Advertisements
Chapter 85 Reading A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu BookTok Hausa Novels
Advertisements



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

A Lokacin Mu Ke by Zainab Idris Makawa Seenabu

Author :  Zainab Idris Makawa Seenabu Category :  Complete Novels

Chapter   85 / 92

252K to 255K   out of 275.8K words

Yana fadin Fatima don Allah ki kula da kanki ki tausayawa abinda ke a jikin ki
please.
Idan baki ci abinci ba yaya zaki samu kuzari har baby na ya samu shima please ki
tausaya min ko ba dadi ki dan dinga cin yan abubuwan gina jiki don kuzarin ku.
Kune rayuwana Fatima kune zan kalla nayi farinciki don kune jindadin farin
cikina.
Nasan bakya jin dadi amma ki kara tausayawa kanku please badon ni ba for the sake
of our baby please.
Idanuwa na na dago sun ciko da hawaye nace yaya ina son ci amma ko naci din
fitina yake zama min nai ta amai sai na fitar da abinda naci nake dan samu lafiya.
Ya dora kanshi saman goshina ta yadda muke iya shakan nufashin junan mu.
Yace sorry my baby nasan kina wahala wallahi dada halin karban ciwon nan a
hannuki da na karba maki kin huta ke ma.
Hawayen da nake dannewa ne suka silalo daga idanuwana a hankali.
Yasa hannu ya goge min yace ko bakya son na tafine Fatima?
Sai na barsu mummy da sagir su tafi su kadai na zauna nai jinyanki da kaina.
Nace cikin kada kai tare da bude bakina da kyat nace no yaya Baba yafi bukatan ka
a hanlin yanzu.
Tausayin ka kawai nake jin irin yadda rayuwa yazo muna cikin wanan dan kankanin
lokaci haka komai ya jagule a lokaci daya.
Yace cikin dan murmushi tare da rugomoni zuwa jikin shi da kyau yace duk bawa
yana da tashi kalar jerabawan a kullun don haka wanan wani sabon gwajin Imanin bawa
ne yazo muna.
Ki kula da rayuwan ki don likita ta fada min kina matukar bukatan hutu sosai
saboda kalar mahaifan ki ba mai daukan wahala bace haka.
Nace insha Allahu yaya zanyi yadda kace Allah ya tsare min kai a duk inda kace
yace amin cikin dadin rai.
Yace Fatima wanan baby ya wahal da maman shi da yawa udan yafito ashe bazan yi
punished din shi ba kuwa?
Dariya nayi dama shi yake son ji gare ni kafin ya tafi nace ni har cewa nake a
cire min shi na huta wallahi.
Sai naga ya sake ni ya lame kwance saman gado yana fitar da numfashi tare da
furzo iska daga bakin shi.
Yace Fatima ko bakya son nawa ne da gaske da har kika iya furta wanan kalman haka
a gabana ?
Nace haba yaya kaima ai kasan ina son ka wahala dai ne yai min yawa wallahi yaya.
Yace to kiyi hakkuri please ki haife min shi nai maki alkawari baku kyakyawan
kulla dake da ko maynene a tare da ke insha Allahu nace naji yaya.
Kudi ya ciro masu yawa yabani yace karbi wanan ki boye a gurin ki don ban san
abinda baya zai yi ba.
Nace ni may zan saye anan wanda akace zai kwana biyu a cikin asibiti yace karbi
dai ki rike a hannun ki in case zai maki amfani.
Ya rugomayni na dan tsawo lokaci ya mike yana cewa zamu tafi nima kokari saukowa
nake daga saman gadon da nake kwance.
Ina kuma zaki tafi na dan marairaice nace ina son ganin tafiyan baba ne yaya.
Ido ya kura min kamar zaiyi magana sai kuma ya mika min hannun shi alaman nazo mu
tafi tare muka fito bayan na saka dan silifas a kafana tare da saka hijjib dina.
