Author : Zainab Idris Makawa Seenabu Category : Complete Novels
Gaba daya taji gidan ba dadi ban fito ba sai ma da naga tara da rabi na dare
kawai na kulle kofana na kwanta kawai.
Goma da rabi ya kashe kayan kallon da komai na falon ya shiga daki sai da yasa
kayan barcin shi har ya kwanta ya mike zuwa dakina ya murda a rufe kofan yake a
lokacin haka ya juya ya koma don yasan bazan bude ba.
Bai taba tsanmanin cewa akwai shakuwa haka a tsakanin mu ba kuma ba zai iya daure
rashi na ba a yanzu sai da yaga yai rabin kwana yana lalaban gefen da nake kwantawa
bai jini ba.
Nima a nawa bangaren kusan hakane na kwana da kewan shi duk da haushin shi da
nake matukar ji a lokacin.
Kowan mu da tunanen dan uwan shi ya kwana a ran shi cikin damuwa muke .
Tun da safe ina kitchen ina hada abinci yazo bakin kitchen din nai matukar mamaki
da bai fita motsa jikin shi ba yau.
Kamar ban san yana gurin ba na share shi ya tako har zuwa cikin kitchen din inda
nake tsaye ina motsa dankalin dake saman gas.
Ganin da yayi bazan mai magana ba yasa shi cewa kin tashi lafiya ?
Nabashi amsa da lafiya kawai.
May yasa kike rufe min kofan ki kwanan newai Fatima ?
Dagowa nayi muka hada ido kawai sai na kawar da kaina naci gaba da abinda nake yi
ina tunanen watau bai masan abinda yayi ba ke nan koko tsaban rainin wayyo ne hakan
?
Ke nake tambaya ya maimata min .
Kaina na girgiza mai nace ina kwashe dankalina a tunkuya a hankali.
Nace ban da amfanin komai a gare ka don shaye shayen ka yafini daraja a gare ka
nagani.
Don haka kaje kayi abinka kabarni na yarda na zama ma yar aiki kawai a gida don
shine ya dace dani.
Murmushi yayi ganin zan wuce ya dan ja dabaya ya bani hanya yana fadin wanan kuma
maganar kice amma ni shana baida alaka da kusantar ki a gare ni.
A ganin ka ba amma ni bazan taba mu,amula da mutumin dake a cikin sabon Allah
insha Allahu.
Ido ya zuba min don jin abinda nace ya fahinci a shirye nake na zuba mai bakaken
maganganun dake a bakina a lokacin.
Shiru yayi ya dan dade tsaye a gurin yana kallon yadda nake aikina a cikin tsabta
da gwanewa sai ya juya kawai yabar kitchen din zuwa falo ya zauna cikin damuwa.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
IDAN BAKI BIYA BA KADA KI KARANTA HAKKIN WASU PLEASE,,,,
A LOKACIN MU KE ,,,,,
Ba karamin jiki umma taji ba sanadin kafan nan ta abu ga mai babban jiki irin ta.
Duk halin da take ciki bai hanata makirci ba daga zaune take kulla sheri kulun.
Ranan mama Asiya tazo tanawa Umma gulma wai taga maji da wani sabon waya tana
ganin Sadauki yazo mata dashiba cikin tsaraba.
Umma tace shine mu bai bamu ba ya mayar damu mutanen kawai ko indai waya ce kowa
ma na iya saye ai.
Asiya tace wallahi kona sa sace wayan ma gaba daya mu batar dashi kowa ya huta.
A dole ita yanzu ga mai da mai hali komai sai dai mu ganshi gareta ina haka ma
wallahi bai yuyuwa ko alama.
But Nafisa dake daki tana shirin ta tana sauraren su tafito tace kaikayi dai koma
kan mashekiya.
Kullun ku ke nan cikin kullawa matan nan sheri ita da diyan ta Allah na kareta ya
na komawa kan diyan ku amma baku fasawa ku daina.
Don haka yau wallahi sai na fadawa maji wanan sherin da kuke kulla mata don ta
kama wayan ta.
Yaya sadauki ya nuna min so da kauna wanda duk duniya yanzun ban da kaman shi don
ni ko bai min komai ba ya bani so da kauna na yan uwan taka da ba wani dan uwa da
ya taba bani shi.
In kin yi haukan e da gaske yau ina son ki gwada min kije ki fadawa Hauwau din ga
abin da muka ce mata.
Murmushi tayi ta koma dakin ta kawai taci gaba da shirin ta har sai da ta gama
tsab tafito tace to ni zan fita.
Ba dama Umma ta hanata ta ci mata mutunci tunda baba ba gida yake zama ba shi don
shi gar yanzu tana dan tsoron shi.
