
Nai matukar mamakin ganin su a gidan mu dakin uwata musa ne ya hango akuyan tai
fitsari akan takalmin dayan su ya shiga koran akuyan ya debo ruwa ya zubawa
takalman.
A hankali na tsaya daga kofa ina masu sannu da zuwa, duk na shiga rudewa da ganin
su.
Bashar yace min humm Bintu kinzo kinga mama shike nan kin manta da zancen an koma
makaranta ko ?
Nai dan murmushi nace ban man taba yaya kawai dai ban tashi dawowa bane a lokacin
nan.
Da sauri yaya sadauki yace sai yau she baki da hankali ne wai ana karatu zaki zo
ki samu guri ki zaman ko a kauye.
Ganin zai sake layi yasa Bashar tare da fadin yanzu dai mama tace muzo mu dauke
ki yau din nan don an koma school tun ranan Monday kin sani kuma.
A hankali nace yau din nan yaya yace eh haka ta bamu umurni shiyasa muka zo ai
daukaki din.
Nace ni gaskiya ban shirya ba fa sai dai idan na shirya zan dawo anytime.
Kafin wanin mu yai magana sai mamana ke fadin may zaki shirya kuma ina kin yi
wanki jiya kitashi kawai ku tafi tunda har kikaga hajiya ta aiko a dauke ki.
Ban so ba haka na shirya zan bisu su suka fara fita yakawo kudi masu yawa yabata
yace tayi hakkuri babu kudi a jikin shine.
Sai da zantafi nace mama ki boye kudin nan kafin mijin ki ya dawo ya kwashe su
kiba musa yakai maki gidan su kakale a boye maki su ku dan samu abincin abincin
rana dashi.
Nakawo sauran kudin dake hannuna sunkai dubu goma nace tace ga abinda aka bata.
Mukai sallama dasu muka fara hanya ina baya sai tunane nakeyi kawai a raina.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,
IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA YA KARANTA ALLAH NAGANIN KI ZAI KARABAN MIN
BASHINA GOBE GARE KI,,,,
A LOKACIN MUKE,,,,
Amaryam kan ta tare gidan angon ta Atiku maria haka ta kwana a cikin bakinciki
ranan don tashin hankali.
Washegari da safe ko kafin ta gama barcin ta data saba tafito ta samu har amarya
ta fito ta gyara gida ta dora ruwan zafi a wuta.
Ganin maria ta fito lokacin tana tsaye tana tara kwanon da tukanen maria, da
yaran ta suka bata tun safen jiya har yau.
Bingidan maria tayi da kallon yadda ya sha gyara ko ina, ina kwana ?
Amarya Sadiya tace mata, cikin haushi ta amsa mata tace lafia kawai,
Ta wuce zuwa bayi ta kewaya tafito tafara alwala duk abinda amarya keyi tana
binta da ido.
Bazata gwada wa amarya sadiya shekaru ba itma dai sadiya din zasu zo sa,a daya da
maria din.
Kafin duk yaran maria su tashi har sadiya ta dama kunu, ko sai ga maigidan ya
shigo wanda tun fitan shi masalaci suna can suna zikiri bai dawo gida ba sai yanzu
da gari yadan haska.
Yana shigowa ya samu sadiya ta zuba kokon da ta dama ga sabbin robobin da tazo
dasu gidan.
Inda taimashi sannu da dawowa ta dauka takai katon roba mai kunu kofan Maria ta
girke masu ta dauki nata da mijin ta tashiga dashi dakin ta.
Sai gata tafito da sabon bucket a hannun ta ta deban mashi ruwan wanka takai
mashi bayi.
Zata fito ne ta samu maria ta idar da sallah tafito waje tace mata ga kokon ku
nan a kofa na aje maku sai ruwan wanka dana sa su fito su fara wanka kada su makara
zuwa makaran ta .
Wani kallon banza maria ta watsa mata tace da baki gidan wake basu ruwan wanka
dama kada ki kawo min sallo da iyawa don gidan kika shigo.
Kuma ki koma ki dauki munafukin kokon da kika aje don mu baza musha abin sihiri
ba wayasan inda kika fito da tarkacen tsiyan ki da zaki wa mutane sihiri kice wai
kin dama.
Haba yar uwa gumbane fa akayo muna shi wanda zamu amfana dashi kwana biyu a gidan
nan.
Munafuka mun san irin ku wazaki cuta sai dai shi daya daukowa kan shi, bata
karasa ba Atiku yafito daga dakin amaryan nashi.