Tare muka fito daga dakin yana rike da hannuna nan naga kowa na gidan mu yana
gurin maza da mata manya da yara.
Idanuwan su akaina har muka karaso suna gaisawa dani bai saki hannu na ba har
lokacin muna tare muka shiga inda Baba yake kwance harkaf an shirya shi kamar ace
ya tashi ya tashi.
Har bakin gadon muka karasa yaya yadan duka daidai kan shi yace Baba ga Fatima
tazo tai maka sallama.
Yadan jawonin zuwa kusa da Baba nace Baba Allah ya tsare hanya Allah ya baka
lafiya ka dawo cikin mu lafiya.
Ikon Allah sai kawai baba ya dan bude idanuwan shi a hankali wanda sunce ya
kwana biyu bai bude idon shi ba.
Yana bin mu da kallo a hankali na kara cewa Baba Allah ya baka lafiya ka dawo ka
dauki jikan ka da hannun ka.
Sai ya dan sake murmushi a hankali wanan yasa kowa dake gurin jin dadi sosai har
likitan dake tsaye yana gyara shi yace gaskiya da za,a samu irin wanan da yake so a
tare dashi ko yaushe za,a samu improvement sosai ga lafiyan shi.
Nace muyi addua kafin a wuce nan na gyara na dinga kwararo mashi adduoin samun
lafiya ana karbawa da Ameen.
Muna tsaye aka fito dashi aka saka shi a ambulance din asibiti zuwa airport.
Sai da aka rufe motar yaya ya dawo har inda nake bai damu da,wai mutane suna
gurin ba yai hugging dina a jikin shi yana dan bubuga min baya kamar yana lalashi
na tace be strong Fatima Allah ya baku lafiya.
Ya juya ya tafi kowa sai kuka yakeyi don yadda aka fita da baba ko mutum baida
Imani sai ya tausaya mashi.
Da gata na kwato bawa daga hannun Alah da gata ya kwato Baba cikin wanan halin
rayuwan da yake ciki a wanan lokacin.
Gaba daya diyan shi yan uwanshi abokan arziki jikoki saraikai duk suna gurin
tsaye cikin tashin hankali a lokacin.
Rahama tana gurin da iyayyenta a gaban idon ta komai yafaru tana kallo.
Wani kishi ya rufe mata idon ta don ganin yadda yaya yake wani jiji dani kamar
diyar wata da wani.
Tace sai tayi magani na sai ta mayar da wanan son tsakanin mu ya koma kiyayya
watarana a cikin ranta take zancen ta.
Uwarta ma kishine ya rufe mata ido suna hanya take magana cewa jifa yadda yaron
nan yake wani jiji da yarinyar nan.
Ai don dai baki tare dashi ne idan kina gidan wane ita yar talkawan tsiya kawai.
Baban yace ai barshi da gaiyya zan daura masu aure inga yadda zai yi da ita idan
nakai mashi ita gidan shi.
Muna kallo suka fice daga asibitin suka barmu nan aka fara watsewa daya bayan
daya ana mai fatan samun lafiya.
Na kalli duk taron nan watsewa zasuyi su tafi su barni a cikin asibitin ni da
Iyya kawai .
Sai naji wasu hawaye sun zubo min Nafisa ta kama min hannu tace kada ki damu
matar yayana Allah na tare da ke.
Tare da ita muka koma dakin da nake bayan nayi sallama da mutane mama da maryam
da mijinta ne suka biyo ni zuwa dakin.
Sun dan jima a gurin mu sukace zasu tafi sai dai da safe idan sun dawo kuma insha
Allahu.
Nafisa tace ita yau a gurina zata zauna mama ta zaci wasa takeyi sai da tace
Allah maji yau a nan gurin Fatima zan kwana na debe mata kewan yayana.
Nan mama ta tafi tabarta sai dai mama bataso haka ba don tasan halin Nafisa na
watsewa.
Amma batai komai ba wallahi sai hiran da mukeyi akan matsalan baba kawai da zamu
kwanta ta hau dogon kujera iya tasa bargo a kasa ta kwanta sai safe.
Washe gari da muka tashi Nafisa bata tsaya an kawo abin karyawa ba ta wuce gida.

