Advertisements
Chapter 37 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   37 / 92

108K to 111K   out of 275.8K words

samay shi bakin kofan gida su dama Bashar yafita da motan shi shiyasa
Imirana bai gane yana gidan ba a lokacin.
Yaya akayi man?
Ya kara cewa wai may ke faruwa ne naganka haka a ya mutse?
Yace hajiyan ka tana garine Bashar yace eh yace zan kwashi yaran nan nakaisu
gurin ta har su baba su dawo.
Anyi wani abune ?
Yabashi amsa da anyi a takaice.
Ina fito da kayana falo ina fafin wallahi Anty Amirah ban kwana a gidan nan
garin mu zan tafi sai gashi ya dago labule ya shigo falon .
Fuska a daure yace ke Amirah maryam ku hada kayan ku dake kuzo na kai gidan
hajiyan Bashar don gobe zanyi tafiya bazan barku a gidan nan ba.
Yan gidan na kallo muka fito da kayan mu mun kashe komai na,wuta a part din namu
tare da rufo kofa muka fita daga gidan.
Daga cikin diyan mama Asiya ta buga ma mutanen saudiya waya ta fada masu halin da
ake ciki a gidan.
Anso boye wa maji amma sai hjy kubura ta tsinci ana maganan itace ta fada mata
abindake faruwa da mu.
Hankalinta yai matukar tashi sosai ranan bata iya barci ba, don gani take kila
yakai gare ni boye mata akayi kawai.
Gashi tayi kiran layin mu duk bata samay mu ba har sadauki din bata samu ba.
Ita ko Umma fada takama yi wai don anga bata gida za,a kullawa dan ta sheri haka.
May Imirana zai yi da wanan kwailar yarinyar mara fasali sai fari, duk tsiyan da
aka kwaso don anga Allah ya azurta ta da yara shine ake mata hassada a gidan.
Sai ga kanin Imiranan ya bugo mata waya yana kuka yace gaskiya Umma abinda yaya
yaki baida kyau fyde wa ya tashi yiwa Bintu yau saida yaya sadauki yacece ta kuma
yace sai ya kashe yaya sadauki ya fadi a gaban kowa.
Nan ta hau yaron da fada tace har dashi ke nan za,a kullawa dan uwan shi sheri a
gidan.
Yace wallahi Umma ba sheri bane a gaban mu akayi baki yadda akai mai jina jina ba
wallahi zaban kunya.
Kashe wayan tayi don bata iya sauraren takaici gashi a gaban hjy kubura suke
wayan.
Nan tahau banbami cewa dama ankawo sune don an hada baki a tozarta mata da acan
bayan ta.
Hjy Kubura tace ai ba wanda yasaki zuwa ko kin manta fada dakikayi kan sai kin zo
dakin zauna gida da yara ai da duk haka baifaru ba.
Amma kun kwaso jiki kunbar yaran can maynene ba zai faru ba tunda basu da
tarbiya.
Nan wani sabon fitina ya fara kamar ba a kasan saudiya suke ba saboda bakin kishin
su.
Muna gidan maman Bashar matar bata da matsala itama tana da yan mata guda biyu
sai wata yar karamar yarinya jikan ta.
Bamu da matsalar komai a gidan don tana bamu kulawa yadda ya dace uwa tabawa
diyan ta.
Gasu da addini duk da sun girma basubar zuwa isalamiya ba daukan hadda da sauran
litattafai.
Zazzabi nayi na kwana biyu da wahalan da nasha Bashar da maman shi suka kaini
asibiti sai da nasha allurai na mike.
Hankalin mu a kwance muke komai a gidan babu tsangwama kuma su kadaine a gidan.
Zamu zauna da uwar muyi hira da ita cikin sake jiki babu ruwan ta.
Sadauki ko ya samu jikin Baba yai sauki sosai don har yafita yai dawafi duk da da
sauran jikin shi.
Sai dai yasan cewa Umma tana hake dashi don irin yadda take mashi tunda ya iso
kasan.