Yace ke Maria wallahi ki shiga taitayin ki idan kikace zaki tirka min tsiya
agidan walle na lahira nafin ki jin dadi.
Ke ga kina iskancin ki nakawo ijjiya na saka maki ba fa fin karfina na kin yi ba.
Raga maki dai nakayi don wa yanga yaran dakin ka gani ko suma yaran ba tausayin
na kikayi ba da kina tasaya masu da baki kaisu mahalaka ba ke illata masu rayuwan
su.
Duk wace tace tashin hankali da diban albarka zata aza min agida bani daukon
shashan ci yanzo don zama da mace ba dole na ba.
Aliyu kai, Aliyu ina kake na ?
Sai ga yaron ya fito yana sharan fuskan shi yace baba gani.
Yace ku tai zuwa sallah in kun dawo ku taho ku karya kutai zuwa makaran ta
kajiya.
Sai amaryam tace gama ruwan wanka ceniya ga na aza masu suyi wanka sutai zuwa
makaranta.
Yace ke baki kunya ba maria, yaushe kika tashi warhaka har ki dama masu kunu su
sha suyi wanka da safiya haka.
Kuna na dai ko inke baki sha diyana sha sukai inga ta tsiya yau inkin isa, in
tsiya kika so ko wane irina samunai ki kai ga Atiku.
Ya juya ya wuce bandaki zuwa wanka nan yabar maria na fadi ashe akwai wadda akai
agidan ga don walle in mace tace makirci ta iya gida nai ta taho wallah.
Ni dai ba tashin hankali nishigo gidan ku yi ba aure na yakkawoni kuma ni tsakani
da,Allah nika zama da kowa a rayuwa na don banda mugun nuhi akan kowa.
Amma fa ki sani inkice ba wanga zama kika,bukata a gare ni ba duk wadda kika so
yinai zamuyi keji na hwada maki wallah.
Ta juya ta shige dakin ta tafara gyarawa kafin mijinta da ya,shiga wanka yafito
ta saka turaren wuta daki ya dauki kamshin safiya.
Maria na jin kamshi har dakin ta rayuwan ta yai matukar baci tace a fili karuwan
banza kawai.
Mamakin ta bai kai karshe ba sai da taga Atiku ya fito cikin wankakun tufafin shi
Sadiya ta rako shi har kofan fita daga gidan ta kai tsugunne tana fadin.
Ya Allah ka tsare muna bawan ga na ka bashi sa,a da rabo na alheri, ka bashi sa,a
ga abin daya fita nemowa yaciyar da mu ta hanyar halal ya Allah ranan taga dariyan
Atiku har sai da hakoran shi suka baiyyana a fili.
Duk maria tana daga kofan ta tana kallon bakon al,amarin da ya shigo masu a gida.
Atiku yafita cikin jin dadi yana fadin Ameen Sadiya nagode nagode Alkah yasa ki
zama min alheri a rayuwana.
Yana fita daga gidan maria tace wai sabon kicihi can muka fito har takalman ya
tsinstinke indai namiji ayi dai mu gani gidan ga.
Sadiya kamar bataji may maria take fadi ba ta,share ta dakin ta takara gyarawa
tsab tafito kofinan da yara suka sh koko kafin su fita ta tattara su ta wanke da
sauran kayan da tai aiki dasu.
Kagin amarya tai kwana hudun ta maria ba karamin wahala tasha ba saboda Sadiya
mace ce mai tsabta da mijin su ya dawo gida kayan da ya cire na aikin shi bata bari
ya kwana bata wanke su ba.
Haka dakin ta duk da ba komai a cikin shi sai ta gyarashi sau kusan hudu a wuni.
Maria sai habaici da bakar magana take yaddawa cikin gida tai ta faman fada da
yaran ta tana sauke haushin uban su, a kan su.
****** ********* ******
Wanka nayi don shirin kwanciya saboda ban tsaya dogon hira ba gobe mu da lecture
mai zafi da zamuyi.
Dogon riga fari mai dan hannu na dauka na saka a jikina ina kokarin daure kaina
sai ga mama tashigo dakin namu.
Tace dauka niyi ai keyi barci Fatima?
Nace a a mama yanzun dai naka shirin kwanci wani abu zan maki mama ?
Na tambaya cikin dan kallon ta a cikin ladabi da nake mata a koda yaushe in muna
magana da ita.