****** ********* ******
Sun isa Germany da baba lafiya an kuma duba lafiyan shi har ana samun sauki sosai
suna isa yaya yake kiran layina tare da tambayana karfin jikina.
Ganin an wuce da baba yasa yaya Ahmed fitowa daga maboyar shi ya na komai nashi
normal.
Sun buga suna fadawa sadauki fitowan shi yace abar case din har ya dawo don kotu
ta fadawa dan masani cewa bai da hujjan tayar da maigida a gidsn shi sai ya samu
lafiya an yi sharia.
Sadauki baya son ayi maganan kan zancen sayar da gidan nasu na gado da akayi duk
da zancen ya karade gari anji labarin abinda Ahmed yayi wa mahaifin shi.
Mama Asiya hankalinta yai matukar tashi yadda taga kowa gidan ya tsane ta ita da
danta.
Don laifin Ahmed ya shafe laifin duk wani laifin yaron dake gidan gashi Alhaji
bai ko yarda ya gaisa da ita a waya.
Ko yana waya akace ga mama zata gaida dashi zai kashe wayan yaki dauka.
Balle ga mummy kusa abin nema ya samu dama ba shiri a tsakanin ta dasu ko kadan.
Duk da baba yana asibiti cikin halin lahulai amma idan mutum ya shiga gidan zai
ga kamar hankalin su a kwance yake.
Irin yadda suke busha shan su agidan ba wani damuwa a tare dasu a lokacin.
Ga wani shakuwa da yashiga tsakani na da Nafisa yanzu don ko wani lokaci tana
gurina a asibiti muna tare.
Wani lokaci anan kawayen ta ke samun ta nan zasu wuni suna debe min kewa.
Banda matsala dasu wani lokaci idan suna hiran busha shan su a gabana nakan ce
haba anty kamata yayi ace cikin maneman ku ku cafke daya ku aura.
Nura kance ke kaunata nifa mijin ki nake so na aura nakance aiko danaji dadi anty
idan har zakiyi aure ki zauna ba sai mu zauna lafiya ba.
Kin sanni na san ki kinga ba fada a tsakanin mu sai so da kauna mu rike mijin mu
tsakani da Allah.
Nuriya wallahi idan kina wanan maganan zamu sami sabani sosai wallahi Raiha ke
fada mata haka duk lokacin da tai irin wanan magana.
Nafisa kuma takance may zaiyi da honko haka may ya rage jikin ki baya cus kin sha
burga kamar rijiyar kwakwara da ke.
Nace ba komai zamu gyara ko anty Nura ai mace mai gyara bata baci ko ?
Raiha takan sha toka tace please abar wanan zancen bata so su ko watace sukaji
mijina yana nema sai inda karfin su ya kare akai.
Tace Fatima kin muna fa wata matar aure ce zata sake jiki damu haka abinda ake
gwada muna kyama keko kin muna rikon tsakani da Allah kamar wasu yan uwan ki naji
fa kika mayar damu.
Yan uwan mu ma naji yanzun haka basu hurda damu don kaaai wanan halin da muka
tsunci kan mu a ciki.
Mutane suna manta cewa ko su Allah yana iya jarabtan su a kan haka?
Duk lokacin da ya tashi yin ikon shi a kan mutum na tabbatar da yan gulma suna
fadawa mijin ki kina hurda damu haka amma sanin koke wacece yasa bai damu ba duk
dai yana halarci ne akan yar uwar shi dake cikin mu amma duk da haka Fatima kunyi
muna wallahi.
Nan zamu wuni da su ai ta shiririta suna matukar bani tausayi ina yi ina masu
gyara.
Yau ma sunzo mun jima muna hira dasu sosai har barci ya kwashe ni na barsu da
Iyya suna hira sun sayo nama mai zafi da drinks sun baje suna ci.
Amira ne tashigo dakin da nake kwance wanda yanzu ya zama min dakina na komai.
Suna gaida ita amma,sai wani basar dasu takeyi sukaci gaba da harkan su kawai.
Bakin gadon da nake kwance ta karaso tana tayar dani daga barcin.
Iya da Raiha ke cewa haba kin san tana son hutu barta mana tai barcin ta kada ki
tayar da ita.