Bai kula taba don maji taja shi a gefe tunnisowar shi take tambayan shi abinda ya
faru.
Hakalin ta ya kara tashi sai dai da taji cewa ai yaranta yanzu suna can uguwar
arkilla gurin mahaifiyar Bashar hankalin ta ya kwanta.
Kwana shi uku tare dasu ya tafi garin Riyahd ya barsu gurin wasu yan team din
kwallo.
Nan ma ya,bugawa wasa inda ya samo riyar masu yawan gaske don yan kan har taya
shi sukayi akan yadawo kasan su da wasa amma yace masu kasan shi ma suna bukatan
shi.
Ya dawo suna shirin tafiya ya ba su kudi kowa tayi tsaraba wa yan uwa da yaran
ta.
Umma tai matukar rudewa da irin kudin daya basu a can hankalinta ya tashi tasan in
bata zake damtse ba sai wanan yaron ya zarce tunanen ta.
Maji ta samu kudi ta sayo muna kaya masu kyau da,tsada zannuwan gado masu kyau
da sauran tarkacen daya dace a sayo.
Sai kuma Umna abin ya tsone masu ido wai yabawa uwar shi kudi yafi nasu ya nuna
masu banbancin cewa ita ce ta haife shi ke nan.
Maji dai tana gyaran kayan ta sai murmushi tayi kawai batacewa mama Asiya uwa ka
iya komai ba.
Don umma ta zugata itace ta fito fili tana maganan cikin hasala da bacin rai.
Sai dai duk iya shegen su basu yarda suyi a gaban Alhaji don yanzu zaici masu
mutunci ne.
Satin su biyu da kwana hudu suka iso sokoto zakace ba jinya sukatafi ba da bauta
don duk suyi kyau abinsu.
Ga zancen tafiyan su ya bi yan uwa da abokan arziki kowa ya san da cewa dan
kishiyan su ne da suke kira mashayin gidan su yakai su saudiya umar da jiyan mijin
su.
Saidai kan kowa na ciki na ciki jira ake a dawo gida a zazzage balain da aka
kullo.
Kafin su dawo mun shigo mun gyara ko ina na part din mu muka koma gidan su Bashar
muna jira su dawo gobe.
Mahaifiyar su bashar tasa ai muna gyara jiki kitso har kumshi saida ta sa akai
muna, siffa mai kyau mun koma kamar wasu amare da mu.
Sai bayan sun dawo har sun huta yaya sadauki yaje ya,kwaso mu har mahaifiyan
Bashar din ta rakomu gida.
Mun samu gida ya rude da murnan dawowan iyayyen su ko wani daki sai hayaniya
akeyi.
Gaba dayan mu muka fada jikin mama cikin murna da farin cikin ganin ta a lokacin.
Maman su Bashar sai kallon mutake cikin sha,awa nan mana ta fara mata godiya, kan
karamcin da tayi mata na rike mu a gidan ta.
Tace haba ai ba komai yaro ai duk na kowane dama absan haka tun farko da can suka
zauna harku dawo.
Yaya sadauki da Bashar na zaune sai kallon mu sukeyi duk nabi na takura da zaman su
a gurin.
Na mike tare da fara daukan jakkunan kayan mu da muja dawo dasu yanzu zuwa cikin
daki.
Maji tace Fatima bazaki bari har ki huta ba nai dan murmushi nace mama bari na
shiga dasu kawai.
Ina shiga maman Bashae tace ai Fatiman nan taki akwai kokari wallahi ko can haka
nake fama da ita gurin aiki.
Mama tace ta riga ta saba bata son zama da kazanta ko kadan .
Ashe aure zatayi bada dadewa ba jiya nake jin suna mata sheri wai angon ta yazo
yaga wanan kwalliyan nta sai nake tambya suke fada min an kusa bukin ta har an kawo
kayan lefen ta.
Hakane hjy nice ban aika maki ba.