Tace, dama magana naka son muyi dake inba ki komai ke jiya.
Nace walle mama mi nikai mashin ?
Kwacinya dai naka shirin yin yanzu don gobe muna da lecture da safe insha
Allahu.
Ta juya tana fadin ki saman a daki na yanzun in ke gama.
Daga haka ta juya tafita daga dakin ina gama daure kaina nabi bayan mama dakin ta.
Na samay ta zaune a saman gadon ta sai dai yanayin ta kaman tana a cikin yar
damuwa a lokacin.
Ganin na shigo takw ce min zonan ki zauna Fatima tana dafa gado daga gefen ta
alama take min a gurin zan zauna ke nan.
A darare na zauna dan bakin gadon kadan dan nesa da ita, sai naji ta dafa hannu
na daya tana fadin Fatima magana nake son yi dake don haka ki fahince ni kuma idan
magana na da takura a cikin shi kada ki damu kanki don Allah Fatima.
Nace mama hwadi dai maganan ki ai babu komai walleh na fadi cikin murmushi don
nasan dai kila laifi nayi zatai min magana.
Tace Fatima ina fatan bazaki fassara min magana ta ba da wani fasara gani ke dai
kinka cancanci hakan shina yasa na aiwatar da hakan akan ki.
Tace, bakomai na ba so dai nakai ki auri sadauki don dai ta kin ka san halinai
kuma kina iya hakkuri akan duk wani baudaden hali nai.
Kamar a mafalki naji zancen mama take duk da sanyin da dakin ta keyi na A C sai
da naji zufa na karyo min.
Tace na san cewa keta zaki iya hakkurin zama da yayan ki kuma ki rufa mai, asiri
ga duk wani rayuwa nashi.
Wanga dalili dana hwada maki shina yasa na yanke hukunci a raina keta zabina dama
shi din.
Tace Fatima nasan cewa a ranki zaki iya cewa missa nai maki wanga mumunan zabi a
rayuwan ki .
To maganan gaskiya gani nayi duk matan da yay aure babu komai cikin wanga aure
nashi in ba tonon asiri ba a garai.
Har da nima uwatai, ke har yan uwa nai sai gori ya ishe su gidan ga.
Ba yau ba na dade ina wanan hwatan ni kadai a rayuwa ta, amma na rasa yadda zan
hito maki da zancen.
Amma yanzu nasan ke dan tasa shekarun ki yakai ta fahinta shinasa naga gara na
hwada maki dai don ki san abinda naka kullawa a tsakanin ku.
Wagga magana kuma da naka hwadi Fatima har tai kunnen Baban ku yasan da ita.
Shima dai ya nuna farin ciki nai akan zancen, sai naji muryan ta ya canza tana
cewa cikin murya mai kuka.
Fatima Allah yasani ban yi wanga hadin don dai na cuta maki ba, nayi shina dai
don samun farin cikin ku baki dai.
Nasan cewa har yanzu bawai ya bar shan abinda yakasha bana ke ma ke san da haka
Fatima, hwada min faina bakiyi.
Don kina gudun bacin ran da zan shiga ciki nai shina yyasa baki son na sani.
Fatima ance wanda ya rigga ka kwance yana riga ka tashi na san komai da sadauki
kayi, a rayuwa nai don nita na haifi abina,.
Nasan halin rayuwa nai sarai shi dai nayi don gujewa masifan da a ciki nai tunda
ya boye min shina yasa nima nabar abin aboye kaman yadda kuka boye min din.
Shin Fatima macen da ka irin wanga halin ai ta san kan ta na inda baki san kan ki
ba duk wadda naka gwada maki halarci sai kin tai kin hwadai wani gurin.
Ko ni ki hwada min nasan mi yaka ciki, amma kinka iya boye zancen sai kokari
kikai kiga ya bar wagga har kan ke dai.
Fatima kiwa Allah ki taimaka min akan wanga yaron don ban san mi, Allah ka nuhi
ga auren ku ba.
Nasan cewa na hada ki da aiki Fatima, amma gani nayi ke ta kadai ka iya tayani
wanga kwaran ba tare da anjiya ba.
Sai tai shiru kuka ne yafi karfin zunciyan ta a lokacin don haka ta kasa ci gaba
da maganan ta.
A hankali na zamo daga saman gadon da nake zaune tare da durkusawa daidai kafan
ta nima dai din kuka nake sosai.
Kaina ta