Tace waye zai hanani tayar da ita Rabin dan musa ko wa wai takai hannu ta tabani
na bude idanuwana.
Ina kallon ta nace anty kin shigo ne ashe tace a wulakance may wa yan nan sukeyi
a nan ne haka ta nuna su a wulakance.
Sai sha,anin su sukeyi kamar basu san da ita ba afurin ko tanayi ma ba wanda ya
kulata.
Na dan kakaro murmushi a fuskana nace anty kawayen anty Nafisa ne fa.
Tace and so what Nafisan may can kuma wai kinga bani son na kara ganin su a tare
da ke kinji na ffada maki ko?
Tace sai dai ban sani ba ko kema harkan taku dayane dasu don banza bai kai zomo
kasuwa.
Wasu hawaye suka zubo min nace haba anty cin fuska baida kyau haka wani abu
mukeyi banda mutunci da zumunci kawai.
Tai mun wani kallon wulakanci tace zaki gane wallahi Nafisa tace Amira wallahi
yadda kike da Fatima nima haka nake da ita don haka baki isa ki rabani da ita ba
don bakece kika hadamu ba.
Tace yanzu ko da yake ba mamaki tunda naga yazama dan uwanku don abin hannun shi
ai.
Tajuya tare da yi min wani kallon mamaki na wullakanci tafita daga dakin.
Tana futa tun a haraban asibitin ta kira dan uwanta cikin fada take mai batanin
karya da gaskiya.
Yace Amira badai zuwa kikayi kika tayarwa Fatima da hankali ba tana fama da kanta
ba nan tace don may zata dinga tara wa yan nan yan iskan haka tare da ita.
Yace kin san halin Fatima fa Amira bazata taba bari tayi wani abin asha ba insha
Allahu a rayuwan ta.
Kuma ai don Nafisa suke zuwa tace min nafusa ko yaushe tana gurin ta tana debe
mata kewa ke da baki son su zo may yahana ki tare a gurin su.
Lalai ma yaya dama ba yau ba nasan cewa Bintu ta gama dakai gaba daya baka son a
fadi abinda tayi don ta shanye ka.
Baiyi magana ba don ranshi yakai kololuwar baci mama ya kira yana fadin daga yau
kada Amira ta koma gurin mamatata don bata san zafin ta ba.
Don may zataje ta tayar mata da hankali bayan ta san irin yanayin da take ciki
likita yace a bata hutu.
Kai wai may ke faruwa ne haka wai nan dai ta kwashe yadda sukayi da Amira ya
fadawa mama komai.
Mama tace ji mahaukaciya kawai Nafisan da koda Fatima ke a gida tana nan like da
ita ko yaushe a dakin nan.
Ko ranan da kuka wuce fa a gurin Fatima Nafisa ta kwana tace bazata dawo gida ba
zata tsaya ta debe mata kewa.
Yace balle zaman Nafisa da fatima Allah ne ya hada su ai maji.
Mama tacs kuma tun yayatana fada har ta gaji yanzu ta daina ta saka masu ido
tsakanin su don waya sani ko hakane zai zama silan shiryuwan ta ma ?
Nan dai sukayi magana sosai ta kashe wayan tana jiran dawowan Amira gidan.
Mummy dake kusa dashi taji fadan da yakeyi tace kai Amira ma dai ita fa bazata
iya tsayawa tayi yadda ya dace ba Fatima da yanzun take son wai raba tsakanin
Nafisa da Fatiman.
Zaman Fatima da Nafisa fa yakawo sauyi sosai yanzu a rayuwan Nafisa fa don yanzu
kan zaman Fatima a gida zata iya kwana barkatai bata fita waje ba.
Aiko wanan abin sai ace abune na dubawa sosai wallahi tabar irin wanan cin fuska
haka baida kyau ga dan adam wallahi.
Baba ta najin su wanda yanzu bakin shi ya dan fara budewa yake cewa Fatima Fatima
ai alheri ce a cikin zuria ta wallahi.
Amira na shigowa gida zata fara fadawa maji mama tai cikin ta da fada sosai har
sai da ta raina kan ta a lokacin.
Ta shige tana cewa indai kan Bintu ne wallahi bazan sake saka kaina ba a
al,amarinta da yardan Allah kuwa tashige ciki abinta.