To Allah ya sanya alheri ai mijinta yai sa,a ya samu yatinyar kirki ta san ya
kamata sosai.
Kai wanan yarinyar dai shu,umace kowa sai kaji yana yabonta ko akan may oho.
Bai zaci maganan zucin shi yafito fili ba sai jiyayi Bashar na fadin kaine kake
ganin ta shu,uma amma ai Fatima mutunce wallahi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU

IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,


IDAN KIN TURAWA WANDA BAI BIYA BA BAMU YAFE MAKI BA ALLAH YA ISAR MU NA AKAN KI,,,,



Tun kawo laife na yaya sadauki ya kara tsananta min a gidan su, dan abu kadan zanyi
ya dinga min fada cikin hasala da bacin rai.
Wanda shi kanshi bai san dalili yi min haka ba haka,kawai yake jin haushin
yarinyar a ranshi.
Duk da maji tana mashi fadan haka amma ya kasa rangwanta kiyayyan da yake ji nawa
a ranshi.
Idan yana gida ban fitowa falo sai naji ya fita daga gidan zan fito falo don nima
haushin shi nake ji yanzu don a matsayin mugu macuci nake ganin shi.
Nasan kuma don saka mai idon da nakeyi ne abaya shine yasa yake jin takaicina
haka.
Maji sai shirin bukina dake kara matsowa takeyi a hankali, irin su kayan kitchen
da wasu uan abubuwa su take sai min.
Kabir yace idan anyi aure a sokoto zan zauna a gidan shi na garin sai idan anyi
hutu zan diga zuwa gurin su Abuja.
Maji yakira ya fada mata tsarin da yayi akaina da ta tambaye shi kan al,amarin
karatuna da nakeyi.
Sadauki ya shigo ya samu mama tana wayan da Kabir yana jin duk abinda suke fadi a
karshe Kabir din ke cewa mama ko tsarin bai maki ba haka?
Maji tace gaskiya naji dadin hakan Allah ya albarkaci rayuwan auren ku, ya amsa
cikin jin dadi da Amin mama.
Mama tace Kabir don Allah ka rike min Fatima amana don Fatima yarinyace dake
bukatan kulawa yace insha Allahu mama kada kiji komai nima nasan da hakan.
Yana zaune ya fahinci da wa mama take waya ya lumshe idanuwan shi jin hiran nasu
yake kamar a fili Kabir yake ya shake shi.
Sai tsuki yayi lokacin suna sallama zata kashe wayan yace tsohon banza kawai.
Kaidawa kuma kake tsuki anyi wani abin ne ko may?
Yace cikin daure fuska kawai dai nayi ne don wanan shirmay danaji anayi.
Shi waye da zai dinga yiwa mutane barazana kamar wani attajiri can.
A,a ikon Allah waikai sadauki ina ruwanka da zancen nan ne?
Ina da ka mayar da kanka abin kwarai agurin kane za,a zo neman auren yaran nan.
Yace wani maji da ban bashi ba kawai mutum ya tsufa amma yana halin yara .
Idan aure yake so bai zuwa ya samu bazawara su shirya sai yafake zai bata yar
mutane.
Ya juya inda nake zaune raina yabaci don abinda yake min yafara isata, yace jita
don Allah daga kawai ance mutumi a abuja yake duk kin wani rude a kan shi don kawai
kije abuja.
Baki tsaya kin tsarawa rayuwan ki abinda zai fishekiba mutum da iyali haka ke
karama dake may zaki gane a gurin shi inba wahala ba.
Kai dakata ya isa haka na,rasa gane dalilin dayasa kake wanan abin haka
Yadago ya kalli uwar yace may nakeyi maji iyaka dai ina fadin gaskiyane ni kawai.
Duk abinda na hango mata kun kasa hangen shi sai faman rawan kai takeyi ita zatayi
aure wawiya kawai doluwa.
A,a wai sadauki kana da hankali kuwa da may wanan abin yai kama hakane wai?