Tana fita ta samu mummy da mama a tsaye suna magana kan wani makwacin su da baida
lafiya suna son zuwa gaida shi.
Nafisa na fito mummy ta bita da ido caaa maji na kallon ta saudaya ta kawar da
kan ta tana fadin a zuciyar ta Allah ya shirya kayan shi.
Maji sai ki kama wayan ki don gasu can ciki daki suna kulla yadda zasu raba ki
dashi kowa ya rasa.
Don kin san su kullun cikin kulla sheri suke basu bari ki kama kayan ki don tun
da suka ce sai sun dauke shi sai sun daka din don ba yau suka fara sheri ba.
Daga haka ta juya,ta,wuce abinta, mamaki ne ya kama su maji da mummy suka shiga
magana kan Nafisa.
Mommy ne tace aiko tunda kika ji sun fadi haka wa yan nan macutan su na da niyar
yin hakan don haka sai kiyi taka tsatsan da kayan ki ba waya ba komai manaki sai ki
dinga hankali dashi don wa yan nan mutanen basu da imani ko kadan.
Bai wa mummy ba da baba ya dawo sai dai ta fada mai abinda Nafisa ta fada ma su.
Ran Baba yai matukar baci ya mike sai dakin Umma don a zaune take kafan ta har
yanzu ba lafiya.
Yana daga labule suna zaune tare da mama daga kofan ya tsaya yake cewa to muna
fukan Allah .
Duk wanan isharan da Allah ke nuna maku bai maku ba sai kunci gaba da kulla
makirci don baku da imani.
Shege ya fasa sace wayan maijidda a gidan nan daga ku har muna fulan diyan ku da
kuka lalata da mugun abu.
Yau gashi abin kuya ke Atika yar cikin ki da Allah ya mayar haka tazo tana tona
maki asiri akan sherin ku.
A na dai kallon Nafisa haka amma ke Atika kece silar mayar da rayuwan, Nafisa
haka kuma har gobe dake nake kuka a gidan nan.
Ku biyun kune silar duk wani balain da yarana suke ciki gaba dayan su don duk da
hannun ku ga lalacewan su.
Allah ya isar min akan da duk wani da nawa da kuka lalata min a gidan nan kada
kuce ban san duk wani sherin da kuke kullawa bane.
Wallahi nasan komai na dai barku ga Allah ne kawai ya fitar min da hakkina a kan
ku.
Daga haka ya juta rai a bace yana fadin Allah ya isa tsakani na daku.
Tunda baba yafara magana jugun sukayi duk kunya da bakin ciki mamaki ya baibaye
su sosai.
Yana ficewa mama Asiya tace yanzu yaya ashe saida ja,iran yarinyar nan ta fada
masu zancen nan.
Amma ko nafisa takai la,ananna wallahi kidaina zaginta haka kada aji tsakanin mu
idan la,anewan yafi haka kuma a kanta yaya kike son nagan ta ne.
Duk fa kece kika jawo muna wanan tsinuwar haka wallahi ina zaune zamana kika
shigo min da wanan tsurkun kinga sabon waya hannun Hawau,
Ni yaya ina nasan wanan mai bakin tsiyan tana dakin bata fita aida ba zan soma
maganan komai ba wallahi tun ita ta zama abinda ta zama.
Umma tace sun dai zama gidan nan waye baida abin fadi tab a tsuliyan shi sai dai
na wani yafi na wani kawai.
Anan dai sukai ta yaba wa junan su bakar magana dama a haka hitan nasu ke kare a
karshe kuma a dawo a samu sun shirya kafin wani dan lokaci.
****** ********* ******
Yana dai zaune Abuja ne amma kwata kwata hankalin shi yana a kan yar matan shi da
yanzu yake jin ta ta zama mai wani rabin rayuwan shi.
Wata rana yankayi matukar mamakin kan shi don bai san lokacin da har son Fatima
yai mashi illa ba haka a rayuwan shi.
Murmushi yayi ya mike daga kwancen da yake tare da dan murmusawa tunanen yake
yadda har yanzu kunyan shi bai fita a idon Fatima ba.
Ya kamata ya san yadda ya fitar mata da wanan kunyan nata hakana lokaci yayi da
ya kamata yai wani abu akan ta don kawar da kunyan dake idon ta dakuma sauran
yarintan dake cin ta hakana.
Yana son mace wace ta san kan ta tasan hanyar da zatabi ta gyara mashi shimfidar
shi.
Fatima zata zata iya zata iya mana, kwai dai wanan bakin kunyan nata ne ke hanata
aiwatar mashi da yadda yake so da ita amma yanzun kan dole ne ya san yadda zai
batar da kunyan nan nata.
Ta dawo daidai irin yadda yake son macen auren shi ta kasan ce mai a rayuwan shi
komai normal.