****** ********* ******
Amira na fita wasu hayen bakin ciki suka zubo mata nace yanzu ni may laifina
kuma?
Idan naki Nafisa kuma zagina za,ayi ace bani son dangin mijina balle ni Nafisa
tsakani na da ita yanzu sai hamdala kawai.
Duk da ta girmay ni amma idan nai mata magana takan daina abinda takeyi a
lokacin.
Amma may zai sa Amira tace wai kila harkan mu daya dasu bayan ta san koni wacece
takuma san halina din.
Yayan ta ma ya ganni dasu bai ce komai ba don shine ta jawota gare ni .
Allah sarki yaya sadauki mutumin kirki mutum mai adalci wanda ta san ya kamata .
Muryan su naji suna fadin sister indai don muna hurda dake zamu jawo maki matsala
zamu daina zuwa gurin ki gaskiya.
Nace akan may anty wanda ya ajeni baiyi bakin ciki da zamana da ku ba sai don
anty tazo da wani zancen ta can na daban.
Nace ba inda zaku idan dai ba maigidan da kanshi yace min bai son hurdana da ku
ba.
Wayan shi ne ya shigo a lokacin jin ina kuka yasa shi cewa Amira tazo ta bata
maki rai ko?
Yace ina Nafisa take nace mai gata nan yaya yace bata waya na mika mata wayan
nace yaya yana magana da ke anty.
Ta karbi wayan daga hannu na yan uwan suka tsura mata ido don son jin may zai
fada mata a lokacin.
Mun dai ga tana cewa ai ba komai yaya duk abinda tai min yar uwata ce ita tace ba
komai komai ya wuce ai don badon ta muke zuwa ba ai dama.
Sukai sallama ta miko min wayan ya tambayi jikina nace naji sauki ni so ma nake a
sallamay ni na koma dakina wallahi.
Yace sallama Fatima likita yace min sai kin haihu zasu sallamayki fa don bazasu
bari ki fita asibitin nan ba hakana.
Banji dadin wanan zancen ba ina cikin asibiti har tsawon wani lokaci ni wani irin
ciki ne dani haka wai ?
Gashi muna batun fara exam haka nake karatu a asibiti sai idan lokaci yayi zasi
yarda na tafi na zana koshi tare da wata nurse zamu tafi suka ce.
Yadda suka fada ko hakane haka zan shirya da safe yaya bashar yazo ya dauke mu
zuwa school dani da,wata nurse da aka dauka haya don dubani ba dama nayi wani dogon
motsi dana gama zamu juyo zuwa asibiti tare da ita a sauke mu.
Bai tafiya gida sai yaga anbani magani na kwanta zai bar asibitin har na kare
exam dina da mukayi.
Gaskiya yaya bashar mutum ne don yana bani duk wani kulawan da ya dace wanda zai
sa banji kewan mijina ba gurin kula.
Haka zai kawo min maryam mu wuni

85 / 92