Mikewa nayi fuuu, nabar falon cikin fushi na shige ciki abina don ban iya tsayawa
sauraren wanan shirmay na shi.
Tun ranan idan yaya sadauki ya shigo falon duk hiran da ake haka zan mike tsam na
shige daki abina.
Ranan muna tahiran mu cikin dariya har maman tamu tana saka muna baki a hiran mu
don hiran wasu samari da suka zo wai suna son maryam muke yi muna dariya.
Ya shigowa suna mashi ina wuni da jan shi da hira yana batun zama namikw tsaye
tsam daga inda nake zaune, ina cewa.
Zan shiga na kwanta maryam tace wazai kwanta yanzu ke da baki barci koda rana
shine yanzu da yamman nan zakice wai zaki kwanta.
Ya dago lumsarsun idanuwan shi masu nuna a gajiye yake a lokacin don tun safe
yafita daga gida .
Ya dora su a kaina gaba daya yaga na canza mashi na koma wata fresh sosai dani
don nima ban san may mama take yawan bamu ba muna ci muna,sha na gyara jiki kawai .
Ko kiftawa bayayi don mamakin sauyawa na a lokaci guda da yaga nayi mashi a
lokaci guda.
Mama taga yadda yake kallona sai abin ya bata mamaki kwarai da gaske amma sai ta
dauka wani sherin yake son fadi akaina kuma.
Don haka tai shiru tana sauraren taji abinda zai fadi a lokacin tai mashi tsiya.
Maryam dai tasan yar tsama muke duk kwanakin nan ta dai dubeni saboda ta san
ba,kwanciyan zanyi ba ganin yaya ne kawai yasani barin falon nashige tana ce min
atashi lafiya ko?
Nashige batare da na,kara,waiga inda yake ba ballw yace ga abinda nai mashi kuma.
A bangaren sadauki kuwa, fuska ya kara,daurewa batare da ya kara bi ta kaina ba
don yasan mama tana jiran shi ne.
Maryam daga inda take tai mashi kuri da ido tana dariya cikin kyata tace ban san
wanan fadan na yaya da Bintu ba wallahi.
Bai tanka mata ba sai tsukin da yaja ya dan dafe kan shi yana fadin rabu
da,wawiyan banza kawai gaskiya ne bata so a fada mata.
Daga gurin da maji take cikin takaici tace gaskiyan may kada tai auren ko may ?
Yace ni fadan gaskiya nake mata saurin may take da,bazata iya tsayawa ta karasa
makatantar taba ne wai, duk tsoho ya, hure mata kunne bata jin kiran yanzu sai
When it's too late to her zata gane kuren ta ai.
Allah dai ya tabbatar muna da abinda yafi zama alheri a gare ta.
Ina shiga daki kamar jira kabir yakw na shiga dakin sai ga kiran wayan shi ya
shigo min.
Mama ta kwalla min kira wai nazo za ai program din da nake so wasan kwaikwayo a
NTA sokoto wanda nake so ina kallo ina dariya don shirin irin namu ne na mutanen
kauye.
Hakan bai hanani yin wayana ba don can na manne gefe guda yadda,ba mai jin abida
nake fadi.
Kallo daya zakai min ka fahinci cewa ina cikin nishadi da wayan da nakeyi ga kuma
kallon film din da nakeyi a tv duk a lokaci daya.
Muryan kabir ce ta ratso dodon kunne na yana cewa Fatima nayi rashin ki kwana biyu
aiki ya hana nazo na gane ki.
Nayi murmushi tare da lunshe idanuwa na na gyara zama da kyau.
Ban bashi amsa ba sai yar murmushin da nayi har yana jiyo ni a,wayan a lokacin .
Ya naji kina murmushi ko baki yarda na damu da nazo na ganki bane wai?
Na koma yin murmushi mai hade da sautin dariya wanda ya jawo hankalin kowa a kaina
a lokacin.