Yana zaune sai faman tunanen al,amarin Fatima ya keyi yaji anyi nocking din
kofan shi kafin ya amsa sallaman shi yaji an turo kofan dakin don dama a bude take.
Linda ce tashigo dakin abinda yasa shi saurin tashi zaune ke nan a lokaci guda.
Da sauri ya mike zaune da kyau cikin dan kaduwa don baiyi expecting din zuwan ta
saboda sun dade basu hadu ba da shi, tun lokacin da ya sasanta da Fatiman shi yaji
gaba daya linda tafita mashi a rai.
Linda may yakawo ki gurina again bayan na fada maki abinda nake bukatan kiyi
kince bazaki iya ba.
Ta watso mashi wani mugun kallo na see you tace to maye don anzo gurin ka saboda
wanan karamar yarinyar daka aura ne da batafi sixth ba.
Yace don't dear insult my wife she is part of my life now.
Ganin da gaske yake nufin maganan shi har cikin ran shi irin yadda taga ya hade
rai a lokaci guda haka don tasan halin shi sarai gurin rashin mutunci idan ya tashi
yi.
Ta dan marairai ce tace haba my man kada ka mance da alkawrin dake tsakani na da
kai mana please.
Yace kema kin manta da alkawarin da nayi cewa idan ba zaki musulunta ba ba zan
iya auren ki a haka ba.
Rashin yardan ki yasa har iyayyena sukai min zabin mace da kan su wanda yakai
yanzu na gane cewa gata sukai min da hakan.
Don haka tunda kin zabi son iyayyen ki a kaina nima yanzu na zabi zabin iyayyena
akan ko wace mace.
Don haka ki tashi kifice min a gida i don't want to see you again, dont ever
think about me again its over now.
Linda tace my man ni kake fadawa haka akan wanan little girl dinka wai wife kake
nufin kayi komay.
Ka sanni ni na wuce ka wullakantani akan wanan yarinyar don kasan asalina ka kuma
san waye ubana a kasan ghana.
Amma tunda kace haka jeka zaka gane kuren ka zaka gane ni Linda ba abin
wullakantawa bace a take lafiya.
Ya ja dogon tsaki tare da nuna mata hanya yace babu abinda zangani sai alheri
tunda bake ce Allah ba banza dake kawai.
Kije ki rike addinin ki da iyayyen ki nima na rike nawa koba shike nan ba.
Tsayawa tayi na dan lokaci tana kallon shi babu abinda zata iya don tasan ba
saurarenta zai yi ba ma yadda yayi.
Ta juya kawai tafice kamar yadda ya umurce ta da yi ran ta a bace tabar dakin
nashi.
Komawa yayi ya kwanta ranshi a bace da Linda duk da yasan tana matukar son shi
amma ya zama dole yanzu ya kawo iyaka a tsakanin su kawai don Fatiman shi tariga da
tai masu zara ko ta ko ina.
Ya sake wani dogon tsuki kawai tazo ta bata mashi jin dadin shi da yake ciki a
lokaci guda na Fatiman shi.
****** ********* ******
Nai wankan tsarki a yau don haka na baro school da wuri don ina son a wanke min
kaina a gayara min shi.
Shagon da muke zuwa da maryam gyaran kai na nufa daga gyaran kai har na jiki sai
da matar tai min shi ban dawo gida ba sai yamma lis na shigo gidan.
Ina farka motana sai ga mai wankin mu Atiku yazo inda nake tsaye ina kokarin rufe
motar ke nan yake cewa.
Hajiya barka da dawowa, sannu da zuwa dama tun dazun nake jiran dawowan ki.
Na juyo nace a,a baba baka tafi gida bane yau yace wallahi hjy ban tafi ba na dan
tsaya don naga dawowanki ne don wallahi ina da bukatane.
Shine nace bari na kawo maki koke na ko zaki taimaka min ki bani koda dubu goma
ne idan anyi biya saina mayar maki ko kuma a cire daga cikin albashi na wanda dai
yafi sauki daga ciki.
Wallahi matata ce amarya na ba lafiya don tana fama da laulayin ciki ina son ta
tafi asibiti dana kuma Aliyu ya gama makaranta zai shiga secondry gashi har an fara
karatu amma shi yana gida a zaune.
Tausayi mutumin yabani don gaskiya gaba dayan su yan aikin gidan suna da matukar
mutunci sosai.
Nace mai ya bari na zo ita kuma mara lafiyan Allah ya bata lafiya mai karatu kuma
Allah yabada sa,a sai na shiga.
Kudin da yaya yake bani ne bani kashewa na dauko dubu ashirin daga ciki nafito
dashi.
Nabashi goma naba maigadin dare dana rana dubu biyar biyar su raba.
Atiku yace hjy nagode insha Allahu da anyi biya zan dawo maki da kudin ki da
yardan Allah.
Nace haba Baba ka barshi na bakane kawai kaje kayi amfani dasu idan zai ishe ka.
Da sauri ya juyo yana cewa hjy kin bani wanan kudin haka dukka ?
Ikon Allah sai naga yakai tsugune tafara fadin Hjy nagode nagode yadda kika rufa
min asiri Allah ya rufa maki duniya da lahira.
Allah yabaku zuria masu albarka a rayuwan ku, Allah ubangiji ya tare ku daga
sherin makiya nagida dana waje.
Nace amin baba nagode da adduan ka baba sai ga sauran sun karaso suna min godiya
da addua su ma.
Nagode masu na shige ciki don duk nagaji a lokacin wanka nake son yi nai sallah
kawai sai na nemi abinda zanci a raina.
Ina shiga malam musa yace Atiku kaga ikon Allah ko yau inane baka shiga ba a
garin nan dan neman rance amma baka samu ba.
Yanzu kaga ikon Allah ko yar arziki irin albarka nikan ai gobe gidana cefane
lafiya na lau insha Allah.
Kai mutane mutane magindanta suna cikin wani hali yanzu na bukata saboda
motsalolin rayuwa da yaiwa mutane yawa a wanan lokacin da muke ciki.
Duk yadda kake ganin kanka a cikin matsi wani nacan yafika don haka ko yayane ko
ba yawa ka taimaka wa na kasa dakai don ita addua ba,a san inda take kamawa ga bawa
ba.
Da wanan irin tunanen na shiga wanka nafito sai na jini wasa ina idar da,sallah
naji abinci kawai nake bukatan ci a lokacin.
Don haka na fito na nufi kitchen don agazawa cikina dake dan kugin yunwa a
lokacin gani ni kadai a cikin gida kamar mayya dani.
Hakan yafi min da zama cikin tashin hankali da anty Amira ke zuwa yi min wai da
sunan zama.
Indomie na dafa na dan cika mai attardu nan da nan ya dafu na zauna naci nasha
ruwa na kawar da kayan danaci abincin.
Kofa na rufe don karfe takwas na dare nasan babu wanda zai zo kuma gidan a
lokacin.
Dakina na koma bayan na kashe duk wani kayan wutan dake falon, wanda shigana
yai daidai da rurin da wayana ya soma a lokacin.
****** ********* ******
Yaya sadauki ne a layin da murmushi a fuskana na dauki wayan nace Assalamu
Alaikum.
May ye hakane sai yace min babu ko dan irin honey, darling, sweet heart din nan
sai ki wani ce min wai assalamu alaikum kawai ?
Nace haba yayana ni wani suna kuma kake so na canza ma,bayan wanda Allah ya dora
maka a kaina na yayana.
Yace No ban yarda,ba gaskiya ni suna nake son kawai a canza min nagaji da yaya
din nan kamar wani mai yaye miya yabar tuwo gaya can dani.
Ban san lokacin da maganan tashi tabani dariya ba nace kai haba yaya baka son
girman ke nan kuma ko?
Yace kin daiji na fada maki ni dai ban son wanan sunan yayana din don haka yanzu
basai gobe ba sai naji sunan da aka rada min din.
Shiru nayi ina tunanen ni yanzu wani suna kuma zan kirashi dashi indai ba son
matsawa rai ba.
Ke fa nake saurare Fatima na nisa nace to yaya love yace daya nace my life ko?
Sai naji yai murmyshi yace to ke fa amna kamar wata tsohuwa can wai kullun yaya
yadan make muryan shi yana,kwakwayona yadda nake kiran shi da sunan yaya.
Nace kai yaya nidai wallahi kana son ace min banda kuya daine wallahi amma idan
akaji na canza maka suna ai za,a kalleni wata mara kunya can ne.
Yace da sauri mutane mutane su zasu hana ki dadada min zuciya ko kuwa ?
Shiru nayi yace abar wanan zancen yaya bakon ki yatafine ko yana nan ?
Da,mamaki na tambaye ina fadi bako kuma yaya ?
Waye yaya ko da wani kike magana,ne acan kusa dake ?
Nai sauri na tuna ina cewa wai yaya love wani bako kake magana ne wai ?
Wanda ya hanani farincikina da aka saba min mana, duk hakan bai sa na kawo tunane
na akan period yake maganan shi.
Murmushi na dan yi a hankali nake cewa yananan har yanzu bai tafi ba da karfi
yace what kina nufin har yanzun mesestration kikeyi nace eh yaya.
Shiru na dan tsawon lokaci baiyi magana ba sai can yace ok kina lafiya dai