Nace may zai hana na yarda duk da dai nasan akwai wasu a,tare da kai ba,wai wani
damuwa zakayi sosai hakana ba ai.
Yace kowa daga cikin ku ina bashi hakkin shi ai nace ai nasan da hakan, yace da
kyau da kika fahince ni.
Yace wai kin san wani abu kuwa nace a,a cikin dan girgiza kaina kamar yana gani
na a fili.
Nace sai ka fada dai,
Yace wai ko Fatima kin san yadda nake jinki a cikin raina kuwa, ?
Wallahi da ina da iko ko kuda bazan yarda ya sauka a kanki ba.
Don ina ji a jikina ke wani abune da,Allah ya jefo min a cikin rayuwana mai
muhinmanci a gareni.
Murmurshi nake irin mai kyalkyatawan nan nace kai amma kuwa nikan nayi
sa,a,a,rayuwana wallahi.
Insha Allahu zanci gaba da kullan maka da kaina a duk inda nake .
Nace ni wallahi zancen kama har yasa na manta ban tabayeka lafiyan anty na ba da
yara.
Yace duk suna nan lafiya yanzu tare muke da uwargida ta dan shiga shago tayi
sayayyane.
A rude nace wai har na zaci ai a gaban ta kake waya dani haka wallahi.
Yace aiko a gaban ta sai nayi don ba ta damuwa tama fini matsuwa kizo gidan ai
yanzu.
Na saki wata yar siririyar dariya nace kai ka taba ganin kishi har tafi ango
damun akawo mata kishiya a duniya.
Yace baki san halin ta bane shiyasa amma ni nasan zanji dadin zaman ku a tare
sosai wallahi.
Nace ni dai ka rufa min asiri kada dayar matarka tani tace zamu hade mata kai don
muna shiya daya da ita.
Yace ai itama tasan cewa Haulatu na waya dake tai fada harta gaji tunda babu
yadda zatayi.
Nace ni nasan dama idan ta sani sai anyi rikici don bata da dama,wallahi gurin
kishi.
Maryam tace kai kai wanan matar dai tun ba,a shiga ba na hango ita ce matsalar ku
ke da Kabir .
Dariya na kama tare da kashe ina cewa kai anty maryam watau kina jin hiran mu
ashe?
Tace duk abinda kuke fadi inajin ku ai in ya damu ba sai yazo ya zauna ba yai ta
kore maki kudan da baison yasauka a kanki.
Ya suke da hiran mu yakai geji yakawo iya wuya sai yaga fita dakin yafi mashi jin
takaici kawai.
Ya mike yanace maji zan fita sai na dawo tace mai a dawo lafiya tare da ci gaba da
kallon ta.
Yana fita Amira tace ke Bintu watarana sai yaya ya make bakin nan naki akan wanan
wayan da baiso.
Mutum da mijin shi zai make ta idan yaji takaici yaje ya samo tashi matar mana
shima inji maji takeba Amirah amsa.

Bai dauki lokaci ba sosai yakoma tafiyan shi don yanzu bai zama a gida shi sosai
ga,wasan kwallo ga kuma business din daya fara gadan gadan na sayar da motoci da
mashin mashin,
Haka yasa baida lokacin zama a gari yana fita business din shi da neman kudin
shi.
Cikin dan lokaci guda sai ga sunan sadauki ya daga sosai a gari.
Abinda su mama suke gudun dai ya faru Allah ya nufi sai ya faru din don suna gani
kuma suna jin yadda Allah yai ikon shi akan abinda suka so kada ya faru da dan
kishiyan su.
Mama Asiya ce suna zaune suna hira take cewa, wallahi yaya wanan yoron shigen
yaro ne kidiba fa,ba yan mu ba yanzu ko uban shi ya tsushe nisa ba kusa ba .
Umma tace ni wallahi ba inda na fara sanin haka zai iya faruwa damu sai wani rana
da natafi dasu gurin buki.
Wata mata irin matan nan masu ido a

37 